Ƴar gwoggo

Page7

by @barista

ƳAR GWOGGO 

***
Book1
Page 7


 Suna isowa su kayi ciki da ita ɗakin da yake ajiye sauran ƴan mata  nan aka sakata sai da ya ɗauki lokaci sannan ya shigo da zummar koya mata hankali yana shiga yaga ba ita bace yace

"Ke me ki keyi anan? ta ina kika shigo?"

A tunaninta yana cikin maye inba haka ba ya shigo da ita kuma yace ta ina ta shigo bata yi magana ba ta ci gaba da kukan da take yi ya daka mata sawa. "ina yarinyar da muka shigo da ita?"

Jikinta na ɓari tace "nice"

What? Bangane ba kece kamar ya? ya fice inda guard's nasa ke zama suna kai yau Boss yayi babban kamu wai yau zamu huta ba fita kenan suna cikin haka ya iso inda suke yayi wulli da table din dake gabansu yace 

"ina take wayace ku sauyata?"

Basu fahimci abinda yake nufiba suka ce

"Boss WACECE kuma kake magana a kanta ae indai yarinyar ce tana ciki"

Ya daka musu tsawa.... Sannan yace "yarinyar da tayi min rashin kunya last some months back nake magana ba ita nace ku ɗauko min ba amman kuka ɗauko min waccen kuchakar"

Kallon kallo suka fara yiwa juna anya Boss yana daidai kuwa ko dai da gaske ita din spirit ce dan tun da Boss nasu ya nemeta ya rasa a duk lokacin da yaga wata mace sai yace itace haka suke fama ko dai this time gamo yayi da Aljana..

"Ba daku nake magana ba kunwani tsareni da idanuwa". 

Cikin girmamawa suka ce "Boss bata fah wajen wannan yarinyar ce a tsaye kuma ita ka nuna mana"

Ya sauke numfashi sannan yace "kuje ku ɗauketa daga nan kada na sake ganin ta" ba shiri sukai ciki suka fito da ita a inda suka daukota anan suka ajiyeta.

Ya kishingiɗe a kan 3setter ya runtse idanuwansa ba abinda yake hangowa sai fuskar yarinyar da ɗan ƙaramin bakinta tana zazzago mai rashin kunya ya buɗe idanuwansa a fili ya furta "wai me yasa ya kasa mantawa da ita why she always comes to his mind?" Ya miƙe batare da ya sami amsar ba ya ɗauki shopping na kakarsa Diddi ya fito ya basu umurnin suyi masarauta dashi bashiri suka tada mota sai masarauta.


 *MASARAUTA*

Ana parking ya fito ba tare da sun buɗe masa motaba ya buɗe ya fito abinsa bai wuce fada ba yawuce wajen kakarsa Diddi yana shiga ya sameta kwance da alamun bacci take har ya ajiye leda zai fice tace

"Maheeru"

Ya juyo a sanyaye yana kallonta a hankali ya tako inda take kwance yace

"Na'am Diddi lfy kike kwance?" Ya dafa kanta sai yaji da zafi murya na rawa yace 

"Diddi meke damunki?" Yana kokarin ɗagata ya jingina ta da jikin garu bayan yasa mata pillow ta bayanta ta kallesa tace

"Kai lfy lau kawai bacci nayi baijima ba na tashi"

Yayi ajiyar zuciya"kai Diddi harkinsa na tsorata"

"Maheeru tsoron meye kuma aini ba zan mutu ba har sai naga ƴaƴanka"

"Da yardan Allah zaki gansu Diddi tashi na haɗa miki tea kisha sannan nayi miki siyayya ma"

Ta tashi zaune ya haɗa mata tea tasha sannan ya mika mata ledar da yashigo da ita yadinga janta da hira tace

"Maheeru yaushe zaka ziyara KAUYEN KUKAWA ne ka gano min yarima ABDULLAHI da maifinsa ko dai lfy shuru²"

"Kai Diddi villege ni gaskiya ba zani cen ba Allah ƙauye babu daɗi bana iya bacci kwanan zaune nake kinsa akwai damisa da kura"

"Maheeru yanzu saboda ƴan uwanka mutan kauye ne ba zaka kaimusu ziyara ba wannan ma tun ina da rai inna mace fah"

"Kai Diddi zanje amman ba yanzu ba"

Ya miƙe ya fice zuwa ɗakinsa.

Sai da yamma ya fito ya kai ziyara kurkukun masarauta ya sallami mutanen da ya rufe su tare da basu jari bayan sun tabbatar masa da cewa sun tuba ba zasu sake ba.

Ya tako zuwa inda matar nan take ya tsaya yana kallonta ga abinci a gefenta da ruwan sha da alamun yanzu aka kawo mata sannan kwanon abincin ta ma da banne ba irin na sauran ba yau ma murmushi ta sakar masa.

Ya maso dab da kofa yace "me yasa da kin kalleni kike min murmushi da alamun da magana a bakinki"

Ta sudda kai ƙasa ta koma da baya ta juya masa baya taƙi ba shi amsa ya gaji da tsayuwa ya fice daga wajen yana barin wajen sai Hajjiya ummah ta fito daga maɓuyarta ta ta kalleta tayi mata nuni da in ki kayi magana sai na kasheki...


