PAGE 13
Yana shiga zaure ya a daddafe ya bud'e d'akin shi ya fad'a, bakin katifa ya laluba ya zauna yana sauke numfashi a wahalce. Ya rab! Wannan wace irin masifa ce ke neman yi wa rayuwarsa karan tsaye. Meke shirin faruwa ne? Bai ta6a jin irin wannan yanayin ba don ya shaki wani abu makamancin turare, Ras! Gaban shi ya fad'i, kar dai ace maganar doctor ne ya tabbata, kar dai ace matakin ciwon shi ne ya k'ara daga stage two zuwa four kamar yadda doctor ya sanar ma shi ce wa hakan na iya faruwa a ko wani lokaci matukar bai d'auki matakin da ya da ce ba. Innalillahi wainnailaihi rajiun! Ba ya fatan ace haka ne, sai dai kuma a kullum lamarin k'ara gaba ya ke. Shi mutum ne mai matuk'ar tsantseni da kiyaye addininsa hadi da dokokin ubangijinsa, tun da ya fahimci lalurar shi, ya kiyayi kanshi da mu'amalantar duk wata d'iya mace, matukar ba muharraman sa biyu ba. Fatima da Ummi. Yana tsoron wata rana ya kasa rike kan shi, yana tsoron wata rana ya kasa controlling kan shi, shin ina mafita? Ya yi zama kusan na awa biyu a d'aki yana sak'awa da kwancewa, batare da yasan lokaci ya ja haka ba, k'arshe ya yanke shawaran zai kai ma doctor ziyara gobe kamar yadda ya ce mashi matukar ya fahimci wani sauyi daga matakin ciwon nashi yayi hanzarin zuwa don a san matakin da za'a dauka a kai. Karar shigowar message wayar shi ya ankarar da shi nisan zangon da yayi cikin tunani, da sauri ya zabura ya mik'e tare da yiyowa cikin gida.
Hankalin Ummi da Fatima ya ta shi kwarai ganin har goma ta gota Al'ameen bai dawo ba, abin da bai saba yi ba, sun shiga damuwa sosai da tunanin ko wani Abu ya same shi ne, ko ya yi hatsari ko makamancin haka, babu irin tunanin da bai zo masu ba a rai ba. Suna nan zaune jigum² kamar masu zaman makoki, ya yi sallama, da gudu Fatima ta mike ta fada jikin shi tare da sakin kukan da take ta son yi tun dazu Ummi na hana ta, Ummi kam wani wawan ajiyar zuciya ta sauke a ranta ta shiga jero hamdala ga Ubangiji.
A dan rud'e ya ce "Subhanallahi! Yar gidan Yaya Ameen menene haka meya faru?" Cikin shagwa6a ta ce "Yaya me yasa baka dawo da wuri ba yau ka dade duk hankalin mu ya tashi.muna ta tunanin ko wani Abu ne ya same ka" Ya ce cikin kulawa "Ya isa haka kanwata share hawayenki babu abin da ya samu Yayanki wani dan uziri ne ya rike ni." Ta ce "To dan Allah yayana idan uziri ya sameke ka ringa sanar mana ko ta wayar yaya Amira ce, zan amso maka lambarta, tunda wayar Ummi ya lalace." Ya ce "To shikenan zan ringa gaya muku daga yau insha Allah." Ya karashe maganar yana share mata hawaye.
Basu yi zaman tsakar gida ba ranar saboda yanayin da yake ciki kuma already dare yayi, abincin shi kawai ya karba ya koma d'aki, suma suka shige nasu dakin suka kwanta.
Bayan ya ci abinci, ya mike ya canza kayan shi zuwa T-shirt da dogon wandon jeans ya nufo katifarsa zai haye, ji yayi ya taka abu kamar takarda, da sauri ya kai duban shi kasa, lettern Joy ne, samun kan shi yayi da faduwar gaba, wanda ya rasa musabbabinsa, tsurawa takardan ido yayi na sakanni kafin ya tsuguna ya dauka, hawaa katifarsa yayi ya kwanta, sannan ya sauke duban shi kan rubutun, a hankali ya fara karanta abinda wasikar ya kunsa.
Kalaman sunyi matukar daukar hankalin shi, bai san sanda murmushi ya subuce mishi ba, karantawa yake yi yana sake maimaitawa a zuciyar shi, matuka gaya abin ya kayatar da shi, sai dai bai wani basu mahimmanci ba saboda Sanin daga hannun wanda suka fito, ajiyewa yayi da nufin ya kwanta, sai dai zuciyar shi taki bashi wannan damar, ta ci gaba da kwadaita mishi son kallon kayataccen drowning din jiki, da kyar ya dake yayi fatali da bukatarta ya samu yayi wurgi da pepan ya rintse ido, take kuma damuwar matsalan ciwon shi ya dawo ma shi, ranar rana dare ya yi bai san sanda barci yayi a won gaba da shi ba.
