Maimoon

Episode Thirty Five : The Storm

by @mamanmaama

A daidai kofar gidan su Moon, Yaya Walid yana kokarin shiga bayan ya dawo daga masallacin sallar ishai sai yaga wani saurayi yana kokarin yi masa magana, kallo daya yayi masa ya gane shi saboda hasken fatarsa da ya sha banban da na mafi yawan mutane, ya tuna yana ganin sa da tare da Moon a london, da ya dauka ma soyayya suke yi dan har gidan su yakan je gurinta sai daga baya kuma ya daina ganin su tare. Ya karbi hannun da yake mika masa suka gaisa da sakakkiyar fuska sai kuma saurayin ya tsaya yana shafa kai yana murmushi. "Bismillah" Yaya Walid ya ce masa yana nuna masa kofarmma sai saurayin ya girgiza kai yace "nagode, amma ba na jin zan shiga. Bani da number dinka ne dama da waya ma kawai zan yi maka. Wata magana ce nake so muyi. Sunanan Mahdi, munyi karatu tare da kanwarka Maimoon a Oxford" Ya Walid ya gyada kai yace "na gane ka ai, sunan ne dai ban sani ba amma na gane fuskar" Mahdi ya gyara tsayuwar sa, he seemed disturb, kamar abinda zai fada ne yake disturbing dinsa. "Ina jinka" yaya Walid yayi encouraging dinsa, ya bude baki ya rufe, ya sake budewa sannan yace "akan Maimoon ne, I feel ya kamata in gaya muku ku kara saka ido a kanta" sai kuma yayi sauri yace "ba wai ina nufin ba kwa saka ido ba, amma nasan halin mu mu matasan yanzu, zamu iya boye abinda muke aikata wa a waje yadda ba za'a sani a gida ba". Yaya Walid ya cigaba da kallon sa fuskarsa cike da confusion, sai kuma yace "menene Maimoon din take aikatawa wanda kake tunanin ba mu sani ba?" Mahdi yayi shiru yana tunanin, he hated seeing that boy destroying that innocent girl's life, amma kuma still baya son ya hada ta da iyayen ta, but he knows a ransa cewa ya kamata yayi something akai, and that something is what he was doing. Yace cikin yanayi na tsintar kalmomi "akwai wani da suke tare da shi mai suna Sultan, ban sani ba ko a gida an san da shi?" Walid yayi shiru yana juya sunan Sultan a ransa sannan yace "Sultan?" Mahdi yace "eh, ban san shi ba but naji ance ɗan Sarkin garin nan ne" Nan take yanayin fuskar yaya Walid ya chanja, ya sake maimaita sunan cikin mamaki "Sultan? Menene hadin Maimoon da Sultan?" Mahdi ya sake jin babu dadi amma kuma yana da tabbas din abinda yayi dai dai ne dan yanayin fuskar Walid ya tabbatar masa a gida ba'a san Maimoon tana tare da Sultan ba, yace "ba wai wani abu ne naga ita Maimoon din tayi ba, kawai dai naga......." Sai kuma ya kasa cewa komai, Maimoon tana da wani kaso mai tsoka a zuciyarsa. Yaya Walid ya sake miƙa masa hannu yana gyada kai yace "I understand, and I am really greatful that you come forward with this information, and I promise you your name will not be mentioned". Daga haka ya juya cikin sauri ya shiga gida, a ransa yana fatan abinda yaji ba gaskiya bane ba amma kuma wani part din zuciyarsa already har ya yarda da maganar dan Mahdi bai yi masa kama da makaryaci ba. "Moon will have a lot of explaining to do" Yana shiga yaji an bude gate motar Mommy ta shigo, dan haka sai da ya tsaya ta fito sannan ya gaishe ta suka shiga cikin gidan tare, baya son gaya mata komai sai yayi confirming daga Maimoon tukunna kuma ya saurari uzirinta. A palour suka tarar da Habib, daga dukkan alama shima