JOY

PAGE 34

by @aishanalado88

Har ya k'arasa shigowa d'akin jikakkun idanunta na kafe a kan fuskar shi, ta kasa koda keftawa, gani take yi idan ta rintse ido ta bud'e zai 6acewa ganinta. Aysha ce ta bashi wajen zama kafin ta fice daga d'akin ta basu guri. Sai lokacin ya samu damar sauke idanunsa a kan ta, wani irin kwance-kwance gabansa ya yi ya fad'i, Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun! ya ambata a zuciya. hankalinsa ya yi k'ololuwar ganin gaba d'aya yadda ta rame ta lalace, ta fice daga hayyacinta kamar na Amiran daya sani ba, take tausayinta ya yi wa zuciyarsa kawanya.

Sassanyar Muryarta daya ratsa dodon kunnesa ya jawo hankalinsa, cikin maganarta 'kasa-k'asa irin ta majinyata take cewa; Yaya Ameen kaine da gaske! Ba gizo idanuna ke min ba, A she zan sake saka ka a idanuna kafin na amsa kiran mahaliccina, nagode sosai da ka zo gareni na yi farin ciki, nagode sosai." Ta karashe maganar tana sakin murmushi, hawayen soyayyarsa na kwaranyo mata ba tare da tasan da kwaranyarsu ba.

Jikinsa ne ya yi sanyi kalau! Gefe guda kuma wani irin kunyarta ya ji ya lullu6e shi, sai ya samu kansa da kasa ci gaba da kallon idanunta. Lallai zuciyar so makauniya ce, duk irin abin da ya aika ta mata Sam! bata ga laifinsa ba, bata yi fushi ba, wata d'aya da kwanaki ta kwashe cur! Tana jinya saboda soyayyarsa, bai ta6a koda aikowa bane yace ace mata sannu, amma take mashi godiya don yau ya shigo dubiyar da bata kai zuci ba.

Dakyar ya d'ago idanunsa da ke kyallin hawayen tausayinta ya sake kallota, da wani irin sassanyar murya ya ce " *Meerah* ya jikin ki."

Kusan suman wucin gadi ta yi, don lokacin da tattausar murya shi ya ratsa kunnenta, cak bugun zuciyarta ya tsaya, kamar sabuwar makauniya haka ta kure fuskar shi da kallo ba tare da ta amsa mishi ba.

Ganin haka yasa ya yi karfin halin sakar mata tattausar murmushi, abin da ya yi sanidiyar lumshewar idanunta a hankali ta sake budewa a kan shi, still murmushin na nan bai 6ace a fuskar ba, cikin k'asa k'asa da murya ya sake kira sunanta da cewa "My Meerah."

Gudun wahayenta ne ya ninku, la66anta ne su ka kama rawa alamar tana son furta wani abu amma ta kasa, gyada mata kai ya yi ya ce "Yess My Meerah, do u lik d name? Bata iya amsa tambayar ba, sai kawai ta tsinci kanta da rintse idanu tare da furta "Ya Allah na roke ka, kar ka farkar dani daga wannan daddadar barcin da nake yi, Ya Allah ka dauwamar dani a cinkasa." Ta karashe maganar da fashewa da kukan da ita kanta bata san na mai zata kira shi ba. Bai san sanda ya isa gabanta ba, cike da tausayi ya shiga share mata hawaye, cikin rad'a ya ke cewa; It's reality Meerah ba mafarki bane, nine Ameen d'in ki a gabanki, bud'e idanunki ki kalleni." Samun kanta tayi da budewar kamar yadda ya umarta, suna hada idanu ta mika hannu ta kama nashi ta rike gam! Cikin kuka da fitar hayyaci ta ke cewa; Dan Allah Yaya Ameen kar ka barni, ka tsaya a tare dani ka dauwama a tare dani, kar ka gusa kusa dani na roke ka, yin hakan daidai yake da yankewar numfashi na, bazan iya rayuwa ba tare da kai ba, Ina son ka Ameen, ina son ka ina son ka, kaine rayuwata farin ciki na, idan babu kai a duniyar Amira zan zamo kamar mutum mutumi." Ta karashe da fashewa da wani irin kuka mai narka zuciyar mai sauraro.

"Shiii! ya isa Meerah, ga Ameen a gabanki, na yi miki alkawarin zan rayu dake zan zamo maji6ancin rayuwarki insha Allah." Ya fad'a cikin wani irin amo wanda yake fitowa tun daga kasan zuciyarsa.

Sun dad'e a haka hannun shi, cikin nata, dakyar ya lalla6a ya zare hannunsa tare da komawa mazauninsa ya zauna, yana ci gaba da gaya mata kamalai masu kwantar da hankali, sai ga Amira tana dariya kamar wayiya, kallonta yake cike da tausayi tare da kara tabbatar da cewa lallai shine farin cikinta.

kiran isha'i ne ya tayar da shi, kafin nan sai da ya yi mata alkawarin shigowa da safe ya dubata kuma ya jaddada mata ta tabbatar ta ci abinci da yawa.

Cikin kwana uku da faruwar haka sai ga Amira ta gyagije ta mike tsaye kan kafafunta, kamar ba itace a kwance rai a hannun Allah ba, lamarin da ya baiwa kowa matukar mamaki banda Aysha Fatima da Zainabu da su ka san abin da ke ciki.

Al'ameen yana iya kokarinsa wajen ganin ya wanzar da farin ciki a gareta, kullum yakan shiga ya dubata suyi hiran hakan ya jefawa Mama zargin wani abu a zuciyar ta, Fatima kam kusan tafi kowa farin ciki don tsakanin ta da Allah har zuciyar ta take kaunar Anty Amira, ba don warning din da Al'ameen ya mata akan kar fa fadawa Ummi ba, da tuni ta fada, duk da haka takan yi su6utar baki wani bin.

Yanzu damuwar Al'ameen bai wuce Aliyu ba, tun daga ranar da wannan abin ya faru basu sake haduwa ba ranar da damuwa yadda su ka rabu ya kwana, a zuciyar sa yaji bai kyauta ma shi ba, ya je gidan su sau biyu baya samun shi, kiran waya kam ya mishi ya fi sau shurin masaki amma baya d'agawa.

*********

Tun da Joy taje gida take ta tunanin albishirin da Fatima ta ce , zata mata a kan Yaya Ameen, kasa juriya tayi don akan duk abin da ya shafe shi zuciyar ta azalzala take, babu yadda bata so ba ta samu hanyar fita ran Sunday zuwa gidan sai dai babu dama, don Mom tasata tayi a gaba tunda sassafe suke wuce church ranar acen suna kusa wuni, haka ta kwana da daukin wayewar garin Monday, sai dai cikin rashin sa'a ranar karatu ta yi musu zafi, kuma da aka yi closing Mom ce da kanta ta zo daukarta, ba don ta so ba ta bita suka wuce gida da kudirin koma menene gobe baza ta rabu da Teetee ba sai ta gaya mata...... [12/29, 2:46 PM] AyshaNalado: ๐ŸŒ€๐ŸŒ€ *JOY* ๐ŸŒ€๐ŸŒ€

~FARHAT~