Ƴar gwoggo

Page 8

by @barista

ƳAR GWOGGO 

***
Book 1 
Page 8


*_KAUYEN KUKAWA_*

Auwal ne zaune a shagonsa jama'a sun yi masa yawa da ya sallami wasu ba za a ɗauki lokaci ba sai wasu su zo haka yake wuni a shago tun safe har 10:00pm kamin ya tashi a shago, yana saka da aiki yaji kiran waya ya shigo ya ɗauka ya kara a kunnen sa tare da yin sallama, aka amsa ta ɗayan bangaren sannan akace

"Baba principal ne na G B S kuma uban ɗakin Deeje"

Auwal dajin haka ya gane shi yace

"Ayya ranka shi daɗe barka dai ya kuke ya Deeje?"

Baba principal yayi ajiyar zuciya me ƙarfi yace

"Alhamdulillah! lafiya ne amman ba lau ba"

"Subhanallah me yake faruwa ne?"

"Da farko naso ɓoyewa sai zuwa wani lokaci amman sai naga yin hakan bawani alfanu yau kusan kwanaki huɗu kenen mun nemi Deeje mun rasa ba inda bamu duba ba muna cikin tashin hankali....

"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun" Auwal ya faɗa cikin tashin hankali garin yaya hakan ta faru?"

"Ta fita aike ne daga nan bamu sake ganinta ba mun yi cigiya har mun gaji amman babu labarinta.

"Ya hayyu ya qayyum gaskiya wannan abin bana ɓoyewa bane zan kira zuwa anjima zanje na sami Gwaggo tukunnah"

Sukai sallama.

Tagumi Auwal yayi idanuwansa sunyi jajir  saboda tashin hankali ya bayyana a fuskansa sai Addu'ah yake Allah yasa Deeje ta faɗa a hannun nagari kada a cutar da ita marainiyar Allah waye kuma yake son ɗaukan alhakin ta Allah yasa tana raye....! Shi kaɗai yake zancen zuci ya mik'e ya rufe shagonsa ya fito dan ba zai iya zaman shago ba ya wuce wajen tuyar Gwaggo.


********
Ana tabka sanyi Gwaggo na tuyar ƙosai ta kusa kammalawa dan da zaran ta fara tuya ake ribibin tsaya saboda ba ko da yaushe take fitowa ba ga kuma ƙosanta daɗi ne dashi duk yawan sa karewa yake ɗaya daga cikin masu sayan ƙosai yace

"Gaskiya Gwaggo kina shiga hakkinmu kin san yadda muke son wannan ƙosan amman baki fitowa sai lokaci zuwa lokaci"

Gwaggo tace "lah tuyar ce yanzu sai a hankali ga jikin tsufa sannan ya haɗu da yawan jinya sannan kuma ba zan iya juriyar zafin wuta ba ai kuma kwa tausayamin"

"Gaskiyar ki Gwaggo amman muna jin daɗin ƙosan duk ranan da baki fito ba bamu jin daɗi"

Salisu ne ya iso yana "yau Gwaggo ta fito ne? Yau zanci ƙosai me yawa"

GWOGGO bata tanka masa ba dan ita bata sakar masa fuska tun ranan da yake son rabata da jikarta ya sanar da ita ba jinin ta bace kawai Gwaggo tace

"Eh Salisu na fito"

"Tho azubanin ta ɗari 500 na tafi da ita shago nayi taci ina shan ruwa"

GWOGGO ta sallami waɗanda suka rigasa sannan ta bashi yace

"Godiya nake Gwaggo ya labarin Deeje yaushe zata dawo?"

"Ta nanan lfynta kalau kwanannan zata dawo"

"Ah barka muna jiran zuwan ta"

Ita dai gwoggo bata wani sake yin magana ba taci gaba da tuyar ta yau duk jikinta a sanyaye jiya mafarki tai taga Deeje na kuka tana kiran sunan GWOGGO.

**********
Auwal ne ya iso wajen cikin sauri ya tadda Gwaggo na shirin tashi yace

"Gwoggo har kin kammala sannu da gajiya"

Gwoggo ta kalli Auwal tace "na saida shi duka saura tafiya"

Ya taimaka mata wajen tattara wa ya ɗauki masu nawin sukayi gida tace

"Kai Auwal na gaji sosai yau ba abinda nake buƙata irin na kwanta na huta wa raina"

Jikin Auwal yayi sanyi ya rasa ta yadda zai sanar da ita.....

