JOY

PAGE 36

by @aishanalado88

A firgice Mom ta shigo cikin makaranta, tana gurin aiki kirata same ta daga principal na school d'in Joy babu lafiya, office d'in principal ta nufa bayan gaisuwa principal da kanta ta yi mata jagora zuwa d'an karamin clinic d'in makarantar in da Joy ke kwance tana hutawa, don koda nurses suka tambayeta cewa ta yi kanta ke ciwo maganin ciwon kai kawai suka bata na kwaya ta sha, daga nan kuma suka bata bed rest kafin a iyayenta su zo.

Tun da ta kwanta idanunta ke lumshe, da gaske kanta ke yi mata ciwo, bayan ciwon da zuciyarta ke yi mata, har zuwa lokacin babu abin da ya ragu dangane da abin da take ji a zuciyarta,wannan kululun na nan tokare a kirjinta, babu abinda ke amsa kuwwa a kunnenta sai maganganun Fatima, babu yadda bata yi ba, don hawaye su zubo daga idanunta ko zata samu sassauci a zuciyarta amma abin ya faskara sai kukan zuciya take wanda irin wanda ke kara ma mutum kunci.

Cikin wannan yanayin Mom da principal suka iso d'akin, sarai ta ji su amma ta kasa bude ido ta kallesu, tana ji d'aya daga cikin nurses d'in wajen na yima Mom bayanin cewa kanta ta ke ciwo kuma sun yi mata abin da ya kamata sun bata magunguna, godiya Mom ta yi musu, ta matsa gaban gadon tare da dafa kanta, kan da d'umi, ga jijiya nan a goshinta sun tashi alamar dai ciwon kan mai yawa ne, kallon principal Mom ta yi ta ce "Dama tana da larurar ciwon kai tun tana k'arama, ina ga shine ya tasar mata, amma kuma gaskiya ya dad'e bai tashi ba don tun tana da shekara bakwai muka fitar da ita kasar Mexico ta ga wani babban likitan kwakwalwa shikenan bai k'ara tashi ba sai yau." Cike da Alhini principal ta jajanta lamarin. "Zan tagi da ita gida sai na kira Dr ya sake dubata." Cewar Mom, "Ok ba damuwa hakan dama shine daidai." Matso da mota Mom ta yi har bakin clinic d'in, da taimakon nurses ta samu ta isa motar don da ta mike jiri ne ya ringa dibanta dole a ka suka rirrik'eta suka taimaka mata.

Har a ka tashi Fatima kuka take yi, ta firgita sosai da yadda Joy ta yi, tunda suke tare bata ta6a ganin ta cikin yana yin makamancin wannan ba,ta yi nadamar fad'i mata wannan maganar yafi sau shurin masaki, sai dai taki baiwa zuciyarta damar gaskata zarginta na cewa Joy tana son Yaya Ameen ne, duk wani kofa da zai bata damar gasgata hakan ta toshe, har suka yi closing bata fahimci wani teacher da wani teacher bane suka shigo class d'in bare tasan me suka koyar, itama da nata kamashon ciwon kan ta koma gida, sa'arta d'aya Ummi bata nan, dama Yaya Ameen ta san baza ta same shi a gida ba daidai wannan lokacin sai da wani kwakkwaran dalili. Sallar azahar ta gabatar ko abinci bata iya ci ba, ta sha paracetamol ta hau gadon Ummi ta kwanta, babbar damuwarta rashin sanin halin da Joy ke ciki, gashi ko giyar wake tasha baza ta iya taka 'kafarta zuwa gidansu ba, haka ta yi kwanta cikin damuwa tana tunane tunane cikin sa'a barci ya yi awon gaba da ita mai cike da mafarkai barkatai.

**********

Dr Solo ya kalli Mom bayan ya gama duba Joy ya yi mata duk abin da ya makata ciki harda alluran barci don ta samu hutun zuciya da kwakwalwa, ya ce "Ciwon kan ta ne ya yi kokarin ta shi dalilin wani yanayin tashin hankali da ta shiga, amma zuwa yanzu da sauk'i, sai dai a kiyaye shigarta cikin irin wannan yanayin, gudun samun matsala." Cike da damuwa Mom ta ce "ok Dr mungode kwarai." A ranta tana mamakin wani irin tashin hankali ne Joy ta shiga haka. Sallama Dr ya yi ma Mom ya tafi tare da alkwarin sake kira zuwa dare yaji halin da ake ciki. Tare suka five da Mom daga d'akin don yi mashi rakiya.

