Maimoon

Episode Six: Friends

by @mamanmaama

Washegari tun kafin assuba na tashi nayi wanka na saka uniform dina, assuba tana yi na tafi masallachi nayi sallah daga nan na wuce islamiyya. Nayi haka ne saboda bana son muyi rigima da Hafsat. Har muka fara karatu Hafsat bata zo ba. Amira ta tambayeni ina Hafsat na daga mata kafada alamar I don't know, har aka tashi daga islamiyya babu Hafsat babu labarinta, sai na ringa jin babu dadi a raina, what if she is sick? Na taho na barta. Ana tashi na kira Amira nace mata please tayi checking on Hafsat, ni class zan wuce bana son komawa hostel, tace min ba problem. Ina yin breakfast na wuce class na zauna ina karatu na har aka fara zuwa class. Karatu nake amma duk hankali na yana kan masu shigowa ina jiran inga shigowar ta. Can sai gata ta shigo fuskar nan babu alamar fara'a, tana zama na mike na tafi wajen ta nace "Hafsat lafiyar ki kuwa yau ban ganki a islamiyya ba?" Tayi min kallon sama da kasa tace "what is it with you idan ban je islamiyya ba? Ko zaki saka shi yayi min bulalar fashi ne?" Nayi murmushi nace "that settled it, dama ina ao in san lafiyar ki, na fahimci kuma lafiyar ki kalau" na koma nayi zama na. Ina zama sai ta mike ta kama jan seat dinta sai da ta kai shi can row din baya sannan tayi zamanta. Sam bana jin dadin abubuwan da Hafsat take yi amma kuma bana son in bata chance din da zata ke controlling rayuwata. Farko Ibrahim ya fara kulata yana tsokanar ta da big sister amma sai ya lura cewa bata so dan haka ya rabu da ita. Rannan muna karatu ya tambayeni "how is your sister" nayi mamakin tambayar amma na maze nace "she is fine" he snickered kafin yace "she hates me" na ajiye rubutun da nake yi nace "no, she doesn't hate you, she has always been like that dama, believe me sometimes I feel like she hates me too" daga nan bai sake yi min maganar Hafsat ba. Bayan munyi wata daya da fara term din su mommy suka zo mana visiting. Tun da aka kira mu gaba na yake faduwa dan bansan me Hafsat zata kulla min a gurin mommy ba. Muna tafiya zamu je gurinsu na matsa kusa da Hafsat nace mata "what are you planning to tell Mommy?" ta kalleni da murmushin mugunta tace "that's my business, me kike ci na baka na zuba?" na hadiye yawun tsoro cikina ya kulle kamar zanyi zawo a wando amma na daure na cigaba da binta a baya ina ɓuya a jikinta kamar munafuka. Muna zuwa visitors room sai muka tarar da Daada da faruk, nan da nan na manta da damuwar da nake ciki na fada kan cinyar Daada ina murnar ganinta, Hafsat ma tazo ta rungume ta muna ta dariya, Daada tace da yaren buzanci "kai ni kar ku ji min ciwo, ku baku san kun zama 'yan mata bane" nace mata "haba Daada, ina abin yake? Sai dai ki gaya wa Hafsat bani ba" Hafsat kuma tace "ai komai girman da zanyi bazan daina hawa cinyar ki ba Daada" muka sake yin dariya. Faruk yana zaune yana kallon mu nace "autan mommy ko magana babu?" Yace "au kuna gani na? Na dauka ai ni invisible ne tunda babu wacce ta kula ni a cikin ku" nan kuma muka tafi da gudu a tare muka rungume shi yana ture mu wai yayi fushi. Hafsat ce tace Daada wai ina Mommy ne?" Daada tace "muna zuwa principal dinku ta kira ta" nan take wani gumi ya karyo min, tunda muka shigo ban ga Mommy ba na dauka bata samu damar zuwa ba har hankali na ya kwanta. Nayi saroro har wani daci nake ji a baki na. Hafsat