Tace "Auwal jiya nai mafarkin Deeje tana kuka tana kiran sunana ɗan ƙira min ita mu gaisa"

Yayi ajiyar zuciya yace "ai wayarta bata shiga kin ga gobe zani birni sai mu tafi tare kije ki ganta"

"Amman da naji daɗi na kwan biyu banje birni ba kaga sai nayi ziyara"

Auwal ya sauke numfashi yace "ki shirya gobe da safe sai mu wuce" daga nan ya fito yayi gidansa dan ko shagonsa ma ya kasa zuwa.

Auwal da kyar ya iso gida sabar tashin hankali baisan inda kafafunsa suke takawa ba, ya turo kofa ya shigo sallamar ma ya kasa ɗansa yayi masa oyoyo amman ina wucesa yayi ya zauna a kan taburman da ke shimfiɗe a verender ya jin gina da jikin garu ya rumtse idanuwan sa......

Matarsa ta iso inda yake ta zauna tana masa "barka da zuwa"

Ya amsa tare da buɗe idon sa ya kalleta ta sake cewa 

"Lafiya me gida?"

"Hmm ba lfy ba gobe zamu tafi birni ni da Gwoggo Deeje ce ta ɓata ba a san inda take ba.

"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun Allah yasa a ganta"

"Ameen"

***************

 _*BIRNI*  __ 

 _REST HOUSE__ 

Farkawa nayi na ganni kwance a wani ɗaki ba ɗakin da nake ba a hankali na bi ɗakin da kallo ɗakin ya haɗu iya haɗuwa set ne aɗakin na makeken gado da mirror da side bed, idanuwa na suka sauƙa kan drip ɗin da ke makale a hannuna kuma dab yake da karewa....

Murɗo ƙofa yayi ya shigo ya ɗan jima a haka sannan ya tako a hankali zuwa inda take tsayawa yayi yana kare mata kallo kanta babu ɗan kwali ya barsa a inda ta faɗi saboda kiɗimewa ba ƙaramin tashin hankali ya shige ba a lokacin da ya ganta kwance sumammiya gashin kanta ya ɗan zubo ta kan fuskarta hannunsa yasa ya maidasa baya kuramata ido yayi yana kallonta sai yaga itama shi take kallo ya furta cikin yanayi mai ban tausayi

"I'm really sorry" ya ɗan karkata kansa ya zauna a kan bedside.

Kallonsa nayi ina son tuna mai ya faru dani har aka sakamin drip nace

Me ya sameni?

"Magungunan da kika sha ba tare da kin bi ka'idan shansu ba shine yayi miki illah ta hanyar fin karfin jikinki shiyasa kika suma"

Na lumshe idanuwana na buɗe ba tare da nace komi ba, ya miƙe ya cire drip din ya ajiye akan bedside ya ɗan sunkuyo ya ɗan sassauta murya ya ce

"Me kike buƙata yanzu?"

Babu, na faɗa ba tare da na kallesa ba.

"Haka zaki zauna ba tare da kinci abinci ba tashi ko tea kisha"

"Nace maka bani son komi ka kyaleni.... Na faɗa cikin ɗaga murya.

Ya miƙe tsaye yana kallona ya wuce bakin ƙofa ya murɗa ya buɗe ya fice ya dawo kan rest chair ya kwanta ya sauke numfashi sannan ya lumshe idanuwansa yana ayyana wasu abubuwa a zuciyarsa yana mamaki yadda wannan yarinyar take wainasa kuma take abinda taga dama ba tare da yayi mata magana ba sannan baya iya taɓa ko da jikinta ne balle ya kaiga ya sami nutsuwa da ita sannan da ya kalleta yake jin tsananin sha'awar ta amman baya iya kai hannunsa jikinta but he will try it again maybe ya sami yadda yakeso.

