Maimoon

Episode Twenty One: When Destiny Calls

by @mamanmaama

Daddy ya tashi ya shige daki. Yana shiga Hafsat ta mike ta fada cinyar Mommy ita kuma ta rungume ta suna dariya, nima dariyar nake yi amma ta yaqe ce, maganar Daddy ce take yi min yawo aka, tabbas nasan Munnir bashi da niyyar hakura, kuma nasan in har na gama school bani da wani sauran excuse, ballantana yanzu idan iyayen Zayed suka je neman auren Hafsat kowa kuma hankalinsa dawo wa kaina zaiyi. Ina cikin wannan lissafin naji maganar Mommy wacce ta sake daga min hankali "ai naji yace ma indai har su Baffan sun amince acikin hutun nan naku yake so ayi komai a gama, in yaso kya karasa project dinki a gidan sa, kinga nan da baifi wata biyar ko shida ba za'a gama komai" Hafsat ta boye fuskar ta a cinyar Mommy wai ita kunya, su yaya Habeeb suna ta tsokanarta da amarya, ni kuwa, shock din maganar ne ya daskarar dani a inda nake zaune, Mommy ta kara da cewa "ni dai kam ni aka tasa a tsaye, lokacin yayi min kadan gaskiya, saboda ni plan dina shine nan da kamar shekara biyu masu zuwa, so nayi yadda kuka taso tare ke da Moon in hada ku rana daya in aurar daku shikenan" I have heard enough, na mike zuciya ta tayi min nauyi na kama hanyar fita, ina jiyo su suna ta making plans, Mommy ta kira Daada a waya tana gaya mata. Ina fita part dinmu na shiga, sai kuma na rasa me zan dauka, sai kawai na dauki hijab dina na saka na kama hanyar gate. Ni kaina bansan inda zani ba, I just want to get away for a while. Baifi saura wata biyu ya rage mana muyi hutu ba, muna yin hutu zamu tafi Nigeria. Allah ne kadai yasan irin abinda zan fuskanta a can. Dan jiki na yana bani Baffa zai iya cewa a hada aure na dana Hafsat, da zarar nace bani da saurayi kuwa za'a ce ai ga munnir nan yana ta zaman jira. Allah ya gani bazan iya auran munnir ba. I despise him. To ko Mahdi zan lallaba ne? But I don't love him and I will end up hurting him. Ya Ilahi. Ina fita gate na hango motar Zayed a gurin da yake tsayawa in yazo gurin Hafsat. Na juya na fara tafiya in opposite direction, ina jinsa yana horn kuma nasan dani yake amma naki juyowa. Ban ankara ba sai ganin mota nayi a gaba na, yayi winding glass din motar ya kalle ni da murmushi a fuskar sa "beautiful one ina zaki je ne haka ke kadai kuma a kafa?" Nayi niyyar inyi banza in rabu dashi tunda duk shi ya ja min daya dauko maganar auren Hafsat amma kuma sai na kasa, it is not in my nature wulakanta mutane. Na karasa kusa da motar sa nace "nan baya zan je ba nisa" daga yadda yake kallona nasan bai yarda da maganata ba, ya bude kofar motar yace "shigo in kai ki" na danyi jim sai kuma na shiga. Ina zama yace "What is wrong" kawai sai jin hawaye nayi yana zubo min, nayi sauri na rufe fuskata da hannuna na fara kuka. Ya gyara packing din motar ya zauna, bai ce min komai ba, bai kuma rarrasheni ba, sai da nayi kuka na me isa ta sannan na buɗe fuskata ina goge idona da hannuna, ya miko min box din klenex, sannan ya sake tambayata "what's wrong?" Nan take na fara bashi labarin tun farkon haduwar mu da Ibrahim, aikin da na saka Daddy ya samo masa, graduation din mu, yadda ta kasance ranar da yazo gidan mu da tafiyarsa, dawowarmu England da labarin aurensa, na kara da cewa "har yau babu shi babu labarinsa, he might be dead for all I know. Amma na kasa chire shi daga raina, na rage tunaninsa amma na kasa mantawa dashi, and now I realized that I can't fall in love again" sannan sai na bashi labarin Munnir, na kuma bashi labarin Mahdi. Na kara da cewa "yanzu muna zuwa Nigeria aka fara maganar ku da Hafsat, shikenan hankalin kowa zai dawo kaina, ko dai in fito da miji, which I don't have, ko kuma a aura min Munnir, who I don't love". Nayi shiru idona a lumshe ina sauraren yadda zuciyata take bugawa. Zayed yayi gyaran murya yace "do you want the truth? Or you want something that will make you feel better?" Ba tare da na kalle shi ba