Page 10
by @barista
ƳAR GWOGGO
***
Book 1
Page 9
Deejee jin an ambaci sunan fatalwa a tunanin ta da gaske Shareefa fatalwar ta gani a tsaye a bayanta saboda dare yayi karfe 10:00pm chub a lokacin sai ko Deeje ta rugo a guje tana ƙoƙarin faɗawa jikin Shareefa da gaske ta sorata..
Ita ko Shareefa ganin Deeje ta nufota a guje kawai ta ayyana fatalwar ce kuma so take ta shige mata jiki aeko ta zabura a guje suka fara zagaye palour sai shiga suke sakanin kujeru Shareefa na ihu Deeje ma na biye da ita tana neman mafaka.
Jin ihun da Shareefa tayi kuma tace fatalwa yasa kowa ya taso daga mankwancin sa suka yi palour gani abin da ta ganine yasa su fidda idanuwa waje kamar haɗin baki suka ambaci sunan ta
"Deejee!"
Tsayawa nayi ina kallon su ina haki mamaki nake da naga Gwoggo da Ya Auwal a tsaye a gidan nan na maida kallona ga Baba principal da Hajjiya Iklima a hankali na furta..
GWOGGO..!
Sai alokacin Shareefa ta dawo hayyacinta ta kalle ni cikin sauri ta ƙaraso inda nake ta dafeni tace
"Khadijah! Tana mamaki ta cigaba da cewa "daman kina raye ina kika shiga cikin kwanakin cen munyi ta nemanki amman bamu ganki ba"
Na rasa ta inda zan fara nayi sauri na faɗa jikin Gwoggo na fashe da kuka ina "Gwaggo ashe zaki zo nemana nayi kewar ki sosai. Gwoggo da ta bushe a tsaye sai al'ajabi take wai shin Deeje take gani ko kuma dai idanuwanta ne tho amman data faɗa a jikin ta kuma ta tabbata fah Deeje ce tace
"Deejee kece har na yanke sammanin ganinki gobe nake shirin barin nan kuma ba zan sake dawowa ba saboda babu ke.... Gwoggo ta fashe da kuka.
Baba principal da Hajjiya Iklima kam sai ido ganin abin suke kamar a shirin film wai daman duk wannan badakalar da akeyi Deeje na raye sannan lafiyarta lau ba abinda ya sameta Baba principal tace
"Ke Khadijah daga ina kike sannan a ina kike a waɗan can ranakun har ba kizo gida ba?"
Jerun tambayoyin da akayi mata yasa duk ta ƙidime ta rasa wacce zata amsa suka ji sallama a ƙofar palour ana ta kwaɗata kamar za a shigo....
Cikin ɗaga murya Baba principal yace "kai waye wannan haka bakasan dare yayi bane kake kwaɗawa mutane sallama....
Cikin sanyin murya Deeje tace me sahu ne ya kawoni bani da kuɗi shiyasa nace ya jira na anso.
Hajjiya Iklima ce ta shige ɗaki ta dauko kudin ta fito ta mika masa 2k ba tare da ya kirga ba yayi tafiyarsa muka zauna a palour baki ɗayanmu kowa ya zuba min ido danjin maizan ce....
Da farko naso faɗa musu asalin gaskiyar cewa YARIMA ne ya saceni amman saboda bani son yasan asalina kada ya zo ya addabi rayuwamu nace.....
Ni dai ina cikin tafiya bayan na fito daga shopping sai na hango wasu mutane sukayo inda nake kamin nayi magana suka kamani cikin ƙarfi suka sakani cikin mota suka kaini wani gida har nayi sati daga bisani sukace bani suke nema ba akasi aka samu shine suka sallameni na dawo.....
Ajiyar zuciya sukayi a tare cikin tausayawa suke kallonta Shareefa ta taso zuwa inta deejee ke zaune ta zauna a kusa da ita ta kwantar da kan Deeje kafaɗar ta tana bubbuga bayan Deeje a lamun rarrashi, Auwal ma cikin tausayawa yace
"Sannu Deeje ni daman jikina yana bani kina raye kuma na san zaki dawo ko saboda ki san asalin WACECE ke!