daga sallah yake, Mommy ta zauna akan kujera cike da gajiya shi kuma Walid ya wuce saman Moon, so yake yaji daga gare ta kafin ya san matakin dauka akan maganar da yaji yanzu. Yayi knocking kofar dakin ta ya jira, shiru babu amsa sai ya sake yi sannan ya tura kofar tare da sallama. Bata nan. Ya sake sallama da ɗan karfi shima shiru dan haka ya juyo ya sauko yana kokarin kiran ta a waya. Sai kuma ya dakata at the foot of the stairs yana kallon Habib da yake yiwa Mommy wani bayanin wanda daga dukkan alama ya dauki hankalin ta sosai, sai dai shi abinda ya dauki hankalin sa shine sunan Sultan da yaji an ambata, sai kuma yaga Mommy ta mike da sauri hankalinta a tashe sannan ta fara kwalla kiran Maimoon tana kallon hanyar dakinta. Asma'u da taji kiran da ake wa Maimoon ta fito daga kitchen tana cewa "Mommy mai sunan Daada bata jin dadi, tace zata kwanta a dakin ta kanta yana ciwo" Walid ya kalle ta sannan ya kalli Mommy yace "bata can, bata dakin ta" Cikin rawar hannu Mommy ta dauko wayarta ta fara kiran number din Maimoon amma ba'a dauka ba, Habib ya fita da sauri ya zagaya part din Daada can ma babu alamar ta, cikin gidan kaf aka bincika babu Maimoon, Daada ta shigo palourn itama hankalin ta a tashe. Sai da suka gama tabbatar wa bata gidan sannan suka zauna kowa yana mayar da abinda ya sani, Mommy girgiza kanta kawai take yi dan zuciyarta da kwakwalwar ta ta kasa dauka, Sultan? Sultan din dai da ta sani? Shine tare da Maimoon dinta? Tun yaushe nema Maimoon din ta fara fita daga gida ba tare da sun sani ba? How much damage was already done to her baby girl? Sunanan zaune ana ta waya duk inda aka san Maimoon tana zuwa amma babu wanda aka fahimci yasan inda take, a haka har dare ya fara nisa, lokacin hankalin kowa ya kai kololuwar tashi, a lokacin ne wayar Walid ta yi kara....... Moon's POV Nayi kokarin raba jikina dana Sultan wanda da kyar ya tsaya. Munir ya kara matsowa yana kare mana kallo, dogon hijab dina duk ya chukuikuye yayi squeezing yace "dama abinda kike aikata wa kenan shi yasa ko waya nayi miki ba kya dauka, haka ne fa ya saka na shirya na taho Abuja da kaina dan inga me yake faruwa. Ashe abinda kike aikatawa kenan har ake yi min gorin baza'a bani ke ba dan kin fini tarbiyya? Ina tarbiyyar take anan? I wish uncle Aliyu zai ganki a yanzu sai ya gane tsakani na dake waye marar tarbiyyar" Da kyar na bude baki nace "Munir kar ka adar da batun da baka tabbatar ba, I was only trying to help him, shi kenan taimako kuma sai ya zama laifi?" Cikin fada Yace "waye shi? Menene tsakanin ki da shi?" Nima nace a fusace "what is your problem with that?" Sultan ne naji yace "I am her husband to be, ko kana da abinda zaka yi akai?" Wata harara Munir ya watsa masa yace "da masu hankali nake magana ba da bugaggu ba" da sauri Sultan ya yunkura zai kai masa duka nayi sauri na rike shi, saura kaɗan duk mu biyun mu fadi, nasan a yadda Sultan yake a yanzu Munir duka zai yi masa dan tsayuwa ma da kyar yake yi tangadi kawai yake. A fusace Munir yace "cika shi kizo mu tafi" nace "I will not leave him here" da mamaki kawai ya tsaya yana kallona yama rasa me zai ce min. Wata taxi ce ta tsaya a gaban mu Amir ya fito da sauri ya karaso in da muke, yace "Moon ya akayi kuka fito