****************

Yana fita bacci ya ɗauke ni sai da nayi awa biyu ina bacci da alamun harzuwa lokacin dana kwanta maganin bai sakeni ba sai da na farka na ɗanji daidai, na miƙe a hankali na buɗe kofan toilet na shige na watsa ruwa sannan na fito ina tafiya ahankali zuwa inda zan shafa mai saboda sanyin ɗakin jikina zai bushe yayi fari kamar banyi wanka ba ganinsa nayi a tsaye yana kallona dar... Da idanuwansa ko kiftawa ba yayi nayi baya da sauri na tsorata banyi tunanin yana gidan ba shiyasa na fito dagani sai towel ɗin da na gani a toilet kayan jikina kuma na saka a bucket din cikin toilet ɗin na zuba ruwa da omo na fito na ɗau bedsheet na rufe jikina na ɗauki kayana. Ganin sa da nayi yasa naji tsinkewar zuciya a hankali ya tako zuwa inda nake still idanuwansa na kaina har ya iso dab dani na rufe ido jin shuru da yayi ba tare da yayi magana ba nace ko ya koma ne na buɗe su a hankali ganinsa nayi dab dani yana sauke numfashi ya sake matsowa ya rike hannuna ina jin bugun zuciyar sa da kuma kamshin turaren sa, nayi motsi kauce kaina amman na kasa saboda riƙon da yayi min na buɗe baki na ce 

Me haka YARIMA....?

Ya fuzgar da iska a hankali yace

"Dama kin sanni a matsayin YARIMA shine ki ka yi kamar baki sanni ba meye ma jiya kika ce ina MASARAUTAR take kuma ina sarki yake?"

"Ni bance komai ba rabu dani na wuce na saka kaya"

Yayi murmushi me nuna alamun yana cikin yanayi yace

"Au ƙarya nayi miki kenan" ya daura hannunsa akan kafaɗa ta ya maida gashin kaina baya nayi saurin bige hannun nace 

Me kuma haka yareema ka cikani na hankaɗesa amman ko gizau baiyi ba jinsa nayi kamar dutse ko motsi baiyi ba, na ɗago na kallesa da sauri naga idanuwansa sun sauya kammanni sun ƙara rinewa sunyi ja dasu na sake cewa 

Ha'a.... mai haka?

"Yareema ya furta" yana kare mata kallon dogon wuyanta da kuma kyakkyawar fuskarta da fararen idanuwanta masu ɗaukan hankali a hankali ya daura labɓan sa a kan ɗan ƙaramin bakinta ya rike hannayenta duka biyu ya haɗa ta da jikin garu....... Daga bisani yayi cilli da ita kan bed.

Kwalla kara deejee tayi me ƙarfi sanadiyyar bakon al'amarin da taji.


Faɗuwar da tayi akan bed ta buge ta hakarkarinta cikin sauri da raɗaɗi ta mik'e zata tashi ta sake kifewa ta ciki mararta ta haɗu da jikin bed ɗin ta bugu sosai tasa ƙara me ƙarfi sabar azaba da raɗadin da taji........

YARIMA maheer yayi nesa baya jin kira bai ma ankara balle ya san halin da take ciki ya juyo da Deeje suna fuskantar juna bayyi wata² ba ya haɗe bakinshi da nata ya fara kissing Deeje cikin ƙarfi hannunsa ɗaya ya tamke gashin kanta ɗayan kuma dashi yake sarrafata......

Deejee sabar takwaici da tashin hankali da yanayin da take ciki yasa ta kasa komai tabarwa sarautar Allah hannun ta ɗaya nakan mararta ɗayan hannun kuma ta daurashi kan goshinta da ke tsaramata saboda rashin wadataccen iska ya rufe mata baki da nasa gashi ya sake mata dukkannin ƙarfin sa....

YARIMA maheer kam abin sai ƙaruwa yake duk da ba a hayyacinsa yake ba amman jinsa yake kamar ya faɗa a cikin auduga jikinsa na ɓari ya dinga luguigwaita iya son ransa sai da ya sami abin da yake so sannan yayi gefe ya kwanta yana sauke numfashi anan bacci ya ɗauke sa.

Deejee ta miƙe da kyar ta zauna ganin jini tayi yabi cibiyoyin ta ya ɓata bed sheets ta sauƙo tayi toilet ta wanke sannan ta fito ta tadda yananan  yadda ta barsa a hankali ta murɗa kofa ta fito tayi ɗakin da kayanta yake, ta shige da niyyar sakawa sai kuma jinin ya sake karyo mata ganin jinin yasa Deeje ƙwalla ƙara tana 

Na shiga uku na lalace wayyo Allah na GWOGGO ki taimakeni yau kwana na ya kare na faɗa a hannun mugu.... Ta zube ƙasa tare da dafe marar ta dake mata zugi da raɗadi mai makon taji zafin a gabanta amman radaɗin iya mararta ce...

