Episode Two: The Strangers
by @mamanmaama
Kwanci tashi har muka gama J.S 1. Sanda za muyi promotional examination ban manta da alkawarin da nayiwa Hafsat ba, dan haka da akazo exams sai nayi ta amsa questions wrongly, wata kuma sai inyi jagwalgwalo yadda ba zai karantu ba, wata question din ma sai in barta blank inyi submitting. Na daina zuwa library sam -sam sai dai in kwanta inyi ta baccina. Rannan ina bacci da yamma Hafsat ta dawo daga karatu, ta daka min duka a cinya na tashi a zumbur a tsorace, ta hade rai sosai ta kalleni tace " what is wrong with you?" Na tsura mata ina mamakin nuna caring dinta. Ta taba jikina kamar mai testing temperature dina tace "are you sick or something?" Na girgiza mata kai still ina kallon ta kamar wata robot. "You are behaving strangely this past few days, what is wrong with you?" Ta sake tambaya ta tana me tsareni da manyan idanunta, na hadiye yawun tsoro nace mata " am OK, am just too sleepy these days" tace "but you know we have exams tomorrow morning right?" Nave mata "I have already read enough before the exams sister, don't worry, I will be okay" na yi murmushin tsokana na kuma ce mata "when did you start caring? This is so unlike u? Tayi murmushi itama tare da bude dan karamin bed side fridge dinmu, ta dauko lemo ta zauna a gefen gadon ta sannan ta kalleni tana yamutsa fuska tace "gobe ma rana ce and besides, I just asked to know what to tell Dad in case something happened. You can do as u wish for all I care, but I don't want to be held accountable for your foolishness" Daga haka ta bude drink dinta ta fara sha. Na juya idona sannan na koma na kwanta, mai hali dai baya fasa halinsa. Babu wanda yasan me nake aikatawa a exams hall, har sai da mukayi hutu, muna 'yalleman principal dinmu ta kira dad a waya ta gaya masa cewa something is wrong, malamai sun kawo mata complain a kaina cewa duk na fadi papers dina kuma daga gani ansan intentional nayi. Muna zaune a dakin Inna, ina kwance a cinyar Inna ina zuba mata shagwaba ita kuma Hafsat tana kan kujera tana karatun wani novel, sai ga daddy ya shigo. Daga ganinsa nasan cewa something is wrong, nan take cikina ya bada kululu saboda nasan abinda na aikata a school. Ya zauna a nutse ya gaida Inna sannan mu kuma muka gaishe shi duka. Direct ya juyo yana kallona da serious face yace min "Maimoon mai yasa kika kayar da kanki a exams?" nan na fara inda inda, nace "am..I ..am sorry daddy, dan Allah kar ka dakeni wallahi bazan karaba?" Hafsat ta ajiye littafin hannunta tana kallon Daddy cike da mamaki. Inna ta jawoni jikin ta tana bubbuga bayana a hankali tana tambayar Daddy me ya faru cikin harshen fulatanci. Inda shi kuma ya kwashe duk yadda sukayi da principal din mu ya gaya mata, ya kara da cewa "ni ba dukanta zanyi ba. I just want to know why tayi hakan cos principal dinsu tana suggesting a mayar da ita school ta sake re-writing duk papers dinta" Cikin muryar lallami Inna ta kalleni tace "memu? Me yasa kika aikata hakan? Ke meson karatu kuma kikayi haka?" Na juya na kalli Hafsat ina hawaye, ita kuma ta harare ni tare da cewa "karki kalleni, I did my best inga kinyi karatu kika cemin you have read enough before exams" ta kalli daddy tace masa "Dad kullum bacci take yi bata karatu, innayi mata magana tayi min rashin kunya, God is my witness, I tried my best" tana gama fadin haka ta koma tayi kwanciyar ta. Daddy ya juyo yana kallona yace "I know you Moon, nasan koda baki yi karatu ba zaki iya cin exams dinki, and your principal