JOY

PAGE 19

by @aishanalado88

Washegari Monday da shirin school ta tashi hakan ne ya d'an d'auke mata hankali daga tunanin Yaya Ameen data kwana yi, jiki a sanyaye ta gama shiryawa, sai kuma ta nema waje ta zauna ta rafka tagumi, ta yaya zata je ta zauna ta zana jarabawa ita kad'ai ba tare da Fatima ba? ta ina zata fara? Me zata rubuta? Ko dai ta je gidan su ne, wata zuciyar ta bata shawara, yayinda wata zuciyar ta hane ta da aikata hakan. A karshe hankalin ta yafi karkata akan ta bari idan sun yi closing ta je, Haka tayi ta zaman gawon shanu har na kusan 30 minutes ba tare da ta ankara ba.

Ringing d'in wayar ta ne ya dawo da ita hayyacinta, da kyar ta mik'e ta isa ma'ajiyar wayar, sunan Mom ta gani yana yawo a fuskar wayar, gabanta ne ya yanke ya fad'i, tunda Mom ta wuce basu yi waya ba.

Jiki a matukar sanyaye ta kara wayar a kunne ta ce "Gud morning Mom." Daga daya 6angaren Mom dake cikin matsananin tashin hankali ta ce "Morning." A dak'ile ta d'aura da "Thank u 4 what u did, nagode sosai kin nunwa duniya ban isa dake ba, na ce karki je ko ina amma sai da kika fita saboda ke mai kunnen k'ashi ne, to baki isa ba, kin yi karya, kin yi kad'an, ni na haifeki ba ke kika haifeni ba don haka baki isa ki juyani, kuma zan nuna miki." Cikin rawar murya ta ce "Kiyi hakuri Mom " Mom ta ce "No don't sorry me, sorry 4 ur self akwai ranar karbar result yana nan tafe. Kuma me kike yi a gida har yanzu, ko ba yaune kika ce zaku fara test ba?" A sanyaye ta ce "Yau ne." "To zaman me kike yi?" "Kiyi hakuri mom na shirya yanzu zan wuce." "Da kyau, ki fita waje driver na nan da zai kai ku kuma zai jira har ku tashi ya dauko ku, idan ki ga dama kar ki bishi,Duk abinda kika yi zan samu labari." Kit ta kashe wayar ta. Wayar ta bi da kallo kafin ta ce "Zai kai mu ni da wa?" Bata da mai bata wannan amsar hakan yasa ta saki ajiyar zuciya a bayyane ta ce "kiyi hakuri Mom ba yin kaina ba ne." Jiki a sanyaye ta jawo jakarta ta sakko downstairs, babu kowa a main parlour, ko kallon 6angaren dining bata yi ba don bata jin zata iya saka koda ruwa ne a cikin ta a halin yanzu.

Tana fitowa compound idanunta ya sauka akan wata bak'uwar mota fake a gaban plat din Mom daf da kofa, bata gama mamakin su wanene a ciki ba aka bude kofar motar, David ne ya fito sanye da uniform d'in shi irin nata fuskarshi dauke da murmushin mugunta, kafin ta gama mamaki aka bud'e d'aya 6agaren mahaifiyar shi ce ta fito Mrs Esther fuskarta a had'e kamar hadarin gabas! cikin wani irin takun isa da tak'ama ta iso gaban Joy, kallon sama da k'asa ta mata kafin a gadarance ta nuna mata motar data fito, da hannu ta mata alamar ta shiga.

Sai lokacin ta fahimci jam'in da Mom keyi d'azu wata ita da David za'a kai school tare me hakan ke nufa? Kar sai Mom Anty Esther ta fito ta zaua da ita kafin su dawo da kuma ta shiga ukunta.

Sai da ta hadiyi wani busassshen yawu kafin, ta kimkimi jakarta jiki a sanyaye ta nufi motar ta bud'e baya ta shiga, David dake tsaye shima ya bud'e inda ya fito ya koma ya zauna, driver yayi ribas ya fice daga gidan.

A rayuwarta tana matukar tsoron Anty Esther, macece masifaffiya ta karshe, uwa uba kuma bata kaunarta ko miskala zarratin, tun bata mallaki hankalin kanta ba ta fahimci hakan, ko kadan jininsu bai hadu ba.

Bata san school ba sai da ta ji k'arar bud'e kofa David, dagowa tayi yana tsaye daga jikin windon suna had'a ido ya d'age mata gira tare da sakar mata murmushin keta ya ce "Muje ko." Harara ta watsa mai kafin ta 6alle murfin motar ta fito a fusace ta nufi cikin school ba tare data kula shi ba, tana jin shi yana biye da ita yana fito kasa-kasa.

Ko a class kasa concentrating ta yi akan abin da ke gabanta, tana kallon sauran student na d'aukan notebooks din su suna dubawa kafin shigowar invigilator, amma ita ko kwakkwaran motsi ta kasa, har zuwa lokacin da aka shigo yi musu first paper wanda English ne, bayan suna babu abinda ta iya rubutawa a script dinta, ajiyewa tayi akan desk ta rafka tagumi, ta fada komar tunani, rintse idanu tayi take kyakkyawar fuskarsa ya shiga yi mata gizo, komai nashi na dawo nata dallah-dallah, especially moment din su na jiya a tare.

Bata san iya adadin time din data kwashe ba sai sai ta ji ana cewa everybody submint, tana kallo aka d'auke script din ta ba tare da ta iya rubuta koda kalma d'aya ba.

