PAGE 26
No editing ayi ta hakuri🙏
Washegari haka Ummi da Fatima su ka tashi da hidamar Al'ameen, abin ma yazo musu da d'an sauk'i ne saboda shi d'in jarumi ne, bai sakar musu ragamar komai ba, yakan yi iya k'ok'arinsa, idan ya kasa sannan ya naimi taimako, yanzu ma Fatima ce ta yi sallama d'auke da abincin karin kumallon shi a hannu, ga mamakinta a tsaye ta same shi yana bin bango zai fito waje har ya kai bakin k'ofa.
"Subhanallah! Yaya ina zaka je?" Murmushi ya sakar mata, ya ce "Na gaji da zaman d'aki ne k'anwata zan fita tsakar gida in sha iska." Kwa'be fuska ta yi ta ce "Shine baka kirani in taimaka maka ba, idan ka fama ciwon ka fa?." Ta karashe maganar tana k'ok'arin rik'e shi, ya ce "No Barshi Fatima zan iya, ki je ki shimfid'a mini tabarma a tsakar gida." Cike da mamakin karfin halinsa ta ce "To Yaya." Ta fi ce.
Kici kicin shimfid'a tabarman da ta ke yi ne yasa Ummi dake kitchen lek'owa "A'a Fatima ya haka kuma?" Cewar Ummi sanin ba wai sun saba zaman tsakar gida da safe bane.
"Yaya ne ya ce na shimfid'a mi shi zai fito yasha iska wai ya gaji da zaman d'aki." Kafin Ummi ta ce komai sai gashi ya shigo da bin bango da dabara ya ke lalla6awa, da sauri Ummi ta zo ta rik'e shi, ta na cewa "haba Amintacce, ai da ka yi magana sai a taimaka maka." Da murmushi ya ce "A'a Ummi zan iya ai." Ita dai bata yarda ba sai da ta rik'e har kan tabarman da Fatima ta gama shimfid'awa ya lalla6a ya zauna, yana rintse ido lamar yana jin azaba, cike da tausayawa Ummi ta ce "Sannu Yayan Fatima Allah ya sauwak'e, ka yi k'o'kari ma wallahi zaman da'ki babu dad'i ga namiji, zaman dak'i ai sai mata, Allah dai ya ta shi kafad'a yasa kaffara ne." Ya amsa da "Amin Ummi."
Kayan tea Fatima ta jera a gaban shi da flask d'in ruwan zafi ta shiga had'a mi shi, kallon ta ya yi ya kalli Ummi ya ce "Ummi yau kuma tea zamu sha, babu kamun ne." Ta ce "A kwai naga baka da lafiya ne, kamar zaka fi son shayin shiyasa na bada kudi ta siyo buredi da sauran kayan hadin tunda shi kokon naga kayan fitsari ne." Yamutsa fuska ya yi alamar baiso ba, amma bai ce komai ba, sai kallon Fatima da ya yi ya ce "Sister ka d'an za ki hada shayin." Ganin yanayin shi yasa Ummi cewa "ko a dama maka kunun ne? Naga kamar baka son shayin." Baya son bata wahala , sai kawai ya ce "A'a Ummi ki barshi kawai zan sha." Kafin Ummi ta ce wani abu Aysha kanuwar Amira, ta yi sallama a tsakar gidan.
A tare suka amsa mata, ummi ta ce "Aysha ke ce tafe." Ta ce "E ni ce, ina kwana ummi ya mai jiki. " "Alhmdllh da sauki." Juyawa ta yi bangaren Al'ameen shima ta gaishe shi tare da yi masa ya jiki, ya amsa da " Alhmdllh."
Basket mai dan girma dauke da kuloli da flask ta fito da shi daga hijabinta, ta ajiye gaban Al'ameen tare da ce wa "Yaya Ameen wai gashi, in ji Anty Amira ta ce na kawo maka wai tana gaishe ka da jiki."
Share Aysha ya yi kamar bai ji abinda ta ce ba, wani banbarakwai ya ke jin lamarin, amma yarinyar nan bata da hankali mai take tunanin Ummi da Maman Amira zasu zata idan suka ga haka.