nace "the truth" A hankali yace "He is not coming back" Na juyo da sauri na kalleshi ya gyada min kai tare da maimaitawa "he is not coming back" na dauke kaina na daina kallonsa, ya cigaba da cewa "he left because he is weak and unsure of himself, yes, sanda ya tafi maybe yana da niyyar dawowa sanda yaji he is strong enough, auren sa ya kara rage chances dinsa of coming back to you saboda matarsa zata yi iya kokarinta wajan janye hankalinsa daga kanki, da zarar ta haihu kuma shikenan hankalinsa zai kara karkata kan 'ya'yansa. After almost five years kuwa the chance of him coming back to you is zero percent. Dole ki saka a zuciyarki kuma ki yadda da fact that he is not coming back. Abu na farko kenan. Abu na biyu shine, dole kiyi opening heart dinki for another man. Love at first sight is very rare dan haka idan guy yace yana sonki kamata yayi ki bashi chance, get to know him sannan zaki san cewa you can love him or not. You are very young and very beautiful Moon, your life is just starting, kar ki bar wani can da maybe ya manta dake yayi ruining happiness dinki. Open your heart to both Munnir and Mahdi and whoever else comes your way. Kina jina Moon?" Na gyada kaina yayinda wasu siraran hawaye suka biyo kuncina. Ya cigaba "daga duk kan stories dinki da nake ji a gun Hafsat, na fahimci cewa you have a good heart, mutane like you, I mean people with good heart sun fi kowa facing challenges a rayuwa akan harkar aure, kasuwanci da sauran al'amuran rayuwa saboda Allah yana testing din su yaga how good they are saboda He is saving something good for them" Tunda muka yi magana da Zayed sai naji tamkar an sauke min wani nauyi daga kaina, maybe dama I needed someone to talk to. Naji na samu confidence na facing ko menene yake tahowa gareni ko da kuwa auren Munnir ne. Kafin mu rabu ranar sai da ya saka nayi masa alkawarin duk halin da nake ciki zan ke zuwa ina gaya masa. Ina zuwa asibiti na samu Mahdi nace masa ni fa bana jin dadin yadda muke yi yanzu, ina so mu koma kamar da, ya nuna min cewa komai ya wuce, nan muka cigaba da al'amuran mu kamar da. A gida kuwa Mommy sai shirye shirye take yi, daddy kuma yayi waya Nigerian embassy da ke UAE ya basu information din Zayed ya saka suyi masa bincike akan sa da family dinsa. Hafsat da Zayed kuwa sun dage sai ɗiga soyayya suke kamar zasu chinye juna, in na gan su sai inyi ta sha'awarsu, both gentle, kuma Hafsat duk rashin kunyar ta in suna tare sai inga tayi laushi, dan ko harara ta zata yi sai taga baya kallonta tukun. Mun kallama clinicals din mu an sallamemu daga asibiti muka koma school, inda acan ne aka bamu project topics wanda kowa ake so ya kammala acikin shekara daya. A bangaren psychology da nake yi ne coordinator din mu ta bani wani strange topic. Abinda tace shine "kowanne mutum yana da sides guda biyu, da akwai side din da yake in the light da akwai kuma side din da yake inda dark. Shi light side din shine wanda mutum yake nunawa kowa yana gani, ma'ana, dabi'unsa da kowa ya san sa dasu. Shi kuma dark side din shine wanda mutun yake boyewa, ma'ana, dabi'unsa wadanda ba kowa ne ya san sa dasu ba. Wannan side din shi ta kira da shadow, kowa yana dashi amma ba'a ganin sa sai mutun ya fito cikin haske. Naturally da akwai mutanen da suke iya boye dark side dinsu yadda babu wanda yake gani, even if you are a psychologist you have to look very deep kafin ka gani. Confused? Kar ku damu kawai dai an bani project a psychology. Task dina shine in samo irin wadannan mutanen in binciko shadow side dinsu, ba tare da sun san ina bincike akan su ba. Hint din da ta bani shine, most of them are attention seekers, saboda suna son su nunawa mutane light side dinsu yadda ba za a ga shadow side din su ba. Don't worry, zaku gane later. Da haka muka tattara ina mu ina mu sai Naija. Muna zuwa Nigeria kamar yadda aka tsara haka ce ta kasance, an bawa su Zayed rana kuma