Episode Twenty Four: The Shadow
by @mamanmaama
Gaba na ne ya fadi da muka hada ido da Munnir wanda ya kasa ya tsare yana kallon duk wanda zai yi min magana. Na tabbatar Sultan yana shigowa zai hangoni tunda ina kan high table, yana gani na kuwa zai taho, Allah ne kuma kadai yasan abinda zai faru tsakanin sa da Munnir. Na rada wa Hafsat "two minutes, ina zuwa" ta yi sauri ta rike hannuna alamar bata so in tafi in barta, nayi mata alamar yanzu zan dawo. Cikin friends din mu na ɗan shiga, ina kallon Munnir ta gefen idona yana bina da kallo, sai da na tabbatar baya gani na sannan nayi hanyar entrance da sauri. Ina zuwa kuwa na ga Sultan ya dunkule hannunsa ya naushi wani mai gadi, nan na nan jini ya fara fita ta hanci ta baki, maybe ma hakori ya fita, wanwar gayen ya fadi a kasa yana gunjin azaba, Sultan ya durkusa kusa dashi, na dauka ma hakuri zai bashi, sai naga ya goge jinin daya bata masa hannu a jikin rigar gayen, ya mike tsaye yace "who is next?, dan rainin hankali har ni zanzo ince zan shiga guri ku ce min card admit ne, da card din da admit din duk naci uwarsu gaba daya" Da sauri na karaso gurin cikin tashin hankali nace "what the hell are you doing" sai a lokacin ya ganni, hannu duk biyun ya saka a cikin gashinsa yana matsawa baya a hankali tare da cewa "shit" na durkusa gurin mai gadin da aka daka wanda har yanzu ya kasa tashi na fara jera masa sannu cikin kulawa, da sauri sauran guards din suka karaso suka kamashi suka tafi. Na mike ina kallon Sultan daya kasa hada ido dani nace "what are you doing here?" Ya karaso kusa dani yace "am sorry" sai a lokacin na lura da wanda suke tare, zasuyi kusan tsaho daya da Sultan amma bazan tantance kibar saba saboda uban kayan daya loda a jikinsa duk kuwa da yanayin zafin da ake ciki, kansa yasha kwal kwal amma kuma ya bar saje a fuskarsa. Kallo daya nayi masa na maida kallona kan sultan wanda yasha kwalliya dan daga gani wannan shigar ta musammance. Har yanzu ya kasa magana ni kuma na bata rai na tsare shi da ido. Abokinsa ne yace "so, kece wannan Hafsan da ta hana abokina bacci kenan, you are really worth the trouble" sai a lokacin na tuno cewa ashe fa ce masa nayi sunana Hafsat. Na dan yiwa abokin murmushin yaƙe sannan na kuma mayar da idona kan Sultan na sake cewa "uhum, ina jinka, me ya kawoka nan?" Ya sake hargitsa gashin kansa sannan yace "I just wanted to see you ne, please, number da kika bani bata shiga, shine naje address din shima na tarar wrong ne da kyar yarinyar gidan ta kawo munan" nace "OK, ka ganni zaka iya tafiya yanzu" ina fadin haka na juya zan koma ciki, da sauri yasha gaba na, fuskarsa kamar wani abin tausayi "please kar ki koma" nace "serious, bani da lokaci, biki muke yi, na tabbatar yanzu ma nema na akeyi a ciki" da sauri yace "OK, at least ki gaya min sunanki na gaskiya, ki bani number din ki ta gaskiya" ya saka idonsa cikin nawa pleadingly, kawai sai naji na daina jin haushinsa, ya danyi murmushi tare da cewa "pretty please" na danyi murmushi nima kadan. Abokinsa ne yace "OK, lokacin introducing dina yayi" daga ni har Sultan babu wanda ya kalleshi, sam ya kasa dauke idonsa daga cikin nawa, ni na fara dauke kaina nace "I.....I really must go inside" yace " OK, sunanki na gaskiya" nace "Maimunatu" ya dauko wayarsa yace "phone number?" Har na fara fada masa sai ya dakatar dani yana karkada hannunsa "not again, an sha ni na warke" ya miko min hannunsa "bani wayarki" na gane me yake nufi dan haka nima nayi dariya tare da mika masa wayar, ya karba ya saka number dinsa