JOY

PAGE 40

by @aishanalado88

Mikiya Writer's Association

*Masu facebook ku yi following wannan account ɗin domin samun damar cin giveaway ɗin da muke yi, da kuma tattaunawa akan yanayin rayuwa*

***

Kwantar mata da hankali Zainabu ta yi, tare da ba ta shawara a kan ta yi kunnen uwar shegu da abin ta cire shi daga zuciyarta ta yi kamar bata fahimci komai ba tunda dai hasashe ta ke yi bata da tabbas a kan lamarin. Cikin kuka ta ce "Wallahi Zainabu da idona na gani ya rik'e hannayenta, suna bin juna da wani irin kallo, kollon da bai ta6a yi mini irin shi ba, irin kallon da nake fatan samu daga gare shi koda a mafarki ne. Ta6e baki Zainabu ta yi ya zuwa yanzu lamarin Amira ya fara bata haushi, cike da jin haushi, ta ce " Ke dai Wallahi an yi raguwar banza, yanzu haka ma fa ba abin da ki ke tunani ba ne shegen kishinki ne yasa ki ke ganin hakan, ta yaya Ustaz kamar Al'ameen zai tsaya soyayya da wata arniya mai fistari a tsaye, ai ruwa ba sa'an kwando ba ne, ni kam ko duk jikina kunne ne ban yarda ba." Murmushin takaici Amira ta yi, ta na kallon Zainabu a zuciyarta tana cewa; Hmm! Zainabu don dai ba ki san so ba ne shiyasa ki ke cewa haka, "Kallon fa?" Zainabu ta fad'a tana dan zaro mata ido had'i da d'an hararanta, girgiza kai ta yi tare da sakin murmushin yak'e wanda ya fi kuka ciwo.

Amira ta dauk'i shawaran Zainabu don kuwa koda wasa bata yarda ta yima Al'ameen maganar Joy ba haka ma Fatima duk irin yadda abin ya tsaya mata a rai kuwa.

A haka tafiya ta mik'a a ka kwashe satittika, har zuwa lokacin kuwa Al'ameen bai tura magabatansa wurin kawunnan Amira ba kamar yadda suna buk'ata kuma bai ce musu komai ba, ganin shirun nashi ya yi yawa yasa d'aya daga cikin k'annen marigayin mahaifin nata kiran Al'ameen har gida.

Tare suka shirya da Aliyu suka tafi gidan nasa bayan sallar isha'i, d'aya daga cikin samarin gidan ya musu iso har falon kawu Basiru kamar yadda suke kiran shi, bayan gaisuwa aka gabatar musu da ruwa da abin motsa baki, sai da suka d'an ta6a hira da Aliyu kasancewar kawun mutum mai yawan magana sai dai mafad'aci ne na karshe, haka ma Alin shima magananne ne ba laifi idan ya samu waje. Al'ameen kam kansa na k'asa yana saurarensu gabansa na fad'uwa ya k'agu ya ji kiran me a ka yi masa.

Sun dan d'auki lokaci a haka kafin kawu Basiru ya yi gyaran murya ya ce "Am! Aminullahi." D'agowa Al'ameen ya yi ya kalle shi tare da sake yin k'asa da kai cike da surukuta, "Abinda yasa na kira ka, mun ji shirunkaya yi waya, yau kimanin wata 3 da aka yi maka magana ka turo magabatan ka amma har yanzu shiru, to mun gaji da gafara sa kuma har yanzu bamu ga k'aho ba, domin dai yarinya cikin y'an uwanta wani ya ganta kuma ya nuna yana so , to kaga gida bai k'oshi ba ba'a kai waje ba, sai dai kasancewar mu ba k'ananun mutane bane yasa jiya muka zauna ni da y'an uwana, a kan maganar, yanzu dai an umarceni kasancewar nine k'arami a cikinsu suka wakiltani a kan na kira ka na shaida maka, an baka nan da sati d'aya idan har da gaske ka ke muji wani motsi idan kuma ba haka ba, to gaskiya komai zai iya faruwa, wannan shine mak'asudin kiran da na yi maka da fatan ka fahimce ni."

Tun kafin kawu Basiru ya kai aya a maganarsa, tuni gumi ya tsatsafowa Al'ameen a gaban goshi, banda dukan uku-uku babu abin da zuciyarsa ke yi, sai Aliyu ne ya yi karfin halin amsawa kawu Basiru da cewa; Na'am kawu mun fahimta." Ya ce "Toh dama kiran ke nan idan kuna da abin fad'i kuma ku fad'i ina saurara." Aliyu ne ya sake amsawa da "A yi hakuri kawu, in sha Allah zaku ji mu kafin satin." Da haka suka yi sallama da kawu basiru, Aliyu ya ajiye masa naira dubu uku suka fito.

