Ƴar gwoggo

Page 6

by @barista

ƳAR GWOGGO 

***
Book 1
Page 6


Yana fita daga cikin shop ɗin, na kammala siyayyata ta na biya kuɗaɗen kayan na fito ta ƙofar baya na hau ɗan sahu na dawo quarters ina shiga na tadda Shareefa kwance  kan 3setter tana ganina ta ce

"Ƙawata da naji shiru cewa ma nayi Yarima yasa annaɗe ki an kai masa ke" tana dariya

"Eh lallai kam ga buhun dankali ba, ni zai naɗa wallahi yayi kaɗan ya jada Deejee"

"Tou ya akayi kika tsira amman dai baku haɗu ba? Dan na tabbar da kun haɗu da yanzu wani zancen ake ba wannan ba"

"Uhm tab mun haɗe gani gashi wai ni zayiwa iskanci da futsara na take masa burki, ke in faɗa miki har gaggasa masa magana sai da nayi ƙarshen ma ficewa yayi ya bar wajen ba tare da yayi siyayya ba"

"Kai deejee ke duniya ce"

"To ni dai aban saƙona sai ku ci gaba da hirar ku da bata ƙarewa"

"Oh sorry momy" Na miƙa mata ina "yunwa nake ji"

"Ni ma yunwar nake ji na tsaya jiranki bari na ɗauko muci, Maryam ma tazo nemanki nace ai ke yau sae yadda Allah yayi dake"

"Lah ta shigo kin kuwa san nima nemanta nake ruwa a jallo pass q fa na SSCE tace zata kawo min"

Tace "maybe ta shigo anjima ko kuma ku haɗu a hostel"

"Tou bari na ci nayi haniƙan sai mu wuce nasan Zeenatu yanzu nema na take". Mu kaci abinci sannan muka koma hostel aeko ina shiga na tadda Zeenat ta cika tayi fal

"Ke kuma meye haka kin wani ɓata fuska sai kace dodanniya"

"Ai dole kice haka kin tafi da key din lokata ya ba zan ɓata rai ba"

"Oh my ƙawa kiyi hakuri na manta ne gashi" na miƙa mata cikin fushi ta ansa sannan ta buɗe ta ɗauki abin da zata ɗauka ta fice.

Na hau kan gado na kwanta ina mik'a ina tunanin abin da ya faru ɗazu wannan ai cin zaline dama akwai irinsu har yanzu a duniya.

************************

 *YARIMA MAHEER*

Fitowa su kayi suna haƙi su ka ce dashi "bamu ganta ba boss mun duba ciki da waje bata nan"

"What? Kuna nufin baku ganta ba yanzun nan muka barota a ciki in dai ba Aljannah bace to tana da layan ɓacewa"

Sai hakuri suke bashi shi kam abin mamaki yake bashi ace yanzu su barota sannan su koma bata nan kai da sake ko dai wannan karon gamo yayi ne. Ya shige mota ba tare da sun buɗe masa ba suka tada suka fice. 

Kai tsaye masarauta ya wuce bai tsaya ako'ina ba ya wuce ɗakinsa ya faɗa toilet ya sakarwa kansa shower ya runtse idanuwansa ita yake kallo lulu eyes nata masu ɗaukar hankali, kai yau da ta kuskura ta shigo hannunsa sai ta gane kuren ta da ƙyar ya iya fitowa daga toilet yasa jallabiya mai haɗe da wondonta ya fito zuwa ɗakin Diddi

"Ya naji motsi nace ni ɗin ma ba karni a kazo yi ba sarakan kisan kai Allah ya fiku masu mugun nufi"

"Diddi suwaye kuma makisa a ina suke?"

