JOY

PAGE 46

by @aishanalado88

A cikin wannan hali na kwashe shekara d'aya har da watanni a gidan Mamman kura, har zuwa lokacin babu abin ya canza dangane da muguwar k'iyayya da kyarar da na ke fuskanta daga ahlin gidan sai ma abin da ya 'karu.

A bangaren Al-husain tuni tausayi ya rikad'a ya koma sassanyar soyayya mai cike da dumbin kulawa da kyautatawa, sannan ga wata shakuwa mai tsanani minallahi daya k'ullu tsakaninsa da Al-ameen, har ta kai ga shi Ameen ke kallo a matsayin mahaifi, yayinda ni kuma a bangarena nake matukar ganin mutuncinsa na ke girmama shi na dauke shi tamkar wa na wanda muka fito ciki d'aya.

Hankalina ya tashi, ranar da Al-husain ya bayyana soyayyar sa a gareni, take jikina ya d'auki rawa, fatana Allah yasa wani bai ji mu ba, don nasan akan wannan lamari tsab ahlin gidan nan zasu iya cinna min wuta da raina, kuka na fashe mi shi da shi na shiga rokansa akan ya yi hakuri ya janye wannan maganar a tsakaninmu, take ya lashi takobi tare da tabbatar min da matukar na aminta da shi babu wanda ya isa ya hana shi aurena koda kuwa Dada ce (Mahaifiyarsa)

Ranar tsabar fargaba da zazzabi na wuni, wasa wasa ciwo ya kwantar da ni sosai, hakan baisa Dada ta ji tausayina ba bare y'ay'anta basu raga min da komai ba sai ma k'arin tsangwama ganin bana gama aiyuka da wuri kamar yadda na saba yi.

Al-husain ne kadai ya damu da halin da na ke ciki, bai β€˜bata lokaci ba wajen siyo min gamungunan zazzabi a chemist na sha, sai dai sam babu sauki sai ma canza salo da ciwon ya yi, na shiga amaye-amaye babu abin da nake iya ci sai ruwa, ga kasala da yawan barci, cikin kwana biyu na kara ramewa na yi wani irin haske na d'anyance.

Har d'aki hajiya Dada ta biyo ni, ta kama tafukan hannuna ta duba ta kware idona shima ta duba, sai kawai ta kwantsama salati tana tafa hannaye, take d'aki ya cika abinka da gidan gandu, duk da lokacin hantsine mazan gidan basa nan, ta fashe da kukan kissa tana cewa "Dama na sani tsintacciyar mage bata mage, yanzu da abin da za ki saka mana ke nan, cikin shege a gidan Maman kura." Nan duk kowa ya shiga tafa hannaye ana sallallami, "Wallahi ciki ne da yarinyar nan, ku duba ku gani." Ta fada tana finciko ni tsakiyar d'akin, nan take suka yo caa! A kaina mai zagi na yi mai dunguri na yi, hajiya Dada kuwa sai cewa ta ke "Wallahi yau sai kin bar gidan nan ko na ubanki, baza mu ci gaba da zama da bara-gurbi ba, munafuka annamimiya." ta shiga kwasan y'an kayana da basu da yawan arziki tana watsi da su a tsakar gidan y'ay'anta na taya ta.

Dai dai lokacin Yaya Tanimu ya shigo gidan jin abinda ke faruwa ya harzuka shi, take ya zare belt ya shiga tafta min cike da bakin cikin hanashi cika muradin shi a kaina da na yi na baiwa wani cen banza har yana min ciki a cewarsa, duka na yakeyi a haukace yana furta "Uban wa ya yi miki ciki? Uban wa ki ka baiwa kanki?

Sam bana iya Kare kaina daga mugun bugun da Yaya Tanimu ke min, bare na samu damar amsa mishi tambayar shi, domin tun lokacin da Hajiya Dada ta furta cewa ciki ne da ni kaina ya sara tashin hankalin wannan furucin yasa duk abin da ke faruwa bana wani fahimta, ta yaya zan yi ciki,shin ana shan ciki a ruwa ne? Sune tambayoyin da suka dinga yawo a kwakwalwata.

Rashin samun amsa daga gareni ya k'ara harzuka Tanimu, shakeni ya yi da hannu biyu idanu jajir ya ke cewa a tsawace " Wa ya mi ki ciki Balki! Wallahi idan ba sanar min wanda yayi miki ciki ba sai na kashe ki! Uban wa ya miki cikin na ce!"

A guje ya shigo d'akin yana haki, ganin abin da ke ya faruwa yasa ya ya yi kukan kura ya cakumi Tanimu tare da yi mai wata irin shaka wanda yasa dole ya sake ni ba shiri, na zube a wajen kamar matacciya da dudu Al-meen ya fada kaina na yana girgizani tare da kiran sunana yana kuka.