nan, what if someone sees you?" Sai kuma ya juya ya kalli Munir yace "waye wannan kuma?" Takaici bai barni na bashi amsa ba, babu abinda nake son yi a lokacin sai kuka, nace "ina ka tafi? Dare yayi sosai, I needed to go home, ba zan iya tafiya in bar shi ba, babu wanda na sani a ciki ballantana in nemi taimako, ina ka tafi?" Kamar zaiyi kuka yace "am so sorry Moon, na dauki motar da Sultan yayi accident da ita niyya ta in kaita gida sai in dawo in dauke shi a mota ta, na hadu da police a hanya sunga damage din da motar tayi suka tare ni suna ta yimin tambayoyi, sai da naje station nayi cike cike sannan suka barni na tafi, I thought zaki kira ni a waya ma, dan Allah kiyi hakuri" nace masa "ai babu waya a hannuna, wayar Sultan kuma tana hannunka" ya kuma kallon Munir da har yanzu yake tsaye yana sauraren mu yace "waye shi?" Da takaici nace "shine wanda akayi alkawarin za'a aura min a gida" Amir ya dora hannunsa aka yace "ya Salam, am so sorry Moon" Munir yace "are you guys done? Saboda na matsu muje gida inji bayanin da zaki yi musu" nace "ni ba zan shiga motar kaba, ai ba tare muka zo ba, kayi tafiyarka kawai" wani murmushin mugunta yayi sannan ya dauko wayarsa ya fara dannawa yace "in ba zaki shiga mota taba, bara in kira wanda dole ki shiga tasa" kafin inyi wani yunkuri naji yana cewa "Hello Walid kana ina? Guess wa na gani yanzu? Moon. Au dama nemanta kuke yi? a buge na ganta a hannun wani gardi suna ta marisa a gefen titi. To shikenan in baka yarda ba kazo ka gani da idonka." Daga nan ya fada masa inda muke ya kashe wayar. Har yanzu murmushin yake yace min "mu zuba ni da ke mu gani, lets see idan gobe ba'a daura mana aure ba" Kaina naji yana wani irin juyawa, idona har wani dishi dishi nake gani. Wata zuciyar tace min in kwashi takalma na a hannuna in fita a guje, wata kuma tace min in dauki halin Sultan in rufe Munir da duka. Na juya na kalli Sultan idona cike da kwalla, daga ganin sa kasan zuciyarsa tafasa kawai take yi amma babu karfin yin wani abu akai, a raina nace 'daga yau zaka fara fahimtar illar shan giya'. Amir kam gaba daya hankalinsa ya tashi, da sauri sauri ya wuce ya shiga cikin hotel din can sai gashi ya dawo da motar sa. Ya bude kofa yazo zai kama Sultan amma Sultan ya tubure yaki tafiya, na ɗan durkusa a gabansa ina duba kafarsa mai ciwo amma tight fitted jeans din jikinsa basu bari naga extent din ciwon ba, ina saka ran dai bai taba kashin sa ba tunda yana iya taka kafar amma kamar yadda Amir ya fada in ba'a duba kafar da wuri ba zata iya zama infected. Na mike ina kallon fuskar sa, a raina ina jin kamar kallon karshe nake yi masa nace "Sultan ku tafi gida kafin yaya Walid yazo ya same ku" na juya gurin Amir nace "Amir ka kira doctor din palace sai ku hadu dashi a can ayi dressing kafar nan da wuri. Take care of him please" Sultan ya rike hannuna yace cikin daskararriyar murya "I am not leaving you here, gurin nan bashi da kyau, and am not leaving you tare da wannan mutumin" ya fada yana nuna Munir, na rike hannunsa nima, a raina ina kara jin wannan shine gani na karshe da zan yi masa a rayuwata. Sam babu kwalla a idona nace "Sultan kayi min alkawarin ko ina nan ko bana nan wannan itace rana ta karshe da zaka kuma shan giya, kayi min