JOY

PAGE 14

by @aishanalado88

Ban yi Editing ba🙏

Daga hospital kai tsaye Al'ameen gidan su Aliyu ya nufa, yaro ya samu ya aika cikin gidan kiran shi, sannan ya lalubi dakalin kofar gidan ya zauna, babu jimawa yaron ya dawo ya ce "Wai an ce Aliyu baya nan yayi tafiya." Jim Al'ameen yayi, kafin ya amsawa yaron da "Ok nagode." Agogon hannun shi ya kalla, sha biyu saura, ya san kafin ma ya isa school yanzu an gama lecture yau, kuma baya jin zai iya fita aiki a halin da yake ciki yanzu don haka kawai ya kamo hanyar gida.

Kamar yadda ya zama wa Amira jiki cikin yan kwanankin nan kusan kullum sai ta shiga gidansu Al'ameen , yau ma cike da zakuwa ta shiga fuskarta dauke da madaukakin farin ciki. Jiya da dare dakyar barci ya dauke ta saboda farin cikin Yaya Ameen ya amince zai ringa koya mata karatu, ko babu komai zata samu lokaci ta ke6e da shi, zata samu wani dama wanda kuma ta daukar wa kanta alkawari iya wuya zata yi amfani da shi, zata yi kokarin fahimtar da shi halin da zuciyar ta ke ciki game da shi, ta hanyar kissa irin ta diya mace idan ta kama zata iya kauda zara ta kauda wata ta bude baki ta furta mashi kalmar so, domin kuwa ita kadai ta san irin azabtuwar da zuciyar ta ke yi akan shi.

Tana tsaka da jan ruwa a rijiya, ta cire hijabinta ta rataye a igiyar shanya, kasancewar gidan su biyu ne ita da Fatima Ummi bata nan, ya shigo bakin shi dauke da siririyar sallama, gabanta ne yayi wani irin faduwa jikinta ta bi da kallo sanye take da riga da skirt na atamfa dinkin zamani abinka da budurwa ta yi das da ita kanta babu adiko kananan kitsonta a bayyane, wani irin kunya ne ya lullubeta, ga shi ta riga ta zura guga a rijiya,ji tayi kamar ta saki gugan sai dai ta daure ta, dukar da kanta kasa tare da amsa mashi sallamar da yayi cikin dan rawar murya, kallo daya ya yi mata da dauke kanshi, yana amsa gaisuwar da ta mishi da " Lafiya." Ya wuce ta zuwa dakin Ummi, Fatima na kwance ta na game da wayar Amira, ta ji sallama, amsawa tayi da sauri tana mikewa zaune, ya shigo akan wayar hannunta idanun shi suka sauka, zama yayi akan kujera daya tal dake falon 2 sitter, cike dan in'ina ta ce "Yaya sannu da dawowa." Bai amsa mata ba sa cewa da yayi "Wayar wa ye a hannunki." Ta ce "Na Anty Amira ne." Ya ce "Ki kai mata abinta ki ce na ce ta rufe gashin ta." Da to ta amsa tare da mikewa ta fice, wayam ta Tatar da tsakar gidan babu Amira babu mai kama da ita, da mamaki ta shiga kiran sunanta amma shiru, hakan ya tabbatar ma Fatima bata cikin gidan. Dawoqa tayi da wayar a hannu ta ce "Yaya ban ganta a tsakar gida ba ganin ta wuce." Ba tare da wani damuwa ko daukar lamarin da muhimmanci na ya ce "Ki kai mata gidansu, kuma kar na kuma ganin ki da wayar wani, idan lokacin ki rike wata yayi ni dakaina zan siyo miki." Ta amsa da "To Yaya." Tana zura hijabinta a jiki, har ta kai bakin kofa ya ce "Ummi fa? Ko ta kwanta ne." Juyowa tayi a sanyaye ta ce bata nan da mamaki a fuskarsa ya ce "Ba ta nan?." Ta ce "Eh." "Ina ta je." Ta ce "Bata fada min ba." Ya ce "ya ce ok je ki kai wayar ki dawo." Ta amsa da to ta fi ce.

Da sallama Fatima ta shiga gidansu Amira, da sauri Amira da ke zaune a tsakar gida ta rafka tagumi ta mike tsaye, Fatima ta karaso ta ce "Anty Amira sai kika wuce babu sanarwa, Yaya ya ce na kawo miki wayar ki kuma ya ce na gaya miki ki ringa daura dankwali." Wani irin zaro ido da tayi sai da abin ya ba Fatima dariya, ta ce "Da gaske haka ya ce Fatima?" Fatima na mata dariya ta ce "Wallahi haka ya ce." Amira ta ce "Na shiga uku." Ba tare da tasan ta furta ba duk ta bi ta ruda kanta, Fatima cikin dariya ta ce "Wallahi ke babbar matsoraciya Anty Amira." Ta ce " Hmmm! Baza ki gane bane Fatima, wallahi naji kunya sosai yadda Yaya Ameen ya tarar da ni daga ni sai Riga da skirt babu ko dan kwali wallahi kamar na nutse a kasa saboda kunya, sai naga ma kamar ya harareni" Sa ke kwashewa da dariya Fatima ta yi ta ce "Bari na je na gayawa Yayana wagga batu." Da sauri ta juya zata fi ce, Amira tayi wuf ta rikota, cikin yanayin tsoro ta ce "Dan girman Allah Fatima kar ki gaya mishi." Fatima ta ce "To sakeni Anty Amira bazan fada ba." Ta ce. "Ki rantse." Sai da Fatima ta mata rantsuwa sannan ta saketa tana sauke ajiyar zuciya kamar wacce ta yi gudu, cike da al'ajabi Fatima ta fito gidan ta shige nasu, koda ta koma Al'ameen ya fice data dakin su alamar ya tafi nasa ganin haka ta gane baya son hayaniya don tafi kowa fahimtar shi, bata nemi shi ba ta shiga kitchen ta daura musu sanwar rana kamar yadda Ummi ta bar mata sallahu.