Dakyar Yaya Tanimu ya kwaci kanshi, daga mummunar shakar da d'an uwan nasa ya yi masa.

A matukar fusace cikin daga sauti Al-husain ya shiga cewa, "Ba wanda ya yi mata ciki ku ke son sani ba! To ni ne na yi mata, d'ana ne a cikinta ni ne Uban cikin dake jikinta, kuma babu in da zata je zama a cikin ku yanzu ta fara shi domin ni zan aureta!"

Tasss! Hajiya Dada ta dauke shi da wani wawan mari, "Baka da hankali ne Usaini! A gabana ka ke furta cikin jikinta na ka ne, kuma za ka aureta! To bismillah shege ka fasa tsanin ni da kai, wallahi akan wannan tsintacciyar mahaukaciyar ina daf da daga maka nono."A fusace ta juya ta bar d'akin,Tanimu ya rufa mata baya yana 'kwafa tare da girgiza kai cikin tsanin bakin ciki.

Da sauri ya yo kaina ya dagoni hawaye kawai ke bin fuskata, da shakakkiyar murya na fara girgiza kai ina ce masa " wallahi ni ba fasika ba ce, ban taba kusantar wani d'a namiji ba." Ya ce "Na sani Balkisu ke ba mazinaciya ba ce, ni shaida ne ki kwantar da hankalin ki nasan ba ki da wani ciki sharri su ke miki." Ganin yadda na galabaita yasa ya ce na yi kokari na taka zuwa mota muje asibiti, ban iya ni kadai a dole sai da ya tallafa min.

Gado Dr ya bani ganin mawuyacin halin da nake ciki, a office ya rufe Al-husain da fada akan me za'a yiwa mace me karamin ciki irin wannan dukan, kasak'e Al-husain ya tsaya yana kallon Dr ke nan dai ta tabbata cikin ne da ni, ta ke zufa ya shiga karyo masa.

Hakuri ya shiga bawa Dr, daga bisani ya sanar da shi dukkan abin da ke faruwa, shi kan shi Dr ya kad'u da jin labarina ya tausaya min matuka, sannan ya tattabarwa Al-husain tabbas a kwai ciki a jikina d'an wata biyu, lamarin da ya kara jefeshi cikin tashin hankali, me yasa balkisu zata yi masa haka?

Suna cikin wannan tararrabin wayar Al-husain ta yi kuwwa ya duba ya ga Mallam ne wanda yake bani taimako har zuwa lokacin, bayan sun gaisa Mallam ya sanar dashi, yana neman shi akwai maganar da yake so su yi mai muhinmanci.

Bai bata lokaci ba ya tafi bayan ya baiwa Dr ajiyar Al'ameen.

A zauren Mallam bayan sun gaisa, ya dube shi da kyau ya ce " Yau kimanin kwana biyar, daya daga cikin aljanan da aka yiwa Balkisu asiri da su, ya bayyana a gareni, ya sanar da ni shine wanda aka wakilta ya danne yaron cikin da ke dauke a mahaifarta ya hana shi ci gaba da girma ma'ana ya kwantar mata da cikin, cikin hukuncin ubangiji muka tattauna da shi, mun yi maganganu masu yawa wanda na daukar masa alkawarin bazansanar wa kowa ba, a karshe ya shaida min shi ya tuba ya bi Allah bazai kara cutar da ita ba, don haka ma ya sakar mata cikinta zai ci gaba da girma, a mahaifarta daga in da ya tsaya."

Kakkarfar ajiyar zuciya Al-husain ya sauke a take ya shiga jerowa Allah godiya da kirari, daga bisani ya kwashe labarin halin da suke ciki ya sanarwa Mallam, Mallam ya jinjinawa iko da sarauta irinta mabuwayi Allah, ya kuma baiwa Al-husain wasu shawarwarin da zasu taimaka masa daga haka suka yi sallama.

Lokacin daya dawo asibitin na farka, ina ganin shi na fashe da kuka ina tambayarsa me likita yace game da cikin shin da gaske ne ina da ciki? Cike da tausayawa ya ce, "ki kwantar da hankalinki Balkisu, likita ya tabbatar min babu wani ciki a jikinki." Wannan magana nasa ne ya kwantar min da hankalina ya samar min da natsuwar zuciya.

Kwanana hudu a kwance Al-husain ke jigila da dawainiya da ni shi kadai, ya yi da kudinsa ya yi da jikinsa, sai Dr wanda ya dauki nauyin kawo mana abinci daga gidansa kullum safe, rana da dare , ko Kare bai zo dubami daga gidan Mamman kura ba bare mutum........ [1/18, 12:39 PM] ***: πŸŒ€πŸŒ€ *JOY* πŸŒ€πŸŒ€

~FARHAT~

*BY*

*AYSHA NALADO*

*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*