PAGE 15
Dr S Alto ya sauke ajiyar zuciya cikin sanyin murya ya ce "Bai gaya mani komai game da ahlin shi ba, still yau ma ce min yayi shi maraya ne kamar yadda ya saba fada, game da matakin ciwon shi kuwa, yanzu abin ya kai mataki na hudu a gaskiya yana cikin hatsari ." Barrister Hayat cikin sanyin jiki ya ce "Aboki lokaci yayi da zan dawo 9ja koda kuwa ban gama cike wa'adina a nan ba, ya zama dole na san ko wanene shi, jikina yana bani cewa mafarkina yana gaf da tabbata." Dr S Alto ya ce "Aboki ban katsi hanzarin ka ba, sai dai ina mai kara baka hakuri, kayi hakuri ka zauna ka kammala aikin da ya kaika, kar muyi biyu babu." A dan harzuke Barrister Hayat ya ce "me kake so ka gaya min, wani irin biyu babu, kafin kowa sani na Abdul idan da wanda zai karfafa min gwiwa akan lamarin nan baren ka ne, amma sai naga kamar baka dauki lamarin da muhimmanci ba." Dr ya ce "Ba haka bane Hayat, so nake mubi komai a hankali, ka tuna fa har yanzu, tsammani kawai muke bamu da tabbaci, kuma har yanzu idanunsu ba wai ya dauke akan ka bane, kana dawowa Nigeria ba tare da wa'adin ka ya cika ba, zasu saka maka ayar tambaya duk wani motsin ka zai kasance a kan idanun su, kayi hakuri ka zauna nayi maka alkawari kafin nan da shekaru biyun da suka rage maka ka dawo kasarka zan tabbatar na gama duk wani bincike daya kamata." Ajiyar zuciya B Hayat ya sauke, a sanyaye ya ce "Na yarda da kai Aboki, a duniya bayan y'an uwana bani da wanda ya fi ka, na san zaka iya, na damka maka amanar rayuwata ka kulamin da ita." Dr ya ce "in sha Allah na maka alkwari bazan baka kunya ba." Daga haka ba su yi wani hira ba, suka yi sallama zuciyoyin kowannen su a jagule musamman Barrister Hayat wanda maganar ta yi mishi fami a zuciya.
***********
*JOY*
Zaune ta ke a kyayataccen garden din gidan su, yammaci ne mai cike da ni'ima kasancewar garin yau kwata kwata basu ga kyallin rana ba saboda ruwan da aka kwana ana tsugawa daren jiya kamar da bakin kwarya. Books ne a gabanta da yawa, ta kwaso domin tayi karatu saboda gabatowar lokacin fara mid term test wanda ya kasance na third term ne, wato na canza aji, d'aya daga cikin books din na rike a hannunta tana dubawa, a zahiri idan ka ganta zaka dauka a gaske karatun takeyi amma a badini kwata kwata hankalinta baya kan karatun, tunani ne fal zuciyar ta, kallo daya zaka fahimci bata cikin walwala ko kad'an, yau kimanin kwana biyar kenan data aikawa Fatima letter, amma har satin ya kare bata je school ba, gashi on Monday zasu fara mid term test, bata yi aune ba sai kawai ta ji hawaye na zuba daga idanunta yana diga kan book din da take kallo, Ta na matuk'ar kewar Fatima ji take kamar ta yi tsuntsuwa ta ganta a gidan su, ta ke ta shiga tunano yadda suke gudanar da rayuwarsu a baya, yadda suke nunawa juna tsatanin kauna da kulawa babu kyamata kyashi ko hassada tsakanin su da juna soyayya ce gangariya daga indallahi' ta tuna ranar data fara haduwa da Fatima, farkon shigowar su SS1, wata rana suna zaune a class aka kawo musu new comer Fatima Husain, kallo daya suka yi wa juna a tare suna sakarwa juna murmushi kamar dama sun san juna, lokacin da class Master su yaba Fatima umarnin ta je ta samu sit ta zauna direct ta nufo kujerarta duk da cewa ga sauran empty sit nan a class din da yawa kuma ga musulmai nan yan'uwa ta a ajin, babu musu ko gaddama ta matsa mata ta zauna, ranar ko kalmar A bata shiga tsakanin su ba, sai satar kallon juna da suke yi kamar wasu munafukai, idan suka had'a idanu su sakar wa juna murmushi, tun daga ranar farko da suka fara haduwa zuciyoyin su ya sark'e da soyayyar juna, sun kai kusan kwana uku a haka kullum idan Fatima ta zo sit d'inta ta ke zama suyi ta kallo juna, maganar farko data fara shiga tskanin su a rana ta hud'u maths teacher ya shigo ya yi musu lesson bayan sun gama ya bada class work kowaccensu ta dauko notebook d'inta ta fara solving, Fatima ta gama nata kamar yadda suka saba satar kallon juna