JOY

PAGE 24

by @aishanalado88

Cike da wani irin bacin rai Dr ya katse shi ta hanyar kiran sunan shi a tsawace "Muhammad!!! Baka da hankali ashe, five tablets fa ka ce." Komawa ya yi zauna da6ass "Innalillahi wa inna ilaihi rajiun!!!" Ya furta tare da dafe forehead.

Ganin yadda hankalin Dr Abdul ya ta shi yasa Al'ameen yin k'asa da kai, cikin sanyin murya ya ce "I ha6 no choice, dat is y" Dagowa Dr ya yi idanun shi har sun kad'a ya ce "Ni ka ke gayawa baka da za6i, shin! haka mu ka yi da kai?" Ya girgiza kai. "Then y ka yi hakan, kasan me ka aikata kuwa, hakan fa dai-dai yake da kashe kai." "I'm sorry Dr." D'aga ma shi hannu Dr ya yi , ya ce "Ka rike hakurin ka, ka tashi ka fice min daga office bana bukatar ganin ka, don babu abin da zan iya yi maka a halin yanzu." Jin haka yasa hankalinsa kara ta shi tuno yadda ya baro Ummi a kwance cikin ciwo ya yi, ya sake tuna irin damuwar da tilon kanwarsa ke ciki duk akan wannan matsalar, sannan ya zo in da yake ganin zai samu maslaha amma yana ji yana gani ana neman yi masa sakiyar da babu ruwa.

A raunace ya ce "Dan girman Allah Dr ka tausayin min ka dubi maraicina, ka yi mini wannan alluran, na amince da duk abin da zai biyo baya." Kallon zautacce wanda bai san ciwon kan shi ba Dr ke mishi i zuwa yanzu, hakan yasa ya baiwar iska ajiyar shi ya ci gaba da duba tarin files din dake gabansa.

Magiya da ro'ko Al'ameen ya shiga yiwa Dr amma yayi kamar bai san da zaman mutum a wajen ba, don ran shi a matukar 6ace yake danne zuciyarsa kawai ya yi don tunzira shi ta ce akan ya ta shi ya dinga sharara ma shi mari, amma yaga alamar yaron na neman kai shi bango.

Magiyar duniya Al'ameen yayi wa Dr amma bai kalle shi ba, har k'asa ya duka ya riko kafafusa yana rokonsa, amma kamar da dutse yake, tuni zuciyarsa ta fara tunzira.

Mik'ewa ya yi a fusace cikin tafasar zuciya da matsanancin bacin rai ya ce "Kar ka yi min mana so what!" Kalmar da ta doke kunnen Dr da ya sa ka shi dagowa da sauri a kalle shi.

Cikin tsawa da rufewar idanu ya ci gaba da cewa "Wacce irin zuciya ce a kirjinka Dr? Shin baka da imani da tausayi ne baka san Allah da ma'aiki ba? To shike nan ka je ka rike taimakon na ka, gari da yawa maye baya ta6a cin kansa! Idan baka taimaka mini ba akwai dubban irin ka da zasu iya taimaka mini, duk duniya babu wanda na yarda ya san sirrina ciki da waje sai kai, na gaya maka abin da ke faruwa ban 6oye maka komai ba, na ce maka na amince da duk abin da zai biyo baya ba shike nan ba, ina ruwanka jikin ka ko jikina rayuwar ka ko nawa? So kake na fifita wani jin dad'i na rayuwana akan farin cikin mahaifiyata, to ka sani UK duniya babu wanda ya isa, bani da kamar ta itace komai nawa, kuma zan iya yin komai dan ganin farin cikin ta, dukan table ya yi da karfi har sai da wasu takardun dake kai su ka watse ya ce " Ni muhammadul-Ameen Idan na haifu dan halak na maka alkawarin baza ka sake ganin kafata a cikin asibitinkada zumar naiman taikamo a wajen ka ba."

Daga haka ya juya a fice daga office din tare da buga koda da mugun karfi.

Tun da Dr ya kafe shi da ido bai sauke ba har ya fice daga office din. Ya fi minti goma a haka, kafin ya sauke zazzafar huci, fuskar yaron yake sake kallo a idanunsa maganganun yaron ne ke sake repeating kan su a cikin kunnuwansa, "Ya Rabbi! Kaga niyyata ka dafa mini." Ya furta a bayyane wayar shi ya dauka ya yi dialing lambar Hayatuttdeen, kamar yadda ya tsammata kiran bai tafi ba, kife wayar ya yi akan table, shima ya kife kanshi tare da lumshe idanu.....

***********

Da wani irin fushi hadi da bacin rai ya fito daga asibitin, jefa kafa yake yi duk in da ya samu, idanun shi a rufe, ikon Allah ne kawai ke rike da shi, bai san ina yake nufa ba, don zuciyarsa ce kawai ke jagorantarsa kwkwalwarsa kam ta dau zafi a lokacin da bazata iya tantance komai ba.

Wani irin mugun horn ne hadi da taka burki suka ziyarceshi lokace daya, sai dai kafin ya yi aune tuni motar ta ture shi, duk da ba wani mugun turi bane don direban yayi iya kokarinsa wajen kaucewa hatsarin, sai da ya fadi kasa.

Gigitacciyar kara ta saki a matukar razane. ba ta san yadda a ka yi ba, ta shiga komar tunanin shi kamar yadda ya zame mata ibada, kawai ta ji direbanta ya taka birki, a firgice ta dogo kafin tayi aune kamar kiftwar idanu taga motarta ya ture shi.

Ita da direbanta rige rigen fita a mota suka shiga yi, kusan a tare suka isa inda yake, bata tabbatar shi din ba ne, don duk a tuninta gizon da ya saba mata ne, sai da ta fito daga mortar ta ganshi ra'ayil aini.

Cikin rawar jiki Peter ya isa gare shi don ya taimaka mi shi ya mike, abin mamaki da daure kai dakatar sa shi yayi ta hanyar daga mishi hannu cikin karfin hali da jarumta ya dafa kasan titi ya mike tsaye, bai ji mugun rauni ba sai dan kujewa, sai dai ga dukkan alama ya bugu a kafafun shi ganin yadda tsayuwa ta so gagararsa da fari, amma yayi ta maza ya cije lips ya tsaya cak.

Tuni ta fashe da wani irin kuka tare da karasawa garesa, a gabansa ta tsaya cikin kuka take cewa "Na shiga uku na lalace! Yaya Alamen ka yi hakuri, Peter mu kai shi asibiti, Yaya Alamen ka zo muje asibiti pls jini yana zuba a jikinka." Riko hannun shi ta yi ta soma kokarin jan shi, gaba daya ta rude bata cikin hayyacinta......

Ku yi manage pls.

Masu comment nagode kwarai ina alfahari daku, jiya kun faranta min sosai dana bude data naga ruwan comment na shigowa group di na pls Ku ci gaba hakan shine karfin gwiwata ina sonku sosai masoya mabiya. [12/29, 2:41 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀

~FARHAT~

DAGA ALƘALAMIN👉 *AyshaNalado*

ƘARƘASHIN JAGORANCIN👉 *Mikiya Writer's Association*