PAGE 39
Mikiya Writer's Association.
"Menene mafitar?" Al'ameen ya tambaya idanunsa cikin na Aliyu. Nannauyar ajiyar zuciya Aliyu ya sauke, cike da kwarin gwiwa ya ce "Dr Abdul Hafiz ." Wani irin k'ank'ance ido Al'ameen ya yi, a hankali ya maimaita sunan da sigar tambaya "Dr Abdul Hafiz S Alto?" "Kwarai shi nake nufi." Aliyu ya fad'a shima yana kafe Al'ameen da ido.
Bacin rai ne ya bayyana k'arara a fuskarsa take, a kausashe ya ce "Menene had'in ka da shi?" Dakewa Aliyu ya yi daman yasan hakan zai iya kasancewa, ba tare da shayin komai ba ya ce "Zumunci." Gyada kai Al'ameen ya yi, ya ce "Zumunci ko? Very gud." Daga haka ya mik'e bai kalli side d'in da Aliyu yake ba ya fice daga d'akin jiri na kwasarsa.
Murmushi Aliyu ya saki a yayin da ya raka bayan shi, da kallo, taurin kan Al'ameen ya wuce tunanin mai tunani, idan ya riga ya kau da kai a kan mutum da wuya ya k'ara waiwayarsa ko shi waye, sai dai ya lashi takobi zai yi iya 'kokarinsa wajen ganin komai ya daidaita.
*********
*JOY*
Tun daga ranar da Fatima ta sanar da ita batun soyayyar Yaya Ameen da Amira, bata sake yarda wani hira makamancin wannan ya sake shiga tsananinsu ba domin ta san baza ta iya jurar ji ba, zuciyar ta baza ta iya d'auka ba. Haka suka ci gaba da harkokinsu ba tare da ta bari Fatima ta fahimci komai game da abin da ke lullu6e a zuciyarta ba, ta bi ta toshe duk hanyar da Fatima zata fahimci a kwai wani abu a zuciyarta game da Ameen, tun da ta fahimci kamar Fatin na zargin hakan, sai dai duk wani walwala da kuzarinta ya ragu, sam! ta daina tambayar Fatima game da Al'ameen kamar yadda take yi ada, idan ma Fatima ta dauko hirar shi, da dabara za ta dakatar da ita ta hanyar sako wani hirar dabam ta shashantar da wancen hakan ya saka zuciyar Fatima a wa si wasi a kan zarginta, har ta samu kwanciyar hankali, don ta yi imanin cewa; Joy baza ta ta6a boye mata wani sirri na rayuwarta ba, sai ta watsar da zargin da ta ke yi suka ci gaba da sabgarsu na yau da kullum babu wani sauyi.
Joy kuwa kwantan 6auna ne kawai ta yi, don zuciyarta cike ta ke taf da kaunar Al'ameen, ita kad'ai ta san irin famar da take da zuciyarta, duk daren duniya sai ta sha kuka ta gode Allah, musamman da ta fahimci yadda ya ke kaunar Amira da kuma yadda itama Amiran ta mace a kaunar shi, ganin haka yasa ta gama sadak'arwa ta rasa Al'ameen domin dai da idanunta take ganin zallar soyayyar Amira a tattare da shi, hakan yasa take jin wani irin mahaukacin kishi da haushinta na babu gaira babu sabar, har yau ta kasa bata fuska su dinga ko da gaisuwar mutunci ne, ba yadda bata yi don ta tausasa zuciyarta a kan hakan ba abin ya gagara, Fatima da ke tsakanin su, sai ta bar hakan a kan cewa jininsu ne bai hadu ba.