 *QUARTERS NA G B S*


Muna kitchen muna girke girke kasancewa yau asabar principal yana yawan yin baƙi ranan dan har wuni sukeyi a side nasa, Hajjiya Iklima ce ke koyamana girke girken zamani kala kala kasan cewar yanzu bama zuwa skul tace mukayi girki da wasu abubuwan kamin mu tafi jami'a.

Hajjiya Iklima tace "khadeeja ki yayyanka waccen fruit salat ɗin ke kuma Shareefa ki mayar da hankali kan haɗa Stew ɗin kada ki bari ta kame kina saukewa ki daura farar macaroni. Babu jimawa muka kammala muka wuce muka jera a Dining area dake side na principal ya fito daga ɗakinsa yana gyara a gogon hannunsa mu duka ƙasa Shareefa tace

"Ina kwana Daddy" ya amsa nace

Ina kwana Baba principal ya juyo ya kalleni sannan yace "Deeje baki girma ba na hanaki faɗan wannan sunan ba"

Na ɗan tsosa keya nace "ayi hakuri na manta ne mema kace nace?

Yace "ba kiji sunan da ƴar'uwar taki ta kirani dashi bane?"

"Ah emm da..ddy yauwa Daddy to ae gwamma mu ce Abba ma ae" ya fice tarban baki muka dawo ciki nace

"Kai Allah Baba principal baya son tsufa wai ace Daddy sannan abu kaɗan turanci ni fah kinga turanci ba sonsa nake ba shiyasa ma ko na tafi jami'an Allah fannin girke girke zan karanta nayi ta ƙwalama abina"

Shareefa sai dariya "maimakon kiyi karatun likitanci shine zaki karanta Food and nutrition lallai baki iya zaɓi ba"

Koma food and wanene ma ni dai ta fanni girke girke nake wa zai je yayi fiɗa da ɗinki jikin mutum da kwakule hanji Allah badani ba"

Ita dai Shareefa sai dariya har muka iso kitchen muka sake jido kaya muka sake kaiwa muka jera sannan muka dawo ɗakinmu mukai wanka muka sauya kaya nasa ƴar atampata wacce baba principal ya ɗinka mana riga da skirt tai min kyau muka zauna zaman cin abinci.

Ba ma fita ko ina a gida muke wuni sai bayan la'asar Hajjiya ta aeke muka fito ji mukai ankira sunana muka juyo wannan invigilatorn ne muka saya yace 

"Ina zuwa haka da yammacin nan?"

Shareefa tace "aiken mu akayi" 

Ya kalleni "khadeeja ba magana ne yana kare min kallo. Nace

"Munwuni lfy" dan ni gani nake rainani yayi ranan da yace min ƴar ƙauye.

Yayi murmushi khadeeja sarakan rigima yau kuma mutanen suna kusa kenan"

Nace "ni ka daina dangantani da wasu mutanen ɓoye lfy ta lau ae hira ba dole bace ko dole ce?"

Ya sake kallona yace "ba dole bane amman yinta na da kyau ae"

So yake na kula shi amman nayi fuska muka wuce siyayya nan shop ɗin da wannan Yarima yake zuwa muka kammala muka dawo gida.....

"Daga ina kuke? Muka jiyo muryan Baba principal Shareefa tace "aikenmu Hajjiya tayi dawowarmu kenan"

Dawa naganku ɗazu kuna tsaye a bakin titi kuke zance babu ko kunya" ya faɗa cikin ɗaya murya.

Idonmu ya raina fata ashe ya ganmu ɗazu nace

"Daddy invigilator ne fah Wanda suka zo ranan exam namu shine ya ganmu muka gaisa"

Ya faɗa cikin ɗaga murya ku jini da kyau wacce take son karatu tho ta shirya zuwa nan da watanne result zai fito sai ta fara karatu wacce kuma aure take so ta fito da wanda take so tun wuri ayi mata sannan zabi ɗaya za ayi karatu ko aure kuma wanda ka zaba shi zaka yi babu canji"

Muka zuzzura idanuwana ya wuce abinsa muna shiga muka tadda Hajjiya a palour tana ganinmu ta fara surfa bala'i "Ni na aeke ku dan siyayya shine kuka tsaya zance ko yayi muku kyau da kuka sa akayi min faɗa harda kashedi" ta ɗauki leda tayi ciki jikin mu yayi sanyi tab yau mun taɓo Daddyn.

Da kyar muka bada hakuri Daddyn ya sauƙo yace kada yasake ganinmu da wani ɗa namiji aurar damu zai yi.


 _BAYAN WASU watanni_ 

Result namu ya fito mun yi ƙoƙari muka samu admission a jami'a ni na samu  N U D ita ko Shareefa ta samu poblic admin, nan da sabon wata zamu fara fita Daddyn ya bamu kuɗin siyayya muka je muka yi saura mana abu kaɗan nace zanje babban shop na sayo mana.

Na fito daga wanka duk jikina ba kwari na shafa mai na saka doguwar riga ta atamfah nayi dauri na yafa gyalle na saka plat shoe da side bag nace "Shareefa ban list naki kada nayi mantuwa" ta miƙomin na saka a side bag tace

"Ya dai Deeje ko dai fitarce baki so yau?"

Nayi ajiyar zuciya nace "eh amman ba komai zanje na dawo" na fito nayi shopping area na fara siyayya.



