Page 7
Ita ma Asmah direct sashen mummy ta wuce, a falo ta samu su Zahra da Ummi da y'an biyunta sai buɗe dinku nan suke yi suna kallo, kowacce ta dauki nata, ta na gaisar da ummi bata bi takan su Batool ba da ke son rike ta da surutu, direct ta wuce dakinsu, ruwa ta watsa ta dauro alwala daya daga cikin abayan da ya kamal ya sai mata ta dauki wani maroon color mai shegen kyau yaji tsone ta ko ina,ta saka abinka da farar fata ba ƙaramin kyau ya mata ba, sallan azahar tayi tana idarwa, ko abinci bata nema ba ta hau gado ta kwanta, ba domin yin barci ba sai don ta samun damar yin shawara tsakanin zuciya da ƙwaƙwalwarta, a haka dai barcin ya shammace ba tare da ta shirya ba, saboda bashinsa ta suka ci na daren jiya.
Ummi jin shiru Asmah bata sauko ba yasa tace Alhasan yaje ya kirata, ta zo ta duba nata dinkin.
Dawowa Alhasan yayi yace"tana bacci" Ummi tace "Ikon Allah bacci kuma! Ko da yake jiya fa baku yi bacci da wuri ba."
Haka sukai ta sabgoginsu a falon mummy sai da aka kira la'asar Zahra ta haura sama don yin sallah, Su kuma su Amira su ka bi Ummi part din hajiya Mama.
Har lokacin bacci Asmah ke yi, alwala Zahra ta dauro ta gabatar da sallan la'asar, sai da ta idar ta tashe ta ganin bata da niyyar motsawa.
Tana falkawa taga zahra ta ce "Subhanallahi bacci na yi ashe" zahra tace"Eh gashi har an idar da la'asar ". Da sauri ta miqe ta shiga toilet ta d'auro alwala, pray mat din da zahra ke nilkewa ta amsa ta shimfida ta gabatar da sallah, koda ta idar zahra bata d'akin, don haka itama ita saukowa qasa tayi, falo ta same su yanzu harda Mummy da wasu daga cikin dangi
Gaishe su tayi ta wuce dining don tafara jin cikinta na kiran ciroma, abinci ta zuba kadan taci, ta tashi daga dining din ta dawo falo akaci gaba da hira da ita.
Hanifa ce ta shigo falon Mummy. Da dan tsalle tsallenta na yara, don Hanifah kwata kwata batafi shekaru hudu ba , direct gun Asmah ta nufa ta fada jikinta tare da cewa"Anty Acmah wai kijo inji Uncle kamay" gabanta ya fadi tunawa da tayi ɗazu ya ce zai zo yaji amsarsa, amma ta dake tace "yana inane Uncle kamay din" ta fada cikin kwiykwayon muryar hanifa mai tsami, "yaya garden " Hanifah tace , dan lakace hancinta Asmah tayi tace"oya kije kice masa ina zuwa" tom" hanifa tace kafin ta zura da gudu ta fice , Mummy na kiranta ko amsawa batayi ba balle ta juyo,
Ten minute ta qara zaune a falon, kafin ta tashi ta haura sama , d'akinsu ta shiga gaban mirror ta tsaya , ta dauki turarenta mai sanyin kamshi ta fesa kad'an, kwalli ta zizara a fararen idanunta masu sheqi sai man lebe data shafa mai d'anqo, mayafin abayan jikinta ta dauka tayi rolling dinshi,
ba qaramin kyau tayi ba farin kyakkyawan fuskarta sai shining yake, wayarta ta dauka tare da zura wani plat shoe mai kyau ta sauko falon, kusa da mummy take tadan rusuna dai dai kunnenta tace ," mumyy wai ya kamal na kira na " "ok" Mummy tace mata , don haka ta nufi hanyar fita palon, batool ne tace "sister sai ina" alamar tana zuwa ta mata da hannu ta fice daga palon,
Hanyar garden ta nufa cikin takunta na natsuwa, garden din yana cen ta bayan gidan ne, don haka sai an wuce part din su Aslam dake farkon gidan kafin a isa garden din,
Dai dai ta gifta kofar part din shi kuma Aslam ya fito don ya amsa call, kasancewar falon cike yake da abokanan shi, hayaniya yayi yawa,
Ita bata ganshi ba amma shi ya ganta kuma ya gane itace kasancewar yaga gefen fuskarta datazo giftawa,
Samun kanshi yayi da tambayar kanshi ina kuma wannan yarinyar zata je?, ba mai bashi wannan amsar
Haka kawai ya samu kanshi da bin bayanta a hankali yanda bazata ganshi ba, gani yayi ta nufi garden ta bud'e dan guntun get din wurin ta shiga, ci gaba da binta yayi ba tare da ya bari ta sani ba,
Tana shiga ta hango ya kamal zaune akan wani shimfidadden kafet mai laushi, zaune yake yana facing cage na tsuntsayen kanari kala kala sai shawagin suke yi gwanin sha'awa, hankalinshi gaba d'aya ya raja'a akansu.