"Au kaine ja'irin yaro sai ka faɗo min ɗaki cikin sanɗa, ina choculate ɗin rannan da nace ka shigo min"

"Ke Diddi ba wani haƙorin kirki ba amman sai son shan zaƙi ina ke ina wani choculate ke dai kici Rogo da me ma ake ce masa ummm geɗe"

"Geɗar ce baka sani ba sai kai tunani lallai Maheeru da sauranka yakama ka koma ƙauye wannan karon ko zaka waye"

"Godforbid villege ni a'a ni da ƙauye sai dai naji labarinsa"

"Tou ai ƙauye shine gari, mu a lokacin mu ina ɗaya daga cikin kyawawan mata da aka dinga zuwa neman aure ina ƙi na fi son liman mai goro"

"Dis old woman in kin fara zuba ina ke ina kyau kawai dai kakan mu ya rufa miki asiri"

Ta dau sandar ta laluba ta kwaɗa masa tana 

"Ja'iri matar ka dai baza ta fini a kyau ba"

Yayi dariya yana "aiko da choculate naki nazo kuma ba zan baki ba"

"Miƙomin nan maza" ta fara lalube tana neman inda yake

Ya miƙa mata ta "ungo ba don halinki ba"

Diddi tace "atou ba dai ka kawo ba ae shikenan" ta buɗe ta fara sha tana kai amman baturen da yayi wanga alawar ya iyata"

Yarima maheer sai dariya yakewa Diddi yace "kai kaji tsohuwa da kwaɗayi santi ne fa kike yi Diddi"

Ito ko Diddi ta sami abin yi ko takansa bata yi ba haka nan ya mik'e ya fice ɗakin Hajjiya Ummah ya tafi ya sameta a kwance abin duniya duk ya isheta ga Aminiyar ta Hajjiya Zulai sun raba gari ga kuma ɗanta tilo an fiddasa daga masarautar da ta kudurci niyyar ta mallaketa, har kasa MAHEER ya duka

 Yana "barka da hutawa Hajjiya ya karfin jikin?"

Kamar ta mik'e ta shaƙosa dan a duniya in akwai wanda ta tsana bai wuce wannan MAHEER ɗin ba ta amsa kasa kasa da 

"Lfy"

Ya miƙe dan yasan daga wannan ba zata sake cewa komai ba ya dawo fadar mahaifinsa ya tadda mai martaba sarkin Ahmadu yana tattaunawa da wasu baƙi akan abubuwan da suke faruwa a wannan masarautar da kuma wajen gari yayi mamaki da yaji irin korafe-korafen da ake yi na zallunci a wannan masarautar da kuma wajen gari yayi tunanin komai ya daidai tu tun lokacin SARKI MA'ARUF kakan Yarima maheer anyi kashe kashe anzubda jini na rashin imani alokacin da kisan gilla a tunanin sarki Ahmad tun wancen matakin da aka ɗauka ba asake aikata ba sai gashi kwasam yau yaji labarin ba a daina zalunci ba koda abinci aka baiwa talakawa a raba musu ashe cinyyewa ake yi.

Cikin muryan maji mulki da izza da jarumta yace

"Ran sarki mai adalci ya daɗe kamar naji ana batun kisan kai da kuma zallunci aena kuma ake zallunci din?"

Sarki Ahmad baya son ɗansa Yarima yaji irin waɗannan labaran dan yasansa da zafi indai akai zallunci baya kyalewa sai ya ɓoye abubuwan da suka faru a baya sai dai na yanzun baya iya ɓoye wa sannan akwai tarukan sirrikan da yake ɓoyewa yace 

"Ina wajajen tonan Borehole na ruwa da nace a tone nan gabas damu har na dauraka akai kace min ana kan aekin shine fah nayi bincike akace Borehole 7 kawai aka tona baccin guda 35 nace a tona sannan wannan guraren ana faman rashin ruwa sosai"

Ran Yarima maheer yayi matukar ɓaci yace

"Nayi tunanin an kammala ae dan last tafiya ta wajen an tona guda 5 ashe an dakatar da aekin, kada ka damu yanzu zan wuce cen na duba naga meyake faruwa?"

