JOY

PAGE 47

by @aishanalado88

A rana ta biyar Dr ya sallameni, bayan ya shimfid'a min dokoki, da abubuwan da zan kiyaye don gudun samun wata matsala.

Kaina ne ya 'kulle da jin irin jawaban da Dr ke min, Al-husain ya ce min Dr ya ce bani da ciki, yanzu ga Dr na min wasu irin maganganu da ba na wani fahimta sosai.

Har muka shiga mota nazarin maganganun Dr na ke yi, na yi nisa cikin tunani don banzan iya tantance a ina muke ba, tsayuwar motar ne ya sa na d'ago da kaina dake d'uke, ga mamkina ba gida muka iso ba, gefen hanya ce ya yi parking, kallon shi na yi, ya juyo ya fuskance ni sosai a nutse ya ce "Balkisu ki saurareni da kyau ki nutsu ki ba ni aron hankalinki za mu yi magana ne." Jin haka yasa na tattara duk wata nutsuwa da hankali da ke jikina na bayar gare shi, kamar yadda ya nema.

A nutse ya shiga warware min zare da abawa game da halin da nake ciki a yanzu.

Kaina ne ya shiga juyawa, duhu na neman mamaye ganina, jikina ya dauki rawa kamar mazari, na tabbata ba don a zaune nake ba babu abin da zai hanani fad'uwa, muryarsa na tsinta a kunnena yana fad'in "ki ambaci Allah Bakisu ki kira Ubangijinki" samun harshena na yi da maimaita Kalmar " Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun!" Ban san iya tsawon lokacin da na d'auka a haka ba, kafin na yi 'karfin halin d'agowa na kalle shi ido cikin ido abin da bai ta6a faruwa a tsakaninmu ba tun haduwarmu, cikin rawar murya na fara cewa " Shin wani laifi na yi wa Ubangiji ne Yaya Husain? wannan jarabawar ta yi tsauri a gare ni bazan iya cinye ta ba, ya Ubangiji gara ka kashe ni kawai na huta." "Kul Balkisu! Ki dawo cikin hayyacinki, idan hankali ya gushe da hankali ake nemo shi,Ubangiji ba abin wasa bane, bazai ta6a daurawa bawa abin da bazai iya ba, ki yi maza- maza ki tuba gare shi." Kalaman da suka ratsa kunnena kenan wadanda suka yi saurin maidoni kan mizanin hankalina da ya gushe, da sauri na shiga furta "Astagfirulla! Allah na tuba Astagfirullah!! Allah ka yafe min." Sai lokacin hawaye suka samu damar fara kwaranya daga idanuwa.

Sai da ya bari na yi kuka na sosai na gaji na koma sauke ajiyar zuciya, sannan ya fara rarrashina daga bisani ya daura sa yi min nasiha mai ratsa zuciya, wanda ya kashe dukkan wani laka dake jikina, ya nusar da ni yin imani da kowacce irin kaddarace ta tunkareni me kyau ko mara kyau matsawar ina son kasancewa cikakkiyar musulma mai cikakken imani, a karshe ya daura da tambayar "Shin kin amince za ki aureni Balkisu!"

Ummi ta kai karshen maganar tana mai ba hawayen da ke cike da kaurin idanunta daman silalowa kan fuskarta, tana mai tunano lokacin a ranta tare da hasko fuskar Al-husain d'inta a idanunta.

Da sauri Fatima ta tashi ta isa gareta ta fad'a jikinta tare da k'ara fashewa da wani sabon kukan da dama kan yi take.

Aliyu kam zamowa ya yi daga kan kujera ya zame hullan kan shi ya na kuka kashirban harda shesheka

Al'ameen kukan zuci ya ke yi wanda ya fi na zahiri ciwo.

Zame Fatima Ummi ta yi daga jikinta ta share hawaye da hijabin jikinta, ta ci gaba da cewa;

Ko mahaukaci ya san hallaci balle mai hankali, ta yaya zan iya kallon tsabar idon Yaya Husain in ce bazan auresa ba, sai dai ba a nan gizo ke sakar ba, Mahaifiyarsa da kuma yan uwansa na ke tsoro, hakan yasa na yi shiru na kasa ba shi amsa, sai zuciya ta daketa faman luguden dakan uku-uku.

