PAGE 22
Dunk'ule paper n ya yi bayan ya gama karanta abin da ya k'unsa, ya dafe goshi cike da takaici, ko kad'an bai ji wani karsashi ko shauk'i game da kalamanta ba, sai ma ganin tsananin wautarta da shirmenta da ya yi, dama he is wonder yadda ta ke yawan kallon shi ashe da dalili, guntun tsaki ya ja, ran shi duk ya 6aci, cike da takaici ya ce "Yara tun baku tafasa zaku k'one!" Wurgi ya yi da paper'n ya shiga kimtsa d'akinsa, tattara komai ya yi, ya shere d'akin tass! kamar yadda ya saba, wurin tattara shara ya sake cin karo da paper n kamar ya share da shi ya zubar sai kuma ya dauka ya warware ya linke, zai ajiye saboda evidence, gurin da tarin littfansa suke ya nufa, ya dauki wani babban textbook da yake saka paper's ya bud'e da nufin ajiye wa a ciki, karaf! ya bud'e dai-dai page d'in da ya ta6a ajiye letter n Joy, gaban shi ne ya yanke ya fad'i, kurawa latter n idanu ya yi, brain din shi na tuno masa abin da ya faru tsakanin su rannan' lokacin da take sand'a da za ta shiga gidansu, yadda ta firgice daga jin muryarsa kadai, yadda ta riko kafafunsa tana rokonsa, yadda ya fisge kafarsa da k'arfi ta fad'i ta fasa goshi, yadda ta mik'e tana hawaye ta kakka6e jikinta, ta tashi tana tafiya a slow, bin bayanta da ya yi, guduwan da ta yi ta barshi a tsaye rik'e da handkerchief, k'ak'k'arfar ajiyar zuciya ya sauk'e. Hakan na nufin bata yafe masa ba fa kenan, take jikin shi ya yi mugun sanyi, hakika ya cutar da ita, kuma he regret, zai yi kok'ari ya gyara kuskurensa.
Latter n ya d'auka ya koma bakin mattress d'insa, ya warware yana bi da kallo tare da sake karantawa, yana maimaitawa, zuciyarsa na k'ara shiga matsanancin tausayin yarinyar kamar yadda ya fassara lamarin.
Bai san adadin lokacin daya 6ata a haka ba, ya tsinkayi sallamar Fatima a k'ofar d'akin shi, da sauri ya linke wasikar, ya tura karkashin pillow, sannan ya bata izinin shigowa, kayan breakfast d'in shi ne ta kawo, guri ta samu ta ajiye, godiya ya mata, sannan ya tsareta su ka yi breakfast d'in tare. Yana ta so yayi mata zancen Joy zuciyar shi na hana shi, a haka su ka kammala, ta kwashe kayan ta mayar cikin gida shi kuma ya d'ibi ruwan wanka ya shiga.
Har ya yi wanka ya shirya tunanin Joy ya ke, da kyar ya yakice ta a rai ya samu ya fita, school ya tafi daga can kuma bai dawo gida ba, ya ta fi harkar kekensa.
Karfe takwas ya shigo gida, as usual su Ummi na tsakar gida, nan ya zauna su na shan iska, a nan ya ci abincin suna sauraren shirin kwarmato! A redion Ummi abin mamaki ranar Amira bata shigo karatu ba, Ummi ta ce "Wai ni kam yau banga Amira ba tun safe ko lafiya? " Fatima ta ce "Nima Ummi wallahi tun d'azu abin ke raina."Ummi ta ce "Allah dai yasa lafiya, da safe idan Allah ya kaimu sai Ki dubo mana ita." Al'ameen na jin su bai saka musu baki.
