PAGE 5
Da takaicin wad'annan y'an matan Al'ameen ya kamo hanyar gida, daf magriba ya iso k'ofar gidan su, ganin ana shirye shiryen yin salla yasa bai shiga ba ya nufi masallaci, koda suka idar bai tashi ba zama yayi a cikin masallacin yana addu'o'i tare da neman Allah ya kareshi daga sharrin ta'bar'barewar zamani, bai fito daga masallacin ba sai da aka idar da isha'i, daga nan kuma bai zame ko ina ba sai gida.
A tsakar gida ya samu Ummi zaune kan shimfidar babbar tabarma, tana sauraren labarai a redio kasancewar mace mai yawan sauraren labarai, zama yayi a gefen tabarmar bayan Ummi ta amsa mishi Sallama, "Ummi sannu da gida." Ya fad'a yana gyara zaman shi da kyau, "Yawwa yayan Fatima ka dawo dama yanzu nake zancen ka a zuciya, ashe kana tafe." "Eh Ummi na tsaya na yi sallah ne gaba d'aya." Ummi ta ce "yayi kyau. ya karfin jikin." Ya ce "Alhamdulillah Ummi naji sauki sosai, da nayi sallar la'asar ma na kaima Aliyu ziyara ne." Ta ce "Allah sarki Aliyu yaron kirki makaranta ya boye shi, yana lafiya." "Yana lafiya Ummi yace yana gaisheki sosai, " "Allah sarki Aliyu d'an gidana ina amsawa ." Murmushi Al'ameen ya yi tuna tsakanin Aliyu da Ummi.
Fatima Ummi ta kwalawa kira, daga can kuryar d'aki ta amsa tana tasowa daga kwancen da take har zuwa lokacin riga da skirt din nan ne a jikinta, ji ta yi Ummi na ce wa "Ki zo ki kawowa yayanki tuwon shi ga shi ya shigo." Jin haka yasa da d'aukinta ta koma d'aki ta d'auko ledar yalon data siya mai d'azu a hanyar makaranta ba ta samu ta ba shi ba, ta fito fuskarta washe da fara'a, tana ji dadi zata farantawa yayanta, hankalin shi na kan daddana yar wayar shi buttus, ya tsinci muryar Fatima na cewa "Yaya sannu da dawowa." 'Dagowa ya yi yana amsa mata da "Yawwa Fatima ya gi." Sauran zance ya ma'kale lokacin da ya sauke idananun shi a kanta, ran shi ne ya baci ganin shigar dake cikin ta, ta ke ya had'e rai yana binta da wani irin kallon da yasa gabanta fara dokawa.
Lokaci daya fara'ar dake fuskarta ya juye zuwa tsorata, ta ke ta fara ja da baya, bata kaunar ganin wannan fuskar na yayanta, firgitata yake yi, ya kan mata irin wannan kallon ne a duk sanda ta yi wani abu ba dai dai ba, tunda ta ke da shi bai taba d'aga hannu ya duke ta ba, sai dai ya kan ladabtar da ita da hanyoyin data gwammace gara ya faffala mata mari akan su.
Ummi bata san meke faruwa ba hankalinta na kan rediyonta tana kokarin canza channel ta tsinin ci muryar Al'ameen cikin kaushi ya na cewa "Zo nan Fatima." Ya karashe maganar yana nuna mata gaban shi.
Bata iya mishi musu run tasowarta, hakan yasa ta shiga matsawa a hankali kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki, nesa kaɗan da inda yake nuna mata ta tsuguna, ta re da duƙar da kanta kasa, a banza ma wani lokacin bata iya haɗa ido da shi balle yana cikin iri wannan yanayin.
Ummi dai da ido ta bisu su bata tanka ba a ranta tana kunfi kusa.