yayi dialing, da kiran ya shiga wayarsa sai da ya dauka ya tabbatar shine sannan ya katse ya daddanna, na fahimci saving number dinsa yayi a waya ta sannan ya miko min. Ina karba naga an bude kofar hall din an fito, a tsorace na waiga, yaya Habeeb na gani a tsaye yana kallon mu ni da Sultan, sai kuma ya koma ya maida kofar ya rufe. Na sauke ajiyar zuciya nace "zan koma kaga already ana nemana" ya gyada kai yace "it is OK, nagode sosai, and please don't block my number" nayi murmushi nace "I won't" na juya na kama hanyar komawa ciki, naji abokin sultan yana cewa "hey, bakayi introducing din mu ba fa". Tunda na koma na cigaba da activities dina har aka tashi ban kuma tunawa da wani Sultan ba ballantana his troubles, bayan an tashi munje gida duk mun sallami friends din mu, zamu hau samanmu kenan sai yaya Habeeb ya kira ni, na juya na koma duk jikina a gajiye, so nake kawai in ganni a kwance. Ina zuwa naga ya bata fuska yace "dazu dawa na ganki a gurin dinner" sai a lokacin na tuno da Sultan. Nayi ajjiyar zuciya nace "Sultan ne, dan sarkin Abuja" yace "nasan ko shi waye, kece baki san Sultan ba shi yasa har kika tsaya dashi. Duk inda kike tunanin sa ya wuce nan. In ana zancen top criminals a Abuja sunan Sultan yana daga layin farko" Nace "ya Habibi babu komai fa a tsakanin mu, naga cewa idan ban kula shi ba zai iya tayar da rigima a gurin shi yasa na kulashi, but I know he is a trouble maker and all.. " ya Habeeb ya katseni "trouble maker? He is not just a trouble maker Moon, he is a drunk" ji nayi tamkar ya Habeeb ya watsamin ruwan zafi a fuska, a drunk? Har naje dakin mu jikina a sanyaye yake, can kuma nace a raina, me yasa na damu, it is not as if na damu dashi. Direct toilet na shiga na yi wanka nayi shirin bacci, ina fitowa na ga Hafsat har tayi bacci, nima na kwanta nayi addu'ah. A drunk, but how, me yasa ya zabi wannan rayuwar? Me yasa ya zabi abokai irin wannan da na gan su tare? Dan manyan mutane kamarsa, dan Sarki, sarkin ma na federal capital, how can he be what he is? Me yasa iyayensa ba zasu dau mataki a kansa ba? Waya ta naji tayi kara, na dauka na duba screen "My Sultan" naga an rubuta, nayi murmushi, wato haka yayi saving number dinsa a waya ta kenan. Na ajiye ta na barta tayi ta ringing dinta har ta katse, wani kiran ya shigo sannan wani. A drunk, na maimaita a raina. Take na yanke shawarar in dauki wayar in gaya masa cewa bani da interest a kansa yayi hakuri. Tana fara wani ringing din na dauka "Assalamu Alaikum" naji yace. Assalamu Alaikum, peace be unto you. Wannan itace kalmar daya fara fada min ranar da muka hadu a Hilton. Mutane nawa ne a cikin mutanen kirki suke sallama idan sun kira ko an kira su a waya. Mostly hello ko hi ake cewa wanda ba dai dai bane, amma shi a matsayinsa na known criminal me yasa yake yi min sallama. Ko hakan yana nufin some part of him is good?. Wannan kalmomi na Assalamu Alaikum da Sultan yace min sune suka sa na fasa yanke alakar ta dashi. I felt like I wanted to know him better. "Assalamu Alaikum" ya sake maimaitawa, sai a lokacin na samu damar amsa masa "ameen, wa alaikassalam" ya sauke ajiyar zuciyar da sai da naji daga cikin wayar, "sorry I kept calling, ina so ne ko yaya in ɗanji muryarki kafin nayi bacci" nayi shiru babu amsa, yace "ya taron? Da fatan baki gaji da yawa ba" nace "gajiya kam akwaita, sai godiyar Allah" "sorry" na danyi murmushi saboda yadda ya furta kalmar sorry din, ya sake cewa "am really sorry akan abinda ya faru dazu, I came to your party uninvited kuma na yi creating