Ganin na yi shiru ban ba shi amsa ba ya yi murmushi ya ce "Shiru ma amsa ce Balkisu, nasan baza ki ni ba, kuma nasan abin da da ki ke ma tsoro, Dada da kuma yan uwana, wannan duk mai sauki ne da zaran mun yi aure zan dauke daga gidan gaba daya sai kin so zasu ganki, yanzu abin da nake so da ke, duk juyin duniya kar ki yarda ki furta cewa cikin jikinki ba nawa ba ne kamar yadda na sanar da su tun farko, da sauri na kalle shi , ya girgiza min kai ya ce " Hakan ma wani makami ne da zan yi gwagwarmayar yakin samun nasarar aurenmu, kuma ma banda abinki ba ni din ne uban shi ba, ko yana da wani uba bayan ni." Da sauri ta girgiza kai tare da cewa "Sunan ka fa Yaya Husain." Ya ce "Ban damu ba Balkisu, Ina son ki kuma zan iya bada rayuwata wajen kare taki rayuwar bama suna ba."

Daga haka bai sake ce min komai ba ya tada mota muka dauki hanyar gida.

Fadin irin gwagwarmayar da aka sha da Dada kafin ta barni na saka kafata cikin gidan da sunan ci gaba da zama bata lokaci , da kyar sai da Al-husain ya hadata da wani kawunta wanda shi kadai ya rage mata a iyaye, kuma shi kadai ta ke jin maganarsa sannan ta amince, amma fa babu tausayi babu saukakawa sai ma karin azabtarwa da tsamgwama.

A haka na ci gaba da rainon cikina da tallafawan Yaya Hussain, a bangare daya kuma soyayya na dad'a karfi tsaninmu a boye ta yadda muke jin baza mu iya rayuwar babu juna ba, idan na nuna damuwata akan yadda zamu samu damar yin aure, sai ya yi murmushi ya ce kar na damu ya gama shiri, haihuwata kawai ya ke jira.

Cikina ya shiga wata tara ya yi wani irin girma mai ban mamaki duk wani abu da ake tanada na taron Baby Al-hussain ya tanade shi, yadda yake son cikin nan bana tunanin yana son wani abu a duniya haka, cikin kwanakin ya shiga tashin hankali, damuwarsa yaya zamu yi idan nakuda ya taso min sanda baya gida ko cikin dare, idan ya fadi haka sai na yi murmushi na ce "Karka damu Yaya Hussain ka taya ni da addu'a in sha Allah zan haihu lafiya." Da ni da shi haka muka tashi tsaye da addu'a ba dare ba rana akan Allah ya sauke ni lafiya.

Allah maji rokon bawa wata ranar litinin bayan Al-hussain ya min sallama ya fita da zumar amso abu ya dawo, na haifi Fatima, wata irin haihuwa mai ban mamaki da al'ajabi, na shiga bandaki da niyyar yin fitsari marana ya kulle a wajen, ban tashi ba sai da na haihu.

Kukan jinjirar ya jawo hankalin mutanen gidan, amma tsabar bakar zuciya da tsana a cikinsu aka rasa wacce zata iya daidaida yanke cibiya balle daukarta, ina duke cikin jini rungume da babyna da ke ta rusa kuka, babu abin da nake sai hawaye da neman dauki daga Rabbis sawati wal ardi akan ya kawo min agaji.

Daya daga cikin matan makwafta mai suna Hajo ce ta shigo wajen Dada, ta tarad da abin da ke faruwa, dattijuwa ce mai hankali da wadataccen ilmin addinin islama, ita ce ta yanke cibin ta taimaka min na koma daki ta gyara ni sannan ta koma ta gyara bandaki.

A lokacin ne Al-hussain ya dawo, ya sha mamakin jin wai na haihu da sauri ya karaso d'akin da nake don gane wa idanunsa, sai da ya yi arba da jaririyar wacce a take ya rada mata suna Nana Fatima sannan ya yarda, ya rungumeta tsam a kirjin shi yana godewa Allah daya sauke ni lafiya.

Hajo ta fita da zumar hura wuta ta daura ruwan zafi don ta wanke jaririya Fatima da ke ta kuka amma Dada ta daka tsallen albarka ta ce ba da tukunyarta ba.

Wanna dalilin yasa Hajo ficewa da Fatima gidanta a cen ta yo mata wanka ta shiryata cikin kayan sanyi na jarirai mai kyau da tsada.

Ni kam wankan da ban samu yi ba kenan a gidan nan sai dare, don sai da Al-hussain ya sake hada Dada da wannan kawun nata yazo har gida ya mata tatas sannan ta yarda aka aza ruwan wankana a gidan..........

Ya naga bakwa comment ko dai mu ajiye labarin ne sai bayan sallah? Pls in ji ra'ayin ku akan hakan. [1/18, 12:39 PM] ***: ๐ŸŒ€๐ŸŒ€ *JOY* ๐ŸŒ€๐ŸŒ€

~FARHAT~

*BY*

*AYSHA NALADO*

*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*