Duk abin da Dr yake fada tana ji domin kuwa idanunta biyu, sai dai fitar su daga d'akin bai fi da minti biyar ba wani nannauyar barci ya yi a won gaba da ita.

Awa bakwai cur! Ta kwashe tana barci, kafin ta farka lokacin karfe shidda daidai na yamma, a hankali ta bud'e idanunta da suka mata nauyi, ta ji sauk'i sosai don wasai take jin kanta babu d'igon ciwo, haka ma nauyin zuciyarta ya ragu kaso hamsin cikin d'ari, a hankali ta lalla6a ta mik'e zaune, tankwashe kafa a tsakiyar gadon tare da rafka tagumi da hannayenta bibbbiyu.

Maganganun Fatima ne suka shiga dawo mata filla-filla, "Yaya Ameen ya yi budurwa very soon zai yi aure, zai auri Anty Amira." Kalmomin da su ka yi ta amsa kuwwa kenan a kunnenta suna neman rikitar mata da kwakwalwa, da sauri ta saka hannu ta toshe kunnenta da hannayenta tare da fashewa da kuka, take hawayen da take muradin fitarsu tuntuni suka samu hanya, a guje suka shiga wanke mata fuska.

Kuka tayi sosai don a kalla ta kwashe kusan awa guda tana yi, a hankali ta ji kuncin dake zuciyarta na yayewa, ajiyar zuciya ta shiga saukewa akai akai hadi da shessheka, ita kanta baza ta ce ga dalilin kukan nata ba abin da ta sani kawai umarnin zuciyarta take bi, sam! Zuciyarta baza ta iya jurar jin Kalmar Yaya Ameen yana son wata mace ba, balle har a kai ga batun aure, tabbas a duniya tana ganin babu abin da yafi wannan tashin hankali a gareta, a halin yanzu ita kanta bata san meke damunta ba, bata kishi ba domin ita kadai ta tashi gaban iyayenta abin da ta sani kawai soyayya, shiyasa abin da ya faru da ita yau bata san da mai zata kwatantashi ba.

Shigowar Mom ne ya katse tunaninta, da sauri Mom ta k'araso ganin ta a zaune, zama ta yi a kusa da ita ta kai hannu tana tatta6a goshinta zuwa wuyanta,salam! Babu zafi ajiyar zuciya ta sauke tare da godiya da abin bautarsu. Cike da kulawa tace "Princess ya jikin, yaya ki ke ji yanzu, ina ne ke yi ma ki ciwo?" "I'm fine Mom babu in da ke min ciwo, naji sauk'i." "Ok bari na kira miki Papanki ku gaisa tun dazu yake ta kira yana son yaji muryarki." Da d'unbin mamaki a fuskarta ta ce "Papa kuma?" "Yes Ur Papa." Zun6ura baki ta yi ta ce "Ya daina sona yanzu ai." Murmushi Mom ta yi ta ce "Who tell that, a duniya babu abin da Mr James yake kauna sama dake tillon y'arsa,ina tabbatar miki yafi kaunarki fiye da ni dana kawo ki duniya." Ta karashe maganar cike da d'aci a muryarta, amma sam Joy bata fahimci komai ba saboda kakanun shekaru, "Na sani Mom a da Papa yana sona amma cikin yan kwanakin nan ya canza min, abin ya dame ni amma na yi masa uzuri, nasan aiki ne ya sha kan shi." "Of course princess haka ne, jiya ya kammala duk aikin sa ya kaishi kasar Canada, yanzu hankalin sa gaba daya ya waiwayo kan little princess d'in shi, tun safe yake min waya yana neman ki,. Ta kai karshen maganar tana mika mata wayarta da ta yi dialling lambar Papa.

Cike da shauk'in so irinta tsakanin da da mahaifi ta kara wayar a kunnenta tare da cewa; He'll My Papa." "My Joy My everting." Ya amsa mata cike da soyayya, sun Dade Suna waya ta yi mai korafi akan shareta da yake yi kwana biyu hakuri ya bata da cewa shima bai san mai ya same shi ba cikin kwanakin nan, sun dad'e Suna waya kafin su yi sallama.

Mom ta amshi wayarta tana sakin wani shu'umin murmushi wanda ita kad'ai tasan ma'anarsa.......

Ko kunsan ma'anar murmushin Mom, ni da ban sani ba๐Ÿ˜ข

Oum ummeetarh *** [12/29, 2:47 PM] AyshaNalado: ๐ŸŒ€๐ŸŒ€ *JOY* ๐ŸŒ€๐ŸŒ€

~FARHAT~