commotion, I just can't hold my temper ne most of the times" nace "it is OK, ya wuce, Allah ya kiyaye gaba" "Ameen, thank you for understanding" Ƙasa2 naji suna magana da wani, nace "kai da waye ne?" Da muryar dariya yace "Amir ne, that my friend that kept bugging me dazu, wai koya min zance zaiyi, wai ni ban iya tsara budurwa ba" nace " He is funny" yace "yes he is, bari in barki ki huta kin gaji ko? Na gode da daukan waya ta da kika yi, you have no idea how much it means to me" na runtse ido na inajin wani abu a cikin raina wanda na manta rabon da inji irinsa. Nace "good night" yace "fi amanillah" daga nan ya kashe wayar. Na kara runtse idanuna ina jin wannan abin yana min yawo a jikina. Rabo na da jin hakan tun Ibrahim. Nayi tsaki na gyara kwanciya ta, ya kamata in nutsu in san me nake yi especially after warning din da yaya Habeeb yayi min cewa Sultan is a drunk, but he didn't look or sound drunk to me. Oh dear God, don't let me fall in love with a wrong guy again. Not again. Da kyar na samu bacci ya dauke ni. Washegari tun safe aka tafi 'yalleman daurin aure, mu dai muna Abuja muna ta shirye shiryen kai amarya, Zayed ya dage shi lallai babu zancen wani kayan daki ko gara, su a al'adarsu in kayi aure mata kawai za'a kai maka, shi wai a gurinsa abin kunya ne aga ana shigar da kaya gidansa wai daga gidan surukansa, dan haka Daddy ya hada kudin duk da yayi niyyar yiwa Hafsat kayan daki ya saka mata a account dinta yace inta ga dama tayi jari dasu, in bata ga dama ba kuma ta kashe kayanta, kudin kayan gara kuma ya saya wa Zayed dalleliyar mota ya bashi a matsayin wedding gift. Tunda akayo mana waya an daura aure Hafsat take kuka tamkar wacce aka yiwa auren dole, sanda muka zo tafiya airport kuwa cewa tayi ta fasa auren ta shige daki ta rufe kanta, sai da Daddy yazo da kansa sannan ta bude kofar. A hanyar zuwa airport na duba waya ta naga 5 missed calls daga Sultan da message guda daya "please in kin samu chance call me" sai na samu kaina dayi masa reply cewa yanzu zamu tafi UK, in naje zan kira shi da number ta ta can. Masha Allah, gidan Hafsat ya tsaru iya tsaruwa, tsayawa bayanin gidan bata lokaci ne, likita matar likita, ina kallon gidan ina tunanin cewa some people are so lucky in life, komai yana zuwa musu da sauki, kamar Hafsat, her life have been so simple and so straight forward. Embassy muka sauka, anan zamu yi kwana biyu sannan mu dawo Nigeria. Ranar da muka baro Hafsat a gidan miji kwana nayi ina juyi ina kewar ta, Allah sarki 'yaruwata shi kenan an shiga layin manya. Sai kawai na samu kaina da imagining what wedding night will feel like, ga mamakina kuma a imagination din nawa sai naga Sultan with his muscular body, red lips and shiny brown eyes maimakon Ibrahim da nake gani duk sanda nayi irin wannan tunanin. Nayi sauri na kawar da tunanin daga raina tare da sake sabuwar addu'a amma still babu bacci. Nayi tsaki na jawo wayata na duba time, 12:30am, a Nigeria zai zama around 8:30pm kenan. Nayi dialing number dinsa, bugu daya ya dauka kamar mai jira. "Assalamu Alaikum" na amsa masa, sannan yace "God, saura kadan in running mad, ban taba jin haka a rayuwa ta ba, what have you done to me woman?" A raina nace kai zanyi wa wannan tambayar ai, a fili kuma cewa nayi "haba dai, da girman ka?" Yayi dariya yace "nima na dauka am strong, sai yanzu nake ganewa ashe shayi ma ruwa ne" hmm kawai nace, yace "to ya hanya? Ya kuma amarya" nace "lafiya lau, mun kaita mun baro ta, gobe zamu huta jibi mu dawo insha Allah" yace "so, tell me about