A duk sanda ta zo gidan ta yi rashin sa'a da katarin ganinsu a tare, ranar takan wuni ta kwana da mugun ciwon kai, bata ta6a zaton duk wadannan abubuwan da take ji shafar mai ba ne, sai yau da suke k'ule a uwar d'akin Ummi, Fatima na sanar da ita cewa iyayen Anty Amira sun ce Yaya Ameen ya turo magabatansa a zo ayi zancen aurensu. Kamar saukar gudumar wuta haka zancen ya daki zuciyarta, da sauri ta kai hannu ta dafe saitin zuciyarta da ya yi wani irin dokawa da mugun k'arfi, a dan gigice Fatima ta kalleta tare da cewa "Ar u ok." "yes I'm ok." Ta fad'a da sauri tana ya mutsa fuska jin gefen kanta ya fara sara mata, sannu Fatima ta shiga jero mata, ta gyada kai tare da mik'ewa tsaye, Fatima ta kalleta da mamaki ta ce "Ya dai friend ina zaki je ?." "Teetee I want 2 leave now." Ta fad'a cike da wani irin rauni a muryarta, mik'ewa Fatima ta yi ta riko hannayenta tana kallon cikin idanunta, cikin k'asa-k'asa da murya ta ce "Ki gaya min dan Allah, menene?" Tsura mata idanu ta yi, na yan sakanni take hawaye ya ciko a kwaurin idanunta, can kuma kamar an tsikareta ta fisge hannayenta da sauri ta fice daga d'akin tana sharar kwallah.
Wani irin tafiya take yi tana layi kamar yar caburos, duk in da ta samu jefa kafarta kawai take yi ba tare sa kula ba, gaba daya idanunta sun kulle bata ko ganin gabanta, tuni hawaye ya gama wanke mata fuska cikin kankanin lokaci.
Babu zato babu tsammani ta ji an ca6e hannunta, yana yin sauyin bugun zuciyarta da kuma kamshin turaren shi ya tabbatar mata da cewa shi ne, hannun shi da ke rike da nata ta kalla, kafin a hankali ta d'ago kai ta sauke idanunta a fuskar shi.
Wani irin kallo yake binta da shi, mai dauke da ma'anoni daban-dabam, d'ago idanun da ta yi, ya ba shi damar sauke kwayoyin idanunsa a cikin nata, wani irin kallo suke bin juna da shi mai kama da kallon kuda, hawaye ne ke zurara a kumatunta, hawayen zallar so da kauna, yayinda shi kuma na shi idanun suka kara rinewa jajur, zakarar wuyar shi na motsawa yake alamar yana hadiyar wani abu wanda shi kad'ai yasan ko menene, dawowarsa kenan daga wajen Aliyu zai shiga gida ya ci karo da ita, ganin yana yin da take ciki yasa ya kasa bari ta wuce, domin da gani ba lafiya ba.
Kamar an wuntsilota daga sama ta bayyana a gabansu, wani irin abu ta ke hanga kwance a idanuwansu su duka biyun wanda bata fatan ace gaskiya ne, shin ina ma mafarki take yi' cike da matsanancin tashin hankali, cikin rawar murya ta ce "Yaya Ameen." Sautin muryarta ya daki kunnuwansu baki d'aya, sai dai ko da wasa Al'ameen bai dauke idanusa daga fuskar Joy ba kuma bai saki hannayenta ba.
Yayinda ita kuma ta d'ago manyan jik'akk'un idanunta ta sauke su a kan fuskar Amira dake tsaye tana binsu da kallo hankali tashe, suna had'a idanu ta ji wani irin k'ululun abu ya tokare mata makoshi, wani irin kuka ne ya taho mata daga can kasar zuciyar, da mugun k'arfi ta fisge hannunta daga rik'on da ya mata ta juya da gudu ta bar wajen.
Ba shi da kuzarin tsayar da ita domin jin damuwarta, shi kan shi cikin matsanancin damuwa yake, Sai dai ganinta cikin damuwa ya so mantar da shi ta shi damuwar.
"Yaya Ameen." Sautin muryarta a karo na biyu ya ratsa kunnuwarsa, a hankali ya dauke idanunsa daga hanyar da Joy ta bi, ya sauke a fuskarta, hawaye ya gani kwance a kwaurin idanunta, tsabar wutar kishi da tashin hankali kwance karara a idanunta.
