PAGE 29
Murmushi ya yi tare da gyad'a mata mata kai alamar da gaske ya ke yi. "Oh my god!!! I'm so happy." Ta fad'a cike da mad'aukakin farin ciki, fuskarta dauke da yalwataccen murmushi.
Kallon juna suke yi kowanne zuciyarsa fari 'kal, shima murmushin yake ganin yadda ya wanzar mata da farin ciki, cikin sigar zaulaya ya ce "Miss smiller! Wannan murnar duk na ganin Fatima ne?" Da sauri ta gyada kai, ya girgiza kai tare da ce wa"To Oya let's go to her." A hankali ya juya ya fara tafiya yana d'ingisa k'afarsa. Tsayawa ta yi tana karewa bayan shi kallo, ta na zayyana irin kyawun surar shi a ranta, sai da ta ga yana daf da shigewa zaure sannan ta bi bayan shi da sauri.
Sallama ya yi a tsakar gidan, kusan a tare Fatima da Ummi suka amsa, Ummi na daga d'aki Fatima kuma na kitchen. Da sauri ta mik'e ta fito tana ce wa "Yayana har ka daw......" Sauran zancen ne ya mak'ale lokacin da idanunta suka yi arba da Joy tsaye a bayan Yayanta, cikin rawar murya ta ce "My Joyyyy!" Joy da tuni ta fara takowa wajenta ta ce "My Teetee!" Da gudu Fatima ta k'arasa gareta suka rungume juna, fashewa da kuka Fatima ta yi tana ce wa "My Joy ke ce da gaske ba mafarki nake yi ba kamar yadda na saba, mai yasa baki zo naima na ba, kika bar ni da tarin kewar ki." Joy da tuni itama hawaye ya wanke mata fuska, at d same time kuma tana murmushi, ta ce "I'm sorry My Teetee, ki yafe min, nima na yi kewar Fatima, I missed u my friend, I badly missed u." Tsabar farin ciki bata iya amsa mata ba, sai zame jikinta ta yi a nata da sauri ta isa wajen Al'ameen dake tsaye yana kallonsu, yana murmushi ta fad'a jikin shi ta rungume shi gam ta kwantar da kanta a kirjin shi, cikin shessheka take ce wa "Nagode Yayana, nagode nagode daka dawo min da walwata da farin cikina, yadda ka faranta min Allah ya faranta maka Yayana." Tsam! Ya saka hannu ya zagayeta, yana bubbuga bayanta, gaba d'aya zuciyarsa ta karye ji yake kamar tana melting, tausayin rayan gaba d'aya ya cika shi, ba dadan shi din jarumin namiji ba ne , da babu abin da zai hana ya zubar da hawaye.
Tsayawa Joy ta yi tana kallonsu cike da sha'awa tana murmushi still hawaye na zubar mata.
Daga bayanta taji an dafa kafad'arta, da sauri ta waiga, ganin Ummi yasa ta saurin fad'awa jikinta ta 'kamk'ameta. Ummi kam kasa jurewa ta yi sai da ta dauke kwallah a fakaice, murmushi farin ciki kwance a fuskarta, ta shiga shafa kanta alamar rarrashi.
Dakyar Al'ameen ya raba Fatima da jikinsa, handkerchief d'in sa yasa ya shiga share mata hawaye, lokaci 'daya kuma yana ce mata cikin rad'a da rarrashi, "Ya isa haka k'anwata, ki yi shiru ko kuma na ce ma FARHAT ta wu ce abinta tunda ba ki son ganinta." Da sauri ta mak'e kafad'a tare da ce wa "inyiiiin!" Cikin sigar shgwa6a ya ce "Oya go to her." Ya k'arashe maganar tare da rik'e hannunta ya soma tafiya, gaban Joy da Ummi suka tsaya, a hankali ya ce "FARHAT!" D'agowa ta yi daga jikin Ummi ta kalle shi, murmushi ya sakar mata, tare da kamo hannunta ya had'a da na Fatima.
A hankali ya saki hannayen ya juya ya bar tsakar gidan, Ummi ta kalli Fatima data kamkame hannun Joy gam kamar za'a kwace mata ita, ta ce "Yau kuka da mafarke mafarke da surutan cikin barci ya kare ko?" Zafo ido ta yi ta ce "Laaaa! Ummi ni?" Ummi ta ce "Ke fa, kusan kullum sai kin yi sambatun kiran sunan Joy cikin barci." Duk dariyar farin ciki suka saka, Fatima ta ja hannun Joy ta na ce wa "Friend mu je d'aki ki bani labarin school da bayan rabuwa." Joy ta amsa da "Sai dai na baki labarin irin yadda na yi missed d'in ki." D'akin Ummi suka shige basu tsaya a falo ba har bedroom Fatima ta ja ta.