Bana principal yace "wane batu kake yi Auwal kuna nufin Deeje bata da asali?"
"Hmmm tana dashi amman mu karan kanmu bamu sani ba tun tana da shekaru 2 a duniya ta dawo hannuna amman inaji a jikina bada jimawa ba asalin iyayenta zasu bayyana kuma na tabba Deeje ƴar gata ce"
Allah sarki Hajjiya Iklima jiki yayi sanyi tausayi da kaunar Deeje suka darsu a zuciyarta tace
"Ni na ɗauka alkawarin rike Deeje har zuwa lokacin da asalin iyayenta zasu bayyana"
Baba principal yace "Ni kuma nayi alkawarin ɗaukan nawin karatun ta har ta gama kuma har na nemama ta aeki zuwa karshen rayuwarta"
Gwoggo da Auwal basu so haka ba so suke abasu Deeje kawai su tafi da ita ƙauyen KUKAWA amata Aure amman Baba principal yace insha Allahu babu abin da zai sake samin Deeje zasu kula da ita aekema ta daina zuwa da ƙyar Gwaggo ta amince amman tace ana bada hutu Deeje taje ganin gida, suka ce mata babu komai wannan mai sauki ne daga nan kowa yayi ɗakin baccinsa Deeje tabi gwoggo suka kwanta tare.
************
YARIMA maheer jiki a sanyaye ya iso gida kamar wanda kwai ya fashewa a ciki ɗakinsa ya wuce kai tsaye toilet ya faɗa ta sakarwa kansa ruwa ya rumtse idanuwan sa yasa hannunayen sa duka biyu yana shafa gashin kansa wanda ya jike da ruwa ya kwanta rufrufruf.... Kamar na jariri kayan jikinsa sun jike sunyi masa nawi ya ragesu ya saura vest da gajeren wando sai da ya ɗauki kusan 30 minute kamin nan yayi wanka ya fito ya shirya cikin kayan bacci ya kalli agogo karfe 11:00pm ya wuce ɗakin Diddi ya tadda har ta kwanta amman batae bacci ba ya karaso da sallama ta amsa yace Diddi bakiyi bacci ba har wannan lokacin?"
"Eh banyi ba maheeru yanzu nake shirya yinsa kai ko kana inane sai yanzu ka shigo?"
"Na ɗan fita ne bae jima ba na dawo"
"Tho ya kamata ka kwanta kaga dare yayi ko sae da safe"
"Ya miƙe tho Allah ya tashemu cikin rayayyu"
"Ameen"
Ya wuce ɗakinsa ya faɗa a kan makeken gadonsa ya rumtse idanuwan sa yana tuna wannan yarinyar da ko sunanta bai sani ba yana cikin tunanin ta har bacci ɓarawo ya sace sa.
*WASHEGARI*
"Cikin bacci Deeje taga YARIMA maheer na binta a guje sai tsula gudu take babu kakkautawa shima kuma gudu yake kamar ƙafafunsa zasu tsinke cewa yake
"Ke yarinyar ki dakata mana kibar wannan gudun da kikeyi ki tsaya magana zamu yi"....
Ina Deeje itama tana wallahi ba zan tsaya ba in kaga na tsaya tho ka daina biyoni, so kake na tsaya ka cutar dani"
GWOGGO ta kae mata duka a baya tana "ke ba dae gamo ki kayi da aljanu ba Deeje ko dai wannan aljanin daren ne ya shafoki!"