Sarki Ahmad yace "yauwa haka nake so dan Allah asa ido sosai sannan na aeka da buhun hunan abinci ka tabbatar kowa ya samu"

Babu wani ɓata lokaci Yarima maheer ya ɗauki motaci sukayi cikin gari yana shiga ya ga mutane sai ɗaga masa hannu suke shima yana maida musu duk da asirin da akai masa da kuma izza da mulkin sa hakan bai hanasa jin tausayin talakawa ba yana isowa wajen tonon Borehole ɗin yasa aka kirawo Bulaman wajen yana isowa cikin girmamawa yace

"Barka da zuwa Yarima mai adalci....

Ɗaga masa hannu yayi alamun baya son kirari yace

"Me yasa ba a kammala wannan aekin ba ina waɗanda aka basu kwangila aekin?"

Cikin girmamawa yace "tunda suka tone guda 7 bamu sake ganinsu ba...

"What have you said? Do you mean basu ƙarasa aekin ba kuma suka tafi? Please a ina suke a nemomin su cikin 15mint ya bada umurnin ya fito masa da kujerar zama daga motarsa aka fito masa da ita ya zauna yana jiransu har suka iso wajen mutum 13 suna isowa suka rusuna suna gaidashi.....

Ɗaga musu hannu yayi dan shi baya son hayaniya da yawan gaisuwa yace

"Me yasa aka tsaida aekin ba a ƙarasa ba ina sauran kayan aekin?"

Cikin e'e'na suka ce "Allah yaja kwanan yarima sauran kayan munnemesu muka rasa...

Ya dakatar dasu ta hanyar cewa

"Bangane ba kamar ya annemesu kuma aka rasa kafafune dasu da zasu gudu? Kuma kunsan wannan bazai shiga min kai ba dan haka zan tafi daku kurkukun masarauta in kun shirya faɗan gaskiya sai ku faɗeta acen.

Babu wani ɓata lokaci yace akiramasa iyalen waɗannan mutanen kuma yace abasu abinci na wata ɗaya zai tafi da mazajensu masarauta suna isowa Masarautar yasa aka kaiwa iyalensu abinci mai yawa sannan ya rufe mazajensu kuma yace in sun shirya faɗin gaskiya zai buɗe su amman ba yau ba yarima maheer yayi gaba abinsa ya sanar da mahaifinsa yadda yayi da mutanen, Sarki Ahmadu yayi farin ciki da hukuncin da ya yanke shiyasa yake matukar kaunar sa yarima maheer baya wasa da aekinsa yasan ko da bayan ransa Yarima maheer zaiyi adalci mulkinsa kuma talakawa zasuyi alfahari dashi.

Sannan Yarima maheer yasa hadimansa su dinga kawo musu abinci a kurkuku dan shi a ka'idansa shine duk wanda aka tsare abasa abinci baya son horon yunwa sannan yana kawo ziyara a ƙalla sau biyu a rana dan ganin halin da ake ciki, akwai wata sohuwa a ɗayan ɓangaren da ke cikin kurkukun ita kaɗai aka killace a duk lokacin da ya kawo ziyara sai yaga tana kallon sa tana murmushi yarasa dalili.


 *GIRLS BOARDING SCHOOL ( G B S )*

 Ana washegari zamu zana jarabawa ta ƙarshe na fito muna zaune a compound cikin uniform namu na ranar weekend wasu na wanki wasun mu na ƙiso ni kuma ina zaune akan wani dan dutse ina taje gashina dan sabar yawansa ko kitso bana iya masa shamsiyya ta iso inda nake ta zauna tana

"Kai ƙanwata da kin dan tsammin gashin kanki na hada da gwaguyayyen nawa ko yayi kyan gani"

Nace "tuf kice Ma sha Allah ko kice tabarakallah, ae kema kina da gashi"

Tsaki Fauziyya taja mai ɗan tsawo taci gaba da wanke ƴan patarinta.

Na kalli inda take nace "ae storo kesa mutan ya kasa yin magana kuma kwalelen mutum sai dai mutum ya haɗiyi zuciya ya mutu. Na cigaba da tajewa na kama da ribon.

Maryam tace "ke dai Deeje akwai ki da iya tsara zance daɗina dake ba a tanka miki ki kyale"

Na tabe baki nace "ah wane mutum ni bani sokana amman in an taɓo ni ne bani kyalewa  ko kinga laifina?"

"Ke Maryam ki iya bakinki ina daidai da zamaninki idan kika ce zaki yi dani ba zaki ji da daɗi ba" cewar Fauziyya

Nayi dariya nace "kai daɗina da ɗan Adam akwai saurin fahimta ke maryam ci gaba da aekin gabanki"

Fauziyya tasan halina bana raga mata tunda na gurza bakinta da dutse bata ƙara zagina ba na miƙe na wuce inda na shanya uniform ɗina na kwashe bayan na naɗesu na dawo ɗakina na saka kayan nawa a lokata na haɗa garin kwaki da suger da madara na soma sha ina santi ina kammalawa na tuna da kiran da Hajjiya iklima ke min na mike nayi quarters ina zuwa ko ta aikeni naje nayo mata siyayya na dawo ba wani ɓata lokaci na koma hostel naci gaba da karatuna har zuwa lokacin kwanciya muka kwabta.


    *WASHEGARI*


Muna shiga class kowa yasami wajen zama aka raba mana paper muka fara zana jarabawa ta Chemistry shine last paper mu bamu wani ɗauki lokaci ba muka kammala muka fito ɗaya daga cikin invijilator ya kirani me suna Sanda dan tunda muka fara zana SSCE idonsa akaina yace min nazo na samesa a office na vice principal na shigo tare da sallama na duka kamar yadda ɗalibai suke yi yace

"Ya exam? fatan baki sha wahala ba?"

Na kallesa dogone baƙi dashi yana da kyau ba laifi sannan akwaisa da nutsuwa nace

Eh kam ba laifi yayi daɗi kuma yayi wahala ko dan wannan shine karon farko da nayi"

"Eh hakane bcos this is your first time dole kiji shi haka, amman karki damu ba komi zaku wuce"

Tho Allah yasa duk wannan maganar da nake yi kaina akasa a tunanina tausayina yake ji yace

Anan garin kike? What i mean ke ƴar nan MAIDUGURI ce ko daga wani gari kike?"

Na ɗago na sake kallon sa for the second time dan na fara gajiya da tambayoyin da yake min haba sai kace ɗan jarida nace

"A'a fah daga ƙauyen Kukawa nake.

"Oh are you from local government amman baki yi kamada ƴar cen ba i was surprised kin fi kama da ƴar birni"

Tho nifa Deeje bani son rainin wayo mai yake nufi da wannan zancen.

Nace "tho ni dai ƴar ƙauye ce kuma ƴar Gwaggo" na turo baki.

Yayi murmushi "tho ƴar Gwaggo yanzu me kike son ki zama tun da kin kammala secondary School naki?"

A raina nace yanzu naji batu amman ka tsaya kana wani zance. "Zanci gaba da karatuna na gaba da secondary"

"Ok yayi kyau. 

Na mik'e na fita zuwa inda su Shareefa suke Maryam tace

"Ah su Deeje anyi kamo wai invijilator da kansa"

"Uhm lallai kam Deeje bani da lokacin wata alaƙa da namiji"

Shareefa tace "tab tun wuri yasan inda dare yayi masa karatu zamu yi.

Nace "kina ma ɓata lokacin ki shareefa harda wani tambayata wai yanzu mai zanyi dana kammala skul, ni na rasa dalilin bashi amsa ma.

Mukaci gaba da hirarmu.



 _BAYAN KWANA BIYU_

Bayan kwana biyu da zana SSCE muka tattara kayayyakin mu kowa yayi gida ni kam a gidan Hajjiya Iklima na zauna dan cewa tayi anan zan zauna zuwa wani lokaci sai na koma wajen Gwaggo, inaji ina gani motar Kukawa tazo ta kwashe mutane ta tafi dasu. 

Na ɗauko waya na kira Ya Auwal...