Ganin shigewar su yasa Ummi girgiza kai, lamarin Al'ameen sai shi, ta fad'a a ranta, d'akin shi ta nufa don tana son jin yadda aka yi ya had'u da Joy har ya kawo ta cikin gidan yau dan kan shi.
A d'aki kam, hira ce ta 6arke tsakanin kawayen biyu. Bayan sun gama musu kowa na fad'in shi yafi missed d'in dan uwan shi, Fatima ta ce "Ya aka yi Ki ka had'u da yayana, ni farin ciki ma ya hana ni wannan tunanin sai yanzu." Ajiyar zuciya Joy ta sauke ta ce "Friend labarin da tsayi amma bari na takaita miki." Tiryan tiryan ta shiga bata labarin abin da ya faru da ita tun daga ranar da Fatima ta je gidan su, wasikar data aiko mata da replay din data bata zuwanta gidan haduwar ta da Al'ameen da abinda ya wakana, hatta bige shin da suka yi bata boye mata ba, zuwa yadda aka yi ta samu fitowa, sai dai koda wasa ta kasa fad'a mata yadda soyayar Al'ameen ya mata kamun kazar kuku.
Mamaki gami da dum6in Al'ajabi ne ya cika Fatima jin wai motar Joy ce ta kad'e Al'ameen, lallai Yaya Ameen yana da kyakyawar zuciya ko da wasa bai fad'a musu cewa itace ta kad'e shi ba, kuma harga Allah bai rike ta a zuciya ba, don ko yan dubiya ne suka zo irin masu kumbar bakan nan idan suna tsinewa wanda ya bige shi yakan ce su bari babu komai shi ya yafe, kuma suma ba da gangan suka yi ba. Ranar Fatima da Joy kamar karsu rabu. Dakyar ta yadda Fatima ta rakata ganin karfe shidda ya gota,Fatima kuwa tsoron Mom ya riga ya gama cika ta, shi yasa ta dinga kora Joy akan ta tafi amma ba wai don ta gaji da ganinta ba, ita bata ki Joy ta dawo gidan su da zama ba su dinga kwana suna ta shi tare, Ummi na yi musu dariya suka ta fi, ta ce "Teetee mu je na k'ara gaisar da Yaya Alamein, ba tare da tunani kamaj ba Fatima ta ce "Ok muje."
A kofar d'akin Fatima ta yi sallama, shiru babu amsa, hakan ya sa ta lek'a wayam baya ciki, dagowa ta yi ta kalli Joy ta ce "Ya fito." Kwa6e fuska ta yi ta ce "Ina ya je." Dariya Fatima ta yi ta rik'e ha6a tare da cewa "Iyeeee, wannan sabon salon fa." Sai lokacin ta fahimci mai ta yi, Itama dariyar ta yi ta ce, "Ina son ganin dat his cute face kafin na tafi.Teetee mu jira ya dawo sai na tafi." Zaro ido Fatima ta yi kafin ya ce wani abu sai gashi yana shigowa, fatima ta ce "Yawwa Yaya zo kaji." Da sauri joy ta kai hannu ta rufe mata baki, tana zare ido, bata yi zaton yana kusa ba, jingina ya yi da bango ya yi folding hannayesa a kirji ya ce "Menene sister gayamin, gulma na FARHAT ta yi ko." Girgiza kai Fatima ta yi, ya ce "To menene." Kallon Joy ta yi tana dariya da sauri ta girgiza mata kai, sai kawai ta ce "Yaya babu komai." D'age kafada ya yi ya ce "Ku kuka sani Ku bani hanya na shiga dakina." Kaucewa suka yi ya shige bayan sun yi sallama da Joy.
Har inda suka yi da David zasu hadu Fatima ta rakata, a wurin suka tarar da shi shima isowar shi kenan, kallo Fatima ya yi yana murmushi ya ce "Fatima my classmate." Harara ta watsa mashij, ya kyalkyale da dariya ya ce "Yau ina cikin farin ciki don haka bazan kulaki ba, amma zamu jone, muje Joy time ya wuce sosai." Ya karashe maganar yana kallon agogon dake daure a hannun shi...........
***. [12/29, 2:44 PM] AyshaNalado: ๐๐ *JOY* ๐๐
~FARHAT~