Hira suka shiga yi, sai sha d'aya saura suka ta shi lokacin tuni Fatima ta yi barci. Shi ya kwashe tabarman bayan sun ta shi, sai da ya d'aura alwalar barci sannan ya nufi d'akinsa, shafa'i da wutiri ya gabatar, ya rage kayan jikinsa ya haye katifarsa, sai dai me! Tunanin yarinyar ne ya yi wa kwakwalwarsa kawanya, ya rasa me yasa ya damu da ita cikin y'an kwanakin nan, tun ranar da abin nan ya faru bai ta6a wayar gari ba ta fad'o masa a rai ba koda sau d'aya ne, tausayinta ya ke ji kamar me, sai dai ya alakanta hakan akan abin da ya gifta tsakanin su ran nan, hakan yasa ya daura damaran gyara kurensa, ya dauki tsawon lokaci kafin barci ya d'aukesa.
Cikin barci yaji yanayin shi ya fara sauyawa, tun yana d'aurewa har sai da da ya kai ga bud'e idanu, "Allahumma ajirni fi musabati! Hasbunallahu wa ni'eemal wakeel!" Ya shiga maimaitawa, iya hasashe babu wani abu daya faru cikin abubuwan da ke tasar masa da ciwonsa, babu ruwan sama babu sanyi a garin hasalima zafi ake yi saboda kwallara ranar da akayi a yinin ranar, bai shaki wani abu makancin kamshi ba, bai ga wani sura ko wani abu da zai iya daga mashi hankali ba, to menene dalili?
Jin abin na k'ara yawa yasa ya yi ta maza ya d'auko maganin sa ya 6alla sai dai ko gezau, sai ma ci gaba da hauhauwa da abin ya k'ara, hankalin sa ya ta shi mak'ura, abin da ya lura yanzu tab! 'Din ya daina mishi aiki ma, kardai maganar Dr Abdul ne ya tabbata.
Tuni ya fara ficewa a hayyacinsa, sharkab ya had'a gumi, jikin shi na karkarwa tare da soma daukar zafi, gefe guda ga mararsa da yayi wani irin kumburi ya yi tauri had'i da k'ullewa, numfashi ma dakyar ya ke iya ja da saukewa.
Cikin lalube da malelekuwar da yake yi, hannun shi ya sauka akan sachet din maganinsa, kamar jiya, wawura yayi ciki rufewar ido ya 6alli uku ya watsa a baki.
Da farko kamar ya k'arawa ciwon karfi, don sai da ta kai shi ga fara mirgina a tsakar d'aki.
Kimanin 15 minute ya kwashe a haka, kafin kuma ciwon ya fara lafawa, dakatawa ya yi da mirginan ya yi lamo yana sauke numfashi, a hankali komai ya tsaya cak! Kamar an yi ruwa an d'auke, kumburin maran ya sace, sai dai duk da haka jikinsa na nan da zafi rau, a haka wani wahalallen barci ya kwashe shi.
Kiran farko ya farka as usual, Alhmdllh! Zuwa lokacin zazza6in ya sauka, babu wani alamar ciwo sai idanunsa ne kad'ai su ka nuna, zaune yayi a bakin katifarsa zuciyarsa cike da damuwa, sachet d'in maganin shi dake yashe a k'asa ya dauka ya tsurawa idanu yana kallo, tsakanin jiya da yau ya sa guda takwas, abin da ake shan d'aya d'aya, kuma ba kullum ba don da sai yayi sati biyu uku bai sha ba, hakan na nufin d'aya ya daina mishi aiki ke nan, tabbas akwai gagarumin matsala, dole ya koma wajen Dr Abdul, amma kafin nan yana bukatar shawara, yana bukatar shearing din matsalarsa da wani, wayar sa ya d'auka ba tare da la'akari da lokaci ba ya dan nawa Aliyu kira.
Ringing biyu Aliyu ya daga, tare da sallama, Al'ameen bai taba kiransa a irin wannan lokacin ba, cikin dan tashin hankali ya ce "Ustaz lafiya, hankali ya ta shi da naga kiranka a irin wannan lokaci." Numfashi ya sauke kafin ya ce "Aliyu ina cikin damuwa."
