Episode Thirty Seven: Her Father's Daughter
by @mamanmaama
Yace "Don't worry about Sultan. Kar ki bari Zaliha tasan kin kirani har sai na nemi contact da mijin ta, dashi zamuyi magana. Badan jirgi baya zuwa agadaz ba Moon da yau zanzo in dauke ki. Amma highest jibi. Ki kwantar da hankalin ki kinji?" Na gyada kaina kamar yana kallona sannan nace "I miss you daddy" ya danyi shiru sannan yace "I miss you too, sunshine" daga haka ya kashe wayar. Nayi tunanin in kira Hafsat amma kuma sai na fasa kar ta gayawa Mommy na kira ta. Na mayar da wayar cikin jaka ta na fito daga toilet din ina kalle kalle. Babu kowa a dakin. Na dan tsaya ina tunani, a raina nasan kiran daddy da nayi dai dai ne amma kuma duk da haka sai nake jin feeling kamar nayi ba dai dai ba. Na tsaya a gaban mirror, when was the last time dana kalli fuskata? Tunda muka zo na saka wani towel na rufe mirron dakin saboda bana son kallon fuskata. A hankali na bude, ni kaina sai da na tsorata, babu komai a fuskar sai katon hanci da idanuwa kamar na mujiya, dama haka idona yake? Lallai kiba ma rahama ce. Na kalli wuyana naga wani katon kashin da bansan ina dashi a gurin ba, amma kuma kirjina yana nan dam dam, ramar da nayi ma sai ta karawa girman su fitowa. Na mayar da mirror din na rufe na koma na kwanta. Ina kwance Daada ta dawo tayo alwala tazo tayi sallah sannan ta tashe ni, har da dan magagi na kamar me baccin gaskiya sannan na mike na shiga toilet nayo alwala nazo nayi sallah ni ma, muka fita falo tare. Musbahu ne kadai a zaune yana kallo, Daada ta zauna kusa dashi ya fara bata labarin film din da yake kalla, hankalinta gaba daya yana kam kallon na zaro wayar na ajiye a kusa dashi na koma gefe na zauna. Ina kallonsa ya dauka ya saka a aljihunsa ba tare daya kalleni ba. Muna zaune a palon har akayi magrib, anan muka yi sallah aka fara kawo abinci. Mun fara zubawa kenan mukaji shigowar abban su Mustapha, gaba na ne ya fadi saboda nasan ba lokacin yake dawowa ba, tun daga compound yake kwalla wa aunty Zaliha kira, ta mike tsaye fuskarta da alamar tsorata, yana shigowa ya fara balbalin fada "Zaliha yanzu dama abinda kuke aikatawa kenan ke da Fatima? Kika ce min yarinyar nan hutu tazo yi gidan nan, dama ni ina mamakin tunda tazo ban taba ganin ta fita waje ba, ashe ita nan zaman prison take yi a gidana. Saboda tsabar rashin hankali ku raba yarinya da ubanta da 'yan'uwanta kawai dan saurayin da take so bai yi muku ba?" Kamar zatayi kuka tace "abban Musaddiq dan giya ne fa" yace "to amma baku yi tunanin cewa baban ta shima yana da right na zaba mata miji ba? Ko ita Fatima tana ganin cewa tafi ambassador son ta ne? Yanzu kinga ni kinsa naji kunyar mutumin nan, mutumin kirki wallahi, sai da nayi tayi masa rantsuwa cewa babu hannuna a cikin maganar nan. Yanzu da wani ne da sai dai kawai inga 'yan sanda a gidana" Ya zo gaba na ya sunkuya yace "Maimunatu kiyi hakuri kinji? Dana san halin da kike ciki kenan da tuni na dau mataki a kai, babanki ya taho already, a daren yau zai sauka a Niamey dan da private jet ma ya taho, ni kuma ni zan kai ki Niamey da kaina. Ki tashi kije ki shirya" aunty Zaliha ta ce da sauri "wai a yanzu zaku tafi?" Ya tashi yayi hanyar dakinsa yana cewa "in bamu tafi yanzu ba yaushe zamu isa can?" Yana shiga daki kowa yayi shiru a palourn, na mike sum sum zan shiga daki aunty Zaliha ta danko hannuna fuskarta babu rahama tace "uban waye ya baki waya kika kirashi?" Nan da nan hawaye ya kawo idona saboda zafin rikon da tayi min, nace "ni bani na kirashi ba, bansan yadda akayi yasan ina nan ba" ta juya tana kallon 'ya'yanta har yanzu bata cika ni ba tace "cikin ku waye ya bata wayarsa?" Duk sukayi shiru, cikin tsawa tace "ba za'a bani amsa ba?" Nan suka kama rantse rantse banda musbahu da yake ta game dinsa kamar bai san me akeyi ba, tace "Mustapha kai ne ko? Dan na lura