JOY

PAGE 45

by @aishanalado88

Mikiya Writer's Association

*Assalamu alaikum, barkanku da war haka yan uwa masoya masu kamshin Apple😍 Kamar yadda kuka sani sunana Aisha Nalado, marubuciyar littafin Joy. kwanakin baya kun ji shiru kamar Mallam ya ci shirwa😬 nasan wasunku sun san dalili wasunku kuma basu sani ba, ga wadan da basu sani ba, hakan ya faru ne saboda arzikin da Allah ya yi mini na samun k'aruwa, ina nufin Allah ya azurtani da haihuwa, shiyasa na dauki hutu, to Alhmdllh ina mai farin cikin sanar daku cewa na dawo, in sha Allah zamu daura daga inda muka tsaya da fatan za ku yi farin ciki da jin hakan.*

Sauke kai k'asa Ummi ta yi, kamar bazata kuma cewa komai ba.

Duk ido suka zuba mata falon ya d'auki shiru na y'an wasu mintoci, a hankali ta d'ago, idanunta cike taf da kwallah ta dube su, da wani irin murya mai sanyi wacce basu ta6a jin ta yi irin ta ba, ta fara cewa.

"Ni kaina bansan wacece ni ba, ban san daga wata duniyar na fito ba, ban san komai game da rayuwata ba abin da na sani kawai shine bani da galihu!" Ta kai karshen maganar cikin wani irin rauni, muryarta na rawa alamar kuka ke shirin kwace mata amma ta yi kokarin danne shi da karfi.

Shiru ta yi ta daga kai sama alamar tana tunano wani abu tare da kokari mayar da hawayen da ya ke daf da wanke mata fuska , ta dad'e a haka kafin ta kalle su ta ci gaba da cewa

Wata ranar Alhamis wacce bazan ta6a mantawa da ita ba, na bud'e ido na tsinci kaina a tare da ahlin gidan Mammam kura, bani da masaniyar abin da ya faru a lokacin domin bana cikin hayyacina amma ina da cikakken labari komai, don Al-husain ya sanar dani komai kafin ya bar duniya kamar haka:

Al-hussain Mammam kura shine wanda ya tsince ni a mararrabar dukko a hanyarsa ta dawowa daga kano zuwa cikin garin Minna.

A kallo d'aya baza a kira ni da mahaukaciya ba, saboda tsab na ke cikin shiga ta kamala ina janye da hannun yaro, wanda ke matukar galabaice ya yi kuka har ya gaji ya yi shiru. Yadda na ke tafiya ina tangad'i, kafafuna futu futu da k'ura ne zai tabbatar wa mutum bana cikin koshin lafiya, Allah kad'ai yasan daga duniyar da na ke.

A dai dai wannan lokacin hussain yayi fakin motarsa a dokar daji ya kewaya domin biyan bukatarsa, bayan ya kammala ya taso domin ci gaba da tafiyarsa. tun daga nisa ya hangi mace cikin tsananin galabaita da fitar hayyaci ta rafka karo da motarsa, "Subhanallahi! Ya ambata kafin ya karaso gare ni kuma yaga na zube kasa sharaf a gurin, daga yaron da na ke ja, da gudu ya 'karaso gurin cikin tashin hankali ya shiga waige waige, ganin babu mataimaki sai Allah yasa ya yi bismillah ya dauke ni ya saka a bayan mota bayan ya fara daga yaron dake kuka zuwa lokacin.

Asibiti mafi kusa ya kai ni, bayan samun taimakon gaggawa da nayi daga nurs, na farfado, sai dai babu um babu um um! sannan idanuna a juye suke tabbacin ba na cikin hayyacina, tambayar duniyar nan ya yi domin ya samu ya mayar da ni gidanmu amma babu bakin magana, ganin haka yasa Alhussain dauka cewa ma'aikatan asibitin ne basu san aikinsu ba, sai kawai ya nemi sallama, a ganinsa gara ya karasa da ni cikin gari ya kai ni babban Asibiti, babban likita ya duba ni.

Muna shiga cikin garin Minna direct general Hospital ya nufa da ni, na samu ganin babban likitan da ke kan aiki ya kuma rubuta mana test din da zamu je mu yi ciki harda na kwakwalwa don shima kansa a tunaninsa mahaukaciya ce.

Sai dai wani kudirar Ubangiji test din ya nuna lafiyar kwakwalwarta kalau, shi kansa a Alhussain bai za ci haka ba bare kuma likita, hakan yasa ya sake tura mu wani asibitin domin sake yin wani test din, nan ma dai kamar cen, aka sake tabbatar da komai normal, tun daga nan Alhussain ya d'iga wa lamarina Ayar tambaya, kwanana uku aka sallameni , har zuwa lokacin bana iya bude baki bare na furta wani kalma, idanuna a juye hasalima ban san a ina nake ba.