alkawarin duk sanda ranka ya baci zaka rungumi alqur'ani not alcohol. Sultan please promise me that you will fight for us, bawai fada zaka yi ba, show people your true self wannan shi kadai zai saka a baka ni. Please sultan, ka manta da zancen destroying family name dinka, ko da ba za kayi dan kanka ba, do it for me and for our unborn children, tunda in dai na aureka shi family name din naka shi ne dai sunan da zamu yi bearing ni da 'ya'yan mu" ya saki hannuna daya ya jawo ni jikinsa, ina jin yadda zuciyarsa take bugawa da karfi a kirjinsa, a kunne na ya rada min "please don't leave me, let's runaway together, let's go back to America" nayi kokarin kwace jikina ya kara rikeni "please, I can't live without you" na zame jikina ina girgiza kaina nace "no Sultan, guduwa ba shine solution ba, solution shine mu samu albarkar iyayen mu, in muka gudu ba zamu taba ganin dai dai ba a rayuwar mu" duk da irin son da nake wa Sultan, bazan taba iya guduwa daga gurin iyayena ba, duk da nasan irin abinda yake jira na a gida amma nasan abinda zan fuskanta inna gudu sai yafi wannan, ni ina ji a jikina cewa fitowar da nayi ba tare da sanin iyayena ba shi ya jawo komai ya kara chakude min. A ganina worse abu da 'ya zata yiwa iyayenta shine ta gudu ta barsu, duk duniya babu wanda yake son ki ko kuma wanda zai soki sama dasu, in kika gudu kika bar su kullum zasu zamo cikin tashin hankalin rashin sanin halin da kike ciki, wannan tashin hankalin nasu kuma ba karamin bala'i bane a gurin ki. Tun daga nesa na hango motar ya Walid ta shigo layin, Sultan ya kara rikon da yayi wa hannu na, na kalli Amir na sake cewa "take care of him please". Yana zuwa yayi packing ya fito yana bin mu da kallo daya bayan daya, idonsa ya sauka akan hannayen mu ni da Sultan. Munir ya karasa gurinsa yana cewa "ka gani ko? Yanzu ka yarda da abinda na gaya maka? A rungume take a jikinsa ma ganin ka ne ya saka ya sake ta" ya Walid bai ce masa komai ba ya karaso in da muke tsaye ni da Sultan, kallo daya yayi wa Sultan ya dawo da kallonsa kaina, muna hada ido na sauke kaina kasa amma na kasa cika hannun Sultan. Wani wawan marin da ban taba tsammanin ya Walid zai min ba shi ya saukar min a fuskata, sai da na dena gani for some seconds sannan naji taste din jini a bakina, ina dago kaina naga ya sake daga hannu zai kara min wani, na runtse idona ina jiran saukar marin, wannan karon nasan completely zan karasa makancewa. Jin marin bai karaso ba yasa na bude idona dan ganin abinda ya tare shi. Hannun Sultan na gani rike da na yaya Walid, ba zan iya kwatanta expression din fuskar saba, murya can cikin makogwaro yace "don't you dare hit her again" da dayan hannun ya Walid ya wanka wa Sultan shima na shi rabon, daga ganin marin nasan yafi nawa karfi dan sai da Sultan yayi baya kamar zai fadi Amir ya rike shi, sannan yaya Walid ya nuna shi da hannunsa yace "an dake ta din, me zakayi akai?" A raina nace 'ayyah ya Walid, dan dai Sultan ba dai dai yake ba da yau sai ka kwanta a asibiti' ban dawo daga tunani na ba naji ya Walid ya damƙo gashina ta cikin hijab daga baya ya fara jana, wata azaba naji tamkar zan saki fitsari a wando, a haka ya jani har mota, inajin Sultan yana kwalla min kira amma zafin rikon da ya Walid