A halin da yake jin kansa bai san mai zaice mata ba, sai kawai ya samu kansa da cewa; Ban san menene ya saka ta kuka ba, bansan me yasa na damu da damuwarta ba abin da na sani kawai ina jinta a zuciyata misalin yadda nake jin Fatima a raina, bana son ganin hawayenta kamar yadda bana son ganin hawayen Fatima.
Kasancewarta mai tsananin wayo, yasa ta yi murmushin yak'e wanda aka ce yafi kuka ciwo, tana share hawayenta da bayan hannu a fakaice ta ce " Wata kila hakan nada nasaba da yadda suna shaku da Fatima ne, tabbas nima ina kaunarta a raina kamar yadda nake kaunar Fatima." Tsura mata idanu ya yi, shin da gaske take abin da ta fada ya ke tambayar kansa, yayinda maganganunta suka maimaita Kansu d'aya bayan d'aya a kunnuwansa.
Ganin haka yasa ta ra6a ta fice ta gefensa ba tare da ta sake kallonsa ba.
************
Ragwab! Fatima ta koma ta zauna a kan gadon Ummi, hankalinta a tashe, shin' me abinda Joy tayi yake nufi, wannan shine karo na biyu da shigen irin haka ya faru, kar dai ace zargin da ta dade da cirewa aranta ne ke shirin tabbatuwa, zumbur ta mik'e, ya zama dole ta tabbatar kafin ta zartar da wani hukunci da mugun sauri ta biyo bayanta, a zaure suka yi kicibus da Al'ameen, kallon tuhumar daya jefe mata yasa da sauri ta ce "Yayana ka had'u da Joy a waje." Girgiza mata kai kawai ya iya yi ya bude d'akinsa ya shige,yana tambayarta Ummi ta dawo? A sanyaye ta amsa mashi da "A'a Taya." Kafin ta juya jiki a sanyaye ta kima cikin gida zuciyar t ciek da tunani kala-kala.
Sai da Joy ta kwashe kwana biyar bata je gidansu Fatima ba kuma bata je school ba, tana gida tana fama da mikin zuciyarta don sai da ta kwashe kwana biyu kwance tana fama da zazza6i da ciwon kai, lamarin da sai da Mom ta kira Dr solo ya daura mata drip kafin ta ji dama dama, wannan shurun na Joy ya saka Fatima a cikin matsanacin damuwar da ya kasa 6oyuwa a tattare da ita duk kuwa yadda ta so boyewar, Al'ameen ne ya fara lura, ritsata ya yi a d'akinsa ya tambayeta meke damunta, bata 6ata lokaci ba wajen sanar da shi damuwarta ba, san da ta ambaci Joy sai da gabansa ya fad'i, tun Daga ranar da abin nan ya faru da tunanin ta yake kwana yana tashi, taurin kai da dakiya ce kawai irin ta shi yasa bai bude baki ya tambayi Fatima ba, dakewa ya yi ya shiga bata baki a kan ta cire damuwa a ranta domin dai lafiya ita ke 6uya.
Ranar Monday kamar wasa Fatima na shiga class ta tarad da ita, da gudu ta karasa ta rungumeta ya baya, ranar basu maida hankalin kan darusan da aka koyar ba, saboda yadda sukayi kewar juna, Fatima ta so ta tuhumeta a kan abin da yasa ran nan ta fice ta barta daga ta yi mata zancen Yaya Ameen da Amira sai kuma wani tunani ya fado mata ar rai wanda tilas ya sakata fasawa.
**********
Ajiyar zuciya Zainabu ta sauke bayan ta gama sauraren jawabin Amira, kallon Amira tayi da ke kuka sha6e sha6e ta ce "kin tabbatar da abinda kike fada kuwa Amira." Cikin shessheaka ta ce "Tabbas na tabbar da idanuna na hango tsantsar soyayyar Arniyar yarinyar na kwance a cikin kayan idanunsa dan Allah Zainabu ki bani shawara ya zan yi wallahi zuciyata zata tarwatse."............
Afuwan masoya๐
Oum Ummeetarh *** [12/29, 2:49 PM] AyshaNalado: ๐๐ *JOY* ๐๐
~FARHAT~