JOY

PAGE 16

by @aishanalado88

Da gudu ta k'arasa d'akinta ta fad'a kan bed d'inta tana sakin wani irin numfashi mai zafi, can kuma sai ga hawaye shaaa! kamar an bud'e famfo, wani irin tafarfasa zuciyar ta ke mata. Yanzu shikenan Mom ta yaga mata wasikarta, shikenan Mom ta rabata da letter n ta, ji take kamar wani part na jikinta aka yaga mata ba fallen takarda ba, tana jin son latter n nan sosai a ranta shi kadai me debe mata kewar Teeteenta. Ranta ya matukar baci da abin da Mom ta mata yau, tun da take bata ta6a ja'inja da ita ba amma wannan karon ta lashi takobin ko zata yanka ta baza ta bi ta Oshogbo ba suna tsaka da shirin fara text, Ai ba dole ba ne sai anyi tafiyar da ita, zabura tayi ta mi'ke tare da d'auko wayar ta dake yashe kan madubi, bata damu da waya ba don sai tayi sati bata ta6a wayar ba musamman idan Papa yana gari, idan baya nan dai dama kullum da safe zai kiranta ya ji lafiyarta ko ita ta kira shi.

Lambar Papa da tayi saving da My blood ta laluba ta dannawa kira, lucky ringing biyu ya d'aga, ta na jin muryar shi ya ce "He'll my lovely princess my Joy." Ta daddage ta fashe da wani irin kuka mai k'arfin gaske, kamar yadda ta tsammata a rud'e ya shiga tambayar ta "Menene ? Mekefaruwa ? waya ta6aki? Kina ina ne yanzu? Ina Mom dinki?" Babu d'aya data amsa sai ma k'ara sautin kukanta da tayi, aikuwa Papa dake zaune a office d'in abokin shi Mr Jack dake kasar Canada ya mike tsaye, ya shiga safa da marwa yana mata magiyar ta yi shiru ta daina kuka haka, sai da ta bari ta gama rud'ashi sannan cikin wani irin shagwabebben muryar mai hade da shesshek'a ta ce "Papa Mom ne." Wani irin kankance idanu yayi don bai ta6a tsammanin Mom ce ta saka mishi tilon yar shi irin wannan kukan ba, tausasa murya yayi dan kar ya kara daga mata hankali ya ce "Mom din ki kuma? Me tayi miki." Sai da ta gama jan majina ta ce "Ta ce wai gobe in shirya muje Oshogbo kuma On Monday zamu fara test." Cikin danne bacin ranshi ya ce "Ki ce mata bazan kije ba." "Na ce mata ta ce wai ban isa ba." Zazaafar huci ya fesar ya ce j "Ok haka ta ce, To ki kwantar da hankalin ki ni nace baza ki je ba, yanzu dai ki share min hawayen ki bari na kira Mom din naki muyi magana." Ta amsa da "Toh Papa." Tana share hawaye.

Bayan ficewar Joy daga garden da wani irin mugun harara Mom ta raka bayanta, a bayyane ta ce "Ya zama dole mu tafi Oshogbo tare gobe goben nan kamar yadda bokanta ya umarta bazan yi sakacin da aikina na shekara goma sha biyar zai lalace ba, zan Iya kawar da duk wanda ya ce zai min shamaki da wannan burina kowaye, Ta karashe maganar tana huci kamar kububuwa. Daga haka kuma tabi bayan fuuuu Joy, sai dai kuma kafin kai ga karasawa dakin Joy wayar ta ya dauki ruri, ganin lambar Papa yasa gabanta faduwa kar dai ace yarinyar nan ta kira Mr James ne, shaf ta manta da hakan da kwace phone din ta, dakewa tayi ta daga cikin kissa ta ce"He'll My O..... Kafin ta kai ga karashe maganar ta ya dakatar da ita ta hanyar ce wa "Alice!!!!!" A tsawa ce. Diriricewa ta yi don tsawar ya shigeta, don bata ta6a tsammanin hakan ba,Rabon da ya mata irin wannan tsawar tun kafin su dawo Niger state da zama, kafin ta dawo hayyacinta ya rude da fada akan me zata saka mishi d'iya kuka Akan me zata tilasta ui. Abinda bata so, sai da ya.mata tatass ba tare da ya bata damar amsawa ba ya daura da kuma "Ban amince miki ki fita ko bakin get da ita ba, ki je duk inda zaki je na lamince miki amma ban amince ki tafi min da Y'ata ba wannan umarni nake baki, idan kuma kika ki ji." Ya yi kwata! Bai jira cewar ta ya katse kiran, ya sake kiran Joy ya ci gaba da rarrashinta.