said what you did looks intentional. I just want to know why" "I did it for Hafsat" nace a hankali, hawaye yana zuba daga idona "I want her to get ahead of me, I promised her zanyi repeating js1, I was just trying to keep my promise" Hafsat ta mike zaune da sauri "What? Kunji yarinya zata shafa min kashin kaji ko? Daddy kaji rashin kunyar ko?" Babu wanda ya bata amsa amma duk ni suke kallo ana jiran in kare kaina, cikin kuka naci gaba da cewa "Hafsat ba ta sona, ni ban san me nayi mata ba amma bata son kasancewarmu a aji daya, she is always sad and lonely saboda duk ajinmu kawayena ne ita kuma bata son ta zama friend dina, I just want her to be happy ". A lokacin su Mommy suka shigo falon ita da yaya Walid da Faruk, kallo ta bimu dashi daya bayan daya sannan ta zauna tana tambayar Daddy menene yake faruwa, shiru yayi bai amsa mata ba sai Inna ce ta fada mata brief abinda ya faru. A take Mommy ta dau zafi, daga ni har Hafsat din ta hada ta wanke mu tas. Dama tasan halin Hafsat amma bata dauka har a school bata kulani ba. "She is your only sister, me yasa ba zaki so ta ba? Me tayi miki a rayuwa?" Ta juyo kaina "and you little mouse, ta yaya zakiyi ki yi asarar shekara guda ta rayuwar ki just saboda kina so ki raba class da 'Yar uwarki, why didn't you tell me or your father about what is happening so that we can do something about it, we can put you in separate schools or something" Mommy fada take yi kamar zata ari baki har sai da Daddy ya koma shine mai bata hakuri, ita Mommy takaicinta shine wai ace "ya'yanta mata su biyu kadai da Allah ya bata kuma ace wai basa jituwa. If we didn't look after each other, who will look after us? Sai da kowa yayi shiru sannan Daddy ya fara magana: "tun farko dama nasan basa shiri?. Wannan shine dalilin da yasa na kaiku boarding kuma nace a sakaku a class daya daki daya. Nayi tunanin in sun zauna tare a inda basu da kowa zasu hada kansu, banyi tunanin hakan da nayi zai kara wa Hafsat jin zafin Moon ba. Kuma ku sani wannan ba zai saka in raba muku school ba. Yanzu abinda za'ayi shine, ke Hafsat Ina so ki fada min menene matsalarki da Moon?" Da kamar ba zata yi magana ba sai kuma ta dago kanta ta share hawayenta fara magana a hankali " Daddy ni bansan me nayi wa mutane ba, kowa yafi son Moon, hatta ku kai da Mommy, Daada, Inna, Baffa, yaya Habeeb har Faruk kowa moon yake so, komai aka tashi yi Moon za'ace kuma bayan nice babba. Daddy ko waya kayo sai kace a baka Moon kafin kace a baka ni even though I am the eldest" hawaye ne yake zuba a fuskar ta sosai "a school, teachers dinmu kowa itace tashi haka friends, at school fa ana referring to me as Moon's Sister as if am her shadow or some supporting actress. I am tired of all this dad, I want to get away from her, i want to start shining on my own, not shining in her light. I never know what she planned, I didn't even think she can do something like that for me. I didn't asked her to do it and now you are already blaming me for it" Kuka take yi sosai yanzu, ni kuwa sai na tashi naje na rungume ta muna kukan tare ina kuma rarrashinta. Saboda ni bana so inga mutum tana kuma ballantana Hafsat. Murmushi Daddy yayi yace "duk naji complains dinki Hafsat, kuma inaso ki sani, daga ni har Mom dinku baku da banbanci ke da Moon a gurinmu. Abinda baki fahimta ba shine halinku ba daya bane ke da Moon, Moon ta fiki son mutane, ke kina da saurin fushi, kullum kina daki to waye zai biki daki ya kulaki. For example, yanzu tunda muka zo garin