ta juya ta saci kallon na Joy, zaro ido tayi ganin yadda ta yi solving wrongly, sai dai ta rasa yadda zata gaya mata, ta zauna tana ta sak'e sak'e , har lokacin data mik'e zata je tayi submit, har ta fita daga sit d'in ta ji an riko hannunta, juyowa tayi suka kalli juna cikin ido, cikin inda inda Fatima ta ce "please can I see ur calculation." "Why not." Ta amsa mata da murmushi tare da mik'a mata, bata ce mata komai ba ta shiga gyara mata inda ta yi kuskuren tana gamawa ba tare da ta kalleta ba ta mik'a mata tare da cewa "ki yi hakuri da shisshigina." Sai lokacin ta kula da kuskuren data tafka, murmushi tayi tare da ce mata "Thanks" Itama ta sakar murmushi ba tare da ta amsa ba. Tuna wannan yasa Joy sakin murmushi ba tare da ta san tana yi ba, still ga hawaye a idanunta, Hannu ta saka a aljihun wandonta ta zaro letter n nan na Al'ameen, daya zame mata kamar wani gold duk inda zata je yana tare da ita da shi take kwana rungume a jikinta duk daren duniya, ta warware pepan tana kallo, sai dai har yau bata sauya zani ba a duk sanda zata daura idanu a jikin rubutun gabanta sai ya fad'i, ba tare da tasan dalilin hakan ba, tana kallo tana ci gaba da hawaye ta ce a bayyane "I missed u a lot my Teetee." ba ta san isowar Mom ba sai jin muryar ta tayi akanta, ta na ce wa "Joy what's wrong wit U? me ya same ki, kukan me kike yi." Da sauri ta shiga goge hawayenta at same time tana kokarin boye letter n cikin inda-inda ta ce "Nothing Mom, abune ya fad'a min a idanu." Mom da ta gama karantar rashin gaskiya k'arara a fuskarta ta shammaceta ta fusge letter n, a bayyane ta karanta abinda ke ciki "THANK YOU." A razane ta kalli Joy data zaro manyan idanunta cike da fargaba ta watsa mata, k'ank'ance ido Mom tayi cike da tashin hankali ta ce "Menene wannan Joy?" Ta ce "Babu komai Mom." Mom ta ce " Wannan letter daga ina." Cikin inda-inda ta ce "Ya dade sosai Mom a cikin textbook dina, yanzu dana dauko su ina dubawa shine na gani." Mom ta ce "To naji wannan kukan kuma na menene shi?" Ta ce "Ba kuka na ke yi ba Mom abune ya fada min a ido." Ko kadan Mom bata yarda da batun ta ba, hakan yasa ba tare da wani dogon nazari ba ta daga letter n ta kekketa shi. Rintse ido Joy ta yi don ji tayi kamar zuciyar ta Mom ke ketawa, lura da haka yasa Mom yin gutsi gusti da shi yadda koda ta tattara pieces din baza ta gane komai ba. Tana gamawa ta ce ki tashi muje ciki kiyi yan shirye shirye, tafiyar gaggawa ta kamani gobe da sassafe zamu bi jirgi zuwa Oshogbo . Cike da mamakin me zai kai su Oshogbo tana tsaka da shirin fara mid term test hankali ta she ta ce "Mom Oshogbo kuma." Mom Ta ce "Yes of course." "Ba sai hutun karshen shekara Mike zuwa ba? Kuma next week Monday zamu fara text." Mom ta ce "dat is not my prlm." Cikin shesshekar kuka tace "Gaskiya Mom ni bazan je ba." Wani mugun kallon ta watsa mata tare da saka mata wata uwar tsawa da gufu ta mike tayi cikin gida tana kuka.
*********
Tsawon sati guda Al'ameen bai cewa Amira komai game da batun karatun su ba, iya damuwa ta shiga damuwa gashi tana jin kunyar sake tunkarar shi da maganar, yau a islamiyya, ta zayyane wa Zainabu halin da take ciki, Zainabu ta ce "Ko dai ya mata ne?" Amira ta ce "bana tunanin haka." Numfashi Zainabu ta sauke ta ce "Fatima zaki aika ta tuna masa idan ma mantuwa yayi sai ya tuna." Amira ta ce "nima tunanin da nake yi kenan k'awata.sai dai nake ga kar yaga kamar na cika gajen hakuri." Zainabu ta ce "Bana ganin zai ce haka a yadda kike dan bani labarin halayensa, ni nama fi zargin mantawa yayi." Amira ta ce " to shikenan yau zan mata gamana sai mu ji mai zai ce, amma wallahi ni kunyar sa nake."Tsaki zainabu tayi ta ce "wannan kunyar naki wallahi shi zai kasheki Amira." "Hmmmm wallahi kawa dan dai baki san shi a zahiri bane, kamar zaki haka ya ke da kwarjini bashi da wasa baya daukar wargi at all.".............
Ga masu bukatar shiga group *** [12/29, 2:37 PM] AyshaNalado: ๐๐ *JOY* ๐๐