Ta tashi firgigit tana musussuke idanuwa ta kurawa GWOGGO manya manyan idanuwanta sae ta fahimci a gida take ba a gidan YARIMA ba tae ajiyar zuciya tace
"Gwoggo Allah bugun da zafi mafarki fa nake ba wani aljanin da ya shafeni"
GWOGGO tace "kinga tashi ki idar da sallah ni nayi tawa"
Deejee ta miƙe ta faɗa toilet ta tsabtace jikinta ta fito tae Shareefa dan kar gwoggo ta fahimci halin da take ciki, tana shiga ta tadda Shareefa ta idar da sallah ta zauna a bakin bed har ta kammala laziminta Shareefa ta ce
"Shine jiya kika kwana a ɗakin kakarki kika kyaleni ko yayi miki kyau"
"Hmmm ke dae bari ƙawata nayi missing Gwoggo kuma banyi sammanin ganinta a nan ba"
"Yauwa Khadijah mutanen da suka sace ki ba su faɗa miki komai ba ne sannan kin tabba ta babu abinda sukai miki"
Hmmm Deeje ta kalli Shareefa tace "ina cikin damuwa Shareefa abinda na faɗa jiya ba gaskiya bane naji tsoro ne kada iyayenmu su shiga cikin ukubarsa nasan yana sanin inda nake sai ya addabi rayuwamu"
"Ban fahimce ki ba Khadijah wanene wannan mutumin da kike magana a kansa?"
Deejee ta matso kusa da ƙawarta tace "YARIMA ne ya sace ni ya kaini gidansa har tsawon waɗan cen ranakun.
Shareefa ta zaro idanuwa waje "kina nufin tsawon kwanakin nan kina hannun YARIMA!"
"Shareefa dan Allah yazame sirri a sakanin mu kada ki faɗawa kowa"
"Tho naji kema kada ki ɓoyemin komai ki sanar dani me yayi miki"
"Deejee harda ƴar kwallarta tace FYAƊE yayi min"
"Lahhhhhhhh subhanallah Khadeeja fyaɗe fa kika ce?"
"Har zuwa yanzu jini ke zubomin na samu likita ta bani wasu audugan mata tace inyi amfani dasu amman cewa tae al'adanmu mu matane shiko likita cewa yayi wae babu damuwa YARIMA kam cewa yayi amin wankin ciki naki shine daga asibiti na gudo nan.
Shareefa tae ajiyar zuciya ta fahimci period Deeje keyi saboda Deeje tun da suke da bata taɓa jin cewa Deeje na period ba sannan tana daga cikin matanta basa al'ada da wuri kuma Deeje bata san yadda abin yake ba tace
"Tho lokacin da zayi miki fyaɗen ya cire kayan jikinsa ko kuma da kaya a jikin nasa?"
"Wannan wacce kalar maganace babu kaya a jikinsa kuma nima haka cikin mugunta ya wullani kan gado har na bugu naji ciwo"
Shareefa ta fara gaskata zancen tace "sirara khadeeja amman Yarima bashida imani" tae ta kwantarwa da Deeje da hankali daga bisani suka fito sukayi kitchen dan haɗa breakfast babu jimawa suka kammala suka fito da shi palour anan suka jera kan Dining Area na Baba principal kuma suka kai masa palour nsa da shi da AUWAL.
Deejee ta wuce ta tada GWOGGO saboda karyawa gwoggo na fitowa tace ita bazata iya ba a sauƙo mata da abincin ta kasa taci a sama ba koshi mutum yake ba sannan abincin baya wucewa hanjin ciki.
Sukai ta mata dariya kai GWOGGO akwai ki da drama.......
*MASARAUTAR SARKI AHMADU*
Mai martaba sarki zaune a fada yana hutawa yau baƙinsa basu da yawa ya ɗan kishingiɗe ya lumshe idanuwansa baya jin dadin masarautar nan tun lokacin da yarasa matarsa me son sa da tausayinsa Hajjiya SUWAIBA mahaifinyar YARIMA maheer mace ce wacce ta basa gudumawa wajen bashi shawarwari akan yadda zai tafiyar da mulkinsa amman lokaci guda ya rasata......
Shigowar wani ba fade ne yana "mai martaba sarki Allah yaja zamaninka Gimbiya ta ƙaraso tana dab da shigowa........