Ummi kam murmushi ta yi ta ce "Lallai an gaida Amira harda hidima haka ki ce mata Amintacce yana godiya." Fatima murmushi take yi a ranta tana lallai Anty Amira kin zurma da yawa Allah dai ya tabbatar da wannan lamarin.
Sallama Aysha ta yi musu Ummi ta ce "Tsaya ki amshi tukwuici." Tana kwance habar zani da sauri Aysha ta yi hanyar waje ta na cewa "A'a Ummi wallahi ki barshi nagode."
Yi ya yi kamar bai san an ajiye wani basket a gabansa ba, ya yi kicin kicin da rai, Ummi ta kalle shi, sai kawai ta yi murmushi, ta ce "Fatima bude abincin nan mu gani." Barin hada shayin ta matso ta fara cirowa kula guda biyu ne tuwo da miya, sai jug, babban kulan ta fara budewa kosai ne an yi shi manya manya jan suya gwanin sha'awa, ta bude karamin shi kuma farfesun kayan ciki ne a ciki da romo kadan sai turiri yake da kamshin kayan yaji jug din kuwa kunun tsamiya ne hadadde shima da zafin shi.
Rike haba Ummi ta yi, ta ce "Umm! Lallai Amira, to angode Allah ya yi albarka." Kollonta ta kai kan shi ko kallon side din abincin bai yi ba, ta ce "Amintacce ga abin kari in ji Amira." Ya ce "Angode kuci kawai Ummi, Fatima mikomin shayin da kika hada."Ummi ta ce " Baza ayi haka ba Yayan Fatima, Binta dauko kofi da plate ki zubawa yayanki abinci."
Mikewa tayi ta shiga kitchen ta dauko ta zo ta zuba mishi kunun da kosan zata zuba farfesun Ummi ta ce "Bar wannan Binta ya ci anjima." Ta amsa da "To ummi." Tare da mika mishi abincin gaban shi.
Dakyar da takurar Ummi ya dauki kosai daya ya yi bismillah ya kai baki ya gutsira, babu laifi yaji dadin shi sosai bai san sanda ya tura guntun a baki ba, daga haka ya shiga ci yana kora kunun sai ga Mallam Aminu ya kar kunu da kosai tas.
Ummi da ke mishi dariya a ranta ta ce "A kara ne?", yamutsa fuska ya yi ya ce "A'a Ummi Alhmdllh."
Ummi da Fatima ne suka ci sauran ragowar kunu da kosan, farfesun kuwa Al'ameen aka ajiyewa da rana aka dumama mi shi ya sha.
Makota na ta shigowa yi mi shi sannu da jiki baga mata da matasa tsararrakinsa ba har da dattijan unguwa, domin shi din mutumin mutane ne, yana da kirki da yawan gaisuwa, Maman Amira ma ta shigo haka kafatanin yan gidan gaba daya.
*************
*JOY*
Allah-Allah ta dinga yi gari ya waye ta je ta ga halin da Al'ameen ke ciki idan ba haka ba zuciyarta zata iya tarwatsewa, sai dai gaba daya Daren ranar ya mata nisa, dakyar ya iya jumirin jiran har bakwai da rabi ta yi.
Duk da tarin ciwon kan da take fama da shi, hakan bai hanata tashi ba, cike da karfin hali ta yi wanka ta shirya cikin riga da wando kanana as usual, sakkowa ta yi dining ko Mom bata jira ba ta yi breakfast din ta ita kadai duk da iya tea ne kawai ta iya sha.
Dakin Mom ta nufa, ta tarar bata tashi ba, ji ta yi baza ta iya jira har sai lokacin da ta farka ba, hakan yasa ta zauna a bakin godon ta shiga dan bubbuga pillow, Mom ta bude idanu cike da barci ta kalleta, ganin yadda idanunta suke har zuwa yanzu a rine gashi sun kara kankancewa fiye da jiya, saboda kwanan da ta yi kuka yasa ta mikewa zaune cike da damuwa ta ce "Daughter, me yasame ki?" Ta kai hannu tana tattaba jikinta, rike hannunta ta yi ta ce "Babu komai Mom tun kukan jiya ne da na yi." "Amma Daughter ya kamata ace tunda kin yi barci kin farka idanunki su dawo daidai ba wai su kara rinewa ba." Shiru ta yi ta rasa me zata ce don kare kanta. "An ya kuwa lafiyar ki kalau, idan kina jin wani damuwa ki sanar min muje asibiti." Girgiza kai ta yi, ta ce "I'm ok" "Well!" Mom ta faa tana gyara kwanciya.
