Maimoon

Episode Twenty : Zayed

by @mamanmaama

Tun daga ranar Mahdi ya zama best friend dina, in har ina cikin asibiti to muna tare dashi, rannan muna zaune dashi nace "dan Allah Mahdi in tambayeka" ya cire glasses dinsa yana kallona yace "ina jinki" nace "dan Allah da gaske kai bahaushe ne? I mean biologically?" Straight yace min "no, babana adopting dina yayi" da sauri nace "yes!! I knew it" dariya yayi sosai har yana buga kafa sannan yace "wasa fa nake miki, serious ni bahaushe ne, why do you doubt it?" Sai naji kunya kuma nace "kawai dai ba kayi kama da hausawa ba" yayi shiru sannan yace "my mother was shuwa arab, ni kadai ta haifa Allah yayi mata rasuwa, so.... I am different duk a family, wannan shi yasa na taho kasar waje karatu, I want to feel like I belong, a gida kullum kamar alien nake ji na a cikin siblings dina" na sunkuyar da kaina inajin ba dadi, ace ka zama kamar bare a cikin 'yan'uwanka babu dadi, nace "am sorry about your mom, am sorry I asked you" yayi murmushi yace