Washegari, da wurwuri ya shirya ya fice daga gidan bayan yayi sallama da su Ummi akan ya tafi school, sai dai yana fita ya dauki hanyar, S Alto special hospital, duk da sammakon da yayi sai da ya tarar da layi, zama ya yi a waiting area har layi ya iso kan shi, a hankali ya tura office din doctor ya shiga, kamar kullum kyakyawan matashin likitan wanda a kalla zai kai shekara talatin da takwas da haihuwa ya dago ya zubawa Al'ameen idanun shi dake sanye da farin glass kur kamar zai cinye shi da idanu, hannun da Al'ameen ya mika mishi ya dawo da shi hayyacinsa, hannun ya mika mishi sukayi musabaha, tare da nuna ma mishi wajen zama, zama Al'ameen ya yi a kujerar dake facing din *Dr Abdul Hafiz S Alto* Dr da har lokacin idanun shi na kan Al'ameen ya ce " Muhammadul-Ameen Husain ko?" Al'ameen ya gyada kai yana murmushi, Dr ya ce "Sai yau ka waiwayeni ko? To ya jikin naka, dama nasan zaka dawo ai domin wannan matakin daka za6a ba mai bullewa bane." Al'ameen Ya ce " Kayi hakuri Dr ba laifi na bane na gayaka tun farko a kwai nauyi a kaina bazan Iya hada taura biyu ba, jiki kuma sai godiyar ubangiji." Gyada Dr ya ce ya ce "well! yanzu meke tafe da kai?" Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya kwashe abin da yaji jiya game da shakar kamshin turaren Amira da ya yi, ya d'aura da "Na ji tsoro sosai Dr kar ace matakin ciwon nan ya kara karfi a jikina kamar yadda ka fada zai iya faruwa, Dr I can't hold my self idan abin ya fi haka, bazan Iya ba I'm so scare." Dr dake kallon shi tun dazu ya ce "Then ka yi AURE mana Al'ameen shekarun ka sun kai ai, U ar 25 years by now." Da sauri Al'ameen ya dago ya zuba mishi idanu, Dr ya daura da "Tun a baya na sha fada ma ka dat is d only solution of ur prlm. Duk wani tablet ko injection da zan baka,bazai taba zama total solution a gareka ba, sai ma ya janyo maka wata illar ta dabam, halittanka ne a hakan, wanda ya hade maka da lalura, a halin yanzu abin ya taka mataki na gaba ajikin ka, wanda idan ka bari ya kuma karawa gaba daga haka, to tabbas komai zai Iya faruwa ina tabbatar maka da bazaka iya controlling kanka ba." Kamar zaiyi kuka ya ce "Dr ka taimaka min bazan Iya rike mace a halin da nake ciki a yanzu ba, bani da wannan karfin a kwai nauyi a kaina ni maraya ne."kallon shi Dr S Alto yakeyi cike da nazari, "pls Dr dan Allah ka taimaka min." Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce , "Naji zan taimaka maka amma kafin nan, kamar kullum yauma ina son sanin who ar u Muhammadul-Ameen." Kallon shi cikin ido Al'ameen yayi ya e "Bazan gaji da gaya maka cewa ni mayara bane. Bayan hakan bansan komai a kaina ba." Dr ya gyada kai cike da nazari ya ce " For now ka koma ka ci gaba da amfani da wannan tablet din, idan abin yayi tsamari dole akwai wani injection da zan maka, wanda kuma yin shi is very risk ga lafiyar mazan takar ka, idan akayi either a dace kokuma a ta6e." Godiya Al'ameen yayi mishi gwiwa a sage ya mike ya nufi barin office din, har ya kama handle Dr S Alto ya kira sunan shi, jiyowa ya kalle shi ba tare da ya amsa ba, Dr yaci gaba da cewa "Kayi tunani sosai akan shawarata AURE shine magananin matsalar ka, kaje duk abin da ka yanke ta waiwayeni." Murmushin yayi ya fice ba tare da ya amsa ba.
Da kallo Dr Abdul Hafiz S Alto ya bi bayan shi har ya kule, ajiyar zuciya ya sauke zuciyar shi cike da wani irin yanayin mai wuyar fahimta, ganin yana shirin shiga wani yanayi yasa ya ba next patient damar shigowa don ci gaba da aikin shi.
Cike da wani irin damuwa ya fito daga asibitin, tafe yake akan hanya amma kwata kwata baya cikin natsuwar sa jefa kafa yake yi kawai duk inda ya samu ba tare da ya ankare ba, kamar wani karatu haka ya rin ga maimaita Kalmar AURE a zuciyar shi, gaba daya kalaman Dr sun rikita shi har yana neman rasa nutsuwar sa, shin ta ina zai fara jajibo aure a halin yanzu? Shin wa ma zai aura, da wani ido zai Iya fuskantar Ummi ya gaya mata zai yi aure bayan bata da masaniya akan larurar shi, kai ina impossible, yana bukatar shawarata, lallai yana bukatar shawarata da gaggawa, wa zai fadawa matsalar shi ya bashi shawara, Aliyu! Aliyu ne ya fado mai a rai, a fili ya furta "Yesss! Aliyu ne." Daga nan direct gidan su Aliyu ya nufa, ba tare da sanin yana gidan ko baya nan ba.
********
Joy kwana tayi rungume da takardan da AL'AMEEN ya bayar aka kawo mata a matsayin Fatima ce ta bayar, wani irin magadisu ne a cikin takardan dake janta kamar magnet, ta rasa dalili ta rasa dan mafari, sai kawai ta dangata hakan da kasancewar takardar ya fito daga hannu Fatima ne. Ta ki yarda ta baiwar zuciyar ta damar cewa rubutun Al'ameen ne bana Fatima ba, hasalima duk sanda tayi wanan hasashen gabanta faduwa yake yi.........
Wallahi Ku ringa comment ko kuma sai na bari labari ya dakko dadi Ku nemi sama da kasa Ku rasa, kun san dai halin , hayyaratata in ji me mata tara😬
Me bukatar shiga group ya tuntubeni ta wannan lambar amma in kinsman idan kin shigo baza ki ringa comment ba karki fara yi min magana *** [12/29, 2:35 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