ta dafa ni tace "yayane Moon? Ko bakya murnar ganin Mommy ne?" na ture hannunta na koma kusa da Daada ina tambayar ta su ya Habeeb. Muna cikin haka sai ga messenger daga principal's office wai ana kiran mu ni da Hafsat. Muka tashi muka tafi, nice a gaba Hafsat tana bina. Ina tura kofar office din naga Mommy a zaune a kujerar gaban table din pc daga can gefe kuma Ibrahim ne a zaune yayi folding arms dinsa yana kallon Mommy. Sandarewa nayi a gurin na kasa motsi, komai nawa ya tsaya hatta bugun zuciya ta. Hafsat naji tana fadin in matsa in bata guri ta shigo tunda ni bazan shiga ba. Sai a sannan numfashi na ya dawo sai kuma zuciyata ta fara bugawa da karfi, dacin da nake ji a baki na ya karu, Hafsat ta karewa office din kallo sannan tazo dai dai kunnena tace min "whatever goes up must come down" tana yi min murmushin mugunta ta shige ciki da sallama. Ba yadda zanyi dole na bita a baya. Ga mamaki na sai naga Mommy ta juyo da fara'a sosai a fuskar ta ta mike tsaye ta buda hannayenta tare da cewa "come here my darlings" ban san sanda na manta da komai ba na fada jikin Mommy ina murna. Ta rungume mu sosai a jikinta na wani lokaci sannan ta sake mu, muka gaishe ta, muka gaida pc sannan na juya na gaida Ibrahim. Hafsat ko kallon inda yake bata yi ba Mommy kuma bata lura ba dan suna magana da pc a lokacin. Sun jima suna magana amma ni hankali na ya tafi akan tunanin dalilin wannan kiran da akayi mana kuma gashi an kira Ibrahim shima, lokaci lokaci inna daga ido na sai mu hada ido da Ibrahim sai ya sakar min murmushi amma ni kam ranar bani da damar mayar masa dan gaba daya hankali na a tashe yake. Sai da suka gama hirar su sannan Mommy tace "I am very proud of you Moon. Tun ina gida aka aika min da report na yadda karatunki yake progressing, naji dadi sosai. PC ta gaya min cewa ashe kun daidaita da sabon copper din da da kike complaining akansa, tace yanzu har extra lessons yake yi miki kuma kina samun cigaba sosai" Bani ba hatta Hafsat sakin baki mukayi muna kallon Mommy na juya na kalli Ibrahim shima sai naga bakin ya saki yana kallon ta" principal ce tayi dariya tace "au mamaki kukeyi yadda nasan kuna yin extra lessons? This is my school, I know everything going on in it. Ina da security da suke zagayawa koda yaushe, kuma kullum sai sun kawo min report cewa sun ganku kuna karatu a gaban library, sai na fara tambayar teachers din ku akan performance din moon kuma suka tabbatarmin da cewa she is doing much better than before. Dan haka na rubuta report na aika gidan ku" Mommy ta juya tana kallon Ibrahim tace masa "bawan Allah, thank you so much. I really appreciate what you are doing. Kuma ina so in nemi favor a gurin ka akan ka hada da Hafsat please. I know she can be difficult sometimes but please bear with her. Zanyi making arrangements zamu ke baka allowance duk wata" Ibrahim ya kalleni, he looks confused. Ya chire glasses dinsa sannan yace "Thank you so much ma'am for the offer but it is not what you are thinking. Actually I am not giving Maimunatu any extra lessons. In fact she teaches me sometimes, kawai muna karatu ne tare. She is very intelligent and always ahead of her class so we are both benefitting. There is no need for any allowance Ma'am because I am gaining as well. As for Hafsat, it will be my pleasure" ya karasa yana