PAGE 8
ASSALAMU ALAIKUM
KUYI HAƘURI DA JI NA SHIRU DA KUKA YI KWANA BIYU, HAKAN YA FARU NE SABODA WANI DALILI MAI ƘARFI , AMMA YANZU NA DAWO INSHA ALLAH ZAMU ƊORA DAGA INDA MUKA TSAYA, FATAN DAI BAKU MANTA LABARIN AL'AMEEN DA JOY BA KUCI GABA DA BIBIYA AKWAI FAƊAKARWA, WA'AZANTARWA RIKICIN KABILANCI, TARE DA ZAZZAFAN SOYAYYA MAI TAƁA ZUCIYA.
A bangaren Joy kam jinye take yi hankali kwance, daga Mom har Papa wani irin so da kulawa suke nuna mata na musamman, sai dai kamar yadda Fatima ta shiga damuwa saboda rashin ganin ta, haka itama ta shiga matsanancin damuwa saboda rashin ganin Fatima, hakan yasa ranar Friday ta shirya don zuwa school amma ƙememe Mom ta hana ta zuwa ta ce ta bari sai Monday badan ta so ba ta haƙura saboda kar Mom ta zargi wani abu, ta bari idan ta wuce aiki sai ta saci jiki ta je gidansu koda Ummi ne ta gani, da wannan shawarar ta koma ɗaki ta cire uniform ta yi shirin zuwa gidan su Fatima, sai dai ga mamakin ta ranar Mom ƙememe taƙi fita ko bakin get har wurin sha ɗayar rana, kamar tasan abin da take ƙullawa, gajiya tayi ta miƙe taje ɗakin ta, a kwance ta sameta bata da alamar fita, zama ta yi a bikin bed ta ce "Mom yau baza ki je aiki ba ne." kallon ta tayi kafin ta amsa da "Yes daughter yau na ɗauki excuse zan huta sai on Monday." har ranta bata ji daɗin wannan lamari ba don ta sani in dai ba yau ba to bata da damar fita daga gidan sai ran monday, ita kuma bata jin zata iya jurewa har zuwa ranar ba tare da ta saka Fatima a idanunta ba, haka ta bar ɗakin Mom jiki a sanyaye, ranar haka ta wuni sukuku duk ranta babu daɗi.
Kamar yadda Fatima ta ƙudiri aniyar zuwa gidansu Joy yau, bata yi ƙasa a gwiwa ba, la'asar nayi tayi shirinta na hadda, cikin dogon zumbulelen hijabi ta ruwan toka, ko jiran Ummi ta shafa addu'a suyi sallama da kyau bata yi haka bata biya gidan su Amira su jera da yara gidan kamar yadda suka saba jerawa ba ta wuce.
Direct haryar gidan ta kama tana sauri don kar ta ci karo da idon sani.Sai da ta tsaya a gaban tangamemen get ɗin gidan sannan gabanta ya fara faɗuwa take wani irin tsoro ya shige ta, tsoron mahaifiyar Joy , sau ɗaya rak ta taɓa ganin matar wata rana an tashe su school, tun daga irin kallo ɗaya data mata tsoronta ya ɗarsu a ranta, sai dai bata jin duk da haka zata iya komawa batare da ta san halin da Joy ke ciki ba don ta tabbata baza ta iya rintswaba idan hakan ta kasance.
Ta fi minti goma kafin ta daure ta miƙa hannu tayi knocking ɗin ƙaramin kofar get ɗin a hankali, bata zata za'a jiyota ba balle har a buɗe mata sai dai ga mamakinta taga an buɗe get ɗin wani baba iyamuri da ko zo in kasheka da hausa bai sani ba ya leƙo. Suna haɗa ido gaban ta ya faɗi amma ganin ya sakar mata murmushi, yasa taji hankalinta ya ɗan ƙwanta, cikin harshen nasara daya caƙude da yaren igbo ya ce "My daughter who ar u looking." da sauri itama cikin harshe da ya mata magana ta ce "I'm looking 4 Joy, ni ƙawarta ce naga kwana biyu bata zo school bane shi ne nazo in dubata ko lafiya." ɗan jim ya yi kafin ya ce "kom in." tare da buɗe mata ƙaramin get ɗin, jiki a saɓule ta bi bayanshi gabanta na dakan uku uku.