Koda suka fita break kasa fita tayi, kwanciya ta yi kan desk, duk da irin yunwar dake nukurkusarta.

A haka har lokacin second paper yayi, shima dai kamarna farkon babu abinda ta tsinana, da ta kai hannu ma sai ta samu kanta da yin drowning din hearts da arrow ba tare da ta farga ba, a haka lokaci ya tafi, ta yi submit ba tare da ta goge ba.

Kasancewar suna test sha biyu suka ta shi, ga mamakin ta David ta ga yazo ya tsaya akanta, a hasale ta ce "what?" Yayi murmushinsa dake kular da ita tare da cewa "Nothing, just let's go." Tsoron Anty Esther ne kawai yasa ta bi bayan shi suka wuce, kamar kuwa yadda Mom ta fad'a a bakin get suka tarar da driver'n daya kawo su yana jiran su, kai tsaye gida ya wuto da su ba tare da ta samu damar zuwa gidan su Fatima ba kamar yadda ta tsara.

Cike da fargaba ta bi bayan David suka shiga plat din Mom, a hakimce ta tarar da Anty Esther a falo kafa daya kan daya, ta tara duk ma'aikata gidan a gabanta, ko me take gaya musu oho! A haka suka karasa ciki David dake gaba ya ce "Good afternoon Mama." Ta amsa da "Fine Son kun dawo." Ya ce "Yes Mama." Tare da neman waje gefenta ya zauna yayi balance kamar gidan uban shi. Idanunta ta dawo da shi kan Joy, ta shiga binta da wani shegen kallo mai cike da tsana.

Jikinta ne ya d'an dauki rawa lokacin da sukayi hada idanu rasa abin yi yasa ta samu kanta da maimaita abin da ta ji David ya fada ita ma, a d'arare ta ce "Good afternoon Anty." Harara ta watsa mata kafin ta ce "Afternoon." A dakile daga haka bata kara ce mata komai ba sai tsarabar hahara.

Ganin haka a sukwane ta kimkimi school bag din ta, ta haura dakinta.

Tana shiga ta yi wurgi da jakar, ta fada gado ta fashe da kuka, wata zuciyar ce ta mata, "yanzu haka zaki zauna wannan matar ta yi ta mulkarki a cikin gidanku gidan mahaifinki. Impossible!" Zabura ta yi da nufin ta dauki wayarta ta kira Papa sai dai wayam babu wayar a ma'ajiyarta babu dalilinta, sake fashewa ta yi da sani sabon kukan, ko bata tambaya tasan Anty Esther ce ta daukar mata waya, dan kuwa babu mai ikon shigar mata daki cikin ma'aikan gidan matukar ba ita ta bukaci hakan. Zamewa tayi kasan tiles ta jingina da bed din ta tana matsar kwallah.

Tsawar da Anty Esther ta daka mata aka ne, yasa ta mikewa a firgice, cike da masifa ta ce "Kukan uban me kike yi, iye nace kukan Uban me kike yi." Cikin son hadiye kukanta ta ce "Kiyi hakuri Anty." "Rufe min baki munafuka kin zo kin zauna kina kuka saboda tsabar sangarta da fitsara kamar wacce aka daka ko aka zaga, maza ki cire wadan nan kayan ki fito ki yi lunch."

Tana tsaye a kanta ta cire uniform ta sauya na gida, daga haka ta tasata a gaba zuwa dining, dinning din shake da abinci kamar wanda mutum goma zasu ci saboda almubazzaranci. Uban abinci tayi serving dinta tuli wanda tasan ya mata yawa, ta tasata a gaba wau sai ta cinye shi, tana ci tana kuka ita kuma tana antayata zagi, "Yarinya duk anbi an sangarta ki, kina yiwa mutane fitsara iri iri, babu tarbiya, to ni nan zan gyara miki zama kafin Mom dinki ta dawo." Da kayar ta iya cin rabin abinci, ta shiga kakarin amai, ganin haka yasa Anty Esther kyaleta, tana sharar kwallah ta mike zata wuce daki, hanata tafiya Esther tayi ta sakata ta zauna ta mata massage.

Ranar haka Joy ta wuni cikin wahala da zagi da tsamgwama daga wannan ta shiga wannan , ba ita ta samu kanta ba sai wajajen karfe goman dare, duk wannan wahalar da gajiyar da tayi tana samun hakarkarinta ta kasa tunanin Al'ameen ya mata sallama, Babu abin da yafi tsaya mata a rai irin kyakkyawar murmushi sa, ta tuna ranar da Fatima ke ce mata duk duniya babu wanda ya kai Yayanta iya murmushi, a she da gaske ne. Ta sake tuno daddadar muryar sa lokacin da yake ce mata "I'm sorry! Ban yi don na cutar dake ba." Murmushi ta yi tare da kai hannu ta shafi goshinta dai-dai gurin daya d'an kuje har yayi jini tana sahafawa tana murmushi, bata san iya tswon lokacin data kwashe a haka ba kafin barci barawo yayi gaba da ita...

***********

Masu bukatar shiga group na joy su tuntube ni kai tsaye .

*** [12/29, 2:38 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀

~FARHAT~

DAGA ALƘALAMIN👉 *AyshaNalado*

ƘARƘASHIN JAGORANCIN👉 *Mikiya Writers Association*