da yawan shishshige mata da kake yi?" Mustapha ya kama rantsuwar bashi bane, ko ta kan Musbahu bata bi ba dan sam tunda nazo gidan baya kulani, shi dama ko a cikin 'yanuwansa bashi da harka sosai. Ta sake ni tana girgiza kai fuskarta kamar zatayi kuka "poor you, you have no idea what you have done to yourself. Sai kije ai, shi baban naki ya aura miki wanda yake so din. Duk abinda Fatima tayi, she did it to protect you amma ke gani kike ta takura miki ne saboda bata son ki" ban gane mai take nufi da babana ya aura min wanda yake so ba, ni dai nasan Daddy bai zaba min miji ba kuma shi da kansa ya fada cewa baya son Munir. Ta juya ta shigewarta daki, ina shiga daki Daada ta biyo bayana, tana ta maganganun ta akan ban kyauta ba ni ko ko kulata banyi ba na dauki iya abinda zan iya dauka na zuba mana a akwatinan mu, sauran na barwa 'yan gidan. Ban bi ta kan Daada ba na jayo akwatinan mu na kawo palo, lokacin already gari yayi duhu, Abban su Mustapha na gani yana cin abinci, yace min "ina Daada? Ku zo kuci abinci mu tafi dan kwana zamu yi a hanya" ba musu na zauna na zuba abinci na fara ci, sosai naci na koshi dan nasan wahalar da nasha sanda muka zo. Har muka gama babu aunty Zaliha babu labarin ta, muna gamawa Abba ya kira Musaddiq ya saka mana kayan mu a mota sannan Daada ta shiga dakin aunty Zaliha nima na bita a baya, tana kwance a kan gado, suka yi sallama da Daada nima na matsa kusa nace mata "zamu tafi" ko kallona bata yi ba, tayi fushi, na kara matsawa nace "aunty Zaliha zamu tafi" tace "Allah ya kiyaye hanya" daga haka bata sake cewa komai ba. A waje na samu Daada a kusa da mota nima na tsaya, Musbahu ne yazo yana murmushi yace min "so... Har taimakon gaggawa yazo kenan?" Nayi murmushi, yace "there you are, gashi har kina murmushi, abinda tunda kika zo banga kinyi ba" sai yanzu nima na tuna yaushe rabona da murmushi? A hankali nace "thank you" bai ce komai ba, Daada ta kalleshi cike da zargi tace "kai ka bata wayarka ko?" murmushi kawai yayi mata, ya miko min kati yace "call me when you get your phone back, and...... ki gaida Sultan. Adios for now Moon" nima nace masa "adios" Lokacin Abba ya fito da sauri ya shiga gaban motar driver dinsa ne zai tuka, mu kuma muna baya. Na kalli gidan ina jin a raina kamar wacce na bar prison na samu freedom. Tun kafin mu fita daga gari na kwanta nayi pillow da cinyar Daada na fara bacci. Sai gab da assuba muka isa Tahoua, already Abba ya kira wani abokinsa yace gamunan zuwa, dan haka muna zuwa can muka je, ni kam na jima banyi bacci mai dadin na yau ba, muna zuwa muka yi sallah muka huta muka yi breakfast. Karfe tara muka sake daukan hanyar Niamey, da yake hanyar me kyau ce kuma motar lafiyayya ce karfe biyu muka isa, Daada ce ta ringa yi masa kwatance har muka zo gidan kawu Jibril wanda yake yayane a gurin Daada kuma a gidansa muke zama duk sanda muka zo Niamey. Muna packing naga manyan motoci da number din Nigerian embassy na Niamey nasan Daddy yazo, da kyar na iya controlling kaina saboda excitement, amma ina shiga compound din gidan naga palon kawu a bude da takalman mutane a bakin kofar, bansan sanda na zubar da takalmana a gurin na shiga dakin a guje ina rarraba ido ina nemansa ba, yana ganina shima ya mike tsaye ya bude min hannunsa, ai kuwa a guje na karasa na shige ciki na kankame shi tare da sakin wani kuka mai ratsa zuciya. Sai da nayi kuka na na gama sannan ya raba ni da jikinsa yana kallon fuskata, fuskarsa sam babu fara'a, kallona yayi tayi sama da kasa kamar mai tabbatarwa babu abinda aka gutsira a jikina, sannan yace "are you OK?" Kaina kawai na gyada masa. Na juya ina kallon sauran mutanen dakin, sai a lokacin naga Mommy, tana zaune a kan carpet ta harde kafafuwanta a guri daya, fuskarta tayi ja, akwai uncles dinta su biyu na gurin uwa dana guri uba, na saki Daddy na tafi na