JOY

PAGE 50

by @aishanalado88

Ƙarfe shida na safe ya gama kintsawa tsab cikin fararen manyan kayan da na zabar masa, ya ɗaura tsadaddiyar baƙar hula, ya yi mini kyau sosai, fuskarsa ta yi fayau sai wani annuri ta ke fitarwa.

Har bakin ƙofar falo na rako shi, ina yi masa Addu'a, ya karɓi jakarsa da ke hannuna ya rungume ni a ƙirjinsa, shiru na yi ina sauraren bugun zuciyarsa yayinda nawa bugun zuciyar ke ƙara hauhawa a cikin kowanne daƙika.

Mun daɗe a haka kafin na yi ƙarfin halin janye jikina, muka haɗa ido ya sakar mini tattausar murmushinsa mai narkar mini da zuciya a ko da yaushe, ji na yi kuka na shirin kuɓuce mini, na yi ta maza na dake, tare da sakin murmushin da iyakarsa laɓɓana, don na san idan na kuskura na yi kuka a gabansa to zai iya fasa tafiyar, bayan kuma ya sanar mini da mahimmancin tafiyar a garesa, amma har ga Allah hankalina bai kwanta da tafiyar ba.

Jin saukar hannayensa a marana ya saka ni dawowa gayyacina, ya ɗage mini gira tare da cewa "Har ya yi kwari, watansa nawa yanzu?," kunya na ji ya lulluɓe ni, ya yi dariya mai sauti cike da nishaɗi ya ce "Hmmm! Kin ɓoye mini ko? kin za ci bazan gane ba ko? To ki sani komai kankantar canji a tattare da ke ina ganewa, na yi farin ciki sosai, na so na zuba miki ido na ga iya gudun ruwan ki, sai dai na kasa, sati ɗaya zan yi da, amma saboda shi zan yi ƙoƙari in dawo jibi mu gaisa da kyau." Da langwaɓe kai tare da cewa "Ni fa ba ni da komai Yaya."

Ringing ɗin wayarsa ya katse shi daga amsar da ya ke shirin ba ni, ya ɗaga, ya ce "Ok ga ni nan fitowa." Bayan ya ajiye wayar ya ce "Zan ta fi Balkisu, ki kula mini da yarana da kan ki da unborn ɗi na." Ya ƙarasa maganar tare da rage tsawo ya sumbaci marata.

Take kwallar da na ke ta ƙoƙarin riƙewa ya cika kwaurin idanuna, ganin haka ya sa ya fice da sauri ya na cewa "Take care luv , za mu yi waya kin ji."

Sulalewa na yi na zauna a wajen, gabana na wani irin dokawa, from no where na ji kuka ya suɓuce min, mafarkina na jiya na sa ke dawo min dalla dalla, na daga hannu na shiga kwararo ma shi addu'ar kariya da fatan isa lafiya.

Na daɗe a wajen ina kuka babu mai rarrashi, kafin na yi karfin halin mikewa na shiga ciki domin shirya Al-ameen ya tafi school ganin ya kusa makara.

Wunin ranar haka na yi shi a wahale, musamman da na yi ta traying lambar Yaya Hussain switch off, ga faɗuwar gaban da tsinkewar zuciyar da ke ta hauhawa a gareni, kafin magrib tuni na fara ficewa daga hayyacina, gani na ke kawai mafarkina ne ya tabbata, ba ni da wanda zan gayawa damuwata ya fahimci halin da na ke ciki a lokacin, Al- ameen da Fatima na saka a gaba ina sambatu kamar taɓaɓɓiya, har zuwa lokacin da dare ya raba.

Ko da wasa barci bai yi gigin kawo mini ziyara ba a wannan daren, haka na zauna ina kuka ina sake traying lambar wayarsa amma maganar ɗaya ce a kashe, ganin wannan bazai fishsheni ba, yasa na mike na dauro alwala, na shiga jero nafilfiliq a'a, Ni kaina bazan ce ga iya adadin raka'o'in da na yi ba saboda ɗimuwa, sai da na ji kafata na rawa na zauna na ci gaba da addu'a, ban san yadda aka yi barci ya kwashe ni ba, sai dai mummunar mafarkin da na sake yi ya saka Ni farkawa a hargitse, na fashe da kuka tare da lalubar wayata hannu na rawa na sake kiran lambar Yaya amma bata canza zane ba.