sunzo, a Abuja suka sauka daga nan Daddy zai saka a raka su 'yalleman. Babu yadda Daddy bai yi dasu ba akan su sauka a gidan mu amma suka ki, suka sauka a hotel. Shi kuwa Zayed dama direct nan ya taho, ko kunya baya ji, ya sauka a dakin ya Walid, nan Hafsat aka hau hidimar yi masa girki kala-kala. Kwanan su daya a Abuja suka tafi 'yalleman da ya Walid da wadansu abokan Daddy su biyu. Ranar da suka tafi Hafsat kwana akayi ana sallah. Washegari Amira tazo muka hadu muka saka Hafsat a gaba da tsokana. Nayi mamaki da naji Amira ko mentioning Ibrahim bata yi ba. Zuwa wajen la'asar Zayed ya kirani a waya yace "congratulations, I am going to be your brother inlaw in the next two months" nan na yar da wayar ina ihu, Amira da Amina suka biye min Hafsat kuwa ta shige toilet ta rufe kanta. Shirye2 ake yi sosai na bikin Hafsat, tun ana saura sati biyu gidan mu ya fara cika, mutanen Niger sunzo sun sauka a part din Daada. Amira kusan kullum sai ta zo mun yi namu plans din, ita kuwa Hafsat ba abinda ya dame ta na shirin biki, soyayyarta kawai take zubawa. Zayed ya kira ni ya tambaye ni yadda al'adar mu take na harkar biki, wai ya tambayi mutuniyar taƙi ce masa komai, nayi masa bayani dai dai misali, nan ya saka ni na yi gaya masa sizes din kayan Hafsat da zai saka a lefen da na gaya masa anyi, dan yasan ita ba fada zata yi ba, duk na kwashe abinda na sani na gaya masa. Duk wanda yazo gidan sai yace "dama tare aka hada da Moon da shikenan an huta" a raina sai ince "in kun kawo min mijin ba sai kuyi min auren ba". Mommy ta zage dantse sai siyayya take yiwa Hafsat kamar babu gobe, kayan fitar biki akwati set guda Mommy tayi mata, nima kai na da ba amarya ba na sha kaya har sai da na gode Allah. Mun tsara mu kawaye za muyi bridal shower da dinner, Mommy zasu yi kamu, kunshi da mother's evening, daga nan kuma sai ayi daurin aure. Familyn Zayed suma sun shirya bridal welcome dinner wacce za'ayi a can England in an kai amarya. Tun maganganun mutane basa damuna akan Hafsat zatayi aure ta barni har suka fara damuna, ga hidimomi sunyi min yawa, ga surutun mutane. To rob salt to my wound sai ga Munnir nan yazo tun biki saura sati daya. Ina daki ya kira ni naki dauka, sai ya kira Amina, ina jinsu suna magana sannan tace min "Moon angonki yazo" ji nayi kamar ta watsa min ruwan zafi, nace "in kin gaji da ganin sa babu aure ke ba sai ki aure shi ba" tayi dariya tace "mai da wukar, ni 'yar aike ce. Allah da gaske nake yace kije yana compound" nayi tsaki na gyara kwanciyata a raina nace "ai gidan ba bakonsa bane, kuma shi ba makaho bane" Shikenan kuma yanzu mutane zasu kara takura min, shima kuma zai kara takura min, duk burin da naci na bikin nan bana jin zan ji dadinsa, na sake tsaki na ja bargo ina neman bacci amma yaki zuwa. Tun sanda mukayi magana da Zayed nake kokarin inga ko yaya ne na saka son Munnir a raina amma na kasa, tun ina yarinya bana son sa duk abinda yayi haushi yake bani, He is so arrogant and selfish. A hankali bacci ya fara dauka na. Kamar daga sama naji ance "out, all of you" nayi sauri na bude ido na saboda naji muryar tayi kama data Munnir. Na mike zaune da sauri kawai na ganshi a tsaye a tsakiyar dakin yana korar Amina da Amira. Ina ma Hafsat tana nan dan nasan bazata fita ba. Da sauri na fara neman abinda zan rufe jikina dashi, suna fita yayi locking kofa lokacin na samo hijab ina kokarin saka wa, cikin taku biyu ya karaso inda nake ya warce hijab din yana tsareni da ido, cikin gadara yace "dan baki da kunya shine na kira ki kika ki dauka, na aiko ace kizo kika ki zuwa ko? Who the hell do you think you are? Kin manta akwai alkawarin aure na a kanki? Badan wannan uncle Aliyun ya hana ba da tare Baffa yace ayi dana Hafsat, ni dai Allah ma ya sani ana shiga hakkina" Na tattaro duk bravery dina cikin bacin ran shiga privacy dina da yayi nace "to in an shiga hakkin ka ka nemi wata matar ka aura mana? Ko ni