Qarasawa tayi tare da yimai sallama, juyowa yayi kyakkyawann fuskarshi dauke da murmushi yana amsa mata
Sai a lokacin Aslam dake la'be yaga ahse kamal ne don da baiga fuskarshi ba kasancewar ya juya baya, gani yayi kamal din ya nuna mata gefen shi yace ta zauna, zaman kuwa yaga tayi dan nesa kadan da kamal d'in,itama tana facing cage din,
Samun kanshi yayi da jin haushin ganin su haka da yayi, a zuciyarshi yace yadda suka zauna dan Allah sai kace wani miji da mata kokuma budurwa da saurayi,tsaki tsaki yaja a fili , wata zuciyar ce ta kwa'be da cewa to kai ina ruwanka, tsaki ya kuma ja ya juya zai wuce,
Saidai kuma me! Samun kanshi yayi da son jin abinda zasu fad'a,
Kamar Wanda ake controlling dinshi da remote haka yake bin umarnin zuciyarshi,
Samun kanshi yayi da qarasawa cikin garden din sad'af sad'af. Yadda baxasuji takun step d'inshi ba.
Gurin ya samu dan nesa dasu yadda zai iyajin abinda suke fada ya zauna , kasancewar sun juya mai baya yasa basu ganshi ba, shiko hakan yamai dai dai,waya ya dauko ya qara a kunnenshi kamar yana amsa call nan ko dukkan hankalinshi na Kansu , yayi hakane koda zasu juyo su ganshi sai yayi pretending..
Kamal ya juyo ya kalli Asmah yace" my Asmah" barka da juma'a, dan boye fuskarta tayi tana murmushi alamar taji kunyar sunan da ya kirata dashi, shima murmushi yayi mai sauti yace "yau kuma kunyata kikeji ne,". Still batace komai ba, ya qara cewa "to shikenan ina jinki, bani amsata" shiru tayi kanta na qasa bata ce komai ba, kamal ganin shurun nason yayi yawa ne yace"ke nake saurare my Asmah"
Dagowa tayi ta kalleshi shima din ita yake kallo, idanu suka had'a tare da sakar ma juna murmushi , saurin kauda kanta gefe tayi, sannan a hankali kamar mai ciwon baki tace"na amince da soyayyarka ya kamal Allah ya shige mana gaba,'. Tana gama fadin haka ta saka kanta cikin qafafunta ta 'boye fuskarta, alamar kunya,
Aslam dake zaune a bayan su, da sauri ya dago kanshi yana kallonsu jin abinda Asmah ta fada
What!!! Soyayya, gaban shine ya shigafaduwa, hankalinshi ya tashi, tsoro da firgicine suka ziyarceshi a lokaci daya,
Shi karan kanshi baisan dalilin shi na shiga wannan yanyinba daga jin wannan maganar,
Kamal ko jin amsar data bashi wani irin farin ciki ne ya lullu'beshi, juyowa yayi ya kalleta fuskarshi cike da farin ciki yace "da gaske kike my Asmah". Kanta dake cikin cinyoyinta ta girgiza mai alamar eh,
Hannu ya daga sama yace "Allah na gode maka da kasa wannan baiwa taka ta amince da soyayyata cikin sauqi, ya Allah ka mallakamin ita cikin sauqi,". Sauke hannayenshi yayi ya juyo ya kalleta yace"nagode my Asmah kuma na mika alqawrin insha Allah zaki sameni miji daya tamkar dubu"
Dago kai tayi ta marairaice fuska tace"sai dai ina buqatar wani alfarma a gare ka ya kamal" yace "yace wani irin alfarma kike nema " tace "so nake maganar soyayyan mu ta zama sirri tsakanin nida kai, banason kowa ya sani har sai na kammala karatuna," yace "saboda me" tace "saboda bana son na rasa daman yin karatu a karo na biyu, domin muddin alhaji Mallam yaji wannan maganar nasan bazai barni nayi karatu ba , aure zaimin kuma banaso" ajiyar zuciya kamal ya sauke yace "karki damu indai don wannan ne bazan sanar ma kowa ba, nima bana son ayi auren yanzu sai mun qara fahimtar juna, kafin nan kin kammala karatun ki". , d'ad'ine ya lunlu'beta, jin y amince da maganar ta.
Aslam sad'af sad'af ya tashi ya fice daga garden d'in yana hard'e hanya,
Idan ya fahimci inda maganganunsu ya dosa , kenan soyayyace suka kulla a tsakanin su
Kai! Ina! Hakan bazai taba faruwa ba , wannan ai cin amana ne, kamal yake son yamai, bai taba tunanin kamal xai mai haka ba , yarasa dawa zaiyi soyayya saida ex wife dinshi,
Lallai baiga ta zama ba , bazai taba barin hakan ta faru ba , to ta haramta ga duk wani d'a namiji indai jininsa ne, taje can ta nemi mijinta a wani familyn badai nasu ba
Da wannan tunanin ya qarasa part d'insu, inda ya taradda abokanan nata firansu kamar yadda ya fita ya barsu.....