kallon Hafsat da murmushi ita kuma da dauke kanta sai da Mommy ta harare ta sannan tace masa "thank you sir". Ya amsa da "you are welcome" Mommy ma tayi masa godiya sosai sannan ya fita. Daga nan muma mukayi sallama da pc muka koma gurin su Daada Hafsat tana ta zumburar baki reshe ya juye da mujiya. Ita dai bata da wani evidence da zata nuna wa Mommy cewa akwai wani abu tsakani na da Ibrahim tunda report ya nuna cewa karatu muke yi. Nan mommy ta saka Hafsat a gaba da fada cewa lallai itama ta ringa fita muna karatun tare da ita, tace min duk sanda bata fita ba in gayawa principal nace mata to sannan na faki idon Hafsat nayi mata gwalo. Bayan su Mommy sun tafi muka aika da kayan da suka kawo mana zuwa hostel mu kuma muka koma class. A ranar da daddare bayan na gama shiri zan kwanta sai nazo kan gadon Hafsat wadda already har ta riga ta kwanta na fara yi mata magana da fillanci. "Hafsat nasan yadda kike ji a ranki yanzu, kina jin tamkar duniya duka ta juya miki baya amma ina so ki sani ba haka bane. Ita duniya tana zuwa maka ne a yanda ka dauke ta, inka dauke ta da zafi to babu shakka zata zo maka da zafi. Please Hafsat tunda muke ban taba neman alfarma a gurinki ba, dan Allah wata alfarma nake nema as a sister, idan kika yi min wannan nayi alkawarin bazan sake rokon wani abu a gurinki ba, please ina so komai ya wuce dan Allah kiyi abinda Mommy tace, kizo muke yin karatu tare da Ibrahim, I assure you, you will like him." Bata ce min komai ba sai na kara da cewa "kinga in muna tare da ke ma zaki fi jin dadin saka ido akan abinda muke yi" na karasa ina yar dariya. Duk maganganun da nake bata ce min komai ba amma ni na tabbatar tana jina. Ganin bata da niyyar kulani ya saka na tashi naje na kwanta nayi adduoi nayi bacci na. Washegari ma duk mu biyun bamu je islamiyya ba, nayi wanka ina saka uniform sai ga Hafsat ta fito daga wanka ta bude fridge ta dauko fresh milk tana sha sai ta miko min tace "do you want some?" Nayi murmushi na karba nace mata "thank you" daga nan muka shirya muka fita class tare. Tun daga lokacin muka daidaita da Hafsat akan maganar Ibrahim, muka koma yin al'amuran mu kamar da. Hafsat ta fara zuwa gurin karatun mu da Ibrahim sai dai ba kullum ba, in taje su kan danyi magana kadan ba sosai ba. Shakuwa ce sosai take shiga tsakanina da Ibrahim. Kullum muna tare tun daga 3pm har magrib. Kofar library ya zama permanent gurin zaman mu. Abin mamaki shine, kusan duk interest din mu daya; a duk subject nafi son maths shima haka, sport din da nake yi shi ne basketball kawai ranar sport shima sai na ganshi a gurin basketball, duk kanin mu muna da fara'a da surutu kuma bamu da fada. Kullum in aka tashi daga class Ibrahim sai ya rakani har bakin hostel, haka zalika in aka tashi daga islamiyya ta dare ko ta assuba sai ya rakoni har sai na shiga hostel sannan zai koma. Tun ana min surutu ina damuwa har na saba. Zan iya cewa kusan komai na Ibrahim na sani, duk wani abu da yayi idan bama tare in muka hadu sai ya bani labari. Rannan muna zaune a gurin zaman mu sai sister dinsa ta kira shi a waya, ya dauka suka fara hira da yarabanci, ni sai abin ya bani dariya saboda ban taba jin yana yarensa ba dan har manta wa nake yi shi Yoruba ne, daga dukkan alama fada yake mata. Sai da suka gama sannan ya miko min yace mu gaisa, na karba tare da yi