Kasa jurewa na yi, ban san yadda a ka yi na tsinci kafafuna a tsakar gida ba, duk da duhun dare ga rashin wuta hakan baisa na ji ko ɗar ba, gidan Baaba Hajo zuciyata ke ingiza ni, in je gareta in faɗa mata damuwata ko zan samu sassauci.

Haka na yi ta tafiya ina jin kafafuna kamar ba nawa ba, ko ganin gabana ba na yi, daga ni sai dogon hijabin da na yi sallah akan rigar barcin jikina kafata ko takalma babu, ina isowa zaure na dakata saboda hango mutum da na yi, ya juya baya yana magana a waya ƙasa ƙasa, kafin na gama tantance wanene kunnuwana, suka jiyo mini abin da ya sakani zaman dirshan a wajen, "Ƙusa ka tabbatar Hussain ya mutu?" Ya yi jim kafin ya saki wata irin shaiɗniyar dariya ya ci gaba da cewa "Wondeful wato harda direba, kai dole ma in ƙara maka 500'000, ok ka tsumayeni nan da kwana biyar."

Tashin hankali yasa na ƙasa kwakkwaran motsi a wajen, tuni na dena fahimtar mai ya ke cewa, ina kallonsa ya juya ya yi cikin gidan yana sakin wani irin shu'umar murmushi.

Tsananin tashin hankalin da nake ciki ya sa na rasa a sama na ke ko a kasa, cikin ƙudirar Allah na tsinci harshena da fara maimaita kalmar "Inna lillahi wa Inna alaihi raji'un." Ban san yadda a ka yi na iso dakina ba amma ina kyautata zaton da rarrafene.

Na zuɓe a bakin kofa bayan na rufe ƙofar, a wahalce na ke jan numfashi gefe guda kuma ga wani irin tamkewa da marata ta yi, ban san awa na yi a haka ba, kafin a hankali na fara jiyo kiran Assalatu daga masallacin kusa da gidan, gama kiran sallan ke da wuya, na samo jiyo kururuwar Daada da sauran mutunen gida yara da manya,

"Usaini ya yi hatsari a hanyar shi ta zuwa Lagos, sun mutu daga shi har direbansa har ba a iya tantance gawarwakinsu."

Iya abin da na iya ji kenan daga nan kuma ban sake sanin in da kaina ya ke ba sai farkawa na yi na ganni kwance a falona babu kowa a kusa da ni sai Amintacce yana riƙe da hannuna fuskarsa duk busasshen hawaye, kafin in gama tantance komai, Baaba Hajo ta yi sallama ta shigo, ta karaso da sauri ganin na farka ta na fadin "Sannu Balkisa, sannunmu da haƙuri, Allah ya jiƙan Usaina kaico kaico mun yi rashi mutuwa mai tonon silili." Jin waɗan nan kalaman daga bakinta ya sa na ji wani irin kuka ya taho mini daga can kasan zuciyata. Rungumeni Baaba Hajo ta yi ta na ci gaba da faɗin "Zubar da hawaye Balkisa, zubar da hawaye na taya ki, abin kukan ne ya same mu." A wannan lokaci ji na yi ba ni da sauran amfani a duniya, ba ni da sauran farin ciki, ji na yi dama ace nima mutawan ta zo ta tafi da ni.

Dakyar Baaba Hajo ta yi jarumta ta shiga rarrashi duk da itama ba wai ta yi shirun bane, da kyar na tsagaita ganin haka yasa ta ce "ki tashi ki je ki yi ma shi sallama ku yi bankwana ki yi mi shi addu'a, an riga an shirya shi yanzu za a dauki gawar zuwa gidansa ma gaskiya."

Da taimakon Baaba Hajo na fito tsakar gidan, mata ne dam kam ta ko ina yan uwa da abokan arziki ana zazzaune cikin alhini da tashin hankali, kowa ya yi shiru muryar Daada kawai ke ta shi sai kuka take yi ta na cewa ta shiga uku ta lalace,.