yayi min ya hanani magana, kafin mu karasa mota Munir ya bude kofar baya, ya Walid ya watsa ni ciki tamkar kayan wanki ya mayar da kofa ya rufe, ina jinsa ya tada motar ya ja muka tafi. Sam babu hawaye a idona sai fuskata data kumbura side daya. Na rufe ido na ina jero sunayen Allah a raina dan shi kaɗai ne zai iya kawo min ɗauki. Muna tafiya wayarsa tayi kara ya dauka yace "Hello, Mommy gamu nan mun taho, she is OK but sai munzo dai" Ina jinsa yayi horn aka bude mana gate muka shiga gida, yana packing ya zagayo ya bude kofar baya ya fito dani, he half dragged me zuwa palour, muna shiga ya sake watsar dani flat a tsakiyar palourn. Ban dago kaina ba ballanta na in san suwaye a palourn. Muryar Mommy naji tana magana a nutse tace "ka gayawa Daddyn ku?" Ya Walid yace "a'a, naga yanzu a can cikin dare ne shi yasa na bari sai da safe tukun na" Mommy tace "ka barshi, ni zan gaya masa" yace "Ok Mommy" yadda take maganar a nutse ne ya bani mamaki saboda nayi zaton kafin muzo zan tarar ta hargitsa gidan gaba daya. Amma kuma nutsuwar tata sai ta karamin tsoro a raina. Na dago kaina ina kare musu kallo, Mommy tana tsaye a tsakiyar palourn ta rungume hannayenta, daga can gefe Daada a kan kujera tana ta share kwalla, Ya walid yana tsaye shima a kusa da Mommy, ya Habeeb yana zaune daga bayana. Mommy ta kura min ido tana kallona sannan tace "kai ka dake ta ne?" Ya Walid yace "eh" sannan tace "Habibi kira David kace masa muna bukatar karin securities a gidan nan, kace masa nace munyi receiving threats, duk wanda suka ga zai hauro mana su harbe shi" Wata muguwar faduwa gaba na yayi, na mike zaune daga kwancen da nake. Ta cigaba da magana tana zagaya palourn, tace "ina da labarai da yawa akan yaron nan, he is capable of doing anything, nasan zai iya yin attempting shigowa ya dauke ta. Yazo har gida ya dakar min ɗa, sannan ya dawo yayi kidnapping yarinya ta, in ya sake dawowa for the third time ina da right din da zan saka a harbeshi in self defense" Cikin rawar murya nace "Mommy he did not kidnap me" marin da dazu yaya Walid bai karasa min ba shi yayi min yanzu, wannan karon kunnena ne naji ya dena ji, sanda na dawo hayyacina a kwance na ganni again. Daada ta kara sautin kukanta kamar ita aka mara. Sama sama naji Mommy tana yiwa ya Walid fadan kar ya sake dukana, tace "duka is not the solution to kangararrun yara" kalmar kangararruce ta tsaya min a raina, wato nima yanzu na shiga layin kangararru kenan? Na kuma tashi na zauna ina jinsu suna ta plans na security, a raina nace 'indai sultan yayi niyyar shigowa gidan nan sai ya shigo, but I don't think he is coming, not today' Mommy ta kalleni tace "tashi ki tafi daki" na mike sum sum nayi hanyar stairs sai kuma tace "ah ah ah, bani wayoyinki" na nuna mata hannayena nace "ban fita dasu ba dama" tace "Habeeb bita ta baka ka kawo min, manyan wayoyinta guda biyu da karamar Nokia, da laptops dinta biyu, ta hado maka da ATM cards dinta guda biyu suma. Kayi locking kofar balcony dinta sannan in ka fito ka rufe kofar dakin daga waje ka taho min da keys din" Mommy is surely harder than steel, tun ina yarinya nasan she is thorough a duk al'amuranta. Muna shiga daki na bawa yaya Habeeb duk abinda Mommy tace, bai ce min komai ba ya rufe