PAGE 10
Miƙewa yayi daga gaban Ummi ba tare ya sake cewa komai ba ya bi bayan Fatima, bata falo dama baiyi tsammanin ganinta a nan ba, bed room ya nufa kai tsaye , a kwance ya same ta kan gado tana ta risgan kuka , jin motsin shigowar mutum yasa tayi sauri ta juya baya ta fuskanci bango, yadda mai shigowan bazai iya ganin fuskarta ba ta yi tsit! kamar mai bacci. Daga bakin ƙofar ɗakin ya tsaya ya rungume hannayen shi a ƙirji yana ƙare mata kallo yana jin wani rauni na son ziyartar zuciyar shi, dakewa yayi ya ce "Fatima kuka kike yi???" Da sauri ta girgiza kai, wasu sabbin hawaye na sake wanke mata fuska. Ajiyar zuciya ya sauke ya cigaba da cewa "Kiyi haƙuri Fatima idan hukunci na yayi tsauri da yawa a gareki, amma ki sani bazan iya jurar ganin ana wulakanta ki ba, ya zama dole ki yanke alaƙa tsakanin ki da yarinyar nan tunda iyayen ta itama basa so, bamu da ƙarfin ja da su ta kowanne fanni, shiyasa na yanke hukuncin canja miki makaranta, duk da nasan zakiji babu daɗi, kiyi haƙuri ni mai kare martabarki ne a koda yaushe." yana gama faɗin haka ya juya ya fice don bazai iya jurar ci gaba da ganin kukanta ba.
Ummi na zaune yazo ya wuceta yayi haryar ɗakin shi, kiran sunan shi tayi ya juyo ta ce "ka zo ka dauki kununka ka tafi da shi gaba ɗaya." dawowa yayi ya ɗauka ya wuce . ajiye kunun yayi ba tare da sha ba ya zuba tagumi ya faɗa komar tunani, sosai yayi nazari akan huƙuncin shi bai ga wani cutuwa a ciki ba, kuma hankalin shi ya kwanta da hakan ɗari bisa ɗari, dama shi bai taɓa kaunar alakar su ba , saboda Ummi kawai yake danne zuciyar shi. Sai dai zai iya kokatin shi wajen ganin ya duke mata duk wata damuwa bazai barta ta shi ga damuwa a dalilin hakan ba alkawari ya daukarwa kansa.
*******
Tunda Joy ta shi ga class idanunta na kan kofa, jira kawai take yi taga b'ullowar Fatima amma shiru, har malamin da ke daukar su first period ya shigo, sai lokacin ta ji haushin kanta na k'in biya mata su taho tare da tayi, duk da ta gwada yin hakan sai dai kunyar Yaya Ameen da Ummi bazai barta ta iya zuwa gidan ba, da wani ido zata kalle su, har gara Ummi akan Yaya Ameen da dama can ya lafiyar kura. Sanin da tayi mata gwanar latti ce yasa bata d'aga hankalinta sosai ba, sai dai ganin malamin yaci double period dinsa ya fice wani ya shigo ta tabbatar Fatima bata zo school yau ba, kasa kwanciya hankalin ta yayi gaba d'aya ta daina fahimtar darasin da suke yi, me ya hana Fatima zuwa school?, ta jefawa kanta tambaya. Kar dai ace bata da lafiya, kar dai ace sanadin abin da Mom ta mata wani matsala ya same ta, take taji zazzabi na shirin saukar mata, ta riga ta yi amannna cewar haka ne, gaba daya ranar rasa kanta aka yi a class karshe kwanciya tayi akan desk har akayi closing, da kudirin zuwa gidan su Fatima ta fito daga cikin school, dan ta san zuwa yanzu Yaya Ameen baya gida, sai dai tana fito wa ta tarar Mom ce yau da kanta tazo d'aukarta, babu yadda ta Iya haka ta kirkiro murmushi yak'e ta sakar mata, tare da bude motar ta shi ga suka tafi gida.
Ranar haka ta wuni a kwance kamar ruwa duk bata cikin walwala, sai dai bata bari iyayenta sun fahimci halin da take ciki ba gudun daga musu hankali, da tsoron kar si fahimci ta samu da Fatima su kara karfafa mata tsaro da sanya mata ido.