Ya buɗe lumshashun idanuwansa ya kallesa ya ina mata maraba da zuwa, daman ƙa'idansa ne duk wanda yake son ganinsa sai ansanar dashi ko ma wanene amman kuma YARIMA maheer a duk lokacin da yaso ganin mahaifinsa tho babu hijabi a sakaninsu, ta ƙaraso cikin takunta na isa da gadara me yasa a duk lokacin da taso ganin mijinta ake hanata har sai ansanar dashi tukunnah hakan na damunta amman ba komi zata dau mataki.
Tana isowa ta zauna cikin kirsa da kisisina tace "Ranka shidaɗe barka da wannan lokacin"
Sauke numfashi maimartaba yayi yasan zuwan ta da biyu ne yace " Yauwa gimbiya barka da shigowa, da wani abune?"
Bata ji daɗin tambayar ba amman ta dake "daman akan wannan yaron ne MALEEK hannunka baya ruɓewa ka yankeshi ka yada ko ma menene ɗanka ne kuma jininka ne ina mai neman alfarmar a yafe masa ya dawo MASARAUTA da zama duk da ba a tabbatar da laifin da ya aekata ba kawai zargine.........
Ɗaga mata hannu yayi alamun ta dakata zancen ya ishesa sannan yace
"Ni ba ƙaramin yaro bane da zaki maidani ban san abinda nake yi ba wannan zancen ae mun daɗe da rufe babinsa dan haka kada ki maida hannun agogo baya, in da wani zance ki faɗesa....
Hajjiya ummah ido tsili² tace "Allah ya huci zuciyar ka babu wani batun inda akwai abubuwan da kake bukatar sai nayi maka su......
Ya kalleta da kyau ya gama karantar ta sannan yace "Ba abinda nake buƙata"
Ta miƙe ta fito tae side nata ta tada hadiman ta na ta zance kuskus ta iso ta fara sauke haushinta a kansu jiki na ɓari suka fice suka basu waje ta dau wayar ta ta kira kawarta kuma Aminiyar ta Hajjiya zulai sai da takira sau uku sannan ta ɗauka ba tare da tayi magana ba itako Hajjiya ummah tace
"Haba Zulai mai duniya in ta kiranki kika ƙi ɗaukawa sai kace bamuyi zaman daɗi ba haba .......
"Ummm Hajjiya Ummah kenan daɗina da gobe saurin zuwa daman na san dole ki nemoni abubuwa sun chakuɓe miki ba, ni zakice anyi zaman daɗi ki tuna irin rashin mutuncin da ɗanki yacimun kema haka kika watsamin kasa a ido sai yanzu da kikaga uwar bari shine zaki ne meni"
"Haba ƙawata ae waccen ya wuce yanzu kiyi hakuri kizo ina neman ki"
"Hmm Ummah kenan tho bara kiji in kinaso nazo ki biyani duk kuɗin da nake binki ki turomin ta account nawa ina ganinsu zaki ganni"
"Idai wannan ne angama zan tura miki sai kinjini" sukayi sallama.
Hajjiya Ummu cikin farin ciki ta furta kakusa dawo wa cikin wannan MASARAUTA MALEEK.
***********
YARIMA maheer a kwance a ɗakinsa ya faɗa a tunani bai taɓa bin abu a rai irin wannan ba cikin damuwa da tashin hankali ya mike ya faɗa toilet ya watsa ruwa ya fito ya shirya cikin shigarsa ta sarauta yayi matukar kyau shigar sa ta sarauta kyau take masa musamman indan ya naɗa rawani yana karbansa sai ya fito da kyawunsa gashi da V face, ya wuce kai tsaye ɗakin Diddi tanajin kamshin turaren sa tace
"YARIMA kamarko kasan ina son ganinka"
YARIMA maheer ya zauna kusa da Diddi yace "hausawa sukace in kaji kira samune"
"Ko kuma ansameka ba" Diddi ta bashi amsa tana dariya. Yauwa jiya nayi mafarki kayi Aure har da ɗanka sai kagan shi kyakkyawa da shi.....
"Diddi kwantar da hanka linki zanyi aure amman sai khairat ta bayyana tukunnah kuma inaji a jikina takusa zuwa nan bada jimawa ba"
"Maheeru zuwa yanzu ya kamata ka cire sammanin ganin khairat SBD da zata dawo ae da tadawo tun tuni kai ni ji nake ma bata raye....
