PAGE 27
Wani irin gwalalo idanu waje ta yi tare da dafe kirji a razane ta ce "Ya mutu ko?" Girgiza kai Peter ya yi ya amsa da "Bai mutu ba." "To mai ya same shi?" Ta fad'a cikin shirin fashewa da kuka, Shiru ya yi yana nazarin mai zai ce mata don ba k'aramin tausayin ta yake ji ba, baya so ya fad'a mata abin da zai tayar mata da hankali, muryarta ne ya katse mishi tunani "Na rok'e ka kada ka boye min komai Peter, sanin halin da yake ciki shine kwanciyar hankalina." Ba yadda zai yi hakan yasa ya yi k'asa da kai ya ce "Na samu labarin cewa sanadiyar kad'e shin da muka yi, ya samu targad'e a kafar shi ta hagu sannan......" Shesshekar kukanta ya saka shi dasa aya, da sauri ya dago yana kallon ta, dama yasan za'a rina, an saci zanin mahaukaciya.
Cikin muryar rarrashi cike da girmamawa matsayinta na uwar dakinsa ya ce "I'm sorry Miss ki daina kuka zai samu sauk'i soon, naji labarin tun jiya an gyara kafar an d'aure." Cikin kuka ta ce "Saboda mai ka ke cewa kar na yi kuka, bayan nice sanadin raunatar shi? Me yasa bazan yi kuka ba? Kasan yadda na ke ji a zuciyata kuwa?" Ta fad'a tana ta6a saitin zuciyarta, kasa ya sake yi da kai, tare da cewa "I'm sorry Miss." Zuciyarsa gaba d'aya ta raunana, anya zarginsa bai zamo gaskiya ba kuwa? Ko dai uwar d'akinsa ta fad'a soyayya da wannan yaron ne, domin lamarin ya fi gaban tausayi kad'ai.
Daurewa ya yi dago ya kalleta tare da jeho mata tambayar da ke kai kawo a ransa, "Miss Joy ar u in luv wit him?" Ya fad'a a d'arare.
Tsittt! Kukan ta ya d'auke, ta zuba ma shi rinannun idanunta na yan sakanni, can kuma ta girgiza kai ta ce "Noooo! Babu wani abu makamancin haka a zuciyata game da shi, kuma kar ka sake yi min irin wannan tambayar." Daga haka kuma ta juya da sauri sauri gudu gudu ta bar gurin.
Ajiyar zuciya ya sauke ya san ta fad'i son ran ta ne kawai amma shakka babu tana son yaron nan, shi daga ita har yaron tausayi suke ba shi, yasan wannan abu ne da ba zai ta6a yiwuwa ba ko a tastuniya balle a zahiri. Alice fa! jinin Alice da soyayya da musulmi tabbas akwai k'ura, shi dai zai saka su a addu'a shine k'adai taimakon da zai iya mu su.
Ta d'auka sanin halin da yake ciki zai sama mata sauki a zuciya, amma ina! Babu wani sauki sai ma k'ara mata damuwa da tashin hankali da ya yi. kamar jiya daren ranar sai barci 6arawo ne ya sace ta bayan ta gama tsara yadda za ta yi gobe ta samu fita ta je ta gan shi ko a sace ne.
********
*AL'AMEEN*
Kasancewar sa jarumi kuma sam ba shi da k'an jiki yasa nan da nan ya fara samun sauki, a Washegari rana ta uku da samun tsautsayin ya soma taka k'afarsa, tuni kumburin ya sa6e sai dan abin da baza a rasa ba.
A ranar ma haka Amira ta sake had'o lafiyayyan karin kummalo ta aiko ma shi. Sam bai ji dad'i ba, a ganin shi ta cika zak'ewa, hakan yasa ya kuduri aniyar taka mata birki, yau kam bai ci abincin ba duk irin magiyar Ummi, ya fake da cewa shi ba cimarsa ba ne, shi kunun zai sha, kasancewar Ummi tasan hakan yasa bata tsaurara masa dole sai ya ci ba. Wainar shinkafa ce da miyar taushe yaji tantakwashi da man shanu, Ummi da Fatima ne kad'ai suka ci.
Yau kam a d'aki ya yi zaman shi bai fito tsakar gida ba kasancewar akwai wutar nepa.
Wuraren karfe goman rana Amira ta yi sallama tsakar gidan, direct cikin gida ta nufa don bata za ci yana d'aki ba, a kitchen ta samu Ummi, kamar kullum a mutunce ta gaisheta tare da tambayar mai jiki.
Ummi ta amsa da "Mai jiki Alhmdllh yana samun sauki, sannu da hidima Allah ya saka da Alkhairi Allah ya yi Albarka." K'asa ta yi da kai tana d'an murmushi ta ce "Amin Ummi."