mata sallama ta amsa min da accent din Yoruba. Muka gaisa babu yabo babu fallasa na mika masa wayar sukayi sallama ya kashe. Nace masa "what is her name?" Yace "Maryam" na sake tambaya "how old is she?" Yace "23" sai a lokacin na sake realising age gap din da yake tsakanina da Ibrahim. Nan yake bani labarin cewa maganar auren ta ne ya taso, ta kawo miji step father dinsu baiyi approving ba shine take so shi Ibrahim din ya shiga cikin maganar shi kuma yaki. Anan na fahimci cewa Ibrahim yana mugun yiwa step father dinsa biyayya like shi yake da final say a duk abinda ya shafe su. Ibrahim sam ba mai yawan abokai bane dan ban taba ganinsa ko jin sa yana waya da wani aboki ba. Rannan mun tashi daga islamiyya. Nace "why aren't you going into town? Yace "I have nothing to do in town, ni ban san kowa a garin nan ba, school din nan ta bani gurin zama a cikin quarters, tana bani abinci kullum" ya tsaya da tafiya ya juyo yana kallona "and you are here also, so mai zai kaini cikin gari?" Nayi murmushi naji dadi har cikin raina nace "amma tunda har kazo Abuja, why not baza kayi using this chance ba ka ga gari, it is a very nice town, besides, you never know wa zaka hadu dashi a cikin garin. Ka sani ko kayi budurwa?" Dariya yayi sosai yana kallona da lumsassun idanuwansa, ya langwabe kai gefe kamar mai shirin yin shagwaba yace "ni nayi kankanta da yin budurwa. Baki ganin ni yaro ne" yadda yayi maganar ne ya bani dariya nima nace "yaro a ina? I thought 25years kake? To in bakayi budurwa yanzu ba sai ka fara furfura tukunna?" Ya kalleni da serious look yace "Allah da gaske nake bani da budurwa, sai later, da nace sai na gama service amma yanzu ina tunanin anya zan iya jira kuwa? In na tsaya wasa zuciya ta zata iya fitowa daga kirjina" yadda yake maganar a hankali da yanayin da yake kallona yasa naji tsigar jikina tana tashi. Banyi aune ba sai ji nayi Amira ta kama hannuna tana jana gefe tare da cewa "to love birds, times up, goodnight sir, sleep tight" da sauri da sauri take jana muna tafiya hostel ni kuwa har yanzu ido na a kansa suke shima kuma ni yake kallo, sai da muka wuce bakin gate din hostel sannan naga ya juya yayi hanyar staff quarters. Muna shiga hostel Amira ta jani gefe "what are you doing Moon? Kinga kallon da yake miki kuwa? Shaidan fa is real komai iliminsa kema kuma komai kame kanki da saka hijabin ki ba guarantee bane na cewa shaidan ba zai yi nasara akan ku ba" raina ya baci da accusation din Amira nace mata "Amira mutumin nan fa ba saurayina bane, we are just friends, sannan kuma bama kebewa mu kadai ni dashi, kullum a waje muke zama inda kowa zai gan mu" tace "ni ban taba ganin inda saurayi da budurwa suke wani friendship ba, you are deceiving yourselves, ko makaho ya shafa fuskokin ku yasan cewa something is there" nace "saurayi da budurwa kika ce. He maybe saurayi amma ni ba budurwa bace" tayi min kallon sama da kasa tace "oh ke 'yar jaririyace kenan ko? Ji nake yanzu haka ma period kike yi? Wanne girma kuma zakiyi nan gaba bayan already hormones din adolescent sun fara aiki a jikin ki. You are a woman now whether you are full breasted or not, dole akwai attraction tsakanin ki da shi" nayi sauri na daga hannu na tare da cewa "I am not attracted to him" tace "really?" Sannan ba tare da ta jira amsata ba tayi tafiyarta ta barni.