kadai ce mace a duniya? Ba lallai ba dole kayi hanyar ka inyi tawa" Yana kallona da mamaki yace "me yasa ba kya sona wai" direct nace "baka yi min ba" maimakon yaji haushi kamar yadda nayi tsammani sai naga yana murmushin mugunta "don't worry, I will surely change that duk ranar da aka kai min ke, you will begin to like me then" ya fada yana lasar lebensa, nayi sauri na dauke ido na daga kansa ina kara jin haushinsa, ji nayi bai sake magana ba na dago na kalleshi, idansa na gani kyar akan kirjina, na maka masa irin hararar da nake ganin Hafsat tana yiwa mutane nace "fita mun daga daki Malam" ya sake murmushi still idonsa a kaina yace "in anki fa? Me zakiyi?" Nace "zanyi maka ihu in tara maka mutane" yace "kinga shikenan dole a aura min ke tunda mun bar abin faɗi ni da ke, ba za'a ce Munnir kadai ba cewa za'a yi Munnir da Maimoon aka kama a daki" Nayi kamar banji abinda yace ba na sake maimaita wa "ka fita min a daki ko in yi maka ihu" ya daga pillown kusa da ni ya zauna akan gadon tare da dora kafa daya akan daya sannan yace "you wouldn't dare" ban jira komai ba na dage da karfina nace "moommmyy......" Kafin in kai karshe ya bude kofar ya fice da saurinsa. Nabi kofar dakin da harara nace a raina "ashe dan iskan karya ne kai, ka jira Mommy tazo kaga yadda zata yi da kai" Da yake kofofin gidan sound proof ne sai ya kasance babu wanda yaji ihu na, ni kadai nasan abinda ya faru. How can I marry a man like that? Clearly ba so na yake ba sha'awa ta yake kawai. Ranar Wednesday ita ta kama ranar da za'a fara biki, ranar ce ake yin kunshi da bridal shower, Thursday za'ayi mother's eve da kamu, friday su Zayed za su zo shi da friends dinsa za muyi dinner, Saturday da safe za'a daura aure daga nan za'a tafi a akai amarya. Amarya kam tasha gyara ciki da waje, from head to toe, nima kuwa banda gyaran cikin, duk wani gyara da akayi wa Hafsat na waje to anyi min nima, dan haka jin mu muke yi on top of the world. Tun safe 'yan yalleman suka fara isowa, duk wadanda suka zo sai sun bata min rai "amaryar Manniru, amaryar Manniru" duk sai inji farin cikin da nake ciki ya kau, dan ma dai ni ba mai iya bacin rai bace. Tun safe masu kunshi suka zo duk aka fito compound din gidan ana ta kunshi, ja da baki, Amarya aka fara yiwa nata sannan mu, sannan sauran mutane. Anata hidimar kunshi har yamma sannan mu kuma muka fara hidimar bridal shower din mu. Abin ya tsaru sosai domin Amira akwai iya tsari, amarya tayi kyau a cikin gown army green ta rike pink roses an dora mata pink crown akanta, mu kuma duk munsa gown light pink da light green din jaka da takalmi. Ana tsaka da hidima naji karar waya ta ina dubawa naga uncle Aliyu. Gaba na ya fadi, na koma can gefe inda babu haya niya na dauka na gaishe shi, ya amsa min cikin kulawa sannan yace "Maimunatu tunda aka kawo zancen maganar auren Hafsat gabadaya gida ya hargitse akan maganar auren ki kema, Hajja ta dage akan lallai sai an hada anyi auren ku tare" Numfashina ne gaba daya naji yana neman daukewa, jiri naji yana dibana, "ya Allah" na furta a hankali, yace "ki kwantar da hankalinki, na samu na shawo kan Baffa, nayi masa bayanin cewa ita Hafsat mijinta acan England din yake da zama, ke kuma in akayi miki aure za'a dora miki nauyin aure ne har tsahon shekara guda kafin ki tare da mijinki. Na samu ya yarda sai next year in kin gama project din ki" Wata ajiyar zuciya na sauke wacce karfinta sai da yasa na durkushe a gurin, ya cigaba da cewa "Moon kar ki bani kunya don Allah, kinga na kara nema miki lokaci, ki daure kafin lokacin ya cika ki fito da mijin aure, kin san halin Munnir ba sai na gaya miki ba, Munnir ya wuce duk inda kike tsammani, daga ni har yaya Ambassador bama son hadin nan amma in har kika gama makaranta ba tare da wani tsayayye ba to dole mu bari a aura miki shi". Gaba daya naji taron ya fita daga kaina, muka yi sallama dashi na koma gurin taro amma sam