Guri ya samu ya zauna yana saurarensu baicewa kowa komai ba,jikinshi duk a sanyaye, su karan Kansu abokan sun lura da sauyin da ya samu yanzu yanzu daga fita amsa call,
Asmah kam kimanin awa d'aya suka dauka suna firan su kafin suyi sallama ta koma cikin gida........
A haka wunin ranar ya qare jikin Aslam a sanyaye minti kadan tunanin kamal da Asmah ya fadomai a rai, minti kadan hoton su lokacin da suka sakar ma juna murmushi ya fado mai a rai, da'ker ya samu ya yaqi zuciyarshi yayi fatali da wannan tunanin, yaci gaba da harkokin gaban shi, har zuwa dare,
Dare nayi anan ne ya raina kanshi don kasa bacci yayi. Sai tunane tunane yake, yana saqa yadda zai ruguza wannan soyyaya na cin a mana, yasan ko yakai maganar wurin manya babu mai goyan bayan shi, zasuce meye hujjan shi na hana kamal Auren ta tunda shi ya qita, zasu zata ko sonta yake, shi kuma yanzu a zuciyarshi babu burbushin sonta ko kad'an a ciki zee dinshi ita kadai ce a ranshi ita yake so itace za'binshi, itace irin macen da yakeso wayayya yar boko, shi mai zaiyi da wata Asmah baya sonta baya kaunarta, hasalima shi ya tsaneta, kuma tsanan da ya mata ne yasa baya son ta auri wani makusancin shi,
(kai dai kasani Mallam Aslam muna nan muna jiranka ka gama kewaye kewayenka zaka dawo kan hanya ne😬)
Da ire iren wadannan tunaninkan yaketa juyi akan makeken bed dinsa, baiyi aune ba sai ji yayi ladan na kwada kiran assalatu, zabura yayi ya miqe tsaye ya kunna wutan d'akin ,kallon shi ya kai kan agogon bangon dake d'akin biyar saura kwata ya gani, mamaki ne ya kamashi na tsowan lokacin daya dauka yana tunani, da haka ya shige toilet ya dauro alwala raka'atanil fajir ya gabatar kafin ya wuce masallaci.
A can ya taradda mazan gidan duka,manya da yara , baqi da yan gida, ana idar da sallah miqewa yayi yaje ya gaisar da iyayen shi , da kuma alhaji baba , su amir da kamal ma hannu ya basu sukayi musabaha,sannan ya fice daga masallacin bai jira kowa ba , don bacci yake son yayi kafin lokacin tafiya daurin aure yayi, Amir ne ya biyo bayanshi da sassarfa yana cemai "haba ango kasha kanshi , na zainabu Abu mai tagyayen suna bako jira" share shi yayi bai tanka ba , a haka suka iso part dinsu na samari, Amir nata tsokanan shi yaqi tankawa ,
Kowannen su daki ya shige , Aslam bacci yake ji sosai don haka yana shiga dakinshi ya haye kan bed dinshi ya duqunqune cikin bargo sai bacci, ko azkar da karatun alkur'anin daya sabayi kullum bayan asuba bai samu yayi ba, bacci ne ya kwashe shi mai nauyi, kasancewar bai samu bacci da daddare ba,
Daurin auren qarfe Tara na safe za'ayi don haka , su Abba da daddy da abokansa , da duka wani mai niyyar zuwa wajen daurin auren qarfe takwas kowa ya shirya,
Amir ne ya sakko downstairs cikin manyan kaya harda babban riga light blue, ya murza hula dark blue da ratsin light , sai zuba kamshi yake, a nan falon ya tarad da kamal shima cikin nashi shigar ta manta kaya iri daya dana Amir din, wasu daga cikin friend dinsu ne suka fara shigowa cikin , suma dai shadda light blue dinnne a jikinsu, da alama shadda light blue shine ankon da abokan ango suka fitar don zuwa wajen daurin a auren, zama sukayi , wadannda zasuyi breakfast suka fara yi, don tun saven thirty mami da sukaba kwangilar had'a breakfast din abokan ango ta aiko musu da shi,
Anas ne yace"ya kamata mu hanzarta kundan dai san anguwar da d'an nisa ". Dr bash yace"wai nikam ina angon ne " ya fad'a yana kallon Amir, Amir yace"may be yana shiryawa kasan shirin angwaye daban yake, amma dai barin shiga na fito mana dashi ". Miqewa amir yayi ya nufi upstairs don dubo Aslam,