"No Diddi don't say that it will never happen inaji a jikina zata dawo"
"Tho maheeru Allah ya bayyanata muma zamuyi farin cikin zuwan ta SBD dalilin babu mahaifinta AHMEDU ya karbi sarauta....
"Ban gane ba Diddi dalilin mahaifinta kuma daman mulki ba a hannunmu yake ba a hannun SARKI MAHFOUZ yake?"
Diddi cikin sauri tace "A'a fah YAREEMAH mu bar zancen haka yau da ciwon ƙafa na tashi in kafita ka tahomun da wannan maganin da DR KAMAL yake kawo min"
Ba dan yaso ba haka ya hakura da zancen amman bakinsa na da tulin tambayoyi yana son sanin abubuwa da dama ya ce
"Subhanallah sannu insha Allahu zan karbo miki yanzu ma zanyi waya a kawo"
"Nagode.......
Hadimar Diddi ta shigo tare da sallama batayi tunanin yareemah na ciki ba tana ganinsa ta gaidasa cikin girmama wa ya kalleta
"Jiya ina kika shige ne kika barta ita kaɗai ba ma jiya ba duk lokacin da na dawo sai na tadda ta ita kadai bayan kinsan tana da larurar gani tho kisani duk abinda ya same ta kema bazakiji da daɗi ba sannan ki sauya salon abinci kafar ta na ciwo kisan tana da diebetics amman bakya kiyayewa kina duk abinda kikega dama"
Jiki na rawa tace "ina kiyayewa Yareemah kuma zanci gaba da yin hakan"
"Ki duba duk abinda baku dashi kimin list ki bata zuwa anjima ina dawowa zan karba na aeka a kawo su" duk wannan maganar cikin cool voice yakeyinta.
"Tho da izinin Allah zanyi" ta mike ta fice"
Diddi tace "tana fa kokari har tafi sa'ade ma da tae aure, kai ma da dai da aurenka ae da matar ka ce zata kula dani"
Yayi ajiyar zuciya "Diddi ga hadimai a gidan nan sunfi a kirgasu in baza ta iya ba akwai wanda zasu iya ae" ya mike yana kokarin fita tana masa Addu'ah sai yadawo.
Kai tsaye wajen mahaifin sa ya wuce.
Taku yake cike da kasaita hannun sa ta hagu ya maidasa ta baya hannunsa ta dama kuma yana ɗaga musu ita alamun amsa gaisuwa har ya iso fadar mahaifin sa yana shiga maimartaba sarki Ahmadu yasakar masa murmushi yana alfahari da ɗansa cikin girmama wa Yareemah ya duka har kasa yana gaidasa ya amsa yace
"Sami waje ka zauna" ya zauna yana
"Ranka shi daɗe na fito ne abani izinin sallaman wasu daga cikin mutan kurkuku"
"Ae kana da dama da kuma ikon yanke hukunci a wannan masarautar Yareemah jeka ka saki duk wanda wa'adinsa yayi kuma laifin sa bashi da girma"
Cikin girmamawa Yareemah yace "Ina godiya maimartaba Allah ya kara lfy da nisan kwana"yana shirin mekewa ya kallesa bayan ya amsa da "Ameen" sannan yace
"Yauwa Yareemah zauna muyi magana"
Ya koma ya zauna ya maida hankalinsa kan mahaifinsa dan jin mai zai faɗa masa.
Maimartaba yace "Nasan kasan SARKI SHUA'IB kuma kasan yana da yarinyar mai suna YUSRAH tho ina son kuje ku daidai ta kanku sai azo a daura AURE ba sai an ɗauki lokaci ba....
YAREEMAH MAHEER ya kurawa Mahaifinsa ido yana tuna PRINCESS YUSRAH da irin halayyar ta na girman kai anya wannan tafiyar maiyuwa ce......
"Ya kai shuru YAREEMAH ko dai da matsala ce cikin girmamawa yace
"Babu Matsala amman nine dai bani son yin Auren yanzu a ɗan ɗaya daga min kafa zuwa wani lokaci........