 _YARIMA maheer_ 

Yayi wanka yau shigar sarauta yayi dan zasu tattauna a faɗa da wasu baki ya kalli kansa a madubi ya gyara daurin rawanin kansa sannan ya gyara a gogon hannunsa yasake feshe jikinsa da daddaɗan turare ya fito yayi ɗakin Diddi suka gaisa tace 

"Maheeru yau ina son madara tawa ta ƙare ka karɓo min mana anjima"

Ya kalli inda take ajiyar kayan tea yace "zan shigo dashi amman zuwa anjima yanzu zani fada"

"Ba damuwa indai zaka shigo min dashi"

Ya fito yayi faɗa ya tadda bakin har sun karaso aka fara tattaunawa sai bayan bakin sun watse ya wuce SHOPPING....

Ina saka da siyayya na kammala shopping na Shareefa na fara nawa.... Aka fara sanarwa ga yarima maheer ya iso zai yi siyayya kowa ya fice aka fara fitowa wasu harda haɗawa da gudu na kallesu na sake maida hankalina kan siyayya ta shuru ya ɗan rasa wajen cen ya shigo sai zuba kamshi yake yana tafiya ta kasaita a hankali kamar baya son wahalar da ties na wajen.

Cikin nutsuwa na fara turo keken da na zuba kayana acikin ina turawa na iso wajen turaruka suma suka shigo ta wajen kallo na suka tsaya yi ni ko nayi kamar bangansu ba na zaɓi turaren da zan ɗauka na juyo ta inda suke har na iso basu daina kallona ba kuma basu matsamin na wuce ba.

YARIMA maheer tun da ya daura idanuwansa a kanta gabadaya ya ruɗe da farko gani yake gizau take masa kamar yadda ya saba gani.

Gaurd nasa yace "ke me ki keyi anan da ba zaki kauce ba kuma kinsan dokar nan muddin yarima ya shigo babu mai tsayawa"

Na kallesa sama da ƙasa cikin nutsuwa nace "doka? Wane irin doka kuma aini doka in bata Allah ba bana bi rai ne daku kuma raine da ni kunga na kammala siyayya ta ku bani waje na wuce"

Yarima Maheer sai alokacin ya dawo daga duniyar tunanin da ya shiga tabbas itace yace

"Muma ai bama ƙetare  dokar Ubangiji sannan ki sani akwai na gaba dake kuma ya zama dole kiyi biyayya"

"Haram Allah ake yiwa biyayya ba wani ƙato ba kuma indai siyayya ce anan yanzu na fara"

Ya kurawa ƙaramin bakinta idanu yana kallon yadda take motsa bakinta wajen yimasa rashin kunya yayi murmushin mugunta lallai sai ya koya mata ɗa'ah yace

"Take her with you" bai sake ganin inda muke ba ya ci gaba da ta kunsa yana duba abinda yake so dana Diddi. Kamoni ɗayan yayi ya jawoni waje ta ƙarfi yana zuwa ya jefani cikin mota ya rufe yasa key, na fara kwalla ihu ina ɓarayen mutane wallahi sai na rama wulakanci da ka yi min"

YARIMA Maheer sai da ya gama siyayyarsa sannan ya fito ya shiga ɗaya daga cikin jerarrun motocin dake waje suka tada aka fara tafiya nace wa mutanen dake zaune a gaban mota 

"Ina zaku kaini wannan ae zalunci ne ku saida motar na fice. Na faɗa da ƙarfi.

Ko kulani basu yi ba har muka iso GUEST HOUSE.


 *GUEST HOUSE*

Ana wangale kofar na ganni a wata duniya na bar motsi sai kallo. Na hango wajen wanka an ƙayatasa da wasu furanni gefe dashi kuma garden ne na fruits kala² akwai wani ƙaramin kofa ta sakanin wajen da raga² da alamu nan ake wasan kollon ƙafa sannan ginin tamkar a cikin ƙasa yake ya haɗu matuka....

Ji nayi yace "wuce ciki" na kallesa nace "kamar ya na wuce me zanyi acikin? maidani inda ka ɗauko ni"

YARIMA maheer na mota bai sauƙo ba yana kallon yadda nake karewa gidan kallo babu ko tsoro a tare da ni lallai yana bukatar sanin WACECE wannan yarinyar.

Shigar dani yayi cikin ƙarfi muna shiga nan ma na tsaya kallo palour sai kace ba a duniya ba naga wani makeken TV wanda ya kusa rabin garun wajen ya sake janyo ya jefani a wani ƙayataccen ɗaki wanda yaji gyara da kamshi yasa key yayi tafiyar sa na kurawa kayan ɗakin kallo na buɗe labule ina kollon waje naji an turo ƙofa na waiga naga wannan Yarima ne nace

"Yauwa gwanma da ka shigo ya kuka yi da siyayyar da nayi a ina kuka ajiyemin sannan ka faɗawa wannan guard naka duk abinda yayi min sai na rama komin daren daɗewa.

Yanzu ta daina bashi mamaki tsoro ta fara bashi is she a human being kai akwai duba a cikin al'amarin. Ya tako inda take ya matso dab da ita yana jin ƙamahin da ke tasowa daga jikinta ya ɗago da haɓarta ya kura mata idanuwa....