YARIMA maheer yayi bacci kamar na 30mints ya farka juyowa yayi a hankali yana karewa ɗakin kallo ya fara tuna abubuwan da suka faru da shi ɗazu da sauri ya juya ɓangaren sa sai yaga babu yarinyar ya tashi zaune jinin da yagani yasa ya tsorata ya dafe kansa cikin tashin hankali ya sauko ya saka gajeren wandonsa ya fito yayi palour bata nan yayi ɗakin da take ganinta yayi kwance a ƙasa tana numfashi sama² yayi saurin ƙarasawa ya ɗago da ita ganin jinin yayi malale a jikinta yasa ya furta

"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun"

Cicciɓota yayi yayi waje da ita ba tare da yasan halin da suke ciki ba ita daga ita sai towel shi kuma da gajeren wando yayi wajen mota da gudu.... Luka na ganinsa yayo inda suke yana

"Boss relax, let me help you"

Duk da baya cikin hayyacinsa yace 

"Don't touch her"

Yayi baya yana kollonsa yace 

"You have to put your jallabiyar  Boss don't go with the boxer and she......

Kallon da YARIMA yayi masa ya sashi rufe baki yayi gefe shi kuma yarima yayi ciki ya saka tasa jallabiyar sannan ya wuce ɗakinta ya ɗauko mata doguwar riga ya fito yasaka mata bayan ya goge jinin dake jikinta ya ce Luka ya jasu zuwa asibiti suna isowa ya kira abokinsa Dr KAMAL ya shaida masa gashi a harabar asibiti Dr KAMAL ya fito ganin halin da yaga yarinyar dake tare da YARIMA yasa aka kaita emergency room cikin gaggawa ya bata taimakon gaggawa daga bisani ya fito yayi office nasa inda yabar Yarima maheer yana ganinsa ya miƙe yayi inda yake yana tambayarsa cikin tashin hankali

"Ya take ta tashi?"

Dr KAMAL ya dafa kafaɗar Abokinsa tare da zaunar dashi yace

"Cool down abokina ta sami sauki amman garin yaya hakan ta faru?"

YARIMA maheer yayi ajiyar zuciya sannan yace

"Bana cikin hayyacina nayi mata fyaɗe...."

Dr KAMAL yayi ajiyar zuciya yace ba fyaɗe kayi mata ba saboda nasa Dr A'isha ta binciko min kuma ta tabbatar min da babu abinda yasami ta private part nata but ta sami buguwa a mararta hakan yayi daidai da zuwan period nata shine yake zubowa dayawa, zan haɗa mata magunguna nan da zatayi anfani dasu da izinin Allah zata sami sauki"

YARIMA maheer yayi ajiyar zuciya ya dafe kansa yana hamdala dan yasan bai aekata mata ba daman yasan bazai wuce iyakarsa ba ganin jinin ne yasa ya tsorata.

Dr KAMAL yace "YARIMA haryanzu kana fama da wannan larurar ce nayi tunani zuwa yanzu ka warke"

YARIMA ya sosa keyarsa yace "Abokina da dai sauki ba kaman da ba nima abin na damuna" ya faɗa cikin damuwa.

"Tho ita wannan a ina kasameta?"

Ya ɗan sosa keyarsa yace "yau kusan sati tana gidana a killace...."

Dr KAMAL yace "wannan ba ɗabi'a ce mai kyau ba, ada muda muke aekata wa kai kake hanamu amman yanzu kai da kanka kakeyi gaskiya ka dawo kan hanya"

YARIMA maheer yayi ajiyar zuciya yace "nima babu yadda na iya ne amman zanyi kokari naga na daina"

"Yauwa ko kaifah" ya dinga bashi shawar wari daga bisani ya fita yayi wajen uzurin sa yabar Yarima maheer zaune a office.