Ina fitowa kallo ya dawo kaina, hango ni da Daada ta yi, ya sa ta mike daga in da take zaune ta nufo ni, ta na zuwa ta cakumi wuyan hijabina ta shiga girgiza ni da karfi ta na fa ɗin " Kin kashe shi hankalin ki ya kwanta Balkisu kin kashe mini ɗa, Allah ya isa tsakanina da ke ban yafe miki ba Balkisu abin da ki ka mini Allah ya haɗa ki da wacce za ta yi mi ki ninkin shi sau ɗari." Cikin ihu da karaji ta ke maganar don ba iya matan wajen ba har maza da ke cike da kofar gida suna jiyo muryarta." Ta ke ƙananan magana ya fara tashi ƙasa ƙasa kowa na faɗin Albarkacin bakinsa. Duk da ba na cikin cikakken haiyacina raina ya yi mummunar baci da abin da Daada ta yi, hakan yasa na buge hannunta da ke jikina, na raɓa ta zan wuce zuwa ɗakinta in da gawar ke ciki, ta sake jawoni tana faɗin "Ina za ki je, Algunguma, Wallahi ba za ki gan shi ba, ke da shi har abada." Baaba Hajo ce a zuciye ta ce "haba Daada wannan wane irin ra shin hankali ne, mutuwa Husaini ya yi fa ko gawarsa ba a ɗauke ba, wannan ai shashanci ne jahilci ne Wallahi kin ba ni mamaki,kuma ki sake ta, ta je ta yi sallama da mijinta idan ba haka Wallahi sai rayuka sun yi mummunar ba ci." Kafin Daada ta kai ga bata amsa aka fito da gawar, sai hankalinmu duk ya koma can, ganin yadda jini ya rina farin likkafanin da gawar Yaya Hussain ke ciki ta ke jiri ya shiga diba na, da sauri na dafe Daada ina maimaita kalmar "Inna lillahi wa Inna alaihi raji'un." Daada ta tunkuɗe ni, ta ke na yi wani irin mugun faɗuwa a wajen wanda ban farka ba sai bayan kwana uku da binne gawar Al-Hussain.

Kallo ɗaya na yi wa ɗakin na tabbatar asibiti ne, kafin in gama haɗa tunanina waje ɗaya, ta tsinci Muryar Baaba Hajo ta na mini sannu, kallo ɗaya na mata na fashe da kuka, ta dafa hannuna tana tsaye daga bakin gadon da nake kwance ta ce "Ki yi hakuri Balkisu, kuka ya isa haka, Addu'a za ki yi masa, Addu'ar ki ya fi buƙata a yanzu." Sai kawai na runtse ido na shiga kwararo ma shi Addu'a kamar da bakin kwarya, da larabci da Hausa duk wacce ta zo bakina, Baaba Hajo na amsawa da Amin.

A haka likita ta shigo ta same mu, dama already tun farkawata Baaba Hajo ta sanar mata, bayan ta gama duba ni, ta tabbatar komai normal, sai ta ja kujera ta zauna a gabana, cikin tsananin tausayi da kulawa ta shiga yi mini nasiha, tana yi tana kara ba ni hakuri da kwarin gwiwar tunkarar gobena, ta karkare da sanar mini cewa cikin jikina ya fita sakamakon tashin hankalin da na shiga da kuma faɗuwar da na yi akan cikin.

Kwatanta ma ku yanayin da na shiga da jin wannan furuci ɓata lokaci ne, domin Cak numfashina ya tsaya na hucin gadi, na dinga jin kaina kamar ina yawo a cikin gajimare, "Ki ambaci Allah Balkisa, ki ce Inna lillahi wa Inna alaihi raji'un." Kalaman Baaba Hajo suka doki kunnena, take na bi umarninta, na fara maimaitawa kamar yadda ta ce, hakan ya ɗan samar mini da nutsuwa.

Kwana biyu na kara a asibitin aka sallame, saboda matsawar da na yi, domin zuwa lokacin kwanan Yaya Hussain bakwai a bayan ƙasa.

Har na gama zamana a asibiti, ko karen gidan Mamman kura bai zo duba ni ba bare mutum, abin ya yi mini ciwo duk da nasan basa kaunata amma a tunanina ahalin da nake ciki ni abar tausayi ce ga mai cikakken imani.

karfe biyar na yamma dai-dai mai adaidaita sahu ya dire mu a kofar gidan Maman kura.

