JOY

PAGE 48

by @aishanalado88

Washegari ma Baaba Hajo ce ta shigo da sasassafe ta d'aura ruwan zafi ta yi wa jaririya Fatima wanka ta shirya ta ta goya, sannan ta kwashe wani ruwan nima ta kai min toilet, ta na tsaye a kaina na yi wankan, duk abin da ban yi da kyau ba ta saka hannu ta gyara, sai da ta tabbatar mun yi tsab, sannan ta koma gidanta ta damo kunun kanwa ta kawo min ta tursasani na sha shi da zafi-zafi, da rana kuma ta tuko tuwo da miyar yauki ta kawo, haka ta yi ta hidima damu ba tare da gajiyawa ba, sai da ta yi mana wankan yamma ta tabbatar na ci abinci ta ajiye min duk wani abin da zan bukata sannan ta yi mana sallama wuraren karfe taran dare.

Har 'kasa Yaya Hussain ya zube ya na mata godiya, ta yi murmushi tare da cewa "ka tashi Al-hussain bana son haka, ai yi wa kai ne, dโ€™a na kowa ne."

Har na kuma kwana na hantse babu d'aya daga cikin 'yan uwan Yaya Hussain da ya min barka bare na saka ran cewa zasu d'auki jaririyar, nan na kara tabbatar da cewa lallai ba karamin kiyayya suke yi mini ba.

Dattijuwar kirki Baaba Hajo ce ta yi ta kula da ni da jaririyata da zuciya d'aya tamkar yar da ta haifa da cikinta koma na ce fiye da haka, ranar da na cika sati d'aya da haihuwa Yaya Hussain ya siyo katon rago ya yiwa Fatima ha'ki'ka, ranar kuwa ya sha bala'i wajen Dada kamar zata yi hauka tsabar ba'kin ciki tsine mishi ne kawai ba ta yi ba.

Ranar da na cika kwana arba'in da haihuwa aka daura aurena da Yaya Hussain, lamarin da yazo mana a bazata daga ni amaryar har Dada da y'an uwan shi, tun zuwa na gidan ban ta6a ganin tashin hankalin daya kai na wannan rana ba, tsayawa baku labarin irin tashin hankalin da aka yi wanna ranar 6ata baki ne, tun haduwata da Husain, ban ta6a tunanin barinsa ba sai ranar.

A take a wajen Dada ta yi amfani da kambun ta na uwa ta saka ya rubuta min saki d'aya, ta kuma buga rantsuwa akan bazan sake kwana a cikin gidan nan ba, in dai ta haifu cikin uwarta da ubanta.

Ranar raina ya baci zuciyata ta yi mini kuncin da bata ta6a yi ba, ban ta6a jin tsanar wani mahaluki a zuciyata ba irin yadda na ji tsanar Dada da 'ya'yanta a ranar, ina kuka na goya Fatima na kama hannun Al'ameen idanuna ko gani sosai basa yi na kama haryar barin gidan, ina ji Yaya Hussain yana kuka tare da kirana amma na kasa juyawa in kalle shi, haka na saka kai na bar gidan ba tare da nasan in da zan doso ba.

Tafiya kawai na ke yi cikin karfin hali da dakewar zuciya, idanuna a bude amma sam bana ganin gabana, saka kafa kawai na ke yi duk in da na samu ba tare da kula ko kiyayewa ba, a wannan lokacin zuciyata ta kekashe idanunawa sun bushe, dan ragowar burbushin hankalin da ke tare dani na neman gushewa, ina ji a raina dama Allah bai halicceni a duniya ba, ina ji kamar na kashe kaina na huta, sautin muryar Yaya Hussain a lokacin da yake kirana cikin kuka da kururuwa ne kawai ke amsa kuwwa a kunne na,

Al'ameen sai kuka yake haka ma Fatima, yaran kamar sun san abin da ke faruwa.

Na yi nisa sosai da tafiya, ina daf da shnaye kwanar gidan na hau babban titi, na jiyo muryar Baaba Hajo a bayana tana kirana, a duniyata bayan Yaya Hussain Baaba Hajo ce mutum na biyu da nake mutuntawa sama da kaina, dakatawa na yi ta karaso gabana da sassarfa idanunta jajur alamar ta sha kuka, muna hada ido na ji wani rauni ya lulle6e ni, sai kawai na saki hannun Al'ameen na fada jikinta na kamkameta tare da fashewa da wani irin kuka.

Bata dakatar da ni ba, domin ita kanta hawaye take yi, ganin mutane da basa raina abin kallo sun fara taruwa yasa ta yi karfin halin zare jikinta daga nawa, ta dauki Al'ameen ba tare da ta iya ce mini komai ba ta kama hannuna ta fara jana tamkar rakumi da akala.

A cikin d'akinta ta yi mana masauki, raba dare muka yi tana faman aikin rarrashina da bani baki akan na yi hakuri na rungumi kaddrata da hannu bibbiyu shine cikar imanina,bayan ta baiwa Al'ameen tuwo ya ci tuni ya yi barci.

Kwanana uku a gidan Baaba Hajo na kasa daina kuka, har sai da tayi fushi ta yi mini fada tare da nuna mini bacin ranta san nan na fara daurewa na daina yi a gabanta sai dai idan na shiga ban d'aki, na yi mai isata, Yaya Hussain shine rauni na, bansan wani hali yake ciki ba, nasan duk in da yake yana cikin halin matsanaciyar damuwa ina jin hakan a jikina.