Maimartaba yasan hakan zaya faru SBD ya fahimci babu AURE a lamarin Yareemah ya dakatar dashi da cewa
"YAREEMAH MAHEER har zuwa yaushe za a maka uzuri girma fa kake nima girma nake kuma nan gaba kaɗan kaine akan kujerata ina matukar son naga kayi AURE kaje dai ka kai mata ziyara sai ku daidaita sakaninku"
YAREEMAH MAHEER baya mutsu da mahaifin sa yace "Ba damuwa zanje amman ba yau ba sai zuwa gobe SBD yau a kurkuku zanyi aeki"
"Tho Allah ya nuna mana yau da goben ma ae duk ɗaya ne"
YAREEMAH ya amsa da "Ameen" ya mike ya fito mabiyansa suka maramasa baya suka fice zuwa kurkuku.
****************
*_KURKUKU_*
Babban wajene wanda faɗinsa da girman sa ya kai rabin wani gari ɗakunan ciki sunfi dubu sannan kuma ɓangare² ne acikin kowanne ɓangare da irin laifinsu sannan akwai hadiman da suke kula da wajen kamawa da masu musu abinci, sai kuma masu tsaron wajen da masu sharewa kuma duk biyansu akeyi a ko wane rana ana girka abinci akalla sau uku kuma abinci lafiyayye saboda wannan masarautar bata horo da yunwa.
Yauma haka an ɗaura manya manyan tukanen abinci ana dafawa wasu na wanke kwanonuka wasu na shara sai kuma masu saron wajen da suke kaiwa da komowa suna kollon duk abinda akeyi. Ana kammala abinci a ka fito dasu waje dan su sami damar ci da kyau kowa a ka zuba masa shi kadai a kwanun sa aka fara raba musu.....
YAREEMAH MAHEER ya shigo yana taku a hankali yana kallonsu suma suna ganin sa suka bar cin abinci suna ɗaga masa hannu shima ya ɗaga musu hannu yana binsu da kallo ya sa mabiyinsa ya karbo masa sunanyen 'yan kurkuku baki daya da kuma laifukansu, aeko yana sanar dasu suka dauko masa wani babban takarda suka mika masa shi kuma ya mikawa Yareemah amma ce masa yayi ka karanto munsu, mabiyinsa ya fara kira masa sunanyen su da kuma laifukansu.......
YAREEMAH MAHEER da yaji ankira suna da sauka kekken laifi sai yaje a ɗau sunan a cire a rubuta masa a wani littafin sannan a goge haka ko sukayi aka cire dayawa sannan yace a maida littafin sai zuwa wani lokaci sannan a fito masa da waɗanda sunayensu suke hannun sa haka akayi aka je aka taho dasu yayi musu dogon jawabi da kuma jan kunne akan duk wandanda suka fita daga kurkuku kuma suka sake aekata wani kuskure tho hukuncin da za ayi musu mai saurine dan haka su kiyaye sannan waɗanda sukeso suyiwa masarauta hidima a shirye MASARAUTA take da ta amshesa da kuma Albashi mai soka.
Ya fara taku yana kewaye wajen har ya iso inda wannan matar take ya tsaya saya a daidai kofar ya ɗagawa mabiyansa hannu da su koma baya, suka koma ya kalleta ya ce
"Zuciya ta na ɗauke da tarin tambayoyi da son jin Asalin labarin wannan MASARAUTAR sannan nayi bincike nayi tunanin babu wanda zai bani labarin sai ke ina ki bani ko da kaɗan daga cikin labarin ne...