Naga sai kallon fuskata yake nace "sun jimin ciwo ko bani hanya na duba a madubi na bugesa zan rabesa na wuce ya dawo dani baya ya haɗani da gini ya fara shaƙar kamshin jikina nasa karfi na hankaɗesa ya fadi kasa nace

"Wannan ai kwartanci ne meye haka? kaga buɗemin ƙofa na tafi Baba principal yanzu haka na san ya fara sa idon zuwa na"

Ya mike tsaye ya furta cikin cool voice nasa yace 

"Ai ke kinyi bankwana da gida baza a sake jin labarin ki ba sannan ni kike cewa ina kwartanci zaki gane kurenki" ya fice ya sa key.

Na girgiza dajin maganarsa nayi baya kamar zan faɗi mai yake nufi ne? Nayi bakin ƙofa na dinga dukan Kofar amman babu wanda ya tankamin har na zauna a ƙofar ɗakin ina ajiyar zuciya.

Wasa wasa nayi kusan 3 hours a zaune bana jin motsin kowa na miƙe na tura Kofar da nagani a cikin ɗakin sai na toilet ne nayi alwala na fito na gabatar da sallah na juyo na kalli ƙofar dan naji kamar motsi YARIMA nagani a tsaye ɗauke da tray da food flask akai ya ajiye na miƙe da sauri nayi hanyar fita yasa hannu ya riƙe ni ya dawo dani da ƙarfi na faɗi kasa ya nunani da ɗan yatsa yace 

"Kul kada ki kuskura kice zaki yi min taurin kai ba zaki ji da daɗi ba" ya fice ya sake saka key.

Deejee dai na buɗe abincin na gani haɗaddiyar jollof ta macaroni ce wacce taji kayan haɗi da naman kaza na rufe na koma gefe na zauna nayi tagumi wai yau naga ta kaina me haka kuma wani irin abune haka ace azo a killace mutum a ajiyesa ba tare da an san mutum ba tho ko dai yankan kai yake yi? Tab Allah sarki Shareefa ina kike kizo ki ceceni ina zaune har bacci ya daukeni a wajen.


 *QUARTERS NA G B S*

Jin shuru yayi yawa yasa Hajjiya Iklima ta kira wayar Deeje amman bata shiga da dai shurun yayi yawa tasa Shareefa tabi bayana gashi goshin magrib ne Shareefa tayi yawon duniya amman babu labarin Deeje kuma har shop ɗin taje amman cewa akayi cikin customers naso babu wata Deeje tsoro suke su faɗa dan bazasu ji da daɗi ba muddin Yarima maheer yaji sun faɗa haka ta tattaro ta dawo gida jiki a sanyaye ta tadda Hajjiya da Baba principal a tsaye a palour suna jiran isowarta da sallama tashigo suka amsa tace

"Daddyn na zaga duk inda na san zan ganta amman babu labarinta ta fashe da kuka....

Baba principal yayi salati yace "how comes ace mace kamar Deeje ta ɓata ko anemeta a rasa"

Hajjiya Iklima tace "Allah yasa ba kidnaping din ta akayi!

Shareefa ta sake fashewa da kuka tana mun shiga uku Deeje ina kika shega"

A ranan dai babu ci balle sha haka suka kwana.


 _MASARAUTA_ 

Yarima maheer yana fita daga Rest house ya wuce masarauta kai tsaye ɗakinsa yayi ya wuce toilet ya kunna shower a kansa ba tare da ya kwabe gajeren wando da vest ba ya rumtse idanuwan sa fuskar ta kawai yake gani da fararen idanuwanta masu daukan hankali ga kyakkyawar surarta kaiiii! 

Da ƙyar ya iya fitowa daga toilet ya sauya kaya zuwa kananun kaya ya wuce ɗakin Diddi tana zaune yayi sallama ya zauna a kusa da ita yace

"My Diddi barka da hutawa"

"Maheeru barka dai ya tattaunawar taku"

"Sai godiya na wuce nayo miki siyayya ma ga tanan" ya ajiye mata leda a kusa da ita.

"Allah yayi albarka"

Yace "Ameen"

Ya dawo ɗakinsa ya hau lafiyayyen gadonsa ya kwanta amman ya kasa bacci sai juyi yake maisa yaki barin yarinyar ta tafi shi a ka'idansa baya barin yarinya ta wuni ma balle har ya kaiga kwana amman kuma yakasa barinta tayi tafiyar ta ya dinga juyi har bacci ya daukesa cikin bacci ya dinga ganin deejee tana kallonsa tana mai rashin kunya ya kama bakinta ya tsosesa tass sannan ya barta amman bata daina tsiwa ba haka ya fice ya barta a ɗakin..


 *_WASHEGARI_*


Farkawa nayi jiki duk ciwo ga gari yayi haske  kukan tsuntsaye nake ji dana karnuka na miƙe da ƙyar na shige toilet na ɗauro alwala nayi sallah cikina ya daure sabar yunwa sai faman hamma nake na kalli inda abincin yake yananan yadda a ka ajiyesa tun jiya na ɗan kishingiɗe da jikin garu na lumtshe idanuwana wanda basu sami ishashen bacci ba naji alamun motsi a tunanina shigowa za ayi na ɗau ƙaton kwalba nace duk wanda ya shigo rafka masa zanyi yana faduwa sai na fice nayi gida, shuru ba a buɗe ba na koma na zauna ina haki da kuma jin jiri na ɗibana SBD yunwa.