Gurin zama ya nuna mata daga gefe, ya ce ta jira shi ya na zuwa yama Joy ɗin magana, idan ya shiga wa za'a ce mata, ta ce "Fatima Husain." "Ok." ya amsa mata tare da ficewa.
Farfajiyar gidan Fatima ta shiga bi da kallo, bata taɓa shigowa gidan ba sai yau, take ta ji ta raina kanta, ashe girman gidan da tsaruwar shi daga waje duk shafan mai ne akan cikin, baƙauyiya tukuf ta koma tana bin ko'ina da kallo baki sake , tare da tunanin wani irin dukiya mahaifin Joy ke da shi haka, manyan motocin dake fake a parking lot ta ringa kallo tana al'ajabin yanzu duk wannan na mutum guda ne.
Get man direct entarance ɗin first plat na gidan ya nufa, tare da danna doorbell, dai dai lokacin Mom na zaune a main falon tana cin cake, tasowarta kenan daga barci yunwa ya korota ƙasa, ɗaya daga cikin hause maid na gidan waɗanda ke da zarafin shiga cikin part ɗin, ta kira ta ce ta duba wayake knock,dubowa tayi ta dawo ta sanar mata get man ne, umarni shigowa ta bashi, ya shigo ya zube a gabanta ya kwashi gaisuwa duk da ya girme mata nesa ba kusa ba don zai Iya haifarta ma, cike da fariya ta amsa, ya ce "Wata ce ta zo neman Joy yar school din su ce, ta ce sunan ta Fatima Husain wai taga kwana biyu batta zo school ba shine ta zo ta gani ko tana lafiya." Bata rai tayi tare da hade girar sama da ta kasa, ko bata tambaya ba tasan wannan tsinanniyar Muslim girl din ne dake shirin warware mata aiki, wato har abin bai tsaya Iya school ba shine har gida zata biyo ta, aiko zata ci ubanta yau sai ta gwammace kida da karatu a fusace ta mike ba tare da bi ta kan get man ba ta fice daga plat din, bayanta ya biyo da sauri yana tambayarta ko lafiya, Bata saurare shi ba, ta wuce kamar kububuwaa'aikan gidan tuni kowa ya shiga taitayin shi suka bits da kallo, a zaune ta tarar da Fatima in da get man yace ta zauna ta shagala da ka kallon flawers bata san karasowar Mom ba sai dai ta ji saukar gigitacen mari a kumatunta, a firgice ta mike tsaye, tare da sauke idanunta akan mahaifiyar Joy take gabanta ya yanke ya fadi, firgici da tsoro suna bayyana karara a fuskarta, shakar wuyar hijabinta Mom tayi cikin zare ido ta ce "Me ya kawo ki gidan na, Me kike nema a gidan nan,menene tsakanin ki da yata, abin naki har ya wuce school shine kika biyota har gida ko, ina da labarin komai akan gurbata mata tarbiya da kike yi da canza mata akida, to ina miki warning da babbar murya daga yau sai yau na miki tsakani da Joy babu ke babu ita, ba a gida ba, ba a makaranta ba, ki rabu da ita kar ki sake kulata idan kuma ba haka ba na miki alkawarin sai na batar dake a garin na daga ke har zuri'ar Ku gaba daya." Daga haka ta shiga janta keee kamar kayan wanki ta nufi get da ita.
Hayaniyar Mom yasa Joy dake kwance a dakin ta cike da damuwan rashin damun famar zuwa gafan su Fatima saurin mikewal ta daga labulen window tare da lekawa idanunta ya saka a kan Mom rike da wuyan Fatima tana ja, gabanta ne ya yanke ya fadi, da wani irin mugun gudu ta nufo downstairs tana tsallakewa bibiyu ba tare da ta kula ba, tun daga bakin kofar part din ta shiga ce wa "Stop Mom Stop Stop please." Amma ina bata jita ba, ta bude get din tare da hankada Fatima wacce tuni ta fice a hayyacinta Wuyan hijabinta ya yage ya zame kasa, dankwalinta ya fadi kasa gashin kanta ya bayyana waje. Wani irin hankada ta mata mai mugun karfi da biyu niyarta ta tura ta bige da palwayan dake kofar gidan irin na kasan nan, sai dai kawai tajita caraf jikin mutum, wanda ya diro kamar daga sama, dai dai time din Joy ta iso wajen su a guje tare da rike hannun Mom tana kuka..... [12/29, 2:33 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