Yana isa kofar d'akin knocking yayi shiru ba amsa, sake kwankwasawa yayi shiru again ,don haka ya kutsa kai tare da sallama , ba kowa a falon don haka ya nufi bed room tare da sallama ,
Wani irin zaro ido Amir yayi tare da furta"kutumelesi! Dalilin hango Aslam da yayi qudundune cikin bargo yana kwasan baccinsa hankali kwance, kunnna wuta mai haske amir yayi don dama ta cikin dim light yake hangoshi, tsayawa Amir yayi a kanshi ya riqe qugu yama rasa ta ina zai fara tashin shi, takaici duk ya gama cika shi ji yake kamar yata sharara mai mari a fuska,
Da zaimai mugunta da wlh Alhaji bab zaije ya dakko mai, saidai kawai yaji ruwan carbi a kanshi, amma yasan inya tsaya wannan duk bata lokaci ne, Wata yar qaramar waya Amir ya zaro daga aljihunshi, itel ne wayan irin mai shegen qarannan, danno wani ringing turn mai uban tsiwa da kaudi hadi da vibration yayi, saida ya manna wayar a kunnen Aslam sannan ya danna play,
Aslam da yayi Nisan bacci sai jin wani irin kuwwa hade da vibration yayi a cikin kwkwalwan kanshi, a zabure yayi wurgi da duvet din da ya lilliba ya miqe tsaye, kanshi na wani irin sarawa,bude idon shi da sukayi nauyi yayi akan Amir dake ta kwasan uban dariya,
Aslam bai ce mishi komai ba don gaba daya kanshi ciwo yake mai bazai iya magana mai tsawo ba,
Saida Amir yayi dariyarshi mai isansa sannan ya bata rai ya koma serious face ya kalli Aslam dake lumlumshe ido alamar baccin bai ishe shi ba yace"dalla Mallam ware kaje kayi wanka ka shirya, kowa ya shirya ana jiran ka don tsabar iskanci Ashe kai kana nan qudundune cikin bargo kana barci". Sai lokacin Aslam ya tuna da daurin auren dake gaban shi"subhanallahi " ya furta yana mai d'an ware idanun shi dake lumshewa, daddafa bango yayi ya shiga toilet, wanka yayi shap shap ya fito, daure da tawul, nan ya tarad Amir ya ciro mai kayan da ya tanada don zuwa daurin auren,
Gaban mirror ya tsaya ya shafa mayukanshi da turarukan shi masu kamshi na jiki, wasu fararen sababbi fil din singlet da boxer ya ciro daga cikin wardrobe, turare ya fesa musu sannan ya koma toilet ya sanyo, saboda amir daya qureshi da ido,
Yana fitowa ya fara shiryawa cikin shaddan shi milk color mai mugun kyau da tsada, sai maiqo takeyi,
Riga ne da wando da babban riga dinkin zamani, an mishi aiki da zare coffee color, hulla milk da ratsin coffee ya saka, sai takalma cover shoes suma coffee, ba qaramin kyau Aslam yayi ba abinka da kyakkyawa cikin kyawawan kaya, abin ba'a cewa komai sai masha Allah.
Amir ne yace"wow wow angon zainab kaganka kuwa, gaskiya kayu kyau,kayi maza ka gama muje kaga su bash nata kirana, nasan kuma sunga na dad'e ne, shiyasa"ya fad'a yana ficewa daga d'akin zuwa main falo inda su bash suke,
Aslam saida ya daura agogon shi rolex mai kyau sannan ya biyo bayan Amir d'in, yana shigowa falon abokanshi suka dauki sowa da tafi ana tsokanan shi ango kasha kamshi, kasa amsa musu yayi don kanshi ba qaramin ciwo yake mashi ba, saboda baccin da baiyi jiya ba,gashi kuma Amir yazo ya tashe shi da dan iskan itel dinshi mai shegen qara , ya qara mai ciwon kan,
Kasancewar time yaja yasa basu tsaya wani bata lokaci ba suka dunguma suka fito coumpond din gidan,koda suka fito su Daddy da sauran jama'a tuni sun wuce, suma motocin su suka hau suka kama hanya kusan dukkansu suna da mota sai d'ad'd'ya wadan da ba aka rasa ba.
Wucewarsu ba dadewa, yan matan mummy na hango sun fito daga part d'in mami, da alama dai aiki suka taya mamin don dukkansu ba wacce tayi wanka a cikin su, sashen mummy suka nufa donyin wanka su shiya cikin ankon su na yinin biki, gidan yadan fara cika da mutane don haka falon mummy na qasa dana mami ma da suka baro cike yake da mata,
Gaisar da mutanen falon kawai sukayi suka wuce dakin su don shiryawa,.