Daskarewa Mom tayi a tsaye a inda take, tana zazzaro idanu hankalinta a kololuwar tashe, kar dai a ce aikin da ta sha bakar wuya aka yi mata akan Mr James lalace, tashin hankali wacce ba'a saka mata rana, hannu na rawa ta lalubi lambar bokonta Kubal. ta danna mishi kira, cikin sa'a ya daga muryar na rawa ta shiga kwashe abin daya faru tana zayyana mai, tsawa ya faka mata shima , a kausashe ya ce "Na gaya miki matukar baza ki rabata da wad'an nan ahlin ba ba kiga komai ba, duk wani abu da kika binne ina mai tabbatar miki sai ya tonu." Hankali ta she Ta ce "Na rabata da su Kubal duk wani tsaro da takumkumi na saka mata, na shata babbar layi a tsakanin su." Dariya ya kece da shi mai ban tsoro lokaci daya ya gimtse sannan ya daura da "Wannan bai isa ya raba alakar jini da jini ba, kizo da ita garemu kizo da ita garemu kizo da ita garemu zamu rabasu rabuwa ta har abada." Ta ce "Mr James ya hana kubal. ka taimakeni bana son na rasa aurena ba tare da ba samu ci kar burina ba, ka taimakeni da kai kadai na dogara, tsoro nake ji kar Mr James ya rabu da ni." Boka Kubal ya a tswace ce "ki taho ke kadai da gaggawa, zamu canza kalar aikin namu, ki taho da gaggawa." Ka fin ta bashi amsa tuni ya yanke kiran.

A gurin ta zube ta daura hannu akai, ta san idan har asirin data ma Mr James tsohon shekara sha biyar ne ya karye kashinta ya bushe tabbass kashinta ya bushe, bata ga ta zama ba, idan ba haka ba ta tabbata zata kare rayuwarta a prison madadin ta zama daya daga cikin matan da suka yi ficce suka shahara a duniya kamar yadda take buri, zabura tayi kamar zautacciya ta bar gurin a guje, dakin ta ta shiga ta fara hada kayanta.

Ranar daga ita har Joy basu samu barci mai kyau ba, Joy kukan bakin cikin rabata da letter n ta, ta kwana yi, yayinda Mom tsananin tashin hankali ya hanata rintsawa.

********

Kamar yadda suka tsara da Zainabu hakan ce ta kasance, washe gari kamar yadda ta saba ta shiga wajen Ummi bayan ta tabbatar Al'ameen ya fita, a tsakar gida ta samu Fatima na wanke wanke Ummi na daki, dakin ta nifa ta durkusa har kasa ta gaida Ummi cike da lababi,cikin fara'a Ummi ta amsa tana saka mata albarka daga haka ya fito ta saka hannu tana taya Fatima dauraya suna hira, cikin hiran Amira ta ce "Wai ni kam Fatima Yaya Ameen na nan kuwa." Fatima ta ce "Yana nan mana yanzu bai dade da fita ba." Amira ta ce "Ikon Allah wallahi na kwana biyu ban gansa bane, duk zato na yayi tafiya ne ." Fatima ta ce "A'a yana nan wallahi." Shiru Amira ta dan yi can kuma ta ce "To kodai ya manta ne?" Fatima ta kalleta cikin rashin fahimta ta ce "Ban gane ba Anty Amira." Ajiyar zuciya ta sauke ta ce "Wallahi rannan nan mama ta saka na tambaye, wai ko na kawa past question na waec ya dinga koyamin kafin namu jarabawar ya kara so, ya amsa min da to zai ne me ni idan ya shirya amma na ji shi har yanzu shiri shi yasa nayi yunanin ko yayi tafiya ne, Ashe yana nan, shine nake tunanin ko ya manta ne." Fatima ta ce "abin ya kai kwana nawa yanzu." "Ummm! Ina ga yafi sati fa." Cewar Amira, "kai anya kuwa! Yayana bai cika mantuwa haka ba, amma dai ki kara tuna ma shi kiji, zai Iya yuwuwa mantawar yayi" marairai ce murya Amira ta yi ta ce "Fatima dan Allah ki taimake ni ki tuna mishi yau idan ya dawo." "To me zan ce ma shi?" "Ki ce Yaya Anty Amira ta ce wai ya maganar da kuka yi ran nan na karatu. Haka kawai zaki ce masa nasan zai tuna." Fatima ta ce "to shikenan in sha Allah idan ya dawo yau zan dasa masa."