nan baki fita ba, inajin Mom dinku tana yi miki fada dazu, duk kawunnanki da gwaggwanninki babu wanda kika je kika gaisar. Amma Moon duk taje, wasu ma twice taje musu. So tell me, why won't they ask of Moon first before you? Duk sanda bana kasar nan Moon kullum sai ta kirani a phone din Mom dinku amma ke sai in na nemeki. In kina so mutane su so ki to kema dole ne ki so mutane, ba zan ce ki zama kamar Moon ba saboda hakan is not possible dan kowa da halinsa, but at least show care of those who cares for you kamar ita Moon, someone that can put her future in jeopardy just to please you". Nan dai daddy ya yi mana fada sosai. Ni kuma daddy yace min as punishment for what I did, bazan sake exams dina ba, tunda yasan in aka hada first, second and third term scores dina aka dau average to bazan yi repeating ba. Inna ma yayi mana fada sosai akan zumunci da kaunar juna kuma da alama fadan ya shige mu dan tun kafin muyi resuming school na fara ganin chanji daga Hafsat. Muna komawa school muka zama best friends ever. Bayan shekara uku Haka rayuwa ta cigaba da kasance mana cikin jindadi da gata. Daddy yana ta samun ci gaba, yana ci gaba da harkar ambassadorship dinsa kuma yana visiting lecturing a Oxford. Ya Walid ya kammala sec sch dinsa inda Daddy ya tura shi Oxford yake karatun degree dinsa a fannin mechanical engineering. Ya Habeeb ya shiga ss3, Hafsat dani kuma mun shiga ss2. Yaune second day of resumption kuma kamar yadda al'adar school din take, yaune ake gabatar da speech and prize giving. Mommy, ya Habeeb, Daada da Faruk duk sunzo mana, suna zaune a gurinsu na musamman a side din parents. Ni da Hafsat da babbar kawata Amira munyi kwalliyar mu dai dai misali, muka fito gurin taron. Abinda ya bamu mamaki shine ganin wadansu mutane su biyar da kayan NYSC a jikinsu a zaune a bakin hall din taron. Tsayawa nayi ina kallonsu da mamaki saboda tunda muke a school din ba'a taba daukan coppers sunyi service anan ba, ko teachers din ma ba kowa ake turowa ba, sai very qualified teachers wadanda suka san me sukeyi. A hankali na furta "this doesn't look good " amma ga mamaki na sai naga duk sun juyo suna kallon mu alamar sunji abinda na fada. Kunya ce ta kamani, yayin da Hafsat ta tabe baki tace "I guess there is a first time for everything" tana fadin haka tayi gaba tare da fizgar hannuna, babu shiri ni da Amira muka bita a baya. A yanzu kam Hafsat zan iya cewa ta zama budurwa, dan inka ganta ba zaka ce she is just fifteen years ba, ni kuma lokacin ina fourteen amma still bani da girman jiki sai tsaho shima ba sosai ba. Hafsat kuwa masha Allah, dan koni da nake mace wani lokacin tsayawa nakeyi inyi ta kallonta. Fatarta bata kai tawa haske ba amma fa a murje take tana daukan ido, ga laushi. Hancinta yafi nawa tsaho kamar yadda fuskarta ma tafi tawa tsawo. Idanuwanta dara dara farare tas, bakinta mai dan fadi wanda yake dauke da full lips shi kansa abin kallo ne. Kirjinta a chike yake taf haka hips dinta wanda yasa dole mommy ta dinka mata dogayen hijabs saboda in tana tafiya gaba daya jikin ta rawa yake yi. Hafsat mai class ce sosai, ba kowa take yiwa magana ba ballantana kaga dariyarta, amma in tayi dariya wani one sided dimple ne da ita ga kuma jerarrun hakora farare tas abin sha'awa. Ni kuwa mostly English wears nake sakawa saboda nafi feeling comfortable a cikin su. Kuma babu mai yi min magana saboda bani da komai a jiki na sai kyan fuska, wannan kuwa mutane da yawa sukance nafi Hafsat amma ni kam ban yarda ba, a