 *DEEJEE*

Na ɓude idanuwa na a hankali na ganni kwance a kan gadon asibiti nabi ɗakin da kallo hannuna daure da drip na turo kofa yayi ya shigo sanye yake da kayansa na likita fuskansa ɗauke da farin glass ganin na farka yasa ya ƙaraso yana kallona a hankali yace

"Sannu ya kike jin jikinki?"

Idanuwa na lumshe ba tare da na bashi amsa ba yaci gaba da abinda yakeyi ya sauyamin drip sannan yace

"Kada ki damu komai lfy kawai ƙarfin jikinne babu ki hutu zuwa anjima zaki sami ƙarfin jiki"

Na buɗe idanuwana na kallesa ba tare da nayi masa magana ba har ya fice bacci ya sake awun gaba dani.

*************

Sai da na dau lokaci ina bacci sannan na farka ganinsa nayi a zaune ya kuramin idanuwa cikin tsoro na tashi ya riƙe ni yana

"Zakiji ciwo kibi a hankali"

Na bege hannunsa tare da matsawa gefe na zauna.

Dr KAMAL ya shigo yana ganin na sami sauki har na tashi na zauna ya ƙaraso yana "yauwa ta farka ko?"

YARIMA maheer yace 'eh ta tashi"

"Tho madallah"

Ya sake dubani yace "da sauki bari naje na haɗo miki magunguna na kawo" ya fice.

YARIMA maheer ya tashi jiki a sanyaye ya dawo kusa dani ya zauna cikin cool voice yace

"Kiyi hakuri kinji bansan........

Dakatar dashi nayi ta hanyar saukowa daga kan gado na nunasa da yatsa nace

"Kaiii! Kada ka sake matsowa kusani bana son ganin ka bana kaunar ka na tsane ka..... Na fashe da kuka naci gaba da cewa 

Ka cuceni ka ɓatamin rayuwa Allah ya.......

Kamin na karasa yayi sauri ya rufemin baki da hannunsa yace

"Ba abinda kike tunani bane ya faru wlh Ni...


Nayi baya na tufar da yawu nace tir... Kada ka sake taɓamin jiki da wannan hannun naka da zakace babu abinda kayi min tho shikuma fyaɗen da kayi min fah sai Allah ya.....

Nanma ya janyoni ya rufe min baki yace

"Ni ban aekata kuskure ba kuma ba abinda nayi miki period ne naki yazo daman ku mata ae kunayi"

"Hmm kaji rainin hankali kai kasan wani period ni bani da period Allah ya tsareni dashi ni ba ƴar iska bace"

Ya fuzgar da isaka yace "nima ba ɗan iska bane"

Kai kasani ni ka fice min daga nan.

Yayi ajiyar zuciya sannan yace "yanzu ki nutsu ki kwantar da hankalinki kisha magani saboda marar taki tayi kwari da kuma sauki in kinyi lfy sai muyi magana"

"Tab inna yarda wallahi baza yi rainon ciki ba kuma ba zan yi wankin ciki ba so kake na mutu ko tho Allah ya fika"

Lallai sai yanzu ya fahimci inda yarinyar ta dosa yace "ciki kuma me yakawo wannan zancen?

"Kai ka kawo shi ni dai ba wani wankin ciki"

Ya sassauta murya yace "tho shikenan na fahimce ki baza ayi wankin ciki ba amman ki daure kisha magungunan ki zuwa gobe maga abinda Allah zaiyi.

"Ni dai ka kaini wajen ƴan'uwan na shine kawai lafiya ta"

Ya kalleta yace "shikenan zan kai ki bara ki sami sauki a wacce unguwa kuke?"

A unguwar Q........

Shigowan Dr KAMAL ne yasa ta yin shuru yace "lafiya na ganku tsaye?"

Yarima maheer ya kallesa yace "lafiya lau aboki"

Nace "ah faɗi gaskiya kawai ba wani lafiya cewa yayi amin wankin ciki na sami sauki a marata kuma tayi kwari!.

Dr KAMAL ya kallesa da mamaki ya mai maita "wankin ciki!"

"Eh fah haka yake nufi ni kuma ban amince ba kuma bazan taɓa amin cewa ba saboda mutuwa ake yi"

YARIMA maheer ya kalli Dr KAMAL cikin nutsuwa ya sauya harshe zuwa turanci yayi masa bayani"

Dr KAMAL yace ya fahimce sa kada ya damu zata sami sauki.