kofar balcony ya zare key din, ko kallo na baiyi ba ya kwashi kayan ya fita sannan yayi locking kofar daga waje. A gaban gado na durkusa fuskata tana min radadin marin da nasha. Na cusa kaina a tsakanin kafafu wana ina neman kuka amma yaki zuwa. Wani zafi nake ji a kirjina, na cigaba da jero sunayen Allah 99 a fili amma a hankali, kafin in kai karshe naji raina ya danyi sanyi. Hijab din jikina wanda gaba daya warin giya yake na cire na shiga toilet nayo alwala nazo na yi sallar isha sannan na dauko alqurani na na fara karantawa a hankali, wata nutsuwa ce take shigata a hankali, kamar some kind of assurance cewa everything is going to be alright. Sai da naji muryata ta fara dashewa sannan na rufe alqur'anin na kwanta a kusa dashi, na ƙi barin zuciyata tayi tunanin Sultan saboda kaina ba zai iya dauka ba. A hankali bacci ya fara daukana. Ana kiran assuba na tashi na fara kawo nafiloli sannan da akayi assalatu nayi sallar assuba amma da nazo yin addu'ah sai na rasa me zance, what if Sultan ba shine alkhairi a gare ni ba, ko kuma nima ba nice alkhairi a gare shi ba? Dan haka kawai sai na yi addu'ar Allah ya bamu ikon cin dukkanin jarabawar da zai yi mana, ya bamu karfin zuciyar daukan ko menene zai taho mana kuma ya zaba mana mafi alkhairi a duniya da kuma lahira. Da gari ya waye ina kwance a gado naji an bude kofar dakin, nayi sauri na mike zaune, Mommy ce ta shigo sai mai aiki a bayanta, ta ajiye tray da abinci a ciki ta fita, na ce "Mommy good morning" ba tare data kalleni ba tace "ki tashi ki ci abinci" daga haka ta fice tare da rufe kofar. Tunda nazo duniya yauce rana ta farko da na gaida mommy bata amsa ba, It feels really bad, wato haka Sultan yake ji kenan tunda yazo duniya? Ban kalli in da abincin yake ba na cigaba da kwanciyata har zuhr tayi. Ina zaune a kan sallaya aka sake bude kafar, wannn karon Asma'u ce, ta ajiye trayn hannunta ta kalli na safen da ko taba wa banyi ba. Tace "mai sunan Daada ki ci abinci mana, ya za'ayi mutun ya zauna babu abinci?, murmushi kawai nayi mata na cigaba da jan charbi na. Bata dade da fita ba aka sake bude kofar, wannan karon Mommy ce ita kadai. Ta zauna akan bedside drawer sannan tace "tashi kici abinci" banyi mata musu ba na dauko trayn ba bude na zuba abincin na fara ci, sam ji nake abincin babu taste amma haka nake hadiyewa da kyar, ina gama cin abincin ta dauke trayn ta fita ta rufe kofa. Sai da akayi la'asar sannan ta dawo, yanzu ma ina kan sallaya ta zauna akan bedside tace "zo nan" na mike naje gabanta na tsugunna, tace "tashi ki zauna a kan gado, ba musu na tashi na zauna ina kallon kasa tace "Maimoon ina so ki gaya min gaskiya, in kika yi min karya abinda zanyi miki sai yafi wanda nayi niyya" a hankali nace "to Mommy" tace "tun yaushe kuke tare da Sultan?" Nace "tun bikin Hafsat" tace "shekara daya kenan?" Nace "eh" ta gyada kai tace "good, yaushe ne kuma ya fara koya miki shaye shaye?" Da sauri na dago kaina ina kallonta "Mommy nice fa, Moon ce fa Mommy" ta dauke kanta tace "I don't know you anymore, Moon din dana sani ba zata bi saurayi gidan giya ba, Moon din dana haifa na raina ba ita ce wannan a gaba na ba. Just answer the question" sai yanzu sannan hawaye suka zo idona, na rufe fuskata da hannayena