Maimoon

Episode Eleven: Latifat

by @mamanmaama

Ina zuwa class Hafsat ta taso take tambaya ta "well, what did he said?" Na kalleta da jajayen ido nace "it's none of your business" ta jima tsaye a kaina sannan ta daga kafada tace "OK, in tayi tsami maji" da ace ana sayar da maganin sa ido da saina sayo na bawa Hafsat. Two days suka wuce, zuciyata ta fara sanyi amma har yanzu ban huce ba. Ibrahim duk ya gama rikicewa saboda silent treatment da nake bashi. Amira kuma ta ja baya da komai, ta zama wata irin silent ba ta yiwa kowa magana, musamman ma ni. On the third day muna aji a zaune sai ga Ibrahim nan yazo, ya taho direct gurina ya tsaya a gabana yace da karfi yadda kowa a class din zaiji "nace miki I don't love her, what more do you want from me?" Gabadaya ajin kowa yayi shiru yana kallon mu ballantana su Hafsat sa ido. Nayi kasa da murya nace "what are you doing?" Ya kara daga murya yace "am telling everyone bana son ta ni ke nake so, ke kadai nake so" Wata Jamila tace "sir wacece? A ajin nan take? Cewa tayi tana sonka?" Na dan saci kallon Amira sai naga ta juya ma class din baya tana kallon waje, sai kawai naji zuciya ta ta karye, na dauki wani katon textbook na fara dukan Ibrahim da shi ina korar sa waje, amma yaki tafiya yace lallai saina fada masa cewa maganar ta wuce sannan zai fita, su kuwa 'yan aji sai kara tambayarsa suke ya basu labari. Da naga dai Ibrahim da gaske yake so yake yayi wa Amira tonon silili sai nace masa na yarda, maganar ta wuce, yace "kinyi alkawarin ba zaki kara tayar da maganar ba?" Nace "I promise" sannan ya juya ya fita. Yana fita Hafsat tace "well, dama nace in tayi tsami zanji, 'yan class din nan duk mai son yaji wacece yazo in gaya masa" nan da nan duk suka tafi gurin Hafsat, na kalli Amira naga alamar tsoro a fuskarta, nayi sauri naje gurin Hafsat nace "Hafsat dan Allah ki bar maganar nan" tace "sai kinyi min alkawarin daga yau aunty Hafsat zaki ke ce min" nace "done, Aunty Hafsat from today". Sai da muka je hostel sannan Hafsat tace "ni daga ke har Amira kun bani mamaki wallahi, ni banga abin so a jikin wannan dogon mutumin ba" nayi dariya kawai ba rabu da ita, amma maganar ta ta tsaya min a rai. A lokuta da dama mutum ba shi yake zabar wanda zuciyarsa zata so ba, kawai haka kawai zakaji kana son mutum, wani lokacin kuma daga kaga mutum sai kaji baka son sa, ba tare da yayi maka komai ba. Kamar yadda lokaci daya na ji zuciya ta tana son Ibrahim duk da irin banbancin da yake tsakanin mu kuma ba tare da wani dalili ba dan ba zan iya cewa saboda abu kaza nake sonsa ba, kawai dai nasan ina son sa. Da nayi considering Amira sai naga itama haka ne a wurinta, kawai taji tana sonsa ne amma saboda kusancina da ita ya saka ta boye a ranta har sai yanzu da suke spending time together sannan ta fara nuna masa, it must be hard on her, especially yanzu da yayi declaring a gaban kowa cewa baya sonta, sannan gashi gandantakar mu ta shekaru kusan shida tana so ta baci saboda kawai ta kasa controlling zuciyar ta. She deserves a break from me. Ina yin wanka na shirya sai na tafi dakinsu Amira, na tarar da ita a kwance idonta a rufe kamar mai bacci amma kana ganinta kasan ba baccin take yi ba. Na daka mata duka a cinya nace "sleepy head, ki tashi mu tafi karatu" ta bude idonta tana kallona da mamaki. Ita tasan na sani. A hankali tace "bana jin dadi ne" nace "yeah right, in kika fita zaki warke" a haka na takura ta tayi wanka muka fita. Tun daga nan muka cigaba da kawancen mu da