Na kallesu nace "kanku ake ji ba turanci ba ko Chainanci ma in kunga dama kuyi amman ni baza amin wankin ciki ba.

Dr KAMAL cikin nutsuwa yace "shikenan baza ayi ba ki kwanta drip kawai zan saka miki saura guda ɗaya yana karewa sai in sallameki"

"Yauwa yanzu naji batu" na haura na kwanta ya ɗaura min drip ɗin ya saka wasu allurai zuwa wani lokaci bacci yayi awun gaba dani....

**************

 ƘAUYEN KUKAWA

Gari na wayewa Auwal yayi sallama da iyalen sa ya biyo ta gidan Gwaggo dan tahowa ya tadda ta tana ta shiryawa ta haɗawa jikarta tsaraba kala² biscuits, chuwen gum, aduwa, magarya,tsamiya etc.

Auwal ya kalli Gwaggo cikin tausayawa yace

"Gwoggo waɗannan kayayykin mawa zaki kaiwa?" 

"Wannan leda ta uwar ɗakin Deeje ce kayan miyar garkajiya ce  a ciki wannan ko na Deeje ne kasanta da ƙwalama tana gani zata ji daɗi"

Jikin Auwal yayi sanyi bai san yadda abin zai wakana ba idan akace deejee taɓata ko ya za ayi, ya mike yace 

"Kawo na tayaki kwashe kayan mu tafi tasha kar mu makara mota ta cika"

Ta miƙe itama suka fito ta rufe kofar ta suka hau a daidai ta suka dawo tasha, suna isowa suka sami mota suka shige sai birni....!


Baba principal zaune da baƙinsa a palour suna hira kamar yadda suka saba zuwa kuma anyi musu hidima kamar a ko da yaushe duk da yana tare da baki amman hankalinsa baya tare dasu yana tunanin ko yanzu yarinyar a wani irin hali take ciki. Shigowan Shareefa ne ya dawo daga tunanin da yake yi ta ajiye musu tare da gaidasu suka amsa tafito tai ɗakinsu ta kwanta tana tunani da yanzu deejee na nan da a tare zasu yi aekin nan tai ajiyar zuciya tare da yin Addu'ah Allah yakare Deeje a duk inda take.....

Hajjiya Iklima ce ta shigo tana "ke Shareefa ba zaki sa abu a bakinki bane da kika shigo kika kwanta maza ki tashi kije ki karya dubi kiga 11:30am fah  yanzu zaki ji 12:00pm ya buga kuma kin san kina fama da ulcer"

Shareefa ta miƙe ta biyo bayan Hajjiya Iklima suka fito palour sukayi break fast sun kammala kenan wayar hannun Shareefa ta fara Ringing ta dauka saboda ganin number da Deeje take kiran ƴan uwan ta dashi tayi sallama aka amsa tare da cewa

"Ni ne Auwal yayan Deeje mun shigo gari muna daidai bakin tasha munason hawan ɗan sahu wacce unguwa zamuce akaimu?"

Shareefa ta kalli Hajjiya Iklima tace ɗan uwan Deeje yake magana wai sun shigo gari suna sun nayi musu kwatancen nan gidan"

Hajjiya Iklima tace "bani wayar" ta amshi wayar ta fara yiwa Auwal kwatancen gidan sai da ya gane sannan ya kashe wayar, Hajjiya Iklima tacewa Shareefa ta kira Abbanta.

Shareefa na shiga ta sanar dashi aeko biyota yayi zuwa palo yasami Hajjiya ta faɗa masa mutanen deejee na hanyar zuwa, yace

 "sai sun iso" suka yi zaman jiransu.

Ba wani ɗaukan lokaci suka iso gidan, ya sake kiran Shareefa ta fito ta shigo dasu GWOGGO, take tambayar ina Deeje ya bata zo ɗaukanta ba akace tana wanka sai da suka ci suka sha ruwa sannan Baba principal yake sanar da GWOGGO ga abinda ya faru da Deeje aiko sun ga tashin hankali a wajen Gwaggo dan harda Auwal bata bari ba cewa ma tayi ya sani shine ya ɓoye mata bakinsu ɗaya sayarda Deeje sukayi tun ana rarrashin GWOGGO abin yaso yazama faɗa da ƙyar Auwal ya shawo kanta tayi sai kuka take wai Deeje ta mutu ta barta, ta kalli Baba principal tace

"Anyi mata sadaka ne?"