yourself, I want to know you more" nan na bashi labari na in brief, abinda ya shafi family na da karatu na, ko kadan banyi mishi zancen Ibrahim ba, shima ya fara bani labari da cewa "well, as unbelievable as it may sound, babana shine sarkin Abuja, ni ne first child dinsa sai Abbas, Saratu sannan Fa'iza, nayi primary a Abuja, sec da university duk nayi su a USA. Na karanci architecture first and second degree. I have many friends but Amir shine babban abokina, he is more like a brother to me" daga nan yayi shiru, a hankali nayi tambayar da take raina tun farkon gani na dashi saboda fahimtar da nayi cewa shi jini biyu ne nace "what about your mother?" Yayi shiru kamar ba zai magana ba, can yace "I don't know who my mother is" duk da ta cikin waya ne sai da na fahimci irin zafin da maganar da ya fada tayi masa a ransa. Ba wai bai san babarsa ba, a'a bai ma san wacece babarsa ba. Interesting Nayi shiru maganar tana sinking a raina, sannan nace "bangane ba, how comes?" Sai da na fada sannan na fahimci rashin dacewar yi masa doguwar tambaya irin wannan. Shima shirun yayi kamar baiji abinda nace ba, munfi minti biyu a haka, ina jiyo saukar numfashinsa ta cikin wayar, can yace "can we please not talk about this? In fact yanzu nasan dare yayi sosai a nan, gwara in barki kiyi bacci haka ko?" Na gane waccan maganar ce baya son yi kuma nasan bani da right din da zan matsa masa dan haka nima na bar maganar "OK, good night then" "fi amanillah" na jima bayan munyi sallama ina lissafin maganar sa, me yake nufi? What is his story? Washe gari tun safe nake baccin gajiya har zuhr sannan Inna ta tashe ni nayi sallah naci abinci na sake komawa wani baccin. Sai la'asar sannan na tashi nayi wanka na shirya dan zamu je gidan Hafsat muyi mata sallama tunda gobe da safe zamu koma Nigeria. A gidan Hafsat ne su Inna da gwoggo Sakina babar su Nuraddeen suka yi ta yiwa Hafsat nasiha akan zaman gidan miji, nima na zauna naji kuma na karu sosai, bayan sun tashi suna kara zagaya gidan ne na saka Hafsat a gaba da tsokana wai sai ta gaya min abinda ya faru jiya bayan mun tafi, harara tayi ta watsa min daga karshe tace "wai ke yaushe na fara wasa dake ne? In auren kike so ki fada yanzu zaki ganki a gidan Munnir" wata harara nima na watsa mata, dan ni har mantawa nake yi da wani Munnir a duniya, dariya itama tayi min tunda ta kashe min baki. Sai da muka zo tafiya kuma sannan ta fara kuka, babu kunya Zayed ya kama rarrashinta a gaban su inna, sum2 suka fice ina ta yi musu dariya. Washegari da safe jirgin mu ya daga zuwa Nigeria. Duk 'yan biki kuma kowa ya watse sai fatan Allah ya sanya alkhairi. Sai da aka gama watsewa sannan na fara missing Hafsat, gashi Amina ma bata nan ta bi mutanen 'yalleman zata karasa hutun ta acan. Duk gidan ya gundire ni sam babu dadi. Sultan kuwa kullum sai ya kirani a waya, yayi2 in barshi yazo gidan mu naki, saboda ina tsoron abinda zaije ya zo. A raina nasan ya kamata in dakatar da Sultan amma zuciya ta taki barina in yi haka, sosai nake jinsa a raina, dan wani lokacin ma ni da kaina nake kiransa a waya. Ranar da mukayi sati daya da dawowa ne na tambayi Mommy cewa ina so inje gidan su Amira in wuni acan sai dare zan dawo tunda na gaji da zama ni kadai, babu musu Mommy ta barni tace driver ya kaini da daddare sai ya koma ya daukoni. Na shirya cikin riga da skirt na jar atamfa mai adon fari da baki, na yafa farin mayafi, da farin takalmi, na debi wayoyina muka tafi. Muna cikin tafiya munbi ta wata siririyar hanya sai muka tarar da traffic, gurin