 *Yarima maheer* 

Yana tashi da safe ya dinga tuna mafarkin da yayi da waccen yarinyar ya shafa sumar fuskansa ya mike ya faɗa toilet ya watsa ruwa ya fito ya shirya cikin shigarsa ta kananun kaya yayi kyau ya maka white glass a fararen idanuwansa ya fito yana ɗaura agogon hannu ɗakin Diddi ya wuce ya gaida ta sannan ya wuce ɗakin Hajjiya ummah tana kwance tana sake² a ranta ta yadda zata ɓullo wa lamarin tana son ɗanta ya dawo MASARAUTA amman haryanzu bata sami hanyar yin hakan ba yayi sallama ya shigo ko kallonsa batayi ba taci gaba da kallon gefe ya gaidata bata amsa ba ya fice daman ya saba taja tsaki ta furta "mutum kamar maye" ta dau  waya ta kira kawar ta Hajjiya zulai amman taki dagawa haka ta hakura gashi tana son zuwa inda YARIMA Maleek yake amman Sarki Ahmadu ya hana haka ta hakura.

Yarima yana fita ya wuce hotel yayi order abinci sannan ya ɗauki hanyar Rest house nasa yana isowa gate man ya buɗe masa kofa kan yayi parking ya hango gaurd nasa yana tsula gudu kamar ƙafafuwan sa zasu tsinke sai kwarkwar yake ta area swim pool ya bude murfin mota zai fito yaga gaurd ɗin yayo inda yake yana "ka koma cikin mota Boss wallahi kashemu za tayi aiko YARIMA ya koma mota cikin sauri yarinyar ya hango tayo inda suke da gudu hannunta rike da kwalbar wind🍷  guard nada me suna Luka sai faman sarfa gudu yake suka fara kewaye motar da yarima yake cikin ita dai sai ta maƙa masa zata huce garin maka masa ta daki glass na motar jikake kas ya fashe haba yarima da jin haka ya fito yana 

"Ke! Baki da hankaline zaki fasa min glass kin san sadansa kuwa? Kan ya ƙarasa ta nufo inda yake gudu take da ƙarfinta tana

"Ni za a yiwa iskanci dan anga ina shuru sai amaidani sakarya ku killace mutum kamar dabba tho baku isa ba tai salle ta kaiwa Yarima kwalbar ya kauce sai ga Deeje a kasa ta faɗi sumammiya dan yunwa tai mata illah sannan tana jin jiri.

YARIMA maheer yayi tunanin  pretending ne yayi baya yana idan zaki tashi ki tashi sai yaga ko motsi ta kasa ya matso yasa hannu yaji bata motsi yasa hannu ya ɗaga ta yayi ɗaki da ita yana shiga ya kwantar da ita ya ɗebe ruwa mai sanyi  ya watsa mata a fuska ta buɗe ido tare da ajiyar zuciya a hankali ya furta

"Alhamdulillah"

Deejee ta buɗe idanuwa ta yunkura zata tashi ta kasa sabar yunwa tace

"Sai Allah ya sakamin mugaye"

Bai yi magana ba ya fahimci jikinta ba kwari ya buɗe food flask ɗin da ya kawo jiya sai yaga bata taɓa abincin ba har ya lalace ya juyo ya kalleta yace

"Me yasa bakici abinci ba ko so kike ki illata kanki"

"Illatarwa ta nawa bayan kun illatani so kuke ku kasheni"

Haɗa mata ruwan tea yayi ya dauƙo take away na chips ya ajiye a kusa da ita yace 

"Tashi kici abinci" ko kalle sa ba ta runtse idanuwa.

Yayi ajiyar zuciya ya ɗauki tea cup ɗin ya haura kan gado ya ɗago da ita za tai gardama amman ta ƙasa saboda ƙarfinta ya ƙare haka ta hakura ya ɗura mata ruwan tea ta shanye sa tas sannan ya saketa ya miƙo mata da chibs din taki ansa har zai da ya sake yi mata riƙon maza tace

"Bani nan mugu kawai ae wannan mugunta ne" ta karba ta fara ci ya mike yayi fice tare da saka key a kofa.

Ya fita yayi inda gaurd nasa Luka yake yana isowa yace 

"How comes that happened? Luka kana wasa da aikin ka ko?"

Luka sai sauke numfashi yake yace

"Boss na shiga ɗakin kamar yadda na saba ko da mace a cikin ina mopping ina shiga na nemeta na rasa garin duba ta naji ta hankaɗe ni, she hide behind the door kamin na tashi she escape, i followed her and na kamata na maida ta shine ta ɗau that bottle of wine 🍷 and she start following me ina gudun ceton rai shine kashego wlh oga she is a killer, she's very dangerous.....

Marinsa YARIMA maheer yayi yace 

"Am i ask you to mop the room? Luka da yanzu ban shigo ba me kake ganin zai faru and who told you to touch her?"

Luka tsayawa yayi tare da dafe wajen da ya maresa yana kallon Boss nasa a ransa yace tho kishi ya keyi akanta! A hankali ya furta

"I'm sorry ban san hakan kuskure bane bcos I'm doing my work dan kada nayi laifi"

A lokacin sauran gaurd nasa suka iso dan yawancinsu magidanta ne driver nsa ma yau baizo ba SBD wani dalili da kansa yayi driving. Suka gaidasa cikin girmamawa basuyi tunanin zasu taddasa a wajen ba.

