JOY

PAGE 44

by @aishanalado88

Mikiya Writer's Association

Cike da tsananin tashin hankali Al'ameen ke safa da marwa a bakin d'akin bada agajin gaggawa na karamar asibitin dake unguwarsu, in da suka yi gaggawar kai Ummi bayan sun fahimci suma ta yi ba mutuwa ba, tunda suka kai ta kimanin awa hudu a tsaye yake kamar mashi, a k'ofar d'akin sallar magriba da ishsha ne kadai ya kau da shi daga wajen, Fatima na zaune a kan d'aya daga cikin bencinan da a ka tanada domin zama, sai kuka take yi idanunta sun kumbura sun yi jajur, dawowarta daga hadda ta tarar da wannan tashin hankalin ko gida bata kai ga shiga ba ta ga an fito da Umminta a sume kamar gawa, hakan ya daga mata hankali, a guje ta kutsa kai cikin napep din da aka sanya Ummi ta kamkameta tana kuka, tun lokacin take rusar kuka har zuwa yanzu da ake neman karfe goman dare. Yau dai kam kasa rarrashinta Al'ameen ya yi, Aliyu da Maman Amira wacce ta biyo su asibitin daga baya ne suke kokarin bata baki idan suka ga kukan nata ya yi yawa.

Likita ne ya fito daga d'akin , da sauri suka yi caaa! A kan shi kowanne na jeho mishi tambayar da ya zo bakinsa duk a game da Ummi, kallonsu ya yi cike da tausayawa ganin yadda hankalinsu ke tashe, murmushin kwantar da hankali ya sakar musu, ya daura da cewa "Ku yi hakuri yaran Ummi, Ummi tana lafiya, firgicine ta shiga shine ya haifar mata da daukewar numfashi ta yi, dogon suma, yanzu dai Alhmdllh mun bata taimakon da ya dace ta farfado tun dazu,sa dai mun yi mata allurar barci domin kwakwalwarta ta samu hutu, zuwa safiya in dan Allah ya kai mu zamu sallameta.

Hamdala Aliyu da Maman Amira suka shiga jerowa, Al'ameen ku wa rintse idanu ya yi shima yana jero hamdala a zuciyarsa, wani irin farin ciki da kwanciyar hankali na maye gurbin fargaba da tashin hankalin da ke dankare a zuciyarsa. Yayinda Fatima ta rungume Mama ta na shessheka tun da dama cikin kuka take.

Aliyu da Ameen ne suka kwana a asibitin, Mama da Fatima kuma suka tafi gida, bayan sun shiga sun duba Ummi, tana barci kamar yadda likita ya fada.

Bayan tafiyarsu ne Al'ameen ya samu damar baiwa Aliyu labarin abin da ya sani game da abinda ya faru, yana ba shi labarin zuciyarsa na kara daukar zafi yana sake cin alwashi a kan kassara rayuwar koma waye wannan mutumin, shi kan shi Aliyu ran shi ya baci, zuciyarsa ta tashi har yaso yafi Ameen daukar zafi a kan lamarin, ko da wasa bai ta6a kawo hakan a ransa ba, ya ciji yatsa ya fi sau shurin masaki a kan rike Al'ameen da yayi har mutumin da ko sunan sa basu sani ba ya samu damar guduwa, karshe Ameen ne ya koma tausarsa.

Washegari karfe goma a ka sallami Ummi, a lokacin Fatima da Amira ne ke tare da ita don Aliyu tun wuraren bakwai ya tafi gida da zummar kimtsawa ya dawo, Al'ameen ma ganin sun zo yasa ya tafi gida don yin wanka.

Sosai makota da abokan arziki sukai ta shigowa yi wa Ummi sannu, yinin ranar bata samu kanta ba, kallo daya zaka san bata cikin walwala amma haka ta daure ta saki fuskarta ta dinga amsa gaisuwar yan dubiya.

Ranar da matsanancin damuwa Al'ameen ya kwana, bai iya rintsawa ba, burinsa ya ji daga bakin Ummi 'shin wanene wannan mutumin, domin baya jin har duniya ta nade zai iya yafe mishi.