Ciki muryar shi mai dauke da amon bacin rai ya fara cewa "Fatima wannan wacce irin shiga ce kika yi haka kina yar musulmai," tsuru tsuru ta yi tana zare ido, cigaba yayi da cewa "Ashe ba na hana ki saka kayan da zasu bayyana surar jikinki ba, ina duk tarin suturunki na mutunci da nake dinka miki? Shiru tayi ba amsa ya cigaba "Ok na gane tarayyarki da yar arna abin yayi 'kamari har kin fara kwaikwayon dabi'u da shigarta ko?."
Tuni Fatima ta fara girgiza kai tana kuma jin abin da me fitowa daga bakin yayanta, "ina tambayarki baki bani amsa ba kina kuka, nace tarrayyarki da yar arna abin yayi kamari har kin fara dauka dabi'unta ko, to wlh ba a nan gidan ba, kuma zan yi wa tufkar hanci, tunda ke naga alamar bakin jin magana, don bazan zuba ido ke kadai yar uwata da nake da ita a duniya ta lalace ba, zan dauki kwakkwaran mataki akan ki dake da ita wannan yar arnan, domin hakkinane na kula da tarbiyarki."
Ya kai minti ashirin yana mata fad'a ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba haushi da takaicin daya kwaso na yan matan da ya gani a hanya, da kuam haushin kawancen ta da yar arna da yake ji, duk Sai da ya sauke mata su, kafin ya tsagaita yana kallonta yana huci.
Zuwa lokacin kuka Fatima keyi kamar ranta zai fita, daga yadda take jin amaon sautinsa tasan ba karamin baci ran shi yayi ba,ko daman bashi hakuri bata samu ba, jin yayi shiru yasa cikin shessheka ta ce "Yaya ka yi hakuri walla..." Dakatar da ita yayi da cewa "rufe min baki mutuniyar kawai, kuma ki bace min da gani."
Dasauri ta tashi tana toshe bakin ta saboda sabon kukan da ke shirin kwace mata, ta kai bakin kofa ya d'aga muryar ya ce "kuma ki ciro kayan ki kawo mi yanzu yanzu."
Ajiyar zuciya Ummi ta sauke, bata ce komai ba, a ranta Sai hamdala take da tasbihi ma ubangijinta tasan ko yau ta fadi ta mutu Fatima baza ta tagayyara ba in dai har da Al'ameen a gefenta, kallon shi tayi shima ita yake kallo, kallon tuhuma, saukar da kai kasa yayi cikin taushin muryar ba irin wanda yama Fatima magana da shi ba ya ce "Ummi kinga abinda nake gaya miki, kinga abin da nake so ki hango amma kin kasa hangowa Ummi tararryar Fatima da yar arnan nan wlh na tabbata babu alkhairi a cikin sa, Sai sharri Ummi ki buba wannan lamari dan Allah."
Murmushi Ummi ta yi a ranta ta ce "yaro yaro ne kuma duk abinda babba ya hango akace yaro ko ya hau rima bazai hango ba."
Jin Ummi bata ce komai ba sai bin shi da kallo da take yi yasa ya mike ya nufi haryar zaure ran shi duk ajagule.
*********
Joy na barin dakin Mom dakinta ta koma, ta fada kan bed ta cigaba da kuka har zuwa lokacin ko takalmin makaranta bata cire ba bare uniform haka ta wuni a daki ba ci ba sha, har wurin karfe biyar na yamma hakan kuwa ya saukar mata da zazzafan zazzabi mai hade da ciwon kai, kafin shidda na yamma ta gama fita hayyacinci dakyar take sauke numfashi ko idanunta bata iya budewa.
Abu ne da bai taba faruwa da ita ba tun tasowar ta, jin shi take yi sabo a gareta ,bata saba da hakan ba a kullum tsakanin ta da Mom kulawa ce na musamman da nuna kauna duk girman laifin da zata yi cikin rarrashi ta ke nusar da ita, haka ma Papa shiyasa ta ke ganin abin da girma.
A bangaren Mom kuwa rudanin da take ciki ya shallake tunaninta, hakan yasa bata bi ta kan Joy ba.
