Episode Twenty Two : The Rogue
by @mamanmaama
Na sake daga ido na na kalle shi naga still yana tsaye a inda yake, sai dai ya saka hannayensa a aljihun wandonsa yana karewa gurin kallo, as if he owns the place. Securities ne masu sanye da kaya masu tambarin Hilton suke ta kara shigowa cikin restaurant din, sai a sannan na lura cewa kusan rabin mutanen gurin shi suke kallo amma shi daga dukkan alamu bai ma san anayi ba. Ba zato ba tsammani kawai sai ganin idonsa nayi cikin nawa, nayi sauri na dauke kaina na wayance da daukan kofin tea na da ya kusa sandarewa na kurba. A lokacin ne naji wani security a kusa da inda nake zaune yana yin waya "oga mutumin ka ne fa ya shigo yanzu, eh shi kadai ne yallabai, gamu nan duk mun shigo ciki muna observing dinsa in case ko zai yi halin nasa. Ok sir" na tabbatar akan mutumin da ya shigo yanzu ake waya, a raina nace "interesting, so you are a trouble maker". Na sake kallon inda yake tsaye sai naga kamar wanda na kira shi, ya juyo direct ya taho wajan table dina. Nayi sauri na dauki cokali na fara juya tea dina duk da cewa babu abinda na kara a ciki, zuciya ta kamar ta fito waje, na shiga uku, kodai mutumin nan baya son kallo ne kuma yaga ina ta kallonsa shine zai zo ya kwada min mari? Na kasa daga ido na ballantana in tabbatar gurin nawa ya taho. "Assalamu Alaikum" a firgice ba dago kaina, na kuwa ganshi a tsaye a gaba na. Duk yadda naso in hana kaina kallonsa amma na kasa dauke ido na daga fuskarsa. Fatarsa chocolate ce mai haske, misali ace ka hada coffee ka zuba masa ishashshiyar madara, tas take cike da alamar kulawa da jin dadi. Tunda nake ban taba ganin idanu masu kyau irin nasa ba, farare ne tas masu maiko, bakin ciki kuma ba baki bane ba, light brown ne, wannan ne ya kara tabbatar min da cewa ya hada jinsi da fararen fata. Girarsa mai yalwar gashi ce, lips dinsa jajawur tamkar ya shafa jan baki mai turuwa. Fuskarsa ba mai tsaho bace ba kuma bata cika fadi ba, tana zagaye da kwantaccen saje wanda ya sha gyara. Gashin kansa a hargitse, amma daga gani kasan ba gashin hausawa bane. Finally na dauke ido na daga kansa na cigaba da aikin juya tea din da yake gabana, ina jin kamar zuciyata zata fado cikin kofin gabana, sai da nayi gyaran murya sannan can kasan makoshi na amsa masa sallamar sa "Amin wa alaikassalam" Yace "mind if I join?" Mind If I join? Wani ya taba gayamin exactly wadannan words din. Ibrahim, a library, maganar da muka fara yi daga ni sai shi ranar da naki zuwa class dinsa. Na kirkiro murmushi, at least ba mari na yazo yayi ba, nace "bismillah, zauna babu wani abu" sai da ya zauna sannan na tuna cewa har yanzu fa juya tea nake yi. Na dauki kofin na cigaba da sha, da shi da ruwan fanfo basu da maraba sai sugar. Na dan saci kallonsa ta saman kofin hannuna kawai sai muka hada ido shima yana kallona, a tare muka yi sauri muka dauke kai. Ya danyi gyaran murya yace "so.. Me zaki ci?" Na nuna masa kofin hannuna nace "tea nake sha" ya wani bata fuska kamar abin kyankyami yace "tea? Are you telling me kin baro gida kin taho nan dan ki sha tea? In fact restaurant din nan ma basu iya tea mai kyau ba, what is so special about it?" A takaice nace masa "bana jin yunwa ne shi yasa" wani murmushi yayi min wanda sai da naji shi har kafafuwa na yace "in kika ga abinda zanci yanzu, dole ki ji yinwa" daga nan ya daga murya yayi magana da budaddiyar murya yadda nima kaina sai da na dan tsorata "Wai babu waiters ne a gurin nan?" Ya dawo da dubansa kaina yana murmushi mischievously, sannan murya can