Washe gari da safe ko da ya je gaisheta bata ce masa komai game da batun ba, haka ya shirya ya tafi makaranta jiki babu kwari, da yamma tare suka shigo gidan da Aliyu ya biyosa don ya sake gaida Ummi duk da jiya ma yazo, kuma mahaifiyarsa da matar kawunsa harma da kannensa sun zo suma a jiyan.

A falonta suka same ta zaune a kan dadduma, carbi a hannunta tana lazumi, zama suka yi suna jiranta, itama ganin shgowarsu yasa ta yi sauri ta kai karshen lazumin, Aliyu ne ya fara gaisheta da jiki ta amsa cike da kulawa, Al'ameen ma ya sake gaisheta.

Daga haka duk zama suka yi jugum-jugum daga yanayin fuskokinsu ta fahimci da magana a bakunansu, ajiyar zuciya ta sauke dama ta san ko ba jima ko ba dad'e wannan ranar zata zo, bata gama tunanin da take yi ba ta tsunkayi muryar Al'ameen yana cewa.

"Ummi don Allah da manzonsa ki gaya mini wanene wannan mutumin? Kallonsa ta yi sai kuma ta yi shiru, ba tare da amsa shi ba, ganin haka yasa Aliyu kar6ewa da " Ummi don Allah ki daure ki sanar da shi, domin yana cikin matsanancin damuwa ni shaida ne, saboda ni amininsa ne, muna da kusancin da bazai iya boye min duk wani damuwarsa ba, nine na ba shi shawara a kan ya zo ya tambaye ki, shi kuma ya ya dauko ni don na taya shi rokon ki, Ummi don Allah ki fad'a masa menene hadin ki da shi."

Ajiyar zuciya ta sauke a karo na biyu, ta ce "Dama ko baka tambayeni ba Yayan Fatima yau ne na yi niyar sanar maka su wanene ahlin Alhussain a gare ku da nima baki d'aya." Aliyu ya ce "Alhmdllh Ummi, Ameen ya dade yana tsumayen wannan ranar tsayin shekaru." Ya k'arashe maganar cike da tsantsar farin ciki kamar shine Ameen d'in. Murmushi Ummi ta yi tana sake jinjina amintar dake tsakanin Aliyu da Ameen, kamar dai Fatima da Joy.

Fatima ce ta shigo d'akin daga hadda take, ganin yayyinta yasa fara'ar fuskarta k'ara fad'ad'a, ta gaishesu baki d'aya a ladabce, ta wuce uwar d'aka ta ajiye hijabinta da jakar haddarta ta fito zata wucesu, har ta kai bakin k'ofa, Ummi ta dakatar da ita ta hanyar cewa "Fatima! Kema zo ki zauna." Bata musa ba ta dawo ta samu guri kusa da Yayanta ta zauna, zuciyarta na tsinkewa haka kurum take jin gabanta na fad'uwa.

Mikewa Aliyu ya yi, da nufin tafiya gida don ya basu waje, Ummi ta dakatar da shi da cewa; Dawo ka zauna Aliyu, domin kuwa kaima d'ana ne, tamkar Al'ameen haka nake jin ka." Bud'e baki ya yi da nufin yi mata musu, sai dai ganin yadda ta tsare gida yasa ya kasa, sai dai bai koma ya zaunan ba kamar yadda ta umarceshi, idanunta ta watsa mishi, irin kallon da take yi wa Al'ameen idan tana son ladaftar da shi, babu shiru ya koma ya zauna.

Sauke kai Ummi ta yi kasa ta yi shiru duk ido suka zuba mata falon ya dauki shiru na tsayin mintuna biyu, a hankali ta dago idanunta da suke cika taf da kwallah cikin wani irin murya mai sanyi wacce basu ta6a junta da irin shi ba ta fara cewa..............

Oum ummeertah ***

[1/18, 12:39 PM] ***: ๐ŸŒ€๐ŸŒ€ *JOY* ๐ŸŒ€๐ŸŒ€

~FARHAT~