Gutsiri tsoma ya barke tsakanin mutanen unguwa, wasu na ganin watau Baaba Hajo data taimakeni suna zaginta yayinda wasu ke shi mata albarka tare da jinjina mata.

Sati na biyu a gidan amma ban taba leka ko zauren gidan bane, sai dai zuwa lokacin na yi tawakkali na mikawa Ubangiji dukkan lamurana na dage da addu'a babu dare ba rana, sai dai har zuwa lokacin na kasa daina kukan rashin Yaya Hussain.

Ranar da na cika sati uku da yammaci sai ga Dada da Al-hassan sun shigo gidan Baaba Hajo shajaran majaran, hankali tashe Dada na sharar kwalla, Al-hassan kuwa idanu jajur.

Lokacin ina madafi ina izawa Baaba Hajo wuta, jin muryar Dada yasa na dago a razane, Baaba Hajo ma da shiganta d'aki kenan ta fito da sauri har tana tuntu6e da dakalin kofar dakin.

Ganin Dada ta nufo in da nake kai tsaye yasa jikina ya fara 6ari na soma ja da baya, sai dai ga mamakina, tana isowa gabana cikin zubar hawaye take cewa "Balkisu ki dubi Allah da ma'aiki ki yafe mana."

Kaina ne ya kulle, na zaro ido a tsorace ina tunanin ko dai Dada ta zauce ne da take gayamin wannan maganar, ban dawo cikin nutsuwata ba naga tana neman zube gwiwowinta biyu a kasa a gabana, da sauri na dakatar da ita ta hanyar saka hannayena biyu na tarota ina girgiza kai tare da cewa "Kar ki duka a gabana Dada, wallahi na yafe miki har abada saboda Allah saboda darajar Yaya Hussain da soyayyarsa."

Cikin kuka ta shiga cewa "Balkisu zamu rasa Usaini ya na can kwance rai a hannun Allah, tun da kika juya kika fice daga gidan ba tare da waiwayarsa ba ya yanke jiki ya fadi, muka yayyafa mai ruwa, tun muna daukar lamarin da wasa, ashe ya fi gaban nan in takaice miki yanzu haka yana kwance a babban asibiti zuciyarsa ta kumbura,lokaci kawai yake jira, da taimakon iskar oxygen ya ke numfashi ko daga yatsarsa baya iyawa bare ya bude baki ya yi magana, kuma Dr ya tabbatar mana kece kadai wacce za ki iya taimakawa ya samu lafiya, don Allah Balkisu ki dubi, Allah ki taimakeni kar ki bari mu rasa Usaini kar ki bari na rasa dana mai tsananin biyayya a gareni zan yi harasa."

Irin tashin hankalin da na shiga da jin kalaman Dada bazai misaltu ba, hajijiyane ya shiga kwasata jiri na nema kayar da ni , tuni na naimi miyau a bakina na rasa, a haka na yi karfin hali kama tafiya na durfafi hanyar kofar fita daga gidan cikin tashin hankali da gushewar tunani.

Baaba Hajo ce ta karaso jiki a sanyaye ta rike ni ganin yadda jikina ya dauki na mazari, cikin rarrashi take cewa "Ki nutsu Balkisu ina za ki je haka, ki zo ki zauna kar jiri ya kayar da ke." Cikin kuka na ce "Baaba bazan iya zama ba, Yaya Hussain na cikin irin wannan halin asibitin zan tafi."

Dada cikin sharar kwalla ta ce "Yawwa Balkisu, na sani ke yar albarka ce baza ki ta6a juyawa Usaini ba ya ba, ga mota nan kizo muje Hasan ya kai mu asibitin.

Hijabi Baaba Hajo ta dauko min a daki ta ce " kuje Balkisu nima idan na karkare sanwar zan biyo ku."

Ko da muka isa ban samu ganin shi ba, domin inda yake ba a shiga sai da kwakkwaran dalili, ga shi likitan da yace in zo ya ta shi wani ya canji hannunshi.

Ranar asibitin na kwana, don yin duniya Baaba Hajo ta yi in zo mu tafi na ki, dole haka ta wuce ta barni, ban iya rintsawa kwana na yi ina sharar hawaye tare da rokawa Yaya Hussain lafiya.

In takaice muku sai da na yi kwana goma sha biyu cif a asibitin nan ba tare da na koma gida ba, saboda a yadda naga Yaya ban za ci zan kifta ido in bude in tarar da shi yana numfashi ba, sai dai cikin hukuncin ubangiji da taimakonsa da nawa dana Dr Yaya Hussain ya fara samun Lafiya har ana iya mikar da shi zaune, a ranar kuwa da ya fara magana, maganar data fara shiga tsakanina da shi ta farko, shine" Na mayar dake dakinki matata Balkis." A gaban Dada da sauran yan uwanshi ya yi maganar, sosai na tsorata, ganin yanayin da na shiga yasa ya kawo hannuna ya rike yana murzawa a hankali, fuskarsa dauke da murmushin fari n ciki ya sake cewa, "Kar ki damu a wannan karon da sahalewar Dada da kuma yan uwa na aureki." Jin haka yasa na dago kai na kallesu ba ki daya ganin yadda fuskokinsu ke murtuke kamar an aiki musu da sakon mutuwa musamman Dada da Tanimu ya tabbatar min da akwai lauje cikin nadi....... [1/18, 12:39 PM] ***: ๐ŸŒ€๐ŸŒ€ *JOY* ๐ŸŒ€๐ŸŒ€

~FARHAT~

*BY*

*AYSHA NALADO*

*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*