*********

Karfe biyar dai dai Dr Abdul Hafiz S Alto ya danna hancin motar shi cikin kyayataccen compound din gidan sa dake unguwar Brighter, bayan parking kai tsaye ya nufi asalin cikin gidan, da sallama dauke a bakin shi, da sauri yan yaran da ke zaune a falo suka kwaso da gudu suna ga Daddy ga Daddy, Daddy oyoyoo Daddy oyoyoo, suka rungume shi, jin hayaniyar su ya fito da matar gidan daga kitchen, matashiya ce mai kimanin shekaru 28 zuwa 30 fara tass da ita kyakkyawa, da fara'a ta karaso ta na mishi sannu sa zuwa, tare da dan runguma,yana murmushi, ya amsa mata da "Uwar gida ran gida, yaya gida ya yara." Ta ce "Gida da yara lafiya kalau sai hamdala." Zame hannun shi yayi daga cikin na karamin yaron shi ke kimanin shekaru biyu, ya ce "Aboki bari na watsa ruwa na dawo ko." Yaron ya gyada kai yana murmushi, daga nan yayi dakin shi, matar shi ta rufa mishi baya, ruwan wanka ta hada mishi kafin ta dawo ta taya shi rage kaya ya shige toilet don ya watsa ruwa. Minti goma ya kwashe kafin ya fito sanye da rigar wanka, bata dakin bai damu ba don yasan kila tana wani uzirin ne, shiryawa ya shiga yi cikin kananan kaya, yana gama shiryawa ta shigo da sauri ta, tana ganin haka tace "Oh shirt! Kayi hakuri wallahi Ina kitchen ne ban gama hada dinner ba shi yasa na barka." Murmushi yayi yace "Babu komai ai na gama." Ta ce "Nasan halinka yanzu zaka baza kaci abinci ba ka riga kaci abinci a hospital, amma duk da haka bari na kawo naka dan abin tabawa." Fita ta yi jim kadan ta shigo dauke da tray da jug cake ne da pineapple juice da ta hada mishi da kanta ta jawo center table ta daura mishi, godiya ya mata ya zauna ya shiga ci, ita kuma ta bashi hakuri ta sake ficewa kitchen, bayan ya gama ya dauki tissue ya goge baki, mikewa yayi daga gaban table din, ya koma bakin bed ya zauna, wayar shi ya dauka, ya lalubo wata international number da yayi serving da suna Hayatudden Aboki. Sai da ya kalli agogon bangon dakin ganin biyar da arba'in, ya tabbatar inda zaiyi kiran yanzu dare ne a wajen su amma haka ya daure ya yi dialling, lambar yayi ringing sosai kamar baza a daga ba can kuma lucky yaji anyi picking, daga can bangaren aka yi sallama da wata irin nutsattsatsiyar murya, kafin a daura da "He'll Aboki." Murmushi Dr Abdul yayi kafin ya amsa sallamar ya daura da cewa "Hi Aboki." Kamar yadda Abokin nashi ya fada, duk murmushi suka yi, kafin su shiga gaisawa da tambayar lafiyar juna, bayan sun gama suka dan taba hira irin ta amintattun abokai, daga nan kuma, Barrister Hayatudden ya ce "How about d boy, ya sake zuwa." Dr Abdul ya ce "Yes ya sake dazu shi yasa ma na kiraka." Cike da wani irin karsashi Barrister Hayat ya ce "Me ya kawo shi? Me ya ce maka? Yaya matakin ciwon shi zuwa yanzu? Ya fada maka shi wanene? Su waye iyayensa." Dr Abdul ya ce "Easy mana aboki, wadannan irin tambayoyi haka a jere, koda yake ba wani Abu bane tunda da cikakken lawya me zaman kansa nake magana." Barrister Hayat ya katse shi da cewa "All, aboki, duka tambayoyin nake bukatar amsarsu daga gareka."............

Ayi hakuri da wannan, yau bani da naji sosai🙏 masu comment ngd sosai na gani kuma na yaba much luv 2 u ppl all INA yinku irin totally. Da iya masu comment kadai fa nake yi atoh!

Ga masu bukatar shiga group. *** [12/29, 2:36 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀

~FARHAT~