Batool ce tayi wuff ta kama qofar toilet zata shige, zahra tayi caraf ta kamota tace "wlh baki isa ba keda kike shegen dadewa a wanka, shine zakice ke zaki fara shiga,wlh bazaki shiga sai na fito,
Nan batool itama ta cakumo ta suka fara kokawa, dama sun saba kusan kullum sai sun ta'ba,
Amira na ganin haka ta lalla'ba ta shige toilet d'in tana musu dariyar mugunta, karar rufe qofar ne ya dawo dasu haiyacinsu, nan ko suka koma kan amira cacacaca batool harda cewa allah ya isa ci mata layi da amira tayi,
Amira na jinsu tayi muqus gata itama ba baya ba wajen dadewa a wanka,
Asmah dai na zaune gefe kasancewar ta mara son haya niya yasa bata saka musu baki ba,shiru dai tayi tana bin kowa da ido in sunyi abin dariaya ta dara,
Amira don mugunta saida ta kwashe sama da rabin awa sannan ta fito batool ta shiga ,itama sai gungumi take alamar sai ta dad'e itama,
Wani tunani ne ya fado ma Asmah arai, take kuwa ta miqe tace musu tana zuwa, zahra tace"ina zuwa kuma" tace"kedai ina zuwa nace" ta fice d'akin mummy ta nufa don tayi wanka a can ta huta da bin layi , tasan ba kowa a d'akin mummy yanzu, cikin sa'a kuwa tana murda handle d'in, kofar ta bude, mummy bata kulle kofa ba kenan, shiaga tayi kamar yadda tayi tsammani ba kowa a dakin,toilet ta shige donyin wanka.
Karfe tara da minti goma aka daura auren Muhammad Aslam abdallah, da Zainab Abdussalam, akan sadaki masu yawan gaske, Masha Allah daurin aure yayi jama'a saidai muyi fatan Allah ya zaunar dasu lpy,
Aslam da abokanshi sun shiga sunyi gaisuwar surukai kamar yadda yake a al'adar mutanen minna,
Direct kuma gida suka wuto in da zasu gabatar da reception kamar yadda Amir ya shirya,
A part d'insu Aslam din suka yada zango, nan ma'aikatan da aka turo daga galaxy hotel, inda akayi order abincin reception d'in suka shiga serving dinsu,
Abinci masu rai da motsi duk abinda mutum keso shi za'a zuba mai, ga drinks kala kala duk Amir ne ya dauki nauyin komai.
Cin abinbin su sukeyi suna firansu group group , kasancewar falon babbane yasa ya dauke su baki d'ayansu.
Aslam na zaune cikin kujera one sitter ya cire babban riga ya ajiye sai binsu yake da kallo, abin duniya gaba daya yabi ya dameshi, shi d'an farin cikin da mutum keyi bayan daurin auren shi, shi neman nashi farin cikin yayi ya rasa, kanshi ne ke matsanan cin ciwo ga kuma hayaniyar da friend dinsa keyi na qara mai ciwon kai, sai tsokanan shi sukeyi irin yadda abokai keyi, yayi shiru yaqi cewa komai saidai d'an murmushin yaqe, Suma kasancewar sunsan halinshi na rashin son magana yasa basu wani damu ba.
Bacci yakeji sosai kuma yana gani idan har ya samu yayi baccin kanshi zai rage ciwo koma ya bari gaba d'aya, miqewa yayi da nufin yaje upstairs d'akin shi ya kwanta, wani tunani ne ya fado mai a rai, yasan indai ya kwanta a d'akin shi abokanshi baza su bari ya samu bacci yanda yake so ba, don haka rivas yayi daga niyar hawa saman ya nufi hanyar waje, ganin Anas nason tsaidashi yasa ya kara waya a kunnen shi kamar yana amsa call,
Sashen mummy ya nufa, yasan d'akin tane kawai zai samu yayi bacci hankali kwance , kuma su amir baza suyi tunanin yana can ba don ko d'akin mami yaje bai tsira ba tunda sunsan ya saba zuwa, zasu iya cewa bari su duba can in suna Neman shi,
Ganin alamar akwai mata cike da falon yasa yabi ta qofar kitchen ya haye sama ba wacce ta ganshi,
Dakin mummy ya shige ya qure A,c , sannan ya haye kan makeke bed d'inta' ya qudundune cikin bargo, inba mutum ya kula sosai ba bazai san a kwai mutum kwance a wajen ba.