"An cutar dani a wannan masarautar kuma an ɗauki hakkina, ina shirin faɗan gaskiya aka kuma ɗaura min laifi mai girma laifin da babu mai wankeni sai Ubangijin da ya halicce ni, na san kaima amfani dani kake so yi da kaji zakace a yanke min hukunci akan abin da ban aekata ba"
"Nayi miki alkawarin muddin kika faɗamin gaskiya ni zan wankeki kuma zan baki rayuwa mai inganci da walwala a wannan masarautar da yardan Ubangiji"
"Zan faɗa maka amman ba yau ba kawai abinda zance shine wannan masarautar asalin mulkin yakamata a hannun mace ce da tananan yanzu kai ba Yareemah bane sai dai kayi kallo daga gefe"
YAREEMAH MAHEER ya sake kallon wannan matar da kyau sannan yace "Tabbas jikina ya bani akwai abinda ake ɓoye min kuma ba aso na sani amman ba damuwa zanji komai nan da ba da jimawa ba" ya juya ya fice ya ɗauki wayar ya kira Dr KAMAL a waya yake shaida masa ya aeko wa Diddi da magungunan da take sha sannan nan da kwana biyu yazo ya sake dubata sannan sukai sallama.
*G B S QUATES*
Deejee da gwoggo a ɗaki suna hira GWOGGO ke bata labarin har sadaka akayi mata na mutuwa da yadda ta dinga kuka da bala'i akan su Baba principal ne suka saida mata da jika aka kasheta, aeko Deeje sai dariya take tana tafawa tace
"Amman Gwaggo kunyi drama harda rago aka yanka ina ma inanan naci nama"
Gwoggo ta bugeta tana ja'irar yarinya "ke da kika mutu aka yanka ina zakici"
Deejee dai sai kecewa take da dariya...... Har shigowar Ya Auwal yayi sallama ya zauna yana gaida GWOGGO ta amsa deejee ta gaidasa ya kalleta
"Deejee sannu ya gajiya ba komi ko?"
Ya jerawa Deeje tambayoyi tace ba komi ya Auwal nan Auwal yake shaidawa GWOGGO zasu koma gobe yau zai fita cikin gari da akwai ogansa da yake siyan magunguna a wajensa yake turamasa cen Kauyen KUKAWA zai kai masa ziyara, GWOGGO tace
"Ka gaidasa nima naso nayi ziyara Allah sarki ko halima me fura da nono tana raye amman ba zan iya fita ba"
Auwal yace "bakomi GWOGGO ki huta tunda gobe zamu ɗau hanya ba zakiji wahala sosai ba"
Auwal ya fuce ya barmu muka cigaba da hira GWOGGO ke cewa wai da na bisu SALISU ma yana tambayata nace
"Lallai bashi da aeki har yanzu yana nan dama"
Gwoggo tace "tho Ina zai je Deeje ko aure ya kasa yi"
"Daman wa zata auresa yana nan da mugun hali"
"Ke Deeje ki kiyayeni fa ki daina zagarmin sirki" da gangan GWOGGO ta faɗa aeko Deeje ta hau bala'i...Shareefa ta shigo ta kawowa gwoggo abinci tana
"Ashe nan kika zo Deeje kika kyaleni"
"Tana nan tana zuba min shirme ba"
"Tho taso muje muci abinci sannan daddy yace da mun kammala yana son magana damu"
Deejee ta mike sukai palour dan cin abinci Hajjiya Iklima kam har ta fara ci abinda tace
"Ah tho jiranku zanyi yunwa tayi min illah"
Deejee da Shareefa suka zauna ba kakkautawa suka fara ci sai da suka kammala sannan suka wuce side na baba principal.
Da sallama suka shigo palour baba principal ya amsa suka zauna ya kallesu sannan yace
"Tho Alhamdulillah tunda Allah ya nufa Khadijah ta dawo yanzu sai ku fara shirye-shiryen tafiya makaranta nan da jibi gobe sai kowa faɗi duk abinda take buƙata sai asayo mata, ya daura da nasihohi da shawarwari da kuma su kula da ibadah sannan yace su koma ciki dan fara shiri.
Suka dawo suna murna ae ko Deeje ta kwaso kayanta ta fara wanki daman Shareefa ta kammala nata sai ta taya ta sukayi tari wunin ranan sun yita ne a tsaye saboda sai da sukayi gugan kayan Deeje harda na GWOGGO.