Amira, amma duk abinda muke yi da Ibrahim yazo gurin zata tashi, ni ma kuma bana cewa ta tsaya saboda ta ciki na ciki daurewa kawai nake yi. Soyayya sabuwa muke shimfidawa da Ibrahim. Gani nake tunda na shiga SS3 ai I am old enough, shima kuma dama kiris yake jira. Sam Ibrahim baya kunyar nuna min soyayya ko a gaban waye ma kuwa, ni dai duk sai kunya ta rufe ni. Rannan a class ya zo yana cewa wai ya kasa bacci jiya kawai sai yaji muryata yake so yaji, wai saura kadan ya taho hostel, su kuma 'yan ajin sai su biye masa suyi ta tsokana ta, inna ga sun dame ni sai in tashi in bar musu ajin. Rannan muna a gaban chemistry lab muna duba past questions and answers na WAEC sai muka hango Ibrahim da wasu mata su biyu a gaban staff room, Hasiya ce ta taba ni tace "kinga mutumin ki can, ko suwa ya samu kuma" ina dubawa naga mata ne su biyu da kaya a hannun daya, dayar daga gani babbar macece dayar kuma budurwa, budurwar da hijab matar kuma da babban mayafi, sun jima a tsaye suna magana sai naga ya karbi kayan hannun budurwar ya wuce gaba suna binsa a baya suka tafi staff quarters. Har dare ban kuma ganinsa ba kuma ina ta tunanin ko su waye wadan nan? Washe gari da safe sai gashi yazo yace min inzo, muna fita waje sai yace "there is someone here that wants to see you" gaba na ya fadi nace "who?" Yace "my Mother" Nan da nan naji wani tashin hankali yazo min, he wants me to meet his mother? this is serious. To ni yanzu da wacce fuskar zan je mata? Kuma me zance mata? Nace masa "Ibrahim am sorry, I can't" ya bata fuska yace "why can't you?" Nace "tsoro nake ji" dariya yayi yace "tsoron me kuma? Bata cin mutane, besides tare zamu je, just ku gaisa shikenan" na kalli kayan jikina, uniform ne a wanke a goge, hijab dina ya rufe har ko'ina, fuskata babu kwalliya, dama ba kwalliyar nake yi ba. Na sake kallonsa har yanzu da dariya a fuskarsa. Yace "you look great, let's go" yana fadin haka ya shige gaba, na bishi a baya kamar wadda kwai ya fashewa a ciki. Direct visitors room muka je, ya dan tsaya yana kallona yace "are you ready?" na girgiza kaina alamar no, yayi dariya kawai ya bude kofar da sallama. Nima nayi sallama na shiga. Su biyu ne kamar jiya da babba da karama. Ina kallon babbar nasan ita ta haifi Ibrahim sai dai bata kaishi tsaho ba, karamar kuma sam basa kama dan ta fishi hasken fata sosai, dan da kadan zan nuna mata fari, sai dai ita fuskarta duk kuraje da alamar wahala yayin da tawa take tas da alamar hutu. Kana ganin maman su Ibrahim kaga typical yoruba woman. Da daurin zanin ta akan riga, da gwoggoro akan ta. Ibrahim ya zauna a kusa da ita ni kuma na durkusa daga nesa a kasa na gaisheta da turanci. Ta amsa min amma daga gani turancin ba isar ta yayi ba. A raina nace oho dai ni ba iya yarabanci nayi ba sai dai mu tsaya daga gaisuwar. Na gaishe da dayar tunda daga ganinta nasan ta girme ni. Ta amsa tana dariya, na dago kai sai naga Ibrahim ne yake hararar ta, ya wani dora kafa daya akan daya. Maman su kuwa idonta yana kaina. Sai da muka dan jima a haka sannan Ibrahim yace "Maimunatu this is my mother, and that girl over there is my sister" da saurin ta tace "his step-sister" na dago kai na kalleta sai naga idonta a kansa, bansan dalili ba sai naji hankali na bai kwanta ba da kallon da take masa. Mamansu naji ta fara magana da gurbataccen turancinta "Any day I dey called Ibrahim all he talks about is Maimunatu this Maimunatu that, and if I complain about him not coming home for weekend he will say they dey study with Maimunatu, every time na Maimunatu him dey talk about. I then say make I come see this Maimunatu with my own eyes" Naja hijab dina na rufe fuskata, inaji tana masa magana da yarabanci, naji dai tace fulani a ciki, sai naji yace "mu fa yoruba ba'a wani kunyar suruka, in zaki bude ido ki bude, dan duk randa kika haihu ita zata yi miki wanka" Na kara dunkule wa a guri daya a raina ina cewa kai Ibrahim mai ya kawo zancen haihuwa kuma? Gaba daya suka yi dariya. 