Ya kallesu ɗaya bayan ɗaya sannan yace

"Is this the best time to come? Kuna wasa da aekin ku ko yayi kyau ya koma ciki. Tho sukace yau oga da hannun hagu ya tashi.


Bayan na kammala cin chips din na bude robber ruwan da na gani na kwankwaɗesa tass sannan na koma na kwanta bacci ya daukeni sai danayi 2hours kamin na farka na mike na sauko daga kan bed na saya ta tagar window ina kallo compound na gidan  ya turo kufa ya shigo dauke da leda a hannun sa ya kalleni yace

"Take it"

Na kallesa tare da neman ƙarin bayani ya sauke numfashi ya ce

"You have to change"

Na kallesa nace "kai ka sanda wannan idan zaka min magana da hausa kayi min Mallam ka daina aro yaren wasu"

Yayi murmushi yace "ke wacce irin mutum ce wai bakinki baya shuru ne?"

"Ni mutum ce kamar kowa bakina yana shuru amman muddin aka taɓoni tho ba zan yi ba dan haka maidani inda ka ɗauko ni".

Ya sake miƙomin ledar yace "ga kaya jeki cikin toilet ki sauya waɗannan sunyi datti"

"Ina ruwanka da kayan da ke jikina ba zan sauya ba in ana dole ma gani"

Yayi murmushi mugunta ya tako a hankali zuwa inda nake tsaye yace 

"Okey let me help you"

Haba nayi baya nace "meye haka cikani kawai dan iska ni zaka cirewa kaya Allah wadai da halinka"

Ya gaji da faɗa masa bakaken maganganun da take yi da kuma kalmar ɗan iska ya finciko ta ta faɗo kan bed ya rike hannayenta duka biyu ya zuge doguwar rigar ta yayi jifa da ita ya kai hannu zai cire mata bra sai ya tsaya kare mata kallo kamar wani sabon taɓi fatar jikin ta laushine da ita ga ta fara tas sai sheƙi take yi ya kalli fuskarta da gashin kanta ya baje ya rufesa ya sa hannu a hankali ya fara gyara mata ya maida shi baya tace

"Ka cikani bana so wannan bai dace ba idanuwansa suka rufe da sha'awar mace ya kalleta yana fuzgar da numfashi bakinsa na rawa yace

"Ni kike kira da ɗan iska ko?" 

Gaɓa ɗaya na ruɗe da ganin yanayinsa dan ni Deeje duk iyayena bani kusantar ɗa namiji nace

"Ka cikani hannuna na min zafi" 

Ya ɗan tsagaita riƙon, ni kuma na samu na hankaɗesa na ɗau doguwar riga nayi toilet da gudu na saka key ina haki wai ni Deeje yau naga ɗan iska na watsa ruwa na sauya kayan kamar yadda yace na fito a lokacin ya bar ɗakin kuma ya kulle ta waje na zauna nayi tagumi oh ni ƴar Gwaggo ko yaushe zani gida na tuna lokacin yana gudu gashi nanda sati biyu zamu fara fita skul na fara tunanin ta yaya zan samu na tsere.

Shiko yarima maheer da ƙyar ya iya sarrafa kansa bayan ya fita ya dau cigarette nasa ya kuna ya fara busawa da haka ya samu ya ɗan sauko ya kwanta ba jimawa yayi bacci

 *QUARTERS NA G B S*


Yau kimanin kwana ɗaya da ɓatan Deejee Shareefa tai kuka kamar ranta zai fita na rashin deejee da zazzaɓi ta kwana suko iyayenta har zuwa yanzu basu sami nusuwa ba baba principal tun safe ya fita har zuwa wannan lokacin amman babu labarin Deeje haka ya komo gida ya tadda su suna zaman jiransa yana shigowa Hajjiya Iklima tace

"Anganta ne Alhaji?"

Yayi ajiyar zuciya yace "ba a sameta ba amman na bada ayi cigiya a gidan Radio"

"Tho ko zamu sanar da mutanen tane dan ɓoyemusu ba shine dai dai ba"

"Ba yanzu ba mu bari zuwa nan da kwana biyu kafin musanar dasu....


 *BAYAN KWANA UKU*

Kwana na uku a gidan YARIMA a Rest house nasa a killace a ɗaki tun jiya da ya shigo ya fita ban sake jin ko da motsi ba haka na kwana yau ma haka tunda na tashi banci komai ba babu koda ruwa ne a ɗakin inanan kwance har 11:00 shuru yunwa nake ji sosai cikina sai kururuwa yake min na kasa tashi na kwanta a kasan bed sai mususu nake kama mai na kuɗa, na mike nai toilet na kunna zinc ɗin dake cikin toilet din ya fara fidda ruwa nasa baki na dunga sha sai da naji cikina ya cika da ruwa sannan na hakura badan najini a koshe ba amman naji ɗan dama² na yunkura na mike da niyyar fitowa daga ciki sai ko na fara kwarara amai sai da na a mayar da ruwan da nasha baki ɗaya sannan na koma da baya ya haɗa bayana da jikin garu ina sauke numfashi, na ɗan sami nutsuwa na sake komawa na cika cikina da ruwa na ƙasa miƙewa na dawo ƙasa na zauna...