*WASHEGARI*
Deejee da Shareefa ne a kitchen tunda sukayi sallah asubah basu kwanta ba suka hau girka breakfast sauri suke saboda gwoggo cewa tayi motar safiya zasu hau ba jimawa suka kammala suka kai na baba principal da ya Auwal sai kuma suka shirya nasu a nan main palour amman gwoggo cewa tai a kawo mata nata ɗakinta aiko a cen ɗakin taci suka dawo suka karya Hajjiya Iklima ma a tare dasu sukai breakfast bayan ta kammala ci ne ta mike ta haɗuwa Gwoggo goma ta arziki harda matar ya Auwal ta kai mata Baba principal ma haka yayi musu kyauta masu yawa sannan gaba-ɗaya aka musu rakiya tashan mota sai da motarsu Gwoggo ya tashi sannan gaba ɗaya suka dawo gida ko wacce tayi list na abinda take so blBaba principal ya bawa Hajjiya Iklima kuɗi taje tayi musu siyayya ta kawo suna murna barin ma Deeje za aje makarantar jami'a.
*********************
Washegari da safe tunda muka tashi muka hau shirin tafiya sai zumuɗi muke musamman ni sai rawan kai nake saboda yadda baba principal yayi mana siyayyan kayan kwalama da sauransu nace zamuci daɗi tho indai haka boko yake ae an huta kawai mutum yayi ta ciyayya abinsa baba principal da kansa ya kaimu har cikin makarantar sai da aka gama mana komai aka bamu hostel sannan ya koma gida abin haushi shine an rabani da ƴar uwata hostel namu daba amman ta rakoni muka dawo nawa kamin ta tafi wani na gani sanye da wondo da riga kuma da nono gashi yayi haski tankwale akansa sai kuma wata makekiyar sarka da yasaka nace
"Kan bala'i Shareefa see me see trouble na miji da nonuwa Allah sai an kanzamin hostel bazan zauna da gardi ba......
Cike da mamaki Shareefa ta kalli inda nake kallo sai tace
"Ke mace ce fah bakiga da nonuwa ba inyamura ce haka yawancinsu suke dressing"
"Kai ki duba da kyau Shareefa kina gani gardi da nonuwa kina cewa mace ce ni dai bazan kwana ɗaki ɗaya da gardi ba"
Shareefa dai da ta lura da gaske nake na ɗagawa yarinyar hannu alamun gaisuwa cikin harshen turanci ko tayi magana
"Are looking for someone?"
Na kalleta da mamaki muryar macece nace ikon Allah, ban fahimci mai take cewa ba nace kanki akeji mai kama da namiji kawai.
Shareefa ta maida mata akan a'a fah wankan katifar na ƴar'uwar tace kuma anan zata zauna sun samu ƙaruwa. Cikin farin ciki ta zo zata rungumeni alamun farin ciki nayi bayan Shareefa da gudu ina kwal uba ba dani ba wannan ae iskanci ne"
Shareefa tace "she's in new for that just welcome her like this say hey to her" tae mata sign ta ɗaga min hannu ko kuma muyi musabaha, ta ɗa min hannu nace ah gwanda kam.
Aeko gadagam na rike Shareefa kada ta tafi muna zaune sai ko ga wata ta shigo kamar basa mudiya tasa wani ɗangalallen siket da wata riga kamar vest kai yaji gashin doki ta shigo tana ɗaga mana hannu tana mana maraba da zuwa Shareefa ce ta amsa nikam sai kallonsu nake nace kai duniya akwai mutane iri daban² na kalli Shareefa nace
Kut anan zaki wana kina ganin ɗakin harda samudawa.
Ta kalleni tace "ba abin da zasu yi miki kiyi harkar ki kada ki kulasu, uhmm Deeje ashe akwai inda ba zaki iya iya shege ba"
Nayi dariya nace "ke dai bari wai yaro yaga bulala yayi shiru, ni tsorona kada su shaƙoni da daddare mukai ta dariya har lokacin kwanciya yayi ta tafi ni kuma na kwanta ban ma san lokacin da suma suka kwanta ba.
Comments and share fisabilillah