Daga Alin har Al'ameen an rasa mai karfin halin cewa wani abu, har suka yi nisa da k'ofar gidan, shi Aliyu ganin halin tashin hankalin da abokinsa ya shiga ne ya sanyayar masa da jiki hakan ya tabbatar masa da akwai wata matsala, yayinda A bangaren Al'ameen yake hasaro irin tashin hankalin da Ummi ta shiga ranar da ya fara sanar mata da cewa; Iyayen Amira sun nemi ya turo, wannan na d'aya daga cikin abin da yasa har yau bai sake tayar da maganar ba, bawai don ya rasa naira dubu goman da za'a kai a matsayin kudin gaisuwar ba, kwarai ya hangi firgici da tashin hankali a cikin kwayar idanunta, wanda har ya kai ta ga son yin su6ul da baka a gabansa ta furta wasu kalamai da suka hana shi rintsawa a daren ranar.

Aliyu ne ya katse shirun da cewa; Abokina ya kamata fa ka yi wani motsi a kan lamarin nan, ka dai ji abinda kawu ya fad'a, kar ka yi sakacin da zaka rasa Amira domin na lura kiris suke jira shi yasa suka yi maka wannan daurin talalar, duk da nasan kai ko da ta subuce makan ba damuwa zaka yi ba tun da ba wani sonta kake yi ba" Ajiyar zuciya ya sauke, da wani irin sanyin murya wanda Aliyu bai ta6a jin ya yi irinta ba ya ce "Aliyu ina son Amira, wallahi ina kaunarta ina fatan ta zame mini uwar y'ay'ana, sai dai ina jin tsoron wani abu, ina ji a jikina a kwai gagarumar matsala." "Wacce irin matsala? Aliyu ya jefa masa tambayar cikin dan tashin hankali, cike da wani irin k'unci ya ce " Dangin mahai...." Sai kuma ya yi shiru ya girgiza kai, Aliyu ya dafa kafadarsa ya ce "Dan girman Allah kar ka boye mini matsalarka abokina, idan kamin haka zaka saka zuciyata cikin zullumi." Shiru ne ya ratsa tsakaninsu na yan sakanni, kamar bazai ce komai ba, can kuma ya sauke nannauyar ajiyar zuciya, kafin ya kwashe komai ya fad'awa Aliyu, shi kan shi Aliyu abin ya so girgiza zuciyarsa, sai dai bai nuna hakan a fili ba, ya ce "Wannan ba hujja ba ce da zai ka kasa sake tunkararta da wannan maganar, Ameen ka sani anzo gabar da dole ne kusan su wanene ku." Wani irin kallo ya shiga bin Aliyu da shi kamar ranar ya soma ganin shi a duniya, domin ya sosa masa inda ya dad'e yana masa k'aik'ayi." Basu rabu ba sai da suka tsara yadda lamarin zai gudana.

Bai iso gidan ba sai wajajen k'arfe goma da rabi, kamar yadda ya zata a tsakar gidan ya tarad da su, Fatima na kwance barci ya kwasheta yayinda Ummi ke kishingid'e tana sauraran redio, ta amsa masa sallama tana mik'ewa zaune, tare da gyara rik'on carbinta da gyangyadi yasa ya kusa subucewa daga hannunta.

"Barka da gida Ummi." Ya fad'a yana zama a gefen tabarmar, dan tsira mashi ido ta yi ganin kamar yana tattare da damuwa kafin ta amsa masa da "Yawwa barka da dawowa Amintacce." Ganin irin kallon da take binsa da shi yasa ya yi saurin yin kasa da kai, gabansa na faduwa, ya ce "Fatima ta yi barci kenan." Ta amsa da "E ta yi da kyar bayan ta gama dakon jiran ka, kazo ka ji mata hadda." Murmushi ya yi idanunsa kan kanwar ta shi tare sa cewa; "Allah sarki yar uwata." Lamarin da ya saka Ummi sakin murmushi ba tare da ta sani ba.

Bayan ya ci abinci ya fusakanci Ummi gabansa na wani irin dokawa yace "Ummi kawun Amira ya kirani d'azu a kan yana son ganina." Dakatawa ta yi da kokarin canza channel din da take kokarin yi ta zubawa fuskar shi manyan fararen idanunta masu cike da kwarjini...........

Har kullum Afuwan shine abin da zan iya cewa gareku masoya🙏

*Pls a ta6a comment domin shi ke saka min karsashin yi muku typing ko da ban yi niyya ba*

Oum ummeetarh. *** [12/29, 2:49 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀

~FARHAT~