"Subhanallah! Me yake faruwa Ameen? Bai amsa mishi tambayar shi ba, ya daura mishi da wata "Yaushe zaka dawo? Maganar bata waya ba ce." Jim! Aliyu yayi kafin ya amsa da "Zan kai karshen wata, ka fa'di ka d'an daga damuwar ka abokina zaka ji sauki." Girgiza kai Al'ameen yayi kamar suna kallon juna ya ce "Sai dai ka dawon zan kira ka." Daga haka su ka yi sallama jikin Aliyu duk a mace, ya san halin Al'ameen ba tun yau ba, tun da ya bukaci su tattauna akan matsalarsa to ya tabbata babbar matsala ce, zai yi duk yadda zai yi ya samu ya koma gida a karshen watan don su zanta kuma zai taya shi da addu'a Allah ya kawo ma shi d'auki.
Tun daga wannan rana kusan kullum sai ciwon shi ya ta shi, walau da sanyi ko babu, taimakon shi daya bai tab'a tasar masa da rana ba, sai dai wani lokacin tun da yamma zai fara jin alamun shi, da yaji haka ranar da wuri yake komawa gida da ya yi isha kuma yake shiga d'akin shi ya kulle.
A bangare daya ga damuwar FARHAT zuwa yanzu kusan sau hudu yana yin mafarki da ita, tana maimaita masa kalamanta na ran nan, sai dai har zuwa yanzu bai yi nasarar ganin fuskarta ba duk irin kwakwanshi da son ganin hakan, lamarin yana matukar damun shi. Duk wannan matsanancin yanayin da ya shiga bai manta da Joy ba, sai dai idan bai samu sarari ba sai ta fado masa a rai, ya kan alakanta hakan da cutar da ita da ya yi ran nan kuma yana fatan ya samu damar da zai nemi yafiyarta.
*****************
Kamar yadda Al'ameen ke cikin damuwa haka a bangaren Amira, zuwa yanzu ta daina zuwa daukar karatu kasancewar tuni sun fara exam, sai dai kusan kullum tana gidan, bata da aiki sai ajiye masa wasika, a mabanbantan wurare amma koda wasa, Al'ameen bai taba daga ido ya kalle ta ba balle ya nuna ya san da zamata, tuni ta fara rama a tsatsaye kasancewar so ne take masa mai girman gaske, abin na matukar damunta, ya haifar mata da damuwa da duk wani wanda yake makusancinta zai lura, baga iyayenta ba hatta da Ummi da Fatima sun fahimci tana cikin damuwa, sai dai banda Allah! da Zainabu babu wanda ya san halin da take ciki sai ko Al'ameen, wanda shi kuma damuwar gaban shi ta sha kan shi, kwata kwata bata gaban shi , don tun yana bude wasikun shirmenta acewarshi yana karantawa har ta kai ga ya dai na budewa idan ya gani sai da ya dauka ya ajiye ba tare da ya bude ba.
***************
*JOY*
Cikin abin da baifi wata daya ba soyayya ta gama ragargaza jini da bargon jikinta, i zuwa yanzu bata ji bata ganin komai sai Yayan Fatima, tun tana karyata zuciyar ta akan lamarin har ta yi surrender.
Sai dai takan shiga matsanancin damuwa, hankalinta kan tashi a duk sanda ta hango k'urar dake tafe da lamarin, ta ko ina idan ta hanga ta hango babu sauki, baga Al'ameen ba baga Mom da sauran ahalinta ba, har Papa bata tunanin a wannan karon zai kalle ta da idon rahama, a duk sanda tayi irin wannan tunanin takanyi kokari ta yakice shi daga zuciyar ta amma ina! Abin ya ci tura, kullum sai Dada hauhawa ya ke kamar farashi.
Gaba daya ta koma so silent, bata da aiki sai rubuce rubucen kalaman soyayya, sai ko kuka da ya zama mata kamar ibada, tuni ta yi rama ta dishe.
kwarafniyar Anty Esther tuni sun daina gigitata, gani take hargagin Mom da anty Esther ya fiye mata sauki akan tashin hankalin dake tunkarota, zuciyar ta na daf da yi mata bore, sai dai ta lashi takobin ko zata mutu bazata ta6a bata dama ba, don tana ganin yin hakan tamkar tarwatsa rayuka ne, gara ita nata rauyuwar ya tarwatse.