fada kan cinyarta, bata cemin komai ba sai dan bubbuga bayana da take yi. Daada ta shigo tare da Abba suka gaisa da mutanen gurin. Daddy ne ya soma fada, daga dukkan alamu dama fadan ya keyi kafin mu shigo yanzu cigaba yayi "ta nuna min ni ban isa ba. Ta dauke min yarinyar ba tare da sanina ba kuma nayi nayi ta gayamin inda take taki. Ko wanne laifin yarinyar tayi ai kamata yayi ace an gayamin first sannan kuma sai mu hadu ni da ita musan irin hukuncin da zamu yi mata, amma a haka ai ta nuna min ban isa da 'yata ba kenan" Kawu Jibril ne yace min "tashi ki shiga cikin gidan Maimoon" daga dukkan alamu Daddy ya manta ina gurin. Na tashi na shiga cikin gida amma jikina duk yayi sanyi. Tunda nake a rayuwata ban taba ganin Mommy da Daddy suna musu ba ballantana fada, dan ina da burin ace wata rana ni da mijina mu kasance tamkar Mommy na da Daddy na. Har daga cikin gidan ina iya jiyo muryar Daddy yana fada, sam ba halinsa bane ba, dan da wahala kaga Daddy yana fada ballantana a gaban surukansa. Ji nayi gaba daya komawa Nigeriar ma ya fita daga kaina. Na zamanto dalilin samun matsala a tsakanin iyayena, kowa a cikin su was trying to put me first. Nasan duk abinda Mommy tayi tayi ne dan tana ganin shine dai dai a gareni, amma ni abinda ban fahimta ba shine dalilin ta na kin gayawa Daddy bayan kuma nasan komai tayi sai ta gaya masa. Ina nan kwance abin duniya ya ishe ni gwoggo Sa'a ta shigo tace in tashi inyi sallah inci abinci, bayan na gama ne ta tambayeni "Maimoon wai me ke faruwa ne tsakanin Mommyn ki da Daddyn ki?" A raina nace wannan tsegumi take so kenan, na daga mata kafada alamar bansani ba, daga nan bata sake cewa komai ba. Mommy suka shigo tare da Daada, ko kallon inda nake bata yi ba ta shige toilet tayo alwala tazo ta tayar da sallah, Daada tana ta 'yan mitocinta "ba shikenan ba, sai kije ai ya aura miki ko ma waye yaga dama, duk abinda ya faru kuma daga baya kar ki zo gurin mu, ki je can ku karata ke da baban naki" ni duk maganganun da take yi ban fahimci me take nufi ba dan haka kawai kallonta nake yi, Mommy ta idar da sallah ta mike ta tsaya a bakin window tana kallon waje, muna haka sai ga dan aike daga waje "wai ance baƙi su fito su tafi" ya fada da buzanci, na mike ina saka hijab dina, ganin Mommy bata motsa ba sai na dauka bata ji sakon ba nace "Mommy ance mu fito" ta juyo ta kalleni tace "ance ki fito dai, ni ai ba bakuwa bace gidan mu nazo, kema sai ki bi babanki ki tafi naku gidan" Na yar da hijab din hannuna na karasa kusa da ita nace cikin rawar murya "Mommy ba tare zamu tafi ba?" Ta juya min baya tace "no, am going to stay here for a while" nan take naji duk farin cikin komawa gida ya gushe daga zuciya ta, na durkusa na rike kafarta nace "Mommy ni bazan koma gida ba tare da ke ba, Mommy dan Allah kiyi hakuri ki zo mu tafi, Mommy in dai akan maganar Sultan ne wallahi ni na hakura da shi. Kin fiye min dubun Sultan. Dan Allah Mommy kiyi hakuri kice kin yafe min" kuka nake sosai. Ta dago ni ta rungume ni tace "ni na yafe miki tun tuni Moon. I just wanted to clear the mess you created" nayi sauri nace "to in kin hakura kizo mu tafi gida tare. You know me, I will just be creating other messes a gida in ba kya nan, I won't know what to do without you, I will just die" Ta goge min hawayen fuskata tace "Daddyn kine yayi fishi bani ba. And you will not die dan bananan, your Daddy will take care of you and clear the messes" sai na fahimci fushin ba wai nawa ne ni kadai ba har da na Daddy, fushi take yi saboda yayi mata fada a cikin mutane. Na chika ta da sauri na saka hijab dina na fita, I knew I had to do something saboda shima Daddy yadda ya dauki zafi in bata fito ba tafiyarsa zaiyi ya barta, ban san kuma a inda fushin nasu zai kare ba. A compound din gidan na fara rarraba ido ina neman Kawu Jibril, na san zan kara wani laