Episode Eight: The Goodbye
by @mamanmaama
Hafsat ta tsaya saroro tana kallona. Sannan ta sunkuyo saitin fuskata tace "yanzu ke Moon kina ganin har kinyi girman da zaki fara soyayya? Har kina ganin kin isa ki yanke wa kanki hukunci? Har kina ganin kin san menene dai dai menene ba dai dai ba?" I was ready for her dan haka ko gezau banyi ba nace "7 years ago, sanda nace inna girma ina so in zama neorosurgeon murna kuka yi ta tayani kuna cewa nayi making right decision, ta yaya kuma yanzu zaki ce min ban isa in making decisions ba? I know what I am doing I just need you to support me please" Tayi min wani kallon wulakanci tace "lallai yau na tabbatar baki da hankali Moon" tayi tafiyar ta ta zauna. Nayi shiru ina tunani, lallai Hafsat bata gama sanina ba har yau. Mutane da yawa suna cewa I am a genius, amma ni ban yarda ba, na san dai ina da brains kuma I am going to use it here. Tabbas nasan ina son Ibrahim amma hakan bazai sa in barshi yayi messing with my life ba. I said yes to him saboda bana son ya bar makarantar kamar yadda yayi threatening amma hakan ba yana nufin za muyi soyayya bane ba. In dai har yana sona zai jira ni har in gama secondary school in kara girma sannan we will see what will happen. Na gama tsara komai yadda nake so ya kasance. Abu na farko shine; ba zan ke bari muna kebewa ni da shi ba alone. Dan haka ana yin break na tashi a class nayi announcing cewa ina gayyatar duk wanda yake da ra'ayi zamu ke karatu tare. Kusan rabin class din suka ce suna so, nan muka zauna muka tsara timetable ta karatu, kullum da akwai subject din da zamu keyi, za muke fara wa 3pm mu gama 6pm. Nayi inviting duk class din ne saboda nasan kullum dole wani zai zo, baza mu kasance daga ni sai Ibrahim ba. Abu na biyu da nayi shine na fito da duk textbooks dina na jera akan desk dina yadda babu yadda za'ayi mutun ya zauna akai, no more sitting on the desk tactic. Iyakacin sa sai dai ya tsaya a gaban board ya gama abinda zai yi ya fita. The next thing da nayi shine ana tashi a school na tafi gurin HOD na Islamic studies na kai masa complain cewa ina so a chanja min class din islamiyya amayar dani B class, dalilin dana bashi shine ina son raba aji da Hafsat dan tana distracting dina. Da kyar na samu ya amince shima saboda muna mutunci dashi sosai tun jss1. Nasan in Ibrahim ya fahimci abinda nayi he will be mad but I am ready for him. Ai kuwa sanda ya fahimci na chanja class a islamiyya he was furious. Muna zaune muna karatu a new class dina sai gashi ya shigo ya bawa yasaiyadin mu hannu suka gaisa sannan yace "I will like to see one of your students please" nasan ni yake nema amma sai naki dago kaina na dukufa ina karatu, ya sayyadin yace masa "kadan yi hakuri in ba emergency bane yanzu muna karatu in mun gama sai tazo" Ibrahim yayi masa godiya ya fita. Sai da naga saura less than ten minutes mu tashi kuma na riga na biya karatu na sai na tambayi yasayyadi nace zan je toilet, yace min ai it is almost time inna tafi inyi zamana kawai, dama haka nake so dan haka na dauki books dina sai hostel. Hafsat tana zuwa ta fara tuhumata akan menene yasa na chanja class nace mata its none of her business. Ranar da Ibrahim yazo mana maths yaga na cika gaba na da texbooks, kawai ya tsaya yana kallona ni kuwa na dauke kaina kamar ban san yana yi ba. Duk yadda yaso in kula shi naki yarda har period dinsa ta fita, yazo ya tsaya a gabana yace "see me immediately after school" nace "yes sir" amma ko kadan banyi niyyar zuwa ba. Da yamma muka shirya wajan mu biyar muka fita karatu. Muna zuwa muka yi arranging chairs muka samo wani babban table muka saka, mun fara karatu kenan sai ga wasu ma sunzo, haka muka hadu wajan mu goma, muka shiga library muka karbo aron books da syllabus din term din muna tsara yadda zamu fara karatun sai ga Ibrahim. Tsayawa yayi yana kallon mu fuskarsa cike da mamaki. Yayi kwalliyarsa da sabuwar shadda sai, kamshi yake yi. Ya jingina da jikin library ya rungume hannayensa a kirjinsa ya zubo min ido, kallo daya nayi masa na dauke kai naci gaba da abinda nake yi. Amira ta taba ni tace "mutumin ki fa ke yake nema" nace mata "I know" na cigaba da karatu na, can ta sake cewa "duk wannan kwalliyar fa ke akayi wa" na sake ce wa "I know" taga dai bani da niyyar kulata ta rabu dani, ita Amira bata san zafin da nakeji a raina ba, I missed him alot amma still I want to be strong, na leka ta saman littafina ina kallon shi naga ya dauko wayar sa yana dannawa, nan na samu damar kare masa kallo. Sabuwar shaddar sa kalar ash mai haske ta sha dinkin tazarce da aiki kalar ash mai duhu, hular sa da takalmin sa duk ash mai duhu ne, fatar sa tayi tas, fuskarsa fes kamar yanzu aka bare shi daga cikin ledar sa. Na shagala ina kallonsa kawai sai tsintar ido na nayi acikin nasa, nayi sauri na dauke kaina na mayar da ido na kan littafin da yake hannuna duk da cewa na manta ma wanne subject nake karantawa. Sai kuma ya tako ya karaso inda muke, ina jinsa yana tsokanar Hafsat wai taje gida ta kara kiba, ga mamaki na sai naji ta kulashi tace shima yaje gida ya kara fari, ya dawo kusa da Amira yace mai ta kawo masa daga gida. Kusan saida yayi wa kowa magana a gurin amma banda ni, nima kuma bance masa komai ba. Washegari muna cikin class sai gashi yazo yace da teacher din mu zai karbi sako a guri na. Ina jin haka nayi sauri nace "I gave Mr Victor to give to you" ya tsaya yana kallona, ni dashi duk munsan babu wani sako da zai karba a gurina, can yace "OK thanks" ya fita fuskarsa babu alamar annashuwa. Ranar da daddare muna zuwa islamiyya naga 'yan A class suna komawa hostel, na tambayi dalili sai suka ce yasayyadinsu yace baya jin dadi bazai samu damar zuwa ba. Kusan 3 weeks muna haka da Ibrahim, he was so frustrated nima haka, har na fara tunanin anya zan iya kuwa? I am not as strong as I thought I was. San da mukayi wata daya daddy yazo mana visiting tare da yaya Walid, naji dadin visit dinsu saboda I was in need of little love, kuma na samu sosai a gurin Daddy, mun dade muna hira kafin su tafi. A ranar da daddare bayan mun tashi daga islamiyya sai yasaiyadin mu tsayar dani akan maganar saukar mu, by the time da muka gama magana dashi almost kowa ya tafi, shima yana fitowa yayi tafiyarsa, nan naji tsoro ya kama ni, ina tafiya ina waige waige zuciyta kamar zata bar kirjina. Kamar daga sama naji an fincikeni an hada da jikin katanga, na takarkare iyakacin karfi na zan yi ihu aka toshe bakina da hannu. Duhu ne gurin dan haka na kasa ganin fuskar wanda ya rike ni, jikina sai karkarwa yake yi kamar mazari. A hankali na fara nutsuwa sai a lokacin naji kamshin sa. A bangare daya na zuciya ta naji dadi cewa ba barayon mutane bane ko dan yankan kai, a daya bangaren kuma wani tsoron ne ya shige ni, me Ibrahim zai yi min? Nan na fara kokarin kwace kaina daga hannunsa amma maimakon ya sake ni sai ya sake matse ni a jikin bango, na saka hannayena duka biyun na tattara karfina ina tura shi amma ko motsi baiyi ba, kawai sai na saka kuka, ya barni nayi ta kuka na yana sauraro na sannan a hankali a sunkuyo fuskarsa dai dai kunnena yace min "why do you say yes?, tunda kinsan ba kya sona mai yasa kika ce min you want to walk the path to the future with me? Why are you playing with me? Do you have any idea what you are doing to me?" Ya jera min tambayoyin da nasan ba zan iya amsa masa su ba, yasa hannu yana kokarin dago fuskata amma fir naki yarda, ya hakura ya rabu dani, ya sake cewa "ni kawai so nake in san me yasa kika amsa min bayan kinsan bakya sona, kina gaya min zan barki kiyi tafiyarki. You don't love me, right?" A hankali na girgiza kaina, ya saka hannayensa biyu ya dago kaina yana kallon cikin ido na yace "look into my eyes and tell me you love me" wasa ma kenan, na dauke ido na daga cikin nasa nace "I can't" "you can't what" "say it" "say what" "the L word" daga kirjinsa naji sound din dariya amma bata fito bakinsa ba. "Then why are you avoiding me" nan ma shiru babu amsa "are you ashamed to be seen with me?" Nayi sauri nace "No" "please just tell me why" sai da na dauki some seconds sannan na fara magana "I am just not ready for this, ina so in kara girma, at least in gama secondary school, am sorry ban gaya maka haka ba, I just don't want you to go" Ya sake dago fuskata yace "look at me, I will never mess up your life, never. I love you and I will wait for you to be ready, no matter how long, kawai ina so in tabbatar cewa kina sona kema" sai kuma ya danyi dariya kadan "but tunda kin kasa fadar L word a gaba na dole in hakura da gyada kan" Kunya ce ta kara kamani na cigaba da kokarin ture shi yana dariya, na hakura na barshi, sai da ya gama dariyarsa sannan ya sake rage murya yace "I missed you, please ki daina min abinda kike min, please ko yaya ne kike bani lokacin ki, I promise I will behave, bazan kuma yi miki maganar L ba, please ki daina share ni, I will loose my mind, ki gaya min duk abinda ba kya so zan daina, I promise" ina jinsa kuma ina jin maganar sa har cikin raina, a hankali nace "ka daina tabani, babu kyau" ina rufe bakina ya sake ni yace "done, I will never touch you again" muka yi shiru for sometimes, nace "zan tafi, dare yayi" yace "ok, I will see you tomorrow in class" Ibrahim ya cika alkawarinsa, mun bar soyayyar mu very low, ban da occasional smiles babu wani abu da zai nuna maka cewa akwai wani abu a tsakanin mu. Har muka gama second term muka koma third term. Muna shirye shiryen rubuta qualifying exams ne rannan a class ake zancen in mun tafi hutu baza mu dawo mu tarar da coppers ba, sai dai maybe mu tarar an kawo wasu. Sam na manta cewa shekara daya ake yi ana service, nan take naji kaina yana juyawa. Amma Ibrahim bai taba min wannan maganar ba, dole in zauna inyi tunani. Wato shi nufinsa sai dai kawai in mun dawo in neme shi in rasa ko? Amma dai bara in ga gudun ruwansa tukun. Wasa wasa har saura one week muyi hutu Ibrahim bai ce min komai ba. Ranar akayi taro akan shirye shiryen saukar alqur'ani da zamu yi. Ana cikin taron ina kallon Ibrahim yana ta kallona yana yimin murmushi amma na hade rai naki mayar masa. Hafsat sa ido tana lura dashi tace min "yau da alama tsumin ya tashi" nayi banza na rabu da ita. Ana tashi daga taron ya taho gurin mu yace min " I want to see you, please" nace masa "OK, ai gani ko" ya sunkuyo saitin fuskata yace "alone" daga haka ya juya ya fice daga hall din. A raina nace lallai wannan mutumin, amma bance komai a fili ba saboda su Hafsat 'yan bani na iya 💘..Bayan sa nabi na tarar dashi a staff room a zaune shi kadai saboda duk malaman are busy. Ya nuna min kujera na zauna ina ta shan kanshi ni lallai fushi nake yi. Yace "wai wannan fushin na menene Maimunatu?" Na kara tsuke fuskata ina turo baki, dariya ma abin ya bashi yace "ni dai bansan abinda nayi ba, duk dokokin da aka kafa min ina binsu, to me nayi ne ni Ibrahim?" Na kalle shi da fada nace "sai yaushe kake planning zaka gaya min in ka tafi gida ba dawowa zakayi ba?" Nan take murmushin fuskarsa ya bace. Ya gyara zama yace "Maimunatu ina so muyi maganar amma so nake in tsaida tsayayyiyar magana tukun" nace "bangane ba" yace "bana son komawa Ibadan, ina son in nemi aiki anan ko cikin abuja ko school dinnan, inda dai zan ringa ganin ki. To nayi wa principal dinku maganar inda akwai vacancy inaso amma bata bani amsa ba tukun, to ni tunda nazo ba shiga cikin gari nake yi ba sosai sai last two weeks muka fara zuwa da Victor muna raba CV din mu. In har na samu job a Abuja zan dawo nan da zama saboda ke, in ban samu ba kuma babu yadda zanyi Maimunatu dole in koma Ibadan" Naji dadin maganar sa har cikin raina, cewa zai iya dawowa Abuja da zama saboda ni alhalin family dinsa suna Ibadan. Na rage murya tare da langwabe kai nace "amma familyn ka fa? Don't you want to go back to them" yace "family na ina zuwa ganin su ai duk weekend. Bature yace home is where the heart is, and you are my heart Maimunatu. I want to be with you" Na sunkuyar da kaina kasa ina lissafin maganar sa. Tabbas ina son zamansa a abuja saboda bana son yayi nisa dani amma kuma family dinsa fa? Nayi musu adalci? Amma kuma ta wani bangaren samun aikin sa a abuja ai cigaban sane, duk da bansan salaryn sa na Ibadan ba amma nasan na nan sai yafi na can. Wata idea ce tazo min raina kuma nayi alkawarin zanyi trying. Muna zaune wasu staff suka shigo suna kallon mu, sai kawai naji ban damu ba. It doesn't matter tunda barin school din ma zaiyi. Tun daga ranar kullum muna tare da Ibrahim gani nake kamar in muka rabu bazan sake ganin saba, shi kuma kullum yana assuring dina da cewa koda bai samu aiki a Abuja ba to kullum zai ke zama a hanyar zuwa gurina. Ana saura kwana biyu hutu mun fito daga exams muna zaune akan veranda ni da Ibrahim muna ta hirar mu muna dariya, yanzu ban damu kowa ya ganmu tare ba tunda it's almost over. Sai nake tambayar shi maganar auren sister dinshi Maryam, yace "Maryam ta jama kanta ai, yanzu wani cousin din mu za'a aura mata kuma bata so, data hakura da wancan ta fito da wani da shikenan ai" Na sunkuyar da kaina nace "do you think it is easy?" Yace "what?" Nace "idan kana son wata kuma parents din ka suka ce no, do you think it will be that easy ka hakura da ita ka samu wata?" Yanzu ya fahimci cewa ba maganar Maryam nake yi ba, ina magana ne akan abunda zamu iya fuskanta anan gaba. Yayi shiru bai ce min komai ba, har nayi tunanin ba zai amsa ba sai kuma yace "they will not say no. Maganar Maryam is different, wanda take so ba mutumin kirki bane. They only need to get to know you zasu soki sosai" Nayi murmushi kawai a raina ina cewa naka mai sauki ne Ibrahim nawa nake ji, a fili kuma sai nace "idan kuma basu soni ba fa?" Yace "they will" na sake cewa "what if they don't?" Kamar wanda aka mintsina sai ya mike tsaye yace "dan Allah ki bar maganar nan, we will cross that bridge when we get to it " a raina nace Allah ya bamu ikon tsallake wa lafiya. Dama da akwai plan din da nake shiryawa na abinda zanyi. Na jawo school bag dinsa da ya ajiye a tsakanin mu na bude na fara yi masa bincike, ya dawo ya zauna yana cewa "me kike nema a jakar tawa kuma" nace "wasikar budurwar ka nake nema" yayi dariya yace "ai ba a nan zaki samu ba, kin ganta a nan" ya fada yana zaro pink and purple handkerchief dina daga aljihunsa. Nasa hannu na rufe fuskata ina dariya nace "kai yanzu ajiye shi kai?" Yace "eh mana, kuma ajjiyarsa zanyi tayi as a reminder, a reminder to me and to you, a reminder that we promised each other the future" nayi shiru ban bashi amsa ba amma naji seriousness din maganar sa, ya sake cewa "seriously, what are you looking for a jaka ta?" Nace "CV dinka nake nema" yace "me zakiyi da CV dina" nace "ajiyewa zanyi nima as a reminder" yayi dariya yana karbe jakarsa daga hannuna. Nace masa "da gaske so nake in ajiye duk sanda na tashi rubuta CV sai in duba taka" ya jima yana kallona da alama bai yarda da bayani na ba sai kuma ya daga kafada ya dauko ya miko min, na karba nace "thank you" yace "you are welcome" Ranar hutu daga ni har shi kamar marasa lafiya muka zama, tun da sassafe na fito muna tare dashi har akayi assembly aka fara shigo wa daukan students. Yace min "kina da number dana baki" nace "yes" yace "you can call me anytime" nace "to" duk mun rasa kalaman da zamuyi sallama dasu kawai dai muna enjoying company din each other. Ina ta addu'ah a raina Allah yasa kar azo daukan mu da wuri sai na hango motar gidan mu tana shigowa, gaba na ne ya fadi saboda naga sabuwar motar Mommy ce, bana son Ibrahim ya ga motar tunda har yanzu bai san gidan mu muna da kudi sosai ba. Nace "ga daddyn mu chan yazo, will you like to meet him?" Nan da nan naga fuskarsa ta chanza, yace "no, not now" dama nasan haka zaice shi yasa na gayyace shi din. Yace "look at me " na daga kai ina kallon cikin idonsa da yayi kalar tausayi, yace "please in kinje gida call me, da akwai abubuwa da nake so in gaya miki" nace masa to amma still ya kasa tafiya nima kuma na kasa tafiya, sai ga Hafsat nan tazo tana kirana, dole na dauke ido na daga cikin nasa na dau hanyar gate ina hadiye kuka na. Ina jiyo shi yana bawa Hafsat amana ta, ga mamakina sai naji ta biye masa har suna dariya.