ya chunkushe mutane sai hayaniya suke yi, nayi mamaki saboda normally gurin babu traffic, driver nane ya fita ya tambaya sai ya dawo yace min wai wani ne yayi blocking hanyar yace yau babu mai wucewa ta nan, sai dai mu koma baya mubi ta wata hanyar. Nayi shiru ina tunani, sai na dauko waya ta na kira number din Sultan, ya dauka nace masa "kana ina?" Dariya yayi yace "na fita unguwa ne kuma sai na tsaya neman rigima" bance komai ba na kashe wayar nace da drivern ya zauna ina zuwa, na fita na kutsa ta cikin mutane har inda problem din yake, katuwar Jeep Dodge na gani anyi crossing dinta akan titin yadda ta rufe titin completely, duk glasses dinta were tinted dan haka bana hango wanda yake cikin motar, mutane sai hayaniya suke, wani naji yana cewa "to tunda ba zai dauke ba ba sai a kira masa 'yan sanda ba, in yafi karfin mu ai baifi karfin hukuma ba" wani kuma yace "to in an kira 'yansandan ma ya za suyi dashi? In sun kama shima ba zai awa daya ba za'a sake shi, su kansu yanzu sun gaji da kama Sultan" A raina nace da gaske shi din ne. Number motar na duba naga "SULTAN 3" na karasa kusa da motar, inajin wani daga bayana yana cewa "'yan mata kiyi a hankali fa, wannan mutumin is very dangerous". Na karasa dai dai windown driver nayi knocking a hankali, da sauri ya sauke glass din fuskarsa ta bayyana dauke da murmushin mamaki "Hey, me kike yi anan?" Na daura hannayena akan windown nayi tagumi nace "unguwa zanje kuma an tare min hanya" ya kalli dandazon mutanen da suka taru a gefe sannan yace "lallai kice dara taci gida kenan" nayi dariya nace "dama ai hausawa sunce in zaka gina ramin mugunta ka gina shi gajere, yanzu kaga ka haƙa rami ni na rufta ciki" shima dariyar yayi yace "da fatan baki ɓalla kafa ba" wani daga bayana yace "baiwar Allah dama kin rabu dashi, wannan mutumin bai san magiya ba, gashi nan an kira police zasu zo suyi mana maganin sa" Sultan ya leko da kansa yace "kafin suzo suyi magani na ni bara inzo inyi maganin ka, dan rainin hankali kawai" ya bude kofar motar ya fito da sauri, sai kuma ya kalleni ya ga yadda na haɗe rai sai ya koma yana cewa "kaci sa'a, amma na gane fuskarka, zamu hadu wata rana". Ni kawai kallonsa nake yi da mamaki, shi babu abinda ya dame shi wai dan mutane suna zaginsa, kamar ma wani enjoying kansa yake yi. Yasa hannu ya bude min kofar kusa dashi sannan ya karya wuya yace "can I please have this ride? Honor me" na yi jim ina tunani, anya kuwa in shiga motar Sultan? Anya mutunci nane? Besides ba wani sanin halinshi nayi ba, kuma duk a halayensa da ake gaya min babu wani na kirki. Na sake kallonsa naga shima ni yake kallo pleadingly, da wadannan idanun da na fara fahimtar cewa bana iya resisting, oh God, kawai sai na zagaya na shiga. Mutumin da suke fada da Sultan ya saki baki yana kallon mu, ina kallon Sultan ya mika hannunsa ta window yayi masa alamar fuck you. Daga nan ya daga windown ya tayar da motar muka tafi. Wani daddadan kamshi ne a cikin motar, irin kamshin nan da yake sa mutum ya lumshe idonsa, da gaske Sultan dan gayu ne dan cikin motar tsaf yake, kujerun an lullube su da wani tattausan bargo wanda shi kansa kamshin yake yi. Shi kansa Sultan din gani nayi ya kara yi min kyau da kwarjini, yauma kamar kullum rigarsa body hug ce data kama jikinsa sosai amma yau 3 quarter wando ne a jikinsa, gashin kansa a hargize yake kamar kullum. A 30 yake tafiya da motar kuma gaba daya ba titi yake kallo ba ni yake kallo, har sai da naji kunya na rufe fuskata da mayafina. Motoci sai horn suke yi mana daga