Haka ko akayi a ranar da dare bayan Al'ameen ya dawo suna zaune a tsakar gida kamar yadda suka saba, Fatima ta ce "Yawwa Yaya Anty Amira ta ce wai na tuna maka ya maganar da kuka yi ran nan na karatu, wai har yanzu ta ji shiru daga gareka." Dan ya mutsa fuska yayi, jin abinda Fatima ke fada, sarai yana sane da ita shareware yayi don shi a halin yanzu yana tsoron kebewa da wata mace wacce ba muharramarsa ba, bai manta da abin daya faru ranar da tazo tambayarsa ba, common turarenta na neman zamar masa masifa. Ummi kam jin an ambaci Amira, tuni ta maido hankalinta Kansu ta ce "Binta me ya samu Amiran?" Fatima ta ce "A'a Ummi babu komai, ta aikoni wajen Yaya ne akan maganar da suka yi da shi, wai ta tambaye shi zai koya mata karatun jarabawan su dake gabatowa, ya e mata to zai neme ta amma yau kusan sati bata ji daga gareshi ba, shine ta ce idan ya dawo na tuna masa." Kallon Al'ameen Ummi tayi dai dai shima ya kallota suka hada idanu, da sauri ya sauke kai. Ta ce "Yayan Fatima idan da hali ka koya mata dan Allah, Amira yarinyar kirki ce." Shiru yayi kadan kafin ya amsa da "Toh Ummi." Sannan ya dago ya kalli Fatima ya ce "Fatima ki CE mata gobe idan na dawo da daddare tazo sai mu fara karatun." Yana kallon Ummi ta gefen ido yadda fuskarta ta yalwatu da fara'a. Fatima ma taji dadi don ba karya tana son Amira kamar dai Ummi.

*******

Washegari Sunday da sassafe Mom ta fito da trolley dinta, cikin shirinta na tafiya, sai da ta daidaita komai batta driven da zai kaita airport yana zaune a mota yana jiranta sannan ta nufi dakin Joy, tura kofar tayi da karfi, taga ya bude, bata zaci a bude kofar ya ke ba, shiga ta yi, a kwance ta sameta idanunta a rintse kamar mai barci sai dai ba barcin take yi ba, hasalima jin motsin mom din ne ya saka ta rintse idanu, tsayawa a kanta Mom ta yi ta kare mata kallo, sai da tayi mai isarta, sannan ta sauke ajiyar zuciya, a hankali ta ce "Daughter zan wu ce." Sai lokacin Joy ta bude kumburarrun idanunta amma bata ce komai ba, Mom ta sake cewa "Ba yan school ban lamunce miki zuwa ko ina ba, zuwa anjima Madame Esther zata zo ta zauna dake kafin na dawo." Daga haka ta juya ta fice Joy ta rakata da kallo.

Bani da isasshen lahiya banyi editing๐Ÿ™

Ga masu bukatar shiga group Ku tuntubeni. 9116099486 [12/29, 2:37 PM] AyshaNalado: ๐ŸŒ€๐ŸŒ€ *JOY* ๐ŸŒ€๐ŸŒ€

~FARHAT~