*******
Fatima kam kuka tayi sosai har sai da kanta ya fara ciwo, tana jin sandaYayanta ya yi sallama da Ummi ya fi ce daga gidan, bayan tafiyar sa Ummi ta kwala mata kira, murya a dashe ta amsa, tare da mikewa ta kwabe kayan makarntar ta canza na gida sanan ta fito, ta ce "Ummi gani." Kallonta Ummi ta yi ta ce "Kuka kikeyi Fatima akan hukuncin da yayanki ga yanke akanki," da sauri ta girgiza kai, ta ce "Ummi ba hukuncinsa na ke wa kuka ba," "to me kikewa kuka." Narai narai tayi da ido ba tare da ta iya ba Ummi amsa ba, ganin haka Ummi tasan bata da ta cewa , don haka ta Dora da cewa "Ni dai har kullum ina kara umartan ki,ki zama mai biyyayya a gare shi domin shine jagoran rayuwar ki ko bayan raina." Gyada kai ta yi, Ummi ta ce "Tunda kina gida yau ina so zan dan fita unguwa bazan dade ba zan dawo kiyi girkin rana akwai tsakin shinkafa kiyi dambu ki tsinki zogale a ice ki ki gyara." Sake gyada kai tayi. Ummi bata bi ta kanta ta mike ta shige daki ta shirya cikin shigarta na mutunci ta fice daga gidan, ta bar Fatima cike da tunanin Inda take yawan zuwa a y'an kwanakin nan.
Bayan tafiyar Ummi zama tayi ta rafka tagumu tana saka da warwara, tayi nisa cikin tunani, ta ji an gaba ta firgigit ta yi ta dago, da Amira ta yi ido biyu, murmushin yak'e ta kirkiro ta sakar mata, Amira dake tsaye a kanta tana mamakin irin zurfin da tayi a tunani ta ce " Fatima tunanin me kike yi haka, tun dazu Ina ta sallama baki ji ba." Bata amsa tambayarta ba sai cewa ta yi " Anty Amira Ina kwana." Amira ta ce "lafiya kalau baki je school ba ne yau?" Ta ce "Eh bana jin dadi ne." "Allah sarki Allah ya sauwake, ai ga idanunki nan ma sun nuna." Murmushi kawai Fatima ta yi, Amira ta sa ke cewa "Ummi na ciki ne?" Fatima ta amsa da "A'a ta fita." Kasa kasa Amira ta yi da murya cikin rad'a ta ce "Yaya Al'ameen fa?" Kallon ta Fatima ta yi, cike da mamakin yin rad'ar tata ta amsa mata da s "Shima ya tafi school." Ajiyar zuciya Amira ta sauke wanda ya tilastawa Fatima sake kallonta, ganin tana kallonta yasa ta sakar mata Murmushi ta ce "Dauko tsintsiya na taya ki sharar gidan tun da baki jin dadi." Cike da mamaki Fatima ta ce "A'a Anty Amira ki barshi zan yi." Harara ta watsa mata, tare da wuceta ga mamakin Fatima ta ga Amira ta nufi wani dan lungu da suke ajiye kayayyaki irin su tsintsiya da sauran tarkace ta dauko tsintsiya da faka, ba tare da ta jira an nuna mata in da suke ba, da alamar ta Dade da Sanin ma'ajiyar su, ta ke ta shi ga sharar ta hankalin kwance, Fatima mikewa tayi ta koma falo ta bata fili, zuciyar ta cike da mamaki.
Tas Amira ta share gidan ta jawo ruwa a rijiya ta cika drum, falo ta dawo ta samu Fatima kwance nan ta zauna ta shi ga jan ta da hira wanda duk rabin hirar akan Yayanta ne, duk da Fatima bata cikin yanayin mai dadi, ta sake da Amira sosai suka yi hiran Al'ameen wanda gaba daya Amira ce ta karkata akalar hirar cen, sai da ta taya ta hura wuta kafin ta mata sallama ta fi ce, ta ce idan Ummi ta dawo ta gaisar mata da ita.
Sai bayan azahar Ummi ta dawo zuwa lokacin fatima tayi girkin ta kwashe , sai dai ko kadan ta kasa dandanawa, a kwance Ummi ta sameta a daki, sannu da zuwa tayi mata, ta kawo mata abinci ta koma ta kwanta, Ummi bata takura mata ba sanin tana bukatar space, sai ma janta da ta ringa yi a jiki tana mata hirarraki , hakan kuwa ya taimaka sosai wajen rage mata damuwa da tunani makomar kaancenta da Joy.