ganina yawan murmushi na ne yasa ake ganin kyau na. Saboda shi murmushi ado ne musamman a gurin mace. Muna shiga hall din gurin su mommy muka je muka gaishesu sannan muka je muka gaida Maman Amira muka tafi seats dinmu muka zazzauna, saboda an kusa fara taron. Kamar yadda aka saba, bayan bude taro da addu'ah sai aka fara gabatar da jawabai. Hafsat ta dauko novel dinta ta dora akan chinyarta ta fara karantawa ni kuma nayi tagumi da hannu bibbiyu ina sauraren speeches din daki daki. Sai da aka gama sannan aka kirawo passing head girl ta gabatar da farewell speech on behalf of the graduands. Lokacin har kuka nayi saboda tunanin shi kenan bazan sake ganin suba. Hafsat kuwa bama tasan me akeyi ba, sai da taji ina sheshahekar kuka sannan ta dago kanta ta kalleni ta kalli stage sai kuma tayi tsaki ta cigaba da karatun ta. Sai da aka fara rabon gifts sannan ta dago kanta ta rufe littafin da take karantawa ta mayar da hankalinta kan stage. A kayi ta kiran mutane ana basu gifts sannan aka zo kan set din mu. Kamar duk shekara, ni aka bawa overall san nan Hafsat second. Sai da aka gama rabon gifts sannan senior master ya hau kan stage ya fara announcement "I know all of you have noticed some strangers wearing strange clothes here" akayi dariya gaba daya, yaci gaba da cewa "they are NYSC members, they are sent here because they are the best in their various fields. The NYSC board wants this school to start participating in the scheme, that is why they sent this coppers to work with us. I hope you students will give them your maximum cooperation" daga nan sai ya fara kiran su daya bayan daya suna gabatar da kansu tare da fadin subjects din da zasu ke dauka da kuma classes din da zasu dauka. Tunda suka fara naji gabana yana faduwa, haka kawai naji jikina yana bani cewa something not so good is going to happen. Ina cikin haka naji wani daga cikinsu yace "my name is Ibrahim Adeniran Oluwaseun, from Ibadan. I will be taking SS2 mathematics and geography" Innalillahi wa inna ilaihir rajiun shine abinda nayi ta maimaitawa a zuciyata. Ji nayi tamkar an juya min dukkan plans dina na rayuwa ta. Mathematics is my best subject, maths teacher din mu is my best teacher, yaya za'ayi a chanja min teacher a hada ni da unexperienced copper? Ji nayi tamkar inbi su Mommy mu koma gida saboda ji nayi gaba daya makarantar ta fita daga kaina. Ban kuma fahimtar me ake ciki ba saiji nayi ana hayaniya alamar an tashi daga taron. Cikin sanyin jiki na dauki gifts dina na tafi gurin Mommy na kai mata, haka ma Hafsat. Mommy tana gani na tasan something is wrong, tana tambaya ta kuwa na fara yi mata bayani. Mommy akwai daukan zafi dan haka nan da nan ta jamu sai office din senior master ta fara yi masa bayani akan cewa tun da muna senior class bai kamata a dauki subject as important as mathematics a bawa copper ba, kamata yayi ace an bar coppers a junior classes. Murmushi yayi tare da cewa "na fahimci complain dinki Ma, kuma insha Allah in ya fara daukan su in har sunga akwai problem, ina encouraging dinsu su zo su yi complaining. But first they need to give him a chance. We will all need to be given a chance one day in our lives, one way or another". Da haka muka fito daga office din, mommy tana encouraging din mu akan as soon as muka ga bama gane teaching dinsa mu zo muyi complain. In ba'a dau mataki ba in tazo mana visiting mu gaya mata, in yaso sai tayi wa Daddy magana yazo da kansa yayi solving issue din. š *Maimoon* š *2nd Edition* *Maman Maama*