'Yar budurwar ce tayi magana da turanci tace "let me introduce myself properly, ni step sister dinsa ce, babana ne mijin mamansa, sunana Latifat, but can call me Lati, nazo in taya shi assessing saboda nasan ba iya zabe yayi ba. Dama tunda naji Mama tace Fulani nace sai nazo nagani da kaina, gashi kuma naga kinyi kankanta da yawa" Ibrahim yace mata "shut off" sannan yayi mata magana da yarabanci itama ta mayar masa, sai maman tayi musu magana duk sukayi shiru. A hankali maman tace min "your parents nko? Where they?" Nace mata "they live here, in Abuja" tace "dey from Abuja?" nace "'no, Jigawa" kawai sai naji matar tayi min, yadda take magana a hankali irin maganar Ibrahim. Latifat ce dai hankali na bai kwanta da ita ba. Ibrahim ne yace zai mayar dani class dan muna karatu, Latifat ta sake yin magana da yarabanci shi kuma ya sake ce mata shut off maman tayi tsaki tana kallon Latifat da alamar warning. Tunda muka fito bamu yi magana ba sai da muka dan yi nisa sannan yace "how much do you like my mother?" nace "she is OK, you look like her but taller" yace "no, she always say da baban mu nake kama" Har nayi tunanin kar in tambayeshi akan Latifat amma sai zuciya ta ta kasa jurewa, nace "Your sister doesn't like me" yayi dariya yace "yours doesn't like me either" nima nayi dariya sannan nace "but this is different, I felt like there is some tension between you two" yayi shiru bai bani amsa ba, wannan ya tabbatar min da zargina. Nan take naji raina yana kuna. Sai da muka kusa zuwa class sannan yace "koma menene da a tsakanina da Latifat is over tun tuni, abinda yake tsakanin mu sam bashi da dangantaka da Latifat. Amincewar Mama da Baba kawai nake bukata. Please Maimunatu Mama tazo takanas saboda ta ganki, please show her your best behavior yadda in taje zata bawa baba labari shima zai yaba dake, please don't let Latifat get in your head, that is exactly what she wants" muna zuwa gaban class din mu nayi shigewa ta ba tare da nace masa komai ba. Har na zauna yana tsaye a gaban class din ya rungume hannayensa fuskarsa da alamar damuwa. Bayan na zauna sai nayi tunanin ban kyauta wa Ibrahim ba, kuma gaskiya ya fada cewa this is our chance, ya kamata inyi kokari inyi probing to his mother cewa I am good enough, inna bari kishi ya shiga raina tun yanzu to ina da problem. Washe gari da yamma muna kofar library da Amira da wasu kawayen mu sai ga Ibrahim sun taho gurin mu shi da Lati, tun daga nesa nake kallon yadda take ta shishshige masa, gaba daya kowa ya tsaya yana kallon su har suka kara so. Kallo daya nayi masa nasan ransa a bace yake. Suna zuwa yayi introducing dinta generally, sannan yace "she said she wants to look around the school" nayi sauri nace "she is welcome" tare da miko mata hannu, ta kalle ni sannan ta kalli Ibrahim kamar me neman izni shi kuma ya dauke kansa ya juya ya tafi, tayi masa magana da yarabanci bai amsa mata ba, ya saka hannayensa a aljihun wandon sa yayi tafiyarsa. Yana tafiya na fara yi mata hira, nayi mata introducing duk friends