hankali na baya jiki na. Na tsaya kusa da Hafsat kenan muna yin pictures naji hayaniya ta karu, ina juyowa naga Munnir ya doso inda muke fuskarsa dauke da wannan murmushin nasa da yake karamin tsanarsa. Ideally maza basa zuwa bridal shower saboda kayan da ake sakawa masu bayyana jiki ne, to shi in banda iskancinsa mai ya kawo shi? Yana zuwa kusa dani ya bude rafar yan 1000 yana watsa min, ya gama abinsa yace "kinyi kyau, my darling" sannan ya juya ya fita yana wani takun bada fadi wai shi yana ganin ya hadu. Wani tukuki naji a raina saboda ganin duk gurin ni ake kallo daga masu dariya kasa kasa sai masu rada a tsakanin su. A hankali na janye jikina na shige cikin gida. Direct dakin mu na shiga na zauna bakin gado na rufe fuskata da hannayena "Ya Allah, ka bani yadda zan yakice wannan bawan naka daga gareni, Allah ka kawo min mafita. Ina haka naji hayaniya ana hawowa, cousins din mu ne wajan su biyar suka shigo, ciki har da kannen Munnir su biyu, suna shigowa Nusaiba tace "Maimuna ta Munniru, Maimuna ta Munniru" nan take sauran suka dauka suma. Da ace ina da bindiga zan iya harbe su amma su sunki su gane. Na juya da nufin fita kenan aka bude kofar, Amira ce tare da wasu daga cikin kawayen mu na sec sch, suna shigowa Hasiya tace "Moon wai da gaske wannan mutumin zaki aura wai? Ina uncle Ibrahim?" Na juya ba tare da nace mata komai ba, har na kai kofar toilet ta sake cewa "Moon ina Ibrahim?" Na murda kofar toilet din na shiga na rufe. I was Finally alone. Direct shower na shiga na kunna da complete kaya a jiki na har takalmi na ban cire ba, na lumshe ido na ina addu'a a zuciyata "ya Allah ka bani ikon cin wannan jarabawar, Ya Allah idan wannan shine zabinka a gareni ka bani karfin zuciyar dauka, Allah kaine Allah, Allah kayi min jagora zuwa inda yake mafi alkhairi a gareni" nan na fara amfato sunayen Allah, ban fito daga shower din ba sai da na gama su duka 99 din. Ina fitowa na cire kayan jikina na daura robe na koma dakin, har yanzu a cike yake ana ta hayaniya, kayana na diba na koma toilet, doguwar riga ce ta atamfa purple da white, rigar ta kama jikina daga sama, daga kasa ta bude sosai, ban daura dankwali ba na dauko farin veil na yi rolling, na fesa turare. Ji nayi gaba daya zaman gidan ya ishe ni, kamar duk mutanen da suke cikin gidan basa kaunata. Sama sama mukayi magana da mutanen dakin na fice, falo ma a cike yake, compound ma duk samari ne da 'yan mata ana ta hira ana raha, addu'ah nake tayi a raina Allah yasa kar Munnir ya ganni, can na hangoshi ya ritsa wata yarinya amma ban gane fuskar taba, ni dai na wuce su da sauri nayi gate, sai ranar nayi nadamar ya akayi ban koyi mota ba, na duba agogon waya ta naga 9:00pm. Ina ta tafiya har na isa bakin titi na tari taxi nace ya kaini Hilton. Ni kaina bansan dalilin da yasa nace akaini can ba. Muna zuwa na zarce restaurant dinsu na samu guri acan wata corner na zauna. Waiter tazo ta kawo min menu nace ta kawo min tea kadai. Banfi minti goma da zama ba ya shigo gurin. Yana fitowa daga revolving doors din ya tsaya yana kalle-kalle. Kallo daya nayi masa nasan tabbas nasan wannan fuskar, amma na kasa tuna a ina nasan shi. To ko a England ne? Yana tsayawa naga securities out of nowhere sun bayyana a gurin, amma basu ce masa komai ba, they just looked ready. Na cigaba da kallonsa daga inda nake zaune, a half breed, half african half something else. Gashin kansa a hargitse kamar wanda ya tashi daga bacci, rigarsa tayi squeezing itama, body hug ce wadda ta kama jikinsa sosai ta fito da kakkarfan kirjinsa, damatsensa da suke a bayyane a mummurde suke kamar wanda yake wrestling kullum (who knows?). Bashi da tsaho sosai amma ba za'a ce masa gajere ba. Ya saka hannunsa a cikin gashinsa yana dan sosawa kamar mai tunanin wani abu hakan yasa muscles dinsa sukayi flexing, nayi sauri na dauke kaina, zuciya ta naji tana bugawa. Who is this? I know him but where?