YARIMA maheer tun da ya tashi yau sai faman hidima yakeyiwa sarki Ahmadu ya aekesa wani kauye nan kusa da bakin gari dan ya binciko masa mai ke faruwa a garin SBD yawan korafe² da akeyi yana dawowa ya wuce kurkuku ya sallami waɗansu daga cikin su saboda lokacin fitansu yayi ya dawo da baya zuwa inda wannan matar take tananan kamar yadda ta saba ya kalleta yace

"Da alamu akwai magana a tare da ke ki sanar min ni kuma idan maganar me ma'ana ce kuma zata amfaneni nayi miki alkawarin zan fidda ke daga nan kuma zan baki rayuwa mai daɗi"

Matar ta kallesa tace "dani aka kafa wannan masarautar ta mahaifinka tun bayan rasuwar kakan ka Sarki Ma'aruf na jima a wannan masarautar tun kan a a haifeka na san abubuwa da dama amman kamin na faɗa maka ka tambayi Hajjiya Diddi zata faɗa maka komai" daga haka bata sake magana ba ta juya masa baya.

Yayi shuru na wasu lokuta sannan ya juya ya fito yayi ɗakin sa cike da tunani yarinyar ta faɗo masa a kai ya mik'e cikin sauri yayi waje da kansa ya ɗau key mota ya fice ya dinga tsula gudu har ya iso gate man ya buɗe masa ya shigo yana parking yayi sauri ya shigo ɗakin sai yaga babu yarinyar ya ji motsinta a toilet sannan ƙofan toilet ɗin a ɓude yayi sauri ya leka ciki ganinta yayi a durkushe sai kwarara amai take kamar zata a mayar da kayan cikin ta yayi saurin zama kusa da ita ya tallafo fuskar ta yana "I'm really sorry kamar zai yi kuka ya miƙar da ita ya ɗauke ta ya fito da ita palour ya kwantar da ita ya haɗa mata tea mai kauri ya mika mata cup din tea yace 

"Ki daure kisha koda kaɗan ne kinji"

Deejee na galabaita ba bakin magana kai kawai na gyaɗa masa alamun bana so cikin tausayawa yace

"Kiyi hakuri kinji kisha zan maida ke gida ba dai gida kikeson zuwa ba?"

Na gyaɗa masa kai da sauri alamun eh, 

"Tho kisha indai baki sha ba bazan kaiki ba"

"A hankali nace bani da karfi ba zan iya sha ba"

Ya ɗauki tea spoun ya fara bani a baki ina sha na ɗan sha da ɗan dama sannan nace "ya isa"

Cikin tausayawa yace "kiyi hakuri kinji ba a so na hakan ya faru ba aeki ne ya rikeni kinji!"

Na murkuɗa baki nace "daman so kake ka kasheni shiyasa kai zaman ka Allah zai saka min"

Ya sauke numfashi "haba ƴan mata wallahi ba da gangan nayi haka ba kinji kuma hakan ba zai sake faruwa ba"

Tho ka maidani wajen ƴan'uwan na mana me yasa ka ajiyeni anan ko dai kai ɗan yankan kai ne?"

Yayi murmushin da ya bayyanar kyaunsa sannan yace " Nupe ni ba ɗan yankan kai bane kawai dai inabso na nuna miki kuskurenki ne"

Tho me na aikata maka da sai na gane kurena?"

"Uhm ki kwanta kiyi bacci zamu yi magana zuwa anjima" ya mike ya sake daukata ya mai dani ɗaki jikina duk ba karfi bazan iya sayuwa ba balle kuma har akai ga tafiya, ya kwantar dani akan bed ya saka key a kofa yayi ficewarsa.


Nayi bacci har ya isheni na tashi a lokacin da na farka ganin food flask na abinci nayi an jerasu kala² da tea flask sai kuma swan water toilet na faɗa na watsa ruwa na fito na saka ɗaya daga cikin kayakin da ya kawo min doguwar riga ce gaban rigar dutse na ne masu kyau da sheki rigar ta fito min da shepe ɗina na zauna na buɗe kulolin abinci na fara zubawa na soma ci ina santi sai da na cika cikina sannan na rufe na hakura magani na gani daga gefe na dauka nasha ba tare da nasan ka'idansa ba nasha na haɗa da na mura ma na sha aeko ji na naye sama² bana hayyacina.

Turo kofar yayi ya shigo tsayawa yayi yana kare mata kallon "wow! yace a ransa a hankali ya tako zuwa inda take yace 

"Ƴan mata kinyi kyau"

Ina kallonsa uku² nace ɗan samari kaima kasha kyau wato dai wayo zakamin ka cuceni tho ƙaryanka na fika wayo"

"Lfynki kuwa ya na ganki a wannan yanayin?"

"Rass nake na fika lfy ma fita nake son yi na sha iska ka wani tsare ni a ɗaki"

Ya kalleni yace "tho biyoni mu fice"

Nabi bayansa har zuwa inda yake shan iska ina zuwa nayi sauri nayi bakin swimpol zan faɗa yayi saurin dakatar dani da cewa

"Ke ƴan mata meye  haka ? kina faɗawa zaki mutu"

Su Deeje anyi over dosed tayi taga ragar football ta ɗauka ta fara wulli dashi yarima me zai yi banda dariya Deeje tayi baya ta buga ƙwallon ƙafa sai ga Deeje a ƙasa warwas ta gara kanta da jikin ƙarfe a take ta dafe wajen tana ushhh da zafi, yarima maheer yayi sauri isowa yace

"Kibi a hankali zaki ji ciwo"

Na kallesa nace ae na iya ruwa a KAUYEN KUKAWA ma idan mun je rafi wanka na nake yi.