dina da suke gurin. Amira ko kallon ta bata yi ba. Daga nan nace tazo in showing her around, tun daga classes, labs, kitchen, dining hall duk sai da na kaita, sannan na kaita hostel. Hafsat tana kwance muka shiga, ta bimu da kallo, sannan tace min da fulatanci "wannan kuma a ina kika samota?" Na amsa mata da turanci "she is Ibrahim's step sister" sannan na kalli Lati nace "this is my Sister, Hafsat" Lati tace "oh my God she is so beautiful, nice to meet you" ta mika wa Hafsat hannu, kirikiri Hafsat ta ki bata hannu tace da cewa da fulatanci "ni bazan taba hannunki ba, kurwata kur, in mayya ce ke kici kanki ki sha baƙin ruwa" nayi dariya, Lati tace "what did she said?" Nace mata cewa tayi "ai kin fita kyau ma" nan da nan ta washe baki tace "thank you" Hafsat ta harare ni. Nan da nan Efi ta fara santin dakin mu, wai wannan ai ko a gida sai haka, ita in tana nan ai ba zata so ayi hutu bama. Nan da nan na chika mata gabanta da kayan chiye2 muka zauna muka yi ta hira, tana bani labarin gidan su. Amma ni bance mata komai ba akan namu gidan. Har akayi sallar magrib muna tare can sai Ibrahim ya kira ta yace ta fito su koma gida, haka kawai sai na samu kaina da jin babu dadi saboda ya kira ta a waya. Na dauko wani set din toiletries na mu na dove na saka mata a leda na bata. Tayi ta mamaki wai ina student har nake kyautar kaya? Washe gari Ibrahim yace min zasu tafi, na hado sweets da biscuits masu yawa a leda na boye a hijab dina saboda 'yan sa ido, yazo ya kira ni muyi sallama da Mama. Ina shiga na gaishe ta, ta amsa min da sakakkiyar fuska sosai tayi min fada akan karatu, naji dadi har raina, na dauko leda ta na bata nace a kaiwa Abdullahi da Abdulrahman, kananan kannen Ibrahim. Taki karba na ajiye mata a gabanta na tafi. Da daddare Ibrahim yazo yana ta fada wai me yasa na kashe kudi na sayo kaya? In ina son in basu basai inyi masa magana shi ya sayo musu ba? Shi ya dauka siyowa nayi. Bayan kwana biyu sai gashi da kaya niki niki ya kawo min. Sanda muka fara SSCE kullum in mun shiga exam Ibrahim zai zauna a kofar hall din ya jira ni, har sai na fito ya tambayeni ya paper sannan zai tafi. A lokacin ya koya min jin kida, zai kunna slow music ya saka ear piece a kunne daya ni ma in saka kunne daya muna ji tare. Shakuwa ce sosai kullum take kara shiga tsakanin mu. Har tararradin ranar da zamu gama paper nake yi. A week to gama papers din mu PC ta kira ni tace federal government ta aiko a bada sunan best student za a biya mata scholarship zuwa university of her choice. Dan haka tana sanar min cewa sunana zasu bayar. Nayi shiru ina tunani. I don't need the scholarship, Daddy zai iya biya min karatu zuwa kowacce kasa nake so. Scholarship is meant for bright students din da iyayensu ba zasu iya biya musu school fees ba. Kawai sai Amira ta fado min a rai. Nan take nace da pc na barwa Amira, asaka sunan ta instead of sunana. PC ta nuna bata ji dadi ba, I am the best student that they ever had a school din. Nace mata to tayi contacting Daddy ta sanar masa, duk abinda yace shikenan. Ana gobe zamu yi graduating Ibrahim ya kira ni yace zamuyi magana. Muna zama na lura he is serious. Yace "Maimunatu in kunje gida ina so zanzo in nemi iznin neman auren ki a gurin daddyn ku" zuciya ta ta buga da karfi na kalle shi da budaddun ido, yace "yes, ina so in samu permission dinsu saboda insan in da na dosa, just pray for us" I hope you enjoy this episode. Put on your seat belts because the next episode is going to blow you away.