Ranar Al'ameen bai dawo ba sai dare, daga school da ya tashi, gidan daya ke daukar keke ya nufa, ya dauki keke ranar wuni yayi yana aiki sai bayan isha'i ya maida keken daga nan kuma kai tsaye ya nufo gida bayan ya tsaya ya sai ma Fatima Apple sanin yadda take matukar son shi.
Suna zaune tsakar gida bayan sun idar da sallar isha'i, suna dan ta6a hira yayi sallama, a tare suka amsa masa, Fatima ta mik'e kamar yadda ta saba kullum ta kar6i ledan hannun shi, fuskarta ya kalla ganin bata cikin walwala kamar yadda ya saba ganinta kullum ya ji babu dadi, a ran shi , duk da tayi kokarin boye hakan ta hanyar sakar mishi Murmushi kafin daga bisani ta ce "sannu da dawowa Yaya." Murmushi ya yi mata shima ya ce "yawwa yar gidan Yaya Ameen." Sunan da yake kiranta idan yana cikin nishadi, dawowa tayi ta zauna ya biyo bayanta ya zuba a tabarma ya gaida Ummi, cike da kulawa ta amsa shi tana mishi ya gajiya, ta kalli Fatima ta ce " Binta daukowa yayanki abincin shi a kitchen." Da sauri ya ce "A'a Ummi bari na watsa ruwa tukunna." Ya karashe maganar yana mikewa, ya nufi hanyar wajen drum don ya dibi ruwan wankan , da sauri Fatima ta riga shi isa ta dauki boket ta zuba mishi ruwan , kallonta yayi da Murmushi a fuskar shi ya ce "Nagode kanwata." Daki ya koma ya rage kaya hadi da dauko kwandon soson shi da sabulu, har zai shige toilets din ya tuna dagargadin likita akan wankan shi da ruwan sanyi saboda larurar shi, dakatawa ya yi ya ce "Ummi a kwai ruwan dumi ne?" Ta ce eh akwai a flas, kafin ma a umurceta ta mike ta dauko mashi flas din ya juye ruwan ya shige.
20 minute kacal ya kwashe ya fito sanye da jallabiya, dakin shi ya nufa ya shirya cikin kana nan kaya ya dawo, abincin shi Fatima ta dauko mai, ya kalleta ya ce "zauna muci tare." Ummi ta ce "yawwa kamar kasan yau ta ki cin abinci kwata kwata dama jira name ka dawo ba gaya maka." 6ata rai yayi ya ce "me yasa Fatima." Tayi narai narai da idanu, babu alamar wasa a sautinsa ya ce "oya let it." Ba musu ta dauko cokali ta saka suna ci, ganin tana wasa yasa ya Shiga bata da kanshi a baki, hakan ba sabon abu bane a wajensu dama, sai da ya tabbatar ta koshi sannan ya dauko Apple dinta ya bata, nan ta ke ta shi ga fara'a tana godiya, ya ji dadin gani yadda ya sake take farin ciki,nan ta wanko ta ba ummi daya ta dauki biyu, tana ci yana janta da hira, labarai masu ban dariya har da su tasuniyar gizo, Ummi ma ta biye musu tana saka musu baki, kan kace koba Fatima ta wartsake duk wani damuwa dake damunta ya kama gabanshi, sai lokacin take tunawa da batun Amira, kallon Ummi tayi tana gatsar Apple ta ce "dazu Anty Amira ta shigo." Ga mamakinta gani tayi Ummi ta washe baki ta ce "Allah sarki Amira yarinyar kirki, kai yarinyar nan tana da hankali wallahi, na Dade banga budurwa mai natsuwa da hankalin ta ba." Fatima ta ce "Hmmm Ummi ita fa ta share gidan nan ta cika drum da ruwa, ta zauna ta tayani hira sosai, Ummi dama ta saba zuwa ne." Ummi ta ce " ta kan shigo jefi jefi cikin kwanakin nan idan kuna makaranta da yake ita suna hutu kafin su fara zana waec, tana shigowa idan babu kowa a gidan su ta kama mini aiyuka ta tayani hira har wankin kayana tana yi min, kuma ko na ce ta bari bata bari, yarinyar ba dai hankali ba. Haka Ummi ta yi ta yabon Amira Al'ameen na jin su, bai dai tanka ba,sai gurin sha daya sauran suka ta shi.
Pls comment yan Amana, comment dinku shine karfin gwiwana wollah, idan kina comment zaku ringa samun update a kai a kai😬 [12/29, 2:34 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