Ya kalkeni kamar yana son tuno wani abu a hankali ya furta *KAUYEN KUKAWA* 

Ya ɗan bar zancen yace "tho nan da kike gani ba rafi bane kina faɗawa sai lahira"

LAHIRA! Na faɗa ina kallonsa kana nufin zan mutu kenan.

"Eh haka nake nufi"

Tab bakinka ya tsari guntun kashi Gwaggo tace ba zan mutu ba sai naga a halina.

"Baki da ahaline?" Ya jeho min da tambaya.

Tab ina dashi amman..... Gaurd nasa ya iso wajen yana 

"Sakon ya iso"

"Ka ajiye min a palour" ya faɗa ba tare da ya kallesa ba sai gaurd ɗin yayi wucewar sa.

Niko Deeje na hango bishiyar mongoro da gwanda da ayaba na miƙe nayi wajen anyi masa sakani da net da inda ake buga ƙwallon ƙafa sannan akwai ƴar karamar kofar shiga na tura na shige na fara ƙoƙarin hawa kan bishiyar mongoro yayi sauri ya iso wajen yana "ke ƴan mata me haka kada ki kuskura ki hau dan kina faɗowa ba iya ɗagaki zanyi ba".

Na kallesa nace "wa ya faɗamaka zan faɗo? nida nake hawar bishiyar tsamiya ma data Kuka kuma na sauko lfy lau ko gurji babu.

"Tho ni dai nace ba zaki hau ba bari a tsinko miki" ya  dau wayarsa ya kira ɗaya daga cikin gaurd nasa ya iso cikin sauri ya bashi umurnin ya tsinko min sai mamaki yake ace Boss mayen mata ne ya sami santalelitar budurwa amman ya kasa yi mata komi sai ma wainasa da takeyi ya tsinko duk abinda ya umurce sa ya kawo gabansa ya diri yace 

"gashi boss"

"Have you get mad da zaka miƙomin abu ko wankewa baka yi ba oya take them"

Jiki na rawa ya kwashe ya kai ya wanke ya kawo ya zubeminsu a gabana da ƴar karamar wuka a kan trey din nace

"Ah wai kowa dana gaba dashi wannan umurni haka kai kana zaune sai dai ka saka ayi maka abi sai kace sarki! Ni wai ina sarkin ne dama ashe ba a MASARAUTA kake ba tsorata mutane kake yi suna tunanin kai jinin sarauta ne"

Yayi murmushi ya ɗan kaɗa kansa ya cigaba da danne dannen wayarsa a ransa yace zanyi maganin wannan bakin tsiwar.

Ina kammalawa na miƙe da niyar tafiya amman na kasa saboda maganin yaci ƙarfina idanuwa na rufewa suke sabar bacci ina kamin na makare najini a kasa dimm daganan bansan inda nake ba......



 *QUARTERS NA G B S*


Duk inda aka san za a sami Deeje anje amman shuru babu labari gashi kwanaki sai wucewa suke Baba principal ma abin yafi karfinsa zuwa yanzu ya zubawa sarautar Allah ido dan ganin yadda abin zai kasance tare da yin Addu'ah har saukan Alqur'ani ya bada ayi ko Allah zaisa a dace yauma yana zaune a palour nsa yayi tagumi tunanin ɗiyar mutane taɓata a hannun kuma ma babban tashin hankalin ma baisan ta yadda zai sanar da iyayenta ba tho ma maizaice musu baiga diyarsu ba koko taɓata zaice......

Hajjiya Iklima ce ta shigo tare da yin sallama ta zauna a kusa dashi ya amsa batare da yacire taguminsa ba tace

"Alhaji wannan tagumin da kake yi ba shine mafita ba kuma yin hakan sake saka kanka zakayi a damuwa"

Ya sauke nauyayyen ajiyar zuciya sannan yace

"Ya kike so nayi inba tagumi ba anan Gwaggo nta ba yadda batai ba dan ta tafi da Khadijah amman fir naki nace a barta anan gashi kuma abinda yaje ya dawo ba dole nashiga danuwa ba"

Cikin tausayawa tace "ae ba laifinka bane sannan babu wanda yasan gobe sai Allah haka Allah ya ƙaddara kawai mu kira musanar dasu dazafi zaginsa"

Yayi ajiyar zuciya yace "ina Number da za asami ƴan uwan ta dashi?"

"Akwai a wajen Shareefa bara na karɓo" ta mik'e tayi ciki dan ansowa.

SHAREEFA na ɗaki ita da maryam suna jimamin ɓatan Deejee mahaifinyar ta tashigo tace

"Yauwa ɗan bani Number da deejee take kiran ƴan uwan ta dashi"

Shareefa ta baiwa mahaifinyar ta Number jiki a sanyaye sannan bata iya cin abinci dan haka da ta miƙe sai kiri shiyasa take kwance a ɗaki.

Hajjiya Iklima ta kawo Number ta baiwa Baba principal yasaka bugu ɗaya zuwa biyu aka ɗauka daga KAUYEN KUKAWA.




Comments and share fisabilillah