baya, duk wanda yazo wucewa kuwa sai yayi bala'i amma sultan ko kallonsu baya yi hankalinsa gaba daya yana kaina. Nace "wai wannan kallon na menene kuma" yace"duk sanda na ganki sai inga kamar kara kyau kike yi" kamar nima ince masa shima haka sai kuma dai nayi shiru nace "thank you" yace "ina zakije ne?" Sai yanzu na tuna na bar driver da mota a baya, da sauri na dauko waya ta na kira shi nace na tafi, ya danje yawo kadan sai ya koma gida yace ya kaini. A muryarsa naji alamar baiji dadin abin ba amma kuma babu yadda zaiyi. Mun danyi tafiya kadan nace "why do you do it?" Yace " me fa?" Nace "why do you block the road?" Kafin ya bani amsa wani ya danne horn a bayanmu sannan ya zo ya wuce mu a guje yana cewa "malam in ba zaka wuce ba ka bawa mutane hanya su wuce" Sultan yayi dariya yace "that's why" nima dariyar nayi nace "to kai me yasa ba zakayi saurin ba, kana tafiya a cikin Abuja a 30 bayan kasan kowa a garin nan sauri yake" ya wani kwantar da kujera ya kashingida yace "sauri ba gurin zuwa ba" da sauri nace "dan Allah ka rufa min asiri ka tashi, ya za'ayi mutum yana driving kuma ya kwanta" sai da yayi dariya sosai sannan ya tashi zaune, ni kuwa duk na rude, yana tashi wani ya yi masa dakuwa daga waje, ai kuwa ya sauke glass sukayi ta zage2 sannan muka wuce. Sai a lokacin na gaya masa inda zanje, yace "OK, inda kika tura mu rannan ko?" Muka yi dariya tare. Muna tafiya a hanya ne yake tambayata me yasa nake yawo da driver? Nace masa "ban iya driving ba" yayi ta min dariya yana tsokana ta wai abin kunya kamata ban iya driving ba, yace "in kin yarda sai in koya miki" nace "not now, sai na gama school tukunna" yace "OK, Allah ya kaimu" mun danyi nisa na sake tambayarsa "dazu da kayi blocking hanya da mai martaba yazo wucewa fa?" Yace "kinsan kuwa hakan ta taba faruwa" na ware ido nace "haba? Ya akayi kuma?" Yace "kamar yadda nayi dazu, na rufe hanya nace ba shiga ba fita, na rufe glasses din mota na kunna AC na kwantar da kujera ta nayi kwanciyata, mutane suna ta hayaniyarsu da zage2n su, kawai sai ga Takawa nan ni ban sani ba, yana zuwa yaga an tsaya ya tambaya lafiya aka ce ai hanya a rufe take, yace aje a gano me ya faru, aka koma akace masa ai nine na rufe hanya da motata" yayi shiru, nace "me yace kuma?" Yace "dogarai ya aiko yace su farfasa motar su fito da ni suyi min duka su jani a kasa su kaini gida" na rufe baki na ina mamaki nace "ya salam, sunyi ɗin kuma?" Wani murmushi ya jefa min yace "sun fasa mota alright, amma none of them will dare to touch me, duk wanda ya taba ni kuwa sai na kwantar dashi a asibiti" Nayi shiru ina jimamin maganar, it seems like there is crisis between the father and the son, does it have to do with Sultan not knowing who his mother is? Ina so in sake tambaya kuma bana so yaga kamar ina bi masa kwakwkwafi. Mun danyi gaba kadan sai naga ya sake hanya yabi wata hanyar daban, nayi sauri nace "ba nan ce hanyar ba fa" bai kalleni ba yace "eh na sani, sayar dake zanje inyi" nayi shiru yace "kinga kuwa zakiyi tsada" ni dai bance masa komai ba, sai a lokacin na fara lissafin babu wanda yasan tare da wa na fita, shi kansa driver din da muka fito dashi baiga sanda na shiga motar Sultan ba, what if ya sace ni? Ina kallon shi ta gefen ido na yana min dariyar yadda na takure a gefe daya ina rarraba ido. Wata unguwa muka shiga irin ta masu ƙaramin karfi, a raina nace me yake kawo Sultan irin wannan unguwar kuma? I really hope he is not doing drugs kuma? Can gefe ya samu yayi packing yace "please two minutes dan Allah, dama nan zan taho kuma tunda hanyar kine shine na biyo zanje in karbo sako" na gyada masa kai amma a raina ina cewa zaka je ka karbo drugs dinka dai. Ina kallonsa ya fita ya saka hannayensa a aljihu yana tafiya ya shiga wani loko. Da sauri na dauko waya ta na kira Amira, "Amira gani na taho amma ba'a motar gida ba, ina motar Sultan, in case in na bata a gurinshi zaku neme ni" na kashe wayar ina rarraba ido. Ta mirror na hango wani mutum yana tahowa wajen motar daga opposite direction din inda Sultan ya tafi, magidanci ne zai kai kamar 50 years, ta side din driver yazo yayi knocking, ina sauke glass din ya fara kokarin durkusawa zai yi gaisuwa sai kuma yaga babu kowa a gurin. Na gaishe shi ya leko ya amsa cikin sakin fuska sannan yace "yallaban baya ciki ashe" nace "ya fita, wai zai karbi sako" ya girgiza kai yace "zai kawo sako dai, tun dazu mukayi waya yace gashi nan zuwa da naji shiru shine na dan fita" sai kawai naji ina son in san sakon menene zai kawo. Nace "sakon menene zai kawo?" Yace "kudin makarantar yara ne, kinsan an kusa komawa sabon session, to nayi masa list na school fees, kudin books da uniform tunda akwai sababbin dauka shine yace zai kawo min yau" kaina naji ya toshe nace "yara? Wadanna yaran kuma" yace " marayun unguwannin nan mana, ai duk shi yake musu komai na makaranta, mu kam ba abinda zamu ce masa sai sam barka dan da yawa mutanen da suke zaune a unguwannin nan shi yake ciyar dasu, ya ciyar damu ya biya wa yaran mu kudin makaranta ya samarwa matasan mu aikin yi. Kinga wannan sabuwar orphanage din daya gina duk nan unguwar yazo ya dauki ma'aikata maza da mata" cikin cushewar kai nace "orphanage? Sultan din ne ya gina orphanage?" Yayi alamar rufe bakinsa yace "ai na dauka tunda kuna tare kin sani, ai baya so a sani, da nasan baki sani ba da bazan gaya miki ba" nayi sauri nace "dan Allah baba gayamin, wallahi bazan ce kai ka gayamin ba" Ya gyara tsayuwa da alama yana da surutu kuma yana jin dadin yabon gwaninsa, ya ce "ai wannan ta biyu ce, waccan babbar ma ta cikin gari ai shi ya gina ta sai mutane suke cewa dan majalissa ne shi kuma sai ya samu dan majalissar yace yace shine yayi. Ai duk unguwannin nan na marasa karfi yana da representative da yake gaya masa duk bukatun mutane kuma in dai an fada to zai bayar, in dai har maganar kudi ce to mukam sai godiya" Nayi shiru ina jinjina maganar a cikin raina. Nayi wa mutumin godiya ya tafi hanyar da naga sultan yayi, har Sultan ya dawo ina jinjina maganar mutumin nan a raina. Yana zuwa ya shiga muka tafi yace "sorry na barki kina jira" kai kawai na gyada masa, yace "are you OK? Naga kin chanza?" Nan na kirkiri murmushi nace masa ba komai, bai yarda ba dai yace "bayan na tafi wani yazo nemana?" Na girgiza kai nace "babu wanda yazo nemanka" ina ganin fuskarsa ta chanza alamar yaji dadi. Dole na ware nima muka cigaba da hirar mu dan kar ya fahimci wani abu har muka je gidan su Amira. Tun 11:00 na baro gida amma banje gidan su Amira ba sai 1:30, kamar wacce na tafi kano. Muna yin packing Amira ta fito da sauri kamar dama a bakin gate take. Sultan ya tsatstsare ni da ido wai lallai sai na yarda yazo ya mayar da ni gida. Amira tana bude kofar ta finciki hannuna "fito daga motar nan" Sultan yana dariya yace "check her from head to toe, ban ciri komai ba" ita dai bata kula shi ba sai jana take ni kuma naki fitowa. Sultan yace "please yaushe zan zo in dauke ki" Nace "after magrib" yayi murmushi yace "thank you" na juya zan fita muka hada ido da Amira wacce ta saki baki tana kallona.