Kallon gidan ƙadai ya karyar mini da zuciya, sai lokacin na ji wani maraici ya lulluɓe ni "Shikenan Yaya Hussain ya tafi ya barni a wannan gidan ba tare da sanin ina na dosa ba, wacece ni? daga wacce duniyar na ke? Ya Allah me yasa ka fara daukar rayuwar Yaya Hussain kafin nawa, Allah ka sani shine komai nawa, Allah shine Uwata shine Ubana, Yayana, Ɗanuwana, Mijina, kuma Uban ƴaƴana na zahiri, Allah ina roƙon ka ka yi gaggawar daukar raina na bishi ya Allahhh!!!."

Na karashe zancen zucin da na ke yi hawaye na gudu a dakalin fuskata. Muryar Baaba Hajo ne ya katse mini tunani da sauri ka ɗauke hawayen da hijabina don bana bukatar ta gan su faɗa za ta yi mini.

"Ku shiga Balkisa zan shiga gidana idan na yi sallar magriba zan shigo." Na amsa mata da to tare da kama hannu Amintacce ga goyan Fatima a bayana muka durfafi shiga gidan gabana na dakan uku uku.

Gaba ɗaya idanu suka zubo min tamkar sunga sabuwar halitta, hakan ya sa muryata rawa yayinda na ke sake rangaɗa sallama a tsakar gidan.

Ba wasu ba ne a tsakar gidan Illa Daada da iyalanta ba ki ɗaya, idanuna ya sauka cikin na shi, take daren rasuwar Yaya Hussain ya faɗo mini a rai, tabbas shine wannan mutumin da na ji yana waya cikin dare.

Tunanina ya katse lokacin da Daada ta ce "Ke kuma daga ina? gayyar arna a idi, me ya kawo ki, me ki ka zo yi, ko kina da alaƙa da Gidan Maman kura ne?."

Na yi saurin girgiza kai hawaye na bin fuskata.

A wannan yammaci Daada da iyalanta su ka yi mini korar wulaƙanci tare da kora mini kyakkyawar warning akan babu ni babu su har abada, shegiyar ƴar Hussain Fatima sun yafe mini ita halak malak dama bata da ko gadon Allura a cikin dukiyarsa, shi kuma tayin cikin suna farin ciki da zubewarsa domin basa buƙatar bara gurɓi a cikin zuri'arsu.

Ina kuka ina rokonsu su taimake su rufa mani asiri ko takaba ne na yi a ɗakin mijina amma suka ƙi, dakyar suka yi mini Alfarmar daukar wasu daga cikin kayan sakawarmu, a sannan ne na samu damar daukar makulli da takardun gidan da Al-Hussain ya mallaka mini a jajibarin ranar dazai rasu ba tare da sanin su ba.

Ummi ta sauke numfashi ta kalli Fatima Al-ameen da Aliyu da kowannen su ke sharar kwalla, itama kwallar ta dauke a idanunta, ta ce "wannan shine rabuwata da ahalin Mamman kura, yau shekara goma sha biyar cif! Basu taɓa nema na ba haka nima ban taɓa neman su ba, sai da maganar Auren nan ya tashi, na je ne da ƙoƙon barata ina neman su tsayawa Amintacce akan maganar aurensa, domin idan ba su ɗin ba, ba ni da wasu ban san kowa ba sai su, wannan shine abin da na sani game da rayuwata, bacin wannan ban san komai a kaina ba, sai dai ina fatan wata rana ta zo da zan tuna ko ni wacece daga wacce duniyar na ke, ina fata wata rana na tuna wacece Balkisu.........

Masha Allah wannan shine karshen littafi na ɗaya gobe za ci gaba da labarin joy Al-ameen da kuma Amira ina fatan baku manta ba

*Shin Al-ameen zai auri Amira❓ Menene asalin Ummi❓ Wacece Joy❓ Me Mom ɗin Joy ke ƙullawa❓ Yaya batun soyayyar da Joy ke yiwa Al-ameen❓ Mene alakar Dr Abdul Hafiz da Al-ameen da yasa ya damu da shi ya ke son shiga rayuwarsa.❓ Ya batun ciwon Al-ameen zai samu lafiya ko A'a❓ Ya labarin dattijon da ke kwance a asibiti❓* Shin wanene wannan mutumin da Ummi ta ji yana waya cikin dare❓

Amsoshin waɗan nan tambayoyin na cikin littafin Joy kashi na biyu wanda zamu fara posting a gobe idan Allah ya ara mana rai da lafiya.

Alhamdulillah🙏 *** WhatsApp Only