Ya yi matukar shiga damuwa ganin har an sallameni bai ji Daga gareni ba, bare yasan daga ina na fito maida ni gida, hakan yasa dole ya tunkari gidan iyayensa da ni, don ba ya jin zai iya rabuwa da ni a cikin wannan halin, a cewarsa bai san hannun da zan fada ba, bugu da kari haka kawai yeke jin wani feeling a zuciyarsa game da ni, uwa uba a cikin kwanaki ukun nan yayi wani irin mugun sabo da yaron da har zuwa lokacin ya kasa gazgata cewa nawa ne.

Tashin hankali gobarar gemu! An sha gwagwarmaya sosai a gidan marigayi Mamman kura, lokacin da Alhussain ya dawo musu da tsarabar tsintacciyar mahaukaciya kamar yadda suka rad'a min suna, duk bayanin da yayi musu sun ki gamsuwa karshe sai da rayuka da yawa suka baci, an kai ruwa rana sosai tsakaninsa da yan uwansa da kuma mahaifiyarsu kafin ya samu damar ajiyeni a gidan, kasancewar shima kafaffe ne na karshe kuma dai duk cikin yayan gidan shine mai dan abin hannu Allah ya yi masa nasibi, hakan yasa ake daga masa kafa wani lokacin.

Dakinsa dake cikin gidan ya saka ni yayinda shi kuma ya koma Zaure da kwana, babu mai shiga safgata a cikin gidan babu mai ba ni abinci babu mai kula da yarona idan Alhussain baya nan.

Cikin kwanaki goma Alhussain ya dage da neman min magani, inda ya dauko wani babban malami mai bada taimako ya zo har gida ya duba ni ta shin farko ya tabbatar da cewa bakin sihirine a jikina farrak'u ne mai karfi wanda karyewarsa zai yi bakar wahala, sai dai zai yi taimako dai dai gwargwadon iyawarsa da izinin Ubangiji.

Tabbas! Babu abin da ya gagari Allah,Mallam ya yi kokari sosai wajen ganin ya taimakawa min, aiki ya yi tukuru, sati daya cur ya kwashe yana gwagwarmaya , kafin Allah ya nufa na dawo cikin hayyacina, sosai Alhussai ya yi farin ciki da hakan , sai dai kuma da sauran rina a kaba don sam na kasa tuna rayuwarta ta baya, kwakwalwata ta dawo empty kamar dai ace wacce ta samu lost of memory.

An yi an yi na tino koda sunan garinmu ne abu ya gagara, ganin haka Mallam ya bada shawarar akan a bar wa Allah sauran lamarin a dage da addu'a, idan Allah ya nufa wata rana zata zo da da zan tuna ko ni wacece ko Daga ina nake ranar da har yau ba ta zo ba, ranar da nake tsumayen gani kafin Allah ya dau raina" ta dakata tare da share hawayen da sai a sannan ya yi nasarar zararowa daga idanunta.

Zuwa lokacin Fatima kuka take yi sosai kamar ran ta zai fita, Aliyu ma a fakaice ya ke dauke hawaye da handkerchief , ya yin da idanun Al'ameen suka rine jajur kamar an watsa masa barkonun tsidigu.

Dakewa Ummi ta yi ta ci gaba da cewa "Na yi rayuwa a gidan nan cikin mawuyacin hali, tamkar mujiya haka na kasance a wajen mutanen gidan wata irin zazzafan kiyayya suke nuna min, kanne Husain mata har daki suke biyo ni su daka wani lokacin harda uwarsu sannan su hanani kuka, ko kishi zai kashe ni babu mai bani ruwa a gidan bare abinci, aikin gidan karakaf ni ke yin shi, Al'ameen kuwa ba shi da ikon raban koda karen gidan ne bare yaran gidan, a bangare guda kuma Tanimu ya uzzirawa rayuwata, bibiyata ya ke yi ido rufe yake neman mutuncina amma na ki ba shi hadin kai, hakan yasa ya kara tsanata kasancewarsa babba a gidan ya yi amfani da wannan damar wajen kara rura wutar kiyayyar dake tsakanina da yan uwanshi, duk da haka bai barni ba ya sha biyo dare don yi min fyade Allah na tseratar dani daga sharrin sa.

Tsamgama da wulakancin da suke mini baya daga min hankali kamar yadda suke kiran Al'ameen shege dan zina ya ke daga min hankali, na kan shi ga mugun yanayi a duk sanda hakan ta kasance, dai dai da sekon daya ban taba ji a zuciyata cewa maganarsu gaskiya bane, duk da bazan iya tunawa ba, ina ji a gangar jii da zuciyata cewa shi jininane kuma shi dan halak ne ba shege ba..... [1/18, 12:39 PM] ***: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀

~FARHAT~

*BY*

*AYSHA NALADO*

*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*