kasa yace min "enjoy the show". Wait, I know that smile, sai yanzu na tuna a inda na san shi, a tv, suna fada shi da wani mutun akan titi police suka zo suka yi arresting dinsa. Dan sarkin Abuja, Sultan, yes, haka naji ya Walid ya ce sunansa, a real big time trouble maker, no wonder daga shigowarsa aka cika gurin da securities. Wait, hakan yana nufin ina zaune a table daya da criminal kenan? Ta gefen idona naga securities guda biyu sun zo gefen mu sun tsaya, sannan sai ga wata waitress nan tazo da sauri ta kawo masa menu ta ajiye a gabansa, daga ganin ta kasan a tsorace take, nima ta ajiye min a gaba na, na daga mata hannu alamar bana bukata, bai dago kai ba yana duba menu din gabansa yace "don't worry, I will order for you. Please don't say no" bance komai ba har ya gama bada order dinsa ta tafi. Ya sauke ajiyar zuciya yace "Allah yasa kar su dade, dan yunwa nake ji sosai kamar zanci babu kuma bana so kice zaki tafi ba tare da kinci abinda nayi miki order ba" ni dai bance komai ba kawai na cigaba da shan tea dina wanda by now ya tashi daga ruwan fanfo ya koma ruwan fridge. Na ajiye kofin nayi signal na akawo min bill zan tafi, ya bata fuska sosai yana cewa "dan Allah karki tafi" waitress ta taho zaka kawo min bill yayi mata wani kallon banza ba shiri ta koma da sassarfa. Yau na ga ta kaina ni Maimunatu. Na kalleshi with serious tone nace "am serious tafiya nake so inyi, dare yayi kuma a gida ba'a san na fito ba" ya gyada kai alamar gamsuwa sannan ya sake daga murya "waiter!!" Sai gata ta dawo har tana sassarfa, yace "na fasa cin abinda nayi order, just bring us something simple, a fried rice with chicken perhaps" tace "but sir, already an fara shirya maka wancan order din" ba tare da ya kalleta ba yace "i don't care, bring us fried rice and be very quick about it" har tayi gaba ya sake daga murya "make sure the chicken is not burnt" dariya yake yi kasa2, irin dariyar nan ta cikin kirji sannan ya rage murya yace "tsaya kiga wani abu" wayarsa ya zaro ya fara magana da dan karfi "yah Amir kana ina ne? Ina Hilton wallahi yunwa nake ji gashi suna wasting time dina sun wani sa securities sun tsatstsaya a kaina, eh mana, in dai basu kawo min order ta in the next two minutes ba, kuma basu janye securities dinsu ba to abinda zanyi musu sai yafi na last week, kasan halina ai" yayi dariya daga haka ya kashe wayar yana mischievous smile dinsa. Daya bayan daya securities din suka ringa fita, hatta mutanen gurin gani nayi suna tashi suna fita, dariya yayi yace "now a person can eat in peace, amma idon mutane in yayi yawa ma ai mutun ba zai iya cin abinci ba" a raina nace au kasan ana kallonka ashe. Da sauri waitress din tazo tayi serving din mu, babu musu na kama cin abinci na dama nima din ina dan jin yunwar dan in ana taro sam bana iya cin abinci. Daga dukkan alama kuwa yunwar yake ji dan da gaske yake cin abincinsa. Sai da yaci kusan rabi sannan ya fara magana "kinsan har nayi bacci kawai na farka naji ina jin yunwa? Nasan cikin gida babu abinda zan samu sai tuwo shi yasa na taho nan. Amir ya tafi yawo ya barni, i don't like coming out alone. I hate being alone" a raina nace wannan surutu ne dashi kenan, sai kuma nayi dariyar magana ta tunda dai ai kura ba zata ce da kare maye ba. Suddenly naji ya sake cewa "what's bothering you?" Na kalleshi da da sauri na dan bata rai nace "me ka gani?" Ya danyi murmushi "a girl all alone in a restaurant, tana shan tea, it is either you are trying to getaway from something or you are waiting for