Ya sudda kai ƙasa a sanyaye yace "ba muyi ba saboda har yanzu bamu tabbar da mutuwar ta ba ɓatawa tayi kuma muna sa ran zata dawo....

"Kai dakata bani son zancen banza yaushe zata dawo yau kusan sati kace zata dawo kawai dai ku mutan birni baku damu da mutuwa ba sai kuce babu sadaka tho wallahi sai an yiwa Deeje sadaka dan ruhinta ya sami  salama"

Auwal yace "shikenan za ayi gwoggo zuwa gobe insha Allahu"

"Tho yanzu naji batu" ta sake fashewa da kuka tana "wayyo Deeje ta bansu kika rigani mutuwa ba naso ki burne ni naso kiyi karatun ki zama mai kuɗi....

Auwal yace "ya isa GWAGGO kiyi hakuri" ya dunga rarrashin ta har zuwa dare amman Gwoggo da ta tuno da Deeje sai kuka haka dai suka kwana.

     *WASHEGARI* 

Tunda ta tashi da safe ta dinga ɗaga musu hankali ayi sadaka kuma ƙoshashen rago za a sayo haka dai Baba principal da Auwal suka shiga cikin gari kasuwan dabbobi suka sayo aka yanka a dafa abinci akayi sada ta mutuwar Deeje.

 _Bayan kwana uku_


Satin Deeje ɗaya da kwanaki da ɓatanta gidan shuru sai zuwa gaisuwan ɓata da kuma mutuwa ake yi GWOGGO cewa tayi nan da kwana biyu zasu koma cen KUKAWA tun da babu Deeje amman zazzaɓi ya kwantar da ita Hajjiya Iklima tashiga jinyar ta abu kamar wasa har asibiti.....


YARIMA maheer sai kaiwa da komowa yake yi a bakin ɗakin da aka kwantar da Deeje yana son shiga amman ya kasa saboda Deeje cewa tayi ba ta son ganinsa haka dai ya turo ƙofa ya shigo tananan zaune tayi tagumi duk ta shiga damuwa gashi jini yaki tsayawa sai zuwa yake kamar bakon watan ta sai dai shi wannan dayawa yake zuba ko dai ta amince ayi mata wankin cikin ne. Shigowan sa yasa ta kalli bakin kofa tana ganinsa ta haɗe rai ya karaso yace

"Sannu ya jikin?"

Cewa tayi "ban sani ba" ta hararesa yace

"Allah baki hakuri zanje na dawo me kike bukata na taho miki dashi"

Nan ma tace "ba a sani ba"

Yayi murmushi aransa yace lallai wannan yarinyar a fili yace "Anyway zanje na dawo"

Tace kai kasani ya fice yayi MASARAUTA yana isowa ya wuce ɗakinsa ya watsa ruwa ya sauya kaya sannan yayi ɗakin Diddi tana jin motsin sa tace

"Kai zonan YARIMA! Yayi mamakin kiransa da tayi da yarima ba maheeru ba ya iso ya zauna yana  gani Diddi na sameki lfy?

"Yau kusan kwananka uku baka MASARAUTA a ina kake?"

Yayi ajiyar zuciya"ina Gidan hutawa ta ne Diddi wasu ayyuka nake yi"

"Maheeru karya bai dace da kaiba naji labarinka bige wata yarinya da mota har asibiti ka kai ta shin da gaske ne ya abin yake!"

Cike da mamaki yake kollon Diddi a ina ta ganshi dauke da yarinyar matar da ko iya fita batayi shine har taji wannan lbrin yayi ajiyar zuciya sannan yace "hakane ban sanar dake bane dan bani son hankalinki ya tashi amman da sauki gobe ma za a sallameta" 

"Tho ka dai kula tukin ganganci bashi da amfani amman dai kai bakaji ciwo ba ko?"