 _Ƙauyen Kukawa_


Auwal na zaune a shagonsa bayan ya haɗawa wani matashi magunguna yayi treating nasa na thaifod tunda ya shigo shago bai zauna ba sai yanzu wayarsa ta dau ruri yana dubawa sai yaga Number da Deeje ke kiransa da ya ɗauka tare da sallama sannan yace

"Deejee congrats da kammala secondary School ina taya ki murna"

Cikin jin dadi da farin ciki nace "Thank you Ya Auwal ya aiki ya wajen Gwaggo?"

"Tana lfy Deeje jiyama Gwaggo tazo tace na kira mata ke nayi ta gwada Number amman bata shiga"

"Ayya maybe network ne amman akunne take dan a wajen Hajjiya Iklima take kasan wayar ta ce.

Yayi murmushi Deeje Sarkin sara zance "eh nasani Deeje.. sallamar Gwaggo ce tasa yayi shuru ya amsa sallamar ta yace tsohuwa ƴar halak ga jikarki nan sai ku gaisa" ya miƙa mata wayar tana karɓa kamar zata shige cikin wayar

"Deejee ta ya kike naji labarin motar da take kawo ɗalibai yau zata iso nace ko harda ke acikin waɗanda zasu iso?"

Nayi ajiyar zuciya Allah sarki Gwaggo nima nayi kewarta nace "a'a Gwaggo ba dani za a iso ba Abban Shareefa ne yace na zauna sai zuwa wani lokaci sai na koma"

"Babu komai Deeje ai kamar yaune ki gaidasu baki ɗaya"

Zasu ji gwoggo ya tuyar ƙosai?

"Lfy Deeje bana yawan fita yanzu daman saboda ke ne dan ki samu ki kammala karatun ki amman tun bayan tafiyar ki Auwal ya hanani wai girma ya kamani abinci ma daga gidansa ake kawo min fita tuyarma yanzu jifa_jifah nake yi"

Allah sarki ya Auwal mutumin kirki samun irin su a wannan zamanin basu da yawa nace

"Mun gode sosai ya Auwal Allah yasaka da Alkhairi"

Gwoggo tace "Ameen" 

Ta miƙa masa mu kayi sallama.



 *MASARAUTAR SARKI AHMADU*


YARIMA maheer ne a tsaye yana kallon sabbin ma'aikatan da ya kawo su tone Borehole kuma yace nan da sati ake bukatar su kammala dan unguwar suna bukatar ruwa.

Sanye yake cikin shigarsa ta shadda half jampa ruwan ƙasa ta amshi fatarsa ya kafa hula danshi ba kasafai yake daura rawani ba V face nasa mai dauke da jerarren saje wanda yake shan gyara ko da yaushe ya saka farin glass a fararen idanuwansa ya kalli guard nashi yace ku sanar dasu zuwa anjima zan sake dawowa sannan zan aeko musu da kayan abinci da dai duk abinda za a bukata"

Cikin girmamawa guard din yace "duk yadda kace yarima haka zamuyi" ya koma ya sanar dasu sannan ya dawo suka wuce Shopping.

Kamar yadda ya saba muddin yazo siyayya tho kowa barin cikin shop ɗin yake ya fito sai ya kammala ya fito sannan kowa ya koma yayi abinda ya kawosa, yana shiga bayan kowa ya fita yayi siyayyansa da na rabin ransa Diddi sannan yafito yana fitowa idanuwansa na nuna masa ga yarinyar da tayi masa rashin kunya rannan ya kurawa karamin bakinta ido yana kallo yana tuna yadda take motsasa wajen yimasa rashin kunya a ransa yace "yau  zaki san da yarima kike"

Ya bawa guard's nasa umurnin su taho mishi da ita sannan kowa ya shiga yayi siyayya. Ba wani ɓata lokaci suka sata gaba a dole ta bisu ba tare da tasan laifin me taiba kai saye sai GUEST nasa suka wuce da ita.....




Comments and share fisabilillah