someone" sai kuma ya ajiye spoon din hannunsa ya bude manyan idanuwansa a kaina "ko ni kike jira dama? Maybe we are destined to meet here, har nayi bacci fa na tashi na fito na taho nan, ke kuma only God knows what you were doing kika fito ke kadai kika taho nan" ni ma na ajiye spoon din hannuna ina kallon sa tare da jinjina maganarsa, sai kuma na girgiza kai. He is not my type, too rough for me. Na girgiza kaina nace "it is just a coincidence, I just wanted to be alone shi yasa nazo nan" yayi kasa da murya kamar me rada yace "let me tell you a secret, am a magician, kina gaya min abinda yake damun ki zaki nemi duk matsalolinki ki rasa" yadda yayi maganar ne yasa dariya ta kubuce min, shima dariyar yayi wadda tasa maikon idonsa yayi kyalli, kyawawan hakoransa suka bayyana, shima kallona yake yadda nake dariyar. Sai da muka gama dariyar mu sannan ya sake cewa a hankali "there you go, yanzu kinga ai kinyi dariya har naga dimples din ki" kunya naji na rufe fuskata shi kuma ya cigaba da dariya "wani ya taba gaya miki cewa you are very beautiful? Very unique?" Na bude fuska ta a hankali nace "thank you" har yanzu fuskar tawa yake kallo. Na mike a hankali nace "thank you for the food and the talk" da sauri nayi hanyar fita, yace "wait" ban tsaya ba kuma ban waigo ba, na bude kofa na fice, ina jinshi yana kwalla wa waiter kira. Sai da na fito sannan na tuna cewa ba da mota nazo ba. Na duba agogon hannuna naga after 11.oh God Allah yasa ba'a neme ni a gida ba. Tun daga bakin titin da nake tsaye na jiyo karar cin taya, jikina ya bani shine zai fito kuma na tabbatar nema na yake yi, oh God me yasa banzo da mota ba? Da sauri na kama tafiya ina rufe fuskata da mayafi na, ai kuwa banyi wani nisa ba naji an ci taya a gefena, ban kalleshi ba na cigaba da tafiya ta, ya bude motar ya fito ya sha gabana yana dariya "thank God bada mota kika zo ba da tuni kin gudu, wow, na tsorata da yawa fa" na dago kai na kalleshi, sai yanzu na kara ganin kakkarfan jikin shi. Ya cigaba "ko sunan ki fa baki gaya min ba, and after seeing your face kina tunanin zan iya bacci with out knowing your name?" Direct na bashi amsa "Sunana Hafsat" "I always like the name Hafsat, muje in sauke ki a gida ko?" na girgiza kaina nace "thank you, amma ni ba zan shiga motar ka ba, I don't know you" yace "sunana Sultan, now you know me. shikenan?" Na sake girgiza kaina. Ya fahimci dai da gaske bazan shiga motar saba sai yace "to dan Allah ki bani address dinki mana" ba musu na bashi address din gidan su Amira, bakinsa har kunne yana gyada kai da murmushi yace "ok, saura phone number" ya miko min phone dinsa na karba na saka masa tsohuwar number din Ibrahim da na haddace. Nishadi yake sosai yana jin dadi. Ya tarar min taxi na shiga sannan yazo window yace "it is very nice meeting you Hafsat, I will call you in na je gida" nace masa "ok, nice meeting you too Sultan" Ga mamaki na sai na samu kaina da waiwayensa bayan motar mu ta ja, yana tsaye yana kallon motar mu ya saka hannayensa a aljihun wandonsa. Sai kawai naji tamkar na bar wani part of me with him. Na runtse ido na "ya ilahi, not him please, sultan is not my type, he is a rogue" amma me yasa sanda muke tare dashi naji for the first time na manta da Ibrahim? A lokacin da muka yi dariya ni da shi na manta da duk wadansu problems dina dana fito na bari a gida. Yanzu kam nasan ba lallai ne mu sake haduwa dashi ba, amma kuma nasan bazan taba mantawa da fuskarsa ba. How do you guys like Sultan? Masoyan Ibrahim ga rival anyi muku. Lol