D'aukar tsintsiya ta yi ta tattare hijabinta tana "Ummi bari na tattara gidan naga ba'a riga an share ba." Kallon ta Ummi ta yi ta ce "Kun gaisa da mai jikin ne?" Ta girgiza kai tare da cewa "A'a Ummi." Ummi ta ce "kije Ku gaisa yana d'akin shi." Ajiye tsintsiyar ta yi ta kama hanyar d'akin ,zuciyarta na dokawa da mugun gudu.
A sanyaye ta yi sallama a bakin k'ofa. Ya amsa mata yana daga zaune a bakin katifarsa, duk a tunaninta zata tarar da Fatima a d'akin kamar ran nan sai dai ga mamakinta shi k'adai ne zaune a sanye da singlet da dogon wando, kallo daya ta yi masa ta yi saurin yin kasa da kai, take jikinta ya dauki rawa, kasa zama ta yi don gaba daya gani take ya cika dakin tsabar kwarjini.
Shikam a tsanake yake kare mata kallo, Sam! Bata da makusa sai dai ita zuciya ba'ayi mata tilas.
Ganin bata da niyyar yin magana gashi ta doje a bakin k'ofa ita ba ta koma ba ita ba ta k'arasa shigowa yasa ya yi gyaran murya.
A diririce ta dago su ka had'a ido sai kawai ta zu6e gwiwowinta a k'asa a nan inda ta ke tsayen cikin dan rawar murya ta ce "Ina kwana Yaya Ameen ya karfin jiki."
Maimakon ya amsa gaisuwarta sai ya cewa "Amm! Amira." Da sauri ta dago tare da amsawa da "Na'am." Ya ce "Na ga sa'kon ki nagode, sai dai ina rok'on ki daga yau kar ki sake wahalar da kanki wajen aiko min da wani abu ko yi min girki please bana buk'ata, wani irin tunani iyayenmu zasu yi idan suka ga haka, to dan Allah wannan ya zama na karshe, and maganar wasika shima daga yau na kashe please kar na sake gani bana so, sannan ina mai jan hankalinki da ki zama mace mai kamun kai domin mazan yanzu basu da tabbas wani zai iya yin amfani da wannan irin damar ya sabauta rayuwarki.
Wani irin tafarfasa zuciyarta ya shiga yi, tun kafin ya dasa aya tuni hawaye sun gama wanke mata fuska. Meye laifinta don ta nuna masa soyayya, dama duk tsawon lokacin nan aikin banza take, Ashe kallon sakarya mara kamun kai yake mata, ji ta yi zuciyar ta ya dake duk wani tsoro da kwarjinin daya cika mata ido ya kau. Dagowa ta yi ta kalle shi, ta ce "Shin laifi ne don na nuna maka soyayya da kulawa, ka sani nima ba yin kaina bane kuma bani na daurawa kaina ba, don Allah na rokeka ka daina min kallon sakarya mara kamun ka wallahi ba haka na ke ba, sannan don Allah ka ta ya ni da addu'a Ubangijin daya sanya mini soyayyarka ya yaye min, na maka alkawarin daga yau bazan sake gwada maka wani abu makamancin soyayya ba, zan yi kokarina na taushi zuciyata, amma ka sani bazan daina sonka ba har karshen numfashina." Ta kai karshen maganar tare da fashewa da wani irin kuka wanda ya taso mata daga can k'asar zuciya, to she bakinta tayi da hijabinta saboda kar sautin kukanta ya fita har Ummi ta jiyo ta da sauri ta mike tare da ficewa daga dakin da gudu.
Karo suka yi da Fatima a k'ofar d'akin, bata tsaya ba ta ra6a ta gefenta ta fice daga gidan.
Kur!: ya kurawa hanyar da ta bi idanu, rana ta farko da wani abu mai kama da tausayi game da ita ya tsirgar ma shi a zuciya, me ya aikata kenan ya salam! Ya fad'a tare da dafe kai.
************
*JOY*
Safa da marwa kawai take yi a d'akin ta ganin karfe ukun rana ya gota babu wata dama da ta samu na fita, babu irin tunaune da bata yi ba ciki har da da haura katanga, sai dai ta san ko cikin maye take bazata iya ketare katangar gidan ba. Cak ta tsaya lokacin da zuciyar ta ya hasko mata mafita "David." Ta fad'a a saman lab'b'anta, da sauri ta rarumi wayar ta, ta lallatsa tare da karawa a kunne.
πππ kunya duk ta isheni na rasa da bakin da zan baku haΖuri ma yasinπ¬ π¬π¬ in sha Allah hakan bazai sake faruwa baπππ Ku tayani da addu'a aljanun kiwar yin typing ne su ka kusa sauka a kainaπππ
*** [12/29, 2:43 PM] AyshaNalado: ππ *JOY* ππ
~FARHAT~