Tuni anty Esther ta bata wayarta, sai dai abin mamaki tunda ta karbu wayar Papa bai taba kiranta ba itama idan ta kira shi baya dagawa, idan ya daga ma da sun gaisa sama sama zai kashe gaba daya ya dena nuna mata kulawa kamar da. Bata wani dauki abin serious ba ta mishi uzuri don a ganinta aiyuka ne suke sha kan shi.
A cikin wannan dan tsukin girgin su Mom ya yi dirar mikiya a 9ja, ko gezau bata yi, babu yabo babu fallasa a tare da ita, suka dunguma ita Anty Esther, David, zuwa airport don tarbota, babu wani karsashi ko kewa a ranta su ka iso, lokacin tuni jirgin ya sauka, da sauri Mom ta iso gareta tare da rungumeta, lamarin ya dan so ya daure mata kai, amma tuna yadda Mom dinta ke matukar kaunarta, ada kafin ta soma canzawa yasa ta saki jiki itama ta rungumeta, cikin kunnenta Mom ta rada mata "I missed u a lot daughter." "I missed u 2 my Mom." Ta amsa mata.
"Ki yafe min abubuwan da suka yi ta faruwa a dan kwanakin nan, kuskurene." Hawaye ta ci ya ciki mata idananu, "take daskararriyar soyayya ta fara narkewa." Tsaki Anty Eshart ta za a bayyane, tare da kauda kai zuciyar ta na tafasa, murmushi Mom ta yi, ta saki joy ta rungume Eshart tana cewa "Oh! I'm Sorry my dear sister. Na yi kewarta sosai ne shiyasa." Daga haka ta rungume David da shima yake mata sannu da zuwa, hannunta sarke da na Joy suka shiga mota, Joy na kwance a jikinta har su ka iso gida.
Duk da izza da dagawa irin na Mom, ma'ikatan gidan sunyi murna da dawowarta, daga yadda suka dinga zuwa kwasar gaisuwa kowanne baki har kunne zaka tabbatar da hakan, ko ba komai zasu rabu da masifar Esther.
Ranar Joy na makale jikin Mom din ta, tana lelenta kamar yar five years abinda ta dade rabonta da gani daga Mom din hakan yasa ta saki jikinta sosai ta wuni da farin ciki, koda lokacin barci yayi har daki Mom ta rakata ta tayata shirin barci ta kwantar da ita ta kashe mata wuta sannan ta barta ba yan ta yi kissing forehead din ta tare da shafa kanta.
Mom na fitowa daga d'akin Joy ta tarad da Esther tsaye tana Binta da wani irin kallo, hannunta Mom ta kama ta jata su ka bar wajen, d'akinta ta nufa da ita sunan shiga Esther ta fisge hannunta daga na Mom, tare da watsa mata wani lalatatcen kallo, ajiyar zuciya Mom ta sauke a tausashe ta ce "I'm sorry Esther. Ba abinda kike tunani ba ne." Cikin daga murya ta ce "Ta Yaya zan tabbatar da haka ba yan kina aikata sabanin abin da kika sanar min, na gani lokaci yayi da ya kamata ki cika alkawari." "Calm down Esther ki saurare ni." Daga mata hannu ta yi a zafafe ta ce "Bazan saurare ki ba, zan bar gidan nan don bazan zauna bakin ciki ya kashe niba." Daga haka ta tuya ta fice daga dakin fuuu! A fusace.
Dabass Mom ta zauna tare da rafka tagumi.
Washegari da duku duku safiya Anty Esther ta fito da jakar kayanta ta bar gidan.
**********
*Al'ameen*
Kwata kwata babu sauki a cikin lamuran sai ma kara tabarbarewa da abubuwa ke yi I zuwa yanzu tab! biyar yake sha kafin ya samu relief........
Ga mai bukatar shiga group.
***. [12/29, 2:40 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀
~FARHAT~
DAGA ALƘALAMIN👉 *AyshaNalado*
ƘARƘASHIN JAGORANCIN👉 *Mikiya Writer's Association*