Asmah wankanta ta sheqa sosai a toilet din mummy, bayan ta gama ta d'auki tawul d'aya daga cikin tawul d'in da ta gani a rataye a toilet d'in, ta daura, fitowa tayi kanta tsaye don tasan ba kowa a d'akin,
Aslam jin motsin an bude qofar toilet yasa ga bud'e idanun shi don ganin ko waye, Asmah ya gani ta fito daga toilet d'in daure da d'an,qaramin tawul da bai gama rufe mata cinyoyinta ba Numfashin shi ne ya shiga seizing gabanshi ya shiga fad'uwa zuciyarshi ya shiga bugawa da sauri da sauri,
Asmah kam direct gaban mirror mummy ta nufa kasancewar tasan duk abinda take buqata na shafa akwai a kan mirror mummy, yasa taga gara ta tayi shafe shafenta anan gaba d'aya, inyaso tana komawa sai dai tasaka kayanta kawai,
Madubin na fuskantar gado ne don haka juyama Aslam baya tayi, kwata kwata bata lura da wani Aslam a d'akin ba,
Qurama bayanta ido yayi qur baya ko qaftawa, tun daga sama hara qasa yake qare mata kallo, dogon baqin gashinta dake kwance a bayanta, yabi da kallo kasancewar ta wanke kai yasa gashin kwanciya luf luf a kafad'unta ,sauko da idanun shi, yayi kan mazaunanta da suke nan masha Allah dasu,ga wani irin lafiyayyen hips da Allah ya hore mata kamar wata babban [1/31, 8:07 AM] Sis Aysha: 🌀 *DAMA TA BIYU* 🌀
By Aysher Nalado
*A kwai complete, ga Hajiyoyi wadanda ba su don jira, ki zo ki biya ki mallaka, a tuntube ni kai tsaye ta wannan layin ****
Jin ƙarar kofa alamar ya bar dakin, yasa ta tashi da sauri ta rarumi hijabin Mummy da ta gani, ta zura a kan tawul din jikinta, ta fice daga dakin da mugun sauri, duk ilahirin jikinta na rawa, kamar mazari.
Sai da ta tsaya a ƙofar dakin su ta saisaita kanta sannan ta shiga, samun su tayi suma duk sunyi wanka suna shiryawa, ta wuce su ta faɗa kan gado ba tare da ta cewa kowa ufan ba.
Kallon kallo su zahrya su ka shiga yi a tsakanin su, Amira ce tayi ƙarfin halin ƙarasawa bakin bed d'in, ta dago kanta ta daura kan cinyarata, sannan tace, "lafiya sister meya sameki" alama Asmah ta mata da hannu, wai kanta ke sara mata.
Batool ce ta qaraso da sauri ta zauna kusa da ita tace " ayya sannu Asmah, sannu kinji, kwanta ki huta qila aikin hada breakfast d'in da mami ta saka mu dazu ne, yasa mata ciwon kai kunga ita ta zage taketa aiki sosai , kunsanta da rashin son jiki," Zahra tace barinje na dauko miki maganin ciwon kai a d'akin mummy, girgiza mata kai tayi alamar ta barshi bazata sha ba.
Kwantar da ita Amira tayi suka ci gaba da shirin su, sunyi suna mata sannu,rintse idanuwa tayi kamar mai bacci, take abubuwan da suka faru few minutes ago, suka shiga dawo mata fresh a kwakwalwarta, innalillahi wainnailahi rajiun ta shiga maimai tawa a cikin zuciyarta, gaba d'aya ranta a jagule yake, gsky Aslam ya cuceta , kuma Allah ya isa ganin jikinta da yayi, bata yafe ba.
Sai da ta kwashe kusan fourty minutes a haka kafin ta yunƙura ta mile, ganin tunanin ba abinda zai haifar mata sai qarin takaici da damuwa, tunda abinda zai faru ya riga ya faru , sai a kiyaye gaba.
Zuwa lokacin su Amira sun gama shiryawansu tsab da su sunsha makeup kowacce ta kashe daurin zamani kamar sune amaren.
Ganin ta miqe yasa suka shiga jera mata sannu, tare da tambayar ta ya kan, da sauqi tace musu ta shiga toilet ta wanko fuskarta, tazo ta zauna itama batool ta tsantsara mata makeup, tayi kyau kuwa sosai kamar wata balarabiya, Amira ta miqo mata nata kayan tasanya.
Wow masha Allah Asmah kam tana da kyau sosai tun daga kyawun fuska, kyawun diri, uwa uba kyauwun hali da kyawun zuciya.
Kashe dauri ta yi itama suka fantama cikin gida a ka ci gaba da yinin biki dasu.
Duk abinda Asmah take yi karfin hali ne kawai,domin duk jikinta a sanyaye yake, tun abinda ya faru dazu amma haka ta daure taci gaba da harkokin gabanta, har zuwa dare inda nan suka kuma caba wani adon cikin ankon su na dinner.
Aslam kam yana barin part din mummy, parky lot ya wuce ya bude motarshi ya shiga back sit ya zauna , tunanin abinda ya gani few minutes ago ne ya shima mai yawo filla filla a cikin brain dinshi, yana kisima kyau da tsaruwar halittan yarinyar, tunanin daya dinga yi kenan har baisan tsawon lokacin daya dauka yana zaune cikin mota yana tunanin ba , baccin dai da bai samu yayi ba kenan,
Can kuma kamar daga sama yaji wani bangare na zuciyarshi na kwa'banshi da cewa, meye haka kakeyi Aslam, ka zauna kana bata lokacin ka a banza kana tunanin wannan mayyar yarinyar, me take dashi da har zaka tsaya kana tunanin ta, kaida kake da amarya kamar zee babban yarinya meye na jikin wata mace zai rudeka, har ka zauna kana 'bata time d'inka a banza a hofi, tsaki yaja a fili tare da fitowa daga motar ya nufi sashen su, yana isowa kuwa ya taradda wasu friend d'insa nata neman shi sumai sallama, zasu wuce, yayinda wasu da dama sun riga sun wuce saida a had'u wurin dinner anjima.
A mooris event za a gudanar da dinner Wanda za,a fara 9 a gama 1am,
Misalin 9:30 na dare yammatan mummy na hango zaune a falon mummy sun sha makeup, sai zuba kamshi sukeyi,kamar wadanda zasuje gasar zabar sarauniyar kyau, su biyar ne yau harda Khadijah da suka zo d'azu da mamanta, mamanta bazata kwana anan ba gidan alhaji Mallam zata kwana, ita kuma Khadijah tace anan zata kwana don tana son zuwa dinner, da'ker mama ta barta saida mummy ta saka baki,
Itama Khadijah taci kwalliyarta cikin lece dinta milk colour kasancewar ita batada ankon su Asmah
Kamal ne yayi sallama yace su taso suje, dama shi suke zaman jira, don yace in sun shirya su jirashi ya zo ya daukesu.
Miqewa sukayi suka bishi, suna shiga harabar gurin taron Kamal yayi parking suka fito suka shiga cikin hall d'in, wuri saka nema suka zauna , had'ad'd'un samarin dake wajen kuwa sai binsu da kallo sukeyi sunga kyakkyawan yammata, wuri ya tsaru sosai amarya da ango sun zuba kyau, kamar wasu wata da zahra a cikin sararin samaniya, anfara gudanar da komai cikin tsari da wayewa,an kira amarya da qawayenta sun taka, haka ma ango saidai shi angon baiyi rawa ba sabanin amarya da ta tiki rawar ta, kamar ba itace amarya ba, liqi kam anyishi kamar ba gobe su zahra ma sunje summa yayansu liqi amma basuma zee don duk haushinta sukeji,
(tab zee bata samu shiga ba wajen qannen miji😅)
Kamal kam kasawa yayi ya tsare Asmah ganin irin kallon da mazan gurin ke binta da shi, guri ya samu kusa da ita ya zauna yana gadin kayarsa, suna dan fira jefi jefi,
Amir dake zaune a high table kusa da ango a matsayin babban abokin ango,tun shigowar su Asmah hara zuwa sanda sukaje sukayi liqi hankalinshi na Kansu, ganin yawanci mazan wurin hankalin su na Kansu yasa yaji gaba daya hankalinshi bai kwanta. Shawarar da zuciyarshi ta bashi yabi, sakkowa yayi daga kan high table din, ya nufo inda suke, suna ganin shi suka shiga gaishe shi amsa musu ya shiga yi cikin sakin fuska yana dan tsokanansu irinta abokan wasa, kallon Amira yayi yace"am Amira pls zoki tayani shigo da wasu kaya daga mota ," to Amira tace tare da miqewa tabi bayan shi suka fita daga hall din, suna Zuwa gurin motar shi mai makon taga ya bude mota ya dauko mata kayan daya ce,sai gani tayi ya jingina da jikin motar ya tsaya yana kallonta,itama kallon nashi tayi taga meya tsaya yi bai dokko mata kayan ba, suna had'a ido ya sakar mata wani kyakkyawan murmushi mai dauke da manufofi kala kala, gabanta ne yayi wani irin faduwa,ya salam ta furta a zuciyarta, batun yau ba ya Amir ke burgeta musamman in yana wannan murmushin nashi mai masifar kyau,
Ya Amir kyakkyawan gaske ne gashi da masifar sauqin kai ba kamar ya Aslam mai shegen girman kai da rashin fara'a ba,
Amir ne ya katse mata tunani da cewa "Amiran mami an girma yanzuma shekaran ki nawa " d'ago kai tayi tana kallonshi jin tambayar da ya mata, aiko gani tayi ya qara mata ido sai murmushin shi mai kyau yake saki, kunyarshi taji ya kamata ganin irin kallon da yake mata, fuskarta ta rufe da tafukan hannayenta tana murmushi tace" sha takwas fah'. Amir yace"masha Allah ashe dai yarinyar ta zama ammata, to yaushe zaki turo mana sirikin mu yazo ya gaishemu mu big big brother's". Aiko da sauri ta bude fuskarta tace "laaa ya Amir nifa bani da saurayi" wani boyayyan ajiyar zuciya Amir ya sauke tare da ce mata "da gaske" tace ". Eh " yace "aiko ya kamata kiyi saurayi kin zama ammata yanzu eighteen years fa"
Haka Amir yaci gaba da jan Amira da fira yana bugan cikin ta yana mata wasu tambayoyi da wayau, hakan yafi mai kwanciyar hankali akan ya barta cen wasu qattin banza su dinga kalle mai tanadin shi na shekara da shekaru har a samu wani mai tsaurin ido yazo yamai shigar sauri, wanda yake ganin bazai taba lamuntar hakan ba,
A can cikin hall kam anata ci gaba da gudanar da programs hankali kwance, wayar Amira dake hannun batool yayi qara, kallon su zahra batool tayi tace "kunga Amira daga zuwa dauko kaya shiru shiru tana neman kwashe awa guda, ko lafiya" zahra tace "wlh nima tambayan da zanyi kenan kika rigani, a baki". Wayar ne ya sake ringing batool tace"gashi ma anata kiranta barin kai mata wayar daga nan na duba ko lfy "
Cikin sauri sauri ta miqe riqe da wayar Amira a hannunta, ta nufi qofar fita daga hall hall din, tana d'an gudu gudu sauri sauri dinta samu ta kai mata wayar kar call din ya katse, dai dai qofar fita suka zabga wani uban karan da saida kofin glass d'in daka hannushi cike da ruwan taceccen lemo ya fadi qasa ya tarwatse bayan ruwan lemon ya xubar mishi a jiki, baya tayi taga taga zata fad'i , Allah ya taimaka jinta tayi a jikin mutumin da suka zabga karo ya tarota jikin shi, handset din amira dake hannunta tuni ya fadi qasa, kallon fuskarta Dr bash yayi don yaga da wa yaci karo haka, idanun shi ya sauka ana batool da itama ta dago kai a fusace , fusge jikinta tayi daga nashi, cike da tsiwa da rashin kunya tace"dalla Mallam baka ganine, ko kai makaho ne ko, baka da ido ne ko idonka a tsakiyar ka yake da zakazo ka bangaje ni ka watsamin lemo mai sanyi a jikina, mutane kuna tafiya bakwa kallon gabanku sai kace wasu tumaki, " takwai karshe tare da banka mai wata uwar harara kamar idanunta zasu fad'o qasa,
Zuciya ne ya d'ebi Dr bash ya d'aga hannu zai wanka mata mari sai kuma ya dunqule hannunshi ya naushi iska ya fasa marinta, kallonta yayi cikin bacin rai tare da nunata da yatsa yace ke wacece da zaki bangaje sannan kizo kina gayamin maganar banza maimakon ki bani hakuri, kinsan ko ni wanene, muza hannunshi daya nunta dashi yayi yatsarshi ya bada wani sauti tas tas, yace kinci albarkacin Aslam da mummy da yau saina nuna miki ke qaramar Mara kunya ce tsaki yaja sanan ya ra'bata ya wuce abin shi,
Binshi tayi da harara kafin tana tsaki tare da cewa "aikin banza aikin wofi AI da ka mareni da wlh yau sai kasan ka taba. husaina fatima batool abdallah, "
(Tofah ku kuma kalan naku salon kenan hmmmm ku dai ku biyoni muje zuwa in garin ba nisa)
Daukar wayar amira dake qasa tayi ta duba ba abinda ya samu wayar, fitowa waje tayi dan kaima amira wayar,
Hango amiran tayi ta nufo ta tsayawa tayi har amiran ta isota ,miqa mata wayarta tayi, batace mata qala ba don ranta ya Riga ya gama baci da abinda mutumin da sukayi karo ya mata,
Amsar wayar amira tayi ganin miss call din mummy yasa tabi kiran da sauri, mummy ta daga tace"Amira ina kuka shiga ne inata kiran wayoyinku a kwashe , da'ker ma na samu naki oyaa maza ku kamo hanya ku dawo gida daddynku yace ku dawo haka dare yayi sha daya ta gota,".
Qarasawa sukayi ciki nan ta sanar zasu saqon mummy, aiko babbata lokaci suka miqe da niyyar komawa gida duk da ba'a tashi ba,
Ya kamal d'in da ya kawosu shiya maidasu , a hanyarsu ta komawa gidane batool ke basu labarin karon da tayi da Dr bash tanayi tana kwashe mai albarka tunda ita bawai sanin shi tayi ba, a haka suka iso gida,
A mooris event kuwa sai 1am aka tashi a daga dinner bagan nayi ciye ciye anyi shaye shayen drinks, anyi rabe raben sobeniyas kala kala mutane suka watse , ango ma ya dauki amaryarsa suka wuce gidansu dake Unguwar Waziri bakin dan rakiyan nan da akema amare wai su yan boko😕 sai dai muce Allah ya bada zaman lafiya
Kar ku manta A kwai complete *** [1/31, 8:07 AM] Sis Aysha: 🌀 *DAMA TA BIYU* 🌀
By Aysher Nalado