ina kuka, ta sake cewa "just answer the question, tun yaushe yake kai ki bar?" Nace "wallahi Mommy ban tana shan komai ba. In baki yarda ba kisa ayi min drug test" tace "OK, ina son ki gaya min komai and I mean everything da ya faru tsakanin ku" nan na fara bata labarin tun haduwar mu dashi a Abuja har komawar mu England shima ya bi mu, sannan na bata labarin bina da yayi America da duk abinda mu kayi a can amma na cire labarin abinda ya faru ranar da zan dawo, oh no I can never tell her that, sannan na bata labarin dawowar mu Nigeria da plans din mu na kai maganar gaban iyayen mu, na gaya mata kuma abinda ya faru tsakanin su da yaya Habeeb da kuma bin Amir da nayi zuwa gurin Sultan. Na kara da cewa "mother, he is not a bad person, he is a good person. Dan Allah ku tsaya ku fahimce shi" ta yi ajjiyar zuciya tace "you are not as smart as we all thought you are, Moon, he is playing you. Mutane irinsa abinda suke yi kenan, su samu yarinya kamarki su yaudare ta su bata mata rayuwa suyi dumping dinta. Tunanin ki bai taba baki cewa duk wadanda suke zuwa suke baki labarin abinda kike kira da kyawawan halayen sa shi ya ke turo su ba?" Na girgiza kaina nace "Mother this is for real, wallahi da gaske ne, I trust him" ta mike tsaye tare da ajjiyar zuciya tace "Maimoon, you are no longer allowed to see or talk to Sultan in dai nina haife ki kuma na isa dake" na fado daga kan gadon ina jin zafin maganar ta fiye da zagin marurrukan da na sha jiya, na rike kafafuwanta ina kuka nace "Mommy kiyi min rai, Mommy wallahi in kika raba ni dashi mutuwa zanyi, punish me duk yadda kike so dan Allah karki raba mu" Ta kwace kafarta taje bakin kofa tace "you really have no idea what situation you are in. Already Munir yayi waya 'yalleman ya gaya musu abinda ya gani jiya, it is just a matter of time kafin Baffa ya turo a bincika masa, so you really understand why I want you as far away from Sultan as possible? He is who he is and you are who you are" ta bude kofa ta fita ta barni a durkushe a gurin. Innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Allahumma ajirni fi musibati wa aklifni khairan min ha. I can only imagine yadda Hajja zatayi ta yawo da maganar nan. Allah ne kadai yasan irin karyar da Munir ya kara akan abinda ya gani ɗin. Na dafe kaina daya fara sara min. Washe gari da assuba Mommy ta shigo da breakfast a hannunta ta saka ni a gaba na ci, sannan tace in tashi inyi wanka, naje naji na fito na tarar ta ajiye min kaya har da underwears akan gado tace in saka, a raina nace ina zamu je kuma da sassafen nan? Ni dai na shirya na zauna ina kallonta, ta kalleni cikin ido tace "you are going on a journey, ke da Daada, ba za ku dawo ba har sai kin manta da Sultan" na durkushe a gabanta nan da nan na fara kuka ina rokonta, ko saurare na bata yi ba, tace it's for my own good, a karshe dai nace mata "Mommy, ina son magana da Daddy" tace "mun riga munyi maganar dashi, shine ma ya bada wannan shawarar" Mommy is a bad liar, in dai tayi karya sai an gane, ina kallon fuskarta nasan Daddy bai san maganar tafiyar nan ba. Zata tura ni wani gurin da Allah ne kadai yasan ina ne, ba tare da sanin Daddy ba ballantana wani dan haka Allah ne kadai yasan ranar dawowata. Allah gani gare ka.