"A'a Diddi banji ba"

Nan suka shiga yin hira sai dan magrib YARIMA ya fita daga masarauta zuwa asibiti yayi siyayya ya iso ya shiga ɗakin amman sai yaga babu kowa a cikin sa a tunanin sa tana toilet yayi zaman jira har na tsawon 30 minti shuru ya tashi ya tura kofan toilet din da mamakinsa a buɗe ya kusa kai babu yarinyar ya fito yayi office na Dr KAMAL yana shiga ya tadda sa akan sallaya ya idar da sallah yace

"Abokina shin ka sallami yarinyar ne?"

Cike da mamaki Dr KAMAL ke kallon yarima "Ban fahimce ka ba wacce yarinyar kake magana"

"Yarinyar nan dai wacce na kawo ta bata ɗakin ta"

Dr KAMAL ya mik'e "Kamar ya ɗazu fa na dubata naga tana bacci amman kace bata nan ko dai ba ɗakin ka shige ba?"

"Daga ɗakin nake nace maka bata ciki"

A tare suka fito sukayi ɗakin aiko bata ciki aka duba duk ɗakunan nan ma bata nan yada yasa gaurd nasa suke fita nemanta har sun fice daga layin unguwar amman basu ganta ba ya dawo suka sanar dashi.

YARIMA maheer ya riƙe kansa yana juyashi ya furta "Ta gudu"

Jiki a sanyaye ya kwashi abinda ya sayo yayi kyautarsa ya dawo REST HOUSE ya wuce ɗakin yarinyar ya kurawa ɗakin kollo gani yake gatanan zaune a ɗakin sai ya duso inda take sai ya rasata ya tattaro kayakin ta ya haɗa waje ɗaya ya ajiye sannan ya wuce ɗakinsa nan ma ganin tayake tana mai gizau a ido ya iso bakin bed ɗin har jinin jikin bedsheet ɗin ya bushe ya naɗe da kansa ya kai toilet ya sa a washing machine ya wanke tare da rigarta da tajika a ruwa ta bari ya fito ya zauna yayi tagumi yana tunanin ko wane irin hali take a yanzu Allah yasa ta isa gidansu lfy da tajira ta sami sauki da kansa ma zai kaita ya mike yayi ya fito ya tada mota yayi gida.


 *Deejee*

Ina kwance a ɗakin da nake jinya Dr KAMAL ya shigo ya dubani yace 

"Masha Allah jikin naki yayi sauki zuwa gobe da safe zan baki sallama"

Cikin jin daɗi da farin ciki nace

"Tho madallah Allah ya nuna mana, ina yarima ne?

"Ya fita amman zai dawo"

A raina nace Allah yasa kada ya dawo, Dr KAMAL na fita na tattare kayana na fito ina tafiya ahankali har na fito farfajiyar asibiti babu wanda ya ganni ina fitowa ana sallah kowa na masallaci liyin shuru ba abin hawa da kafa na fito nayi babban titi sai tafiya nake bansan inda zani ba dan bansan  unguwar ba gashi bani da kuɗi nayi dabara na hau dan sahu innaje gida baba principal ya biya, na tare ɗan sahu namai kwatance ya kaini G B S QUATES yace

"Da nisa fah Hajjiya zaki bada 1500"

Nace ba damuwa muje na hau muka wuce gida a lokacin 9:30pm.


Yanzu kam su Hajjiya Iklima sun gama cire rai da zuwan Deeje kuma sun amince mutuwa tayi suka ɗauki hakuri da dangana, Shareefa ma ta fara shirye shiryen tafiya makaranta dan cewa yayi tunda babu Deeje Daddy ya kama mata hostel haka ko akayi aka kama mata saura tafiya nan da zuwa jibi ma zata ta koma.

Jikin Gwaggo yayi sauki ta tada hankali ita gobe zata koma KUKAWA dan ta san zuwa yanzu babu Deeje babu amfanin zaman ta anan Baba principal yayi² da GWOGGO ta hakura ta sami sauƙi amman fir taƙi haka dai aka hakura, Gwoggo na shirin kwanciya bayan tasha magani ji tai ana buga ƙofan palour kan ta mik'e Shareefa ta fito ta buɗe kofar tana cewa Sani (amajirin Hajjiya Iklima) kai kam in ka tashi buga ƙofa sai kayi tayi kamar baza a bi... Ganin wacce ta gani ne yasa tayi baya a tsorace tace

"Fatalwa ce!



Comments and share fisabilillah