Langwabe kai ta yi ta ce "Mom ina son zanje landmark bookshop na duba wani story book da nake nema, da ma wasu books din wadanda nake da su duk na gama karantasu." Tsare ta da idanu Mom ta yi na yan wasu sakannni tana nazartanta, Hankalinta bai kwanta mata da fitar ba, hakan yasa ta ce " Da sassafen nan haka? Ki barshi kawai ba sai kinje ba, ki fadi sunan book d'in zan saka a naimo miki." "Ok Mom Thank U." Ta fada tare da mikewa ta fice a dakin gudun kada kwallan daya ciki idanunta su zubo a gaban Mom.
Sarai Mom ta ga yanayin da ta shiga hakan yasa ta kara gaskata zarginta akanta.
Da gudu ta fada kan gadonta ta rushe da kuka, ya ya zata yi? Ina zata saka ranta ta ji sanyi? Wani hali Al'ameen yake ciki, shin kodai ya mutun ne da gaske kamar yadda ta gani a cikin mafarkinta, yin wannan tunanin yasakata mikewa zaune zumbur! Zuciyar ta ne ke Ingizata akan ta saci hanya ta tafi . Da sauri ta mike tsaye da nufin tafiyar , sai kuma tsoro ya kamata, idan asirinta ya Tonu Mom ta sani mai zai biyo baya, ta tuna sanda Mom ta juya mata baya lokacin da ta gane tana mu'ala da Fatima, ko kadan baza ta so su koma gidan jiya ba, don baza ta iya jura ba da wanne zata ji. Komowa ta yi dabass ta zauna a bakin bed ta ci gaba da kuka.
Wani shawara ne ya fado ranta wanda ya sakata mikewa da sauri kamar an tsikareta, da sauri sauri gudu gudu ta dinga saukkowa stairs, tana fitowa direct boy quarters din gidan ta nufa, bangaren da wasu daga cikin ma'aikatan gidan suke kwana, a kofar dakin Peter ta tsaya ta shiga knocking, da sauri ya fito ko amsa gaisuwar da yake mata bata yi ba ta ce "Peter, ka taimakeni." Ta fada tana hade hannaye hawaye na bin kumatunta, rudewa Peter ya yi, cikin rawar bani ya ce "Miss me ki ke bukata kiyi hakuri ki daina kuka ko meye zan miki matsawar baifi karfina ba." Tunda ta fara zayyano ma shi bukatar ta na tana son ya je gidan su Fatima ya dubo mata wani hali Al'ameen ke ciki, ya ke bin ta da kallon tausayawa ji yake kamar ya zubar mata da kwallah wannan wacce irin jarabta ce, a raunace ya ce "ki yi hakuri Miss na miki alkawarin zan je na dubo miki shi, yanzu dana gama abinda nake yi."
Haka suka rabu da Peter ta koma cikin gida tana jiran tsammani.
Kamar yadda Peter ya yi mata Alkawari karfe goma sha daya a kofar gidan su Fatima ya mi shi, kasancewar gidan ana ta shiga da fice na masu zuwa gaisuwa bai sha wahala gurin sanin halin da Al'ameen ya ke ciki ba, shi kanshi ya tausayawa yaron da fargaban yadda zai sanarwa uwar dakinsa wannna bakin labarin ya koma gida, bai samu haduwa da ita ba a lokacin, sai wuraren karfe shiddan yamma suka hadu. Kallo daya ya mata ya sauke kai, gaba daya ta fice a hayyacinsa kamar ba Miss Joy daya sani ba, "I'm sorry Miss labarin babu dadin ji." Ya fada a sanyaye.
Wani irin Kwalalo ido waje ta yi tare da safe kirji a razane ta ce "Ya mutu ko."............
***. [12/29, 2:42 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀
~FARHAT~