Karfe shida da rabi dai dai motocin Papa suka yi parking a counpound din gidan, fitowa yayi bayan daya daga cikin escort biyu dake biye da shi ya bude mishi kofa, fitowa yayi jacket din suit din shi a kafad'a hannushi rike da briefcase din shi, entrance din gidan ya nufa zuciyar shi cike da bege da kewar iyalan shi, ma'aikatan gidan sai kwasan gaisuwa suke yana amsa musu da fara'a,
Koda ya shiga main parlour babu kowa bai damu ba, upstairs ya haura yana kiran sunan baby kamar yadda yake kiran Joy, yayi mamakin da har ya 'karasa hawa saman ya isa babban kayataccen falon daya fi na kasan kyau da kayatuwa, baiga ta fito da gudu ta tare shi ba kamar yadda ta saba, to ko dai bata gidan ne? Ya jefawa kanshi tambaya.
Bai samu wannan amsar ba Mom ta fito daga dakinta, sakar ma juna murmushi suka yi wanda ita nata iyakarsa la'b'ba, bud'e mata hannayenshi yayi ta fad'a jikinshi suka rungume juna cike da soyayya,cike da kissa take mai sannu da dawowa yana amsa mata da zuciya d'aya cike da kulawa, amsar jakarshi da jacket din shi ta yi ta kama hannunshi zuwa dakin shi.
Wanka ta taya shi yayi, ya shirya cikin kayan zaman gida, zama yayi a falon wanda ke hade da bedroom din shi, yana amsa called, fita Mom tayi ta dawo dauke da ruwa da lemon five alive a tray, zuba mishi ta yi ta mika mishi amsa yayi yana murmushi ya ce "thank you Sweetie." Itama murmushin ta yi ta zauna a gefen shi ta maida idanunta kan TV duk da kallo kawai ta ke yi hankalinta baya gurin, sama da minti talatin Papa ya kwashe yana waya da wani tsohon abokin kasuwancin shi wanda suke shirye shiryen had'akar Samar da wani kamfanin sarrafa 'karafina a Lagos.
Ko da ya ajiye phone din Mom bata kula ba, muryar shi ta tsinta yana cewa "Hala baby bata nan ne?" Ta amsa mai da "tana nan, tana dakin ta." Murmushi ya yi ya ce "yau mulki take ji baza tazo ta ma Papa welcome back ba kenan, bari to ni naje na ganta." Daga haka ya mike ya fice daga dakin.
Tun kan ya karasa dakin yake ce wa "baby where are u, I'm back, your Papa is back." Yana maganar yana murda handle din dakin nata,yana shiga idanun shi ya sauka a kan ta , zaro ido yayi kafin ya karasa da sauri ya haura kan bed din ya shiga jijjgata yana kiran sunan ta, da kyar ta bude idon ta da suka kumbura, murya a shake ta ce "Mom ki yafe Mom kiyi hakuri." Bai jita ba saboda shakewar da muryarta ya yi, a gigice ya ciro waya ya dannawa Dr dake duba su waya, jin yadda Papa ke gigice yasa, ya ce ya bashi fifteen minute gashi nan zuwa.
Yana ajiye wayan ya shiga kwala ma Mom kira, bata ji ba saboda tazarar dake tsakanin dakunan, kuma gashi ko ina a kulle, ganin zai bata lokaci yasa yayi amfani da telephone din dake dakin joy ya kira lambar dakin shi da shi.
Mom dake zaune ganin kira ta wayar tafi da gidanka abin ya bata mamaki, ta shi ta yi ta dauka, jin yadda Papa ke magana a rude yasa taji gaban ta ya fadi da gudu ta kwasa zuwa dakin Joy..........
Kuyi hakuri da jina shiru kwana biyu🙏 yawan comment yawan tsayin page😬
Me bukatar shiga group ya tuntubeni ta wannan lambar *** [12/29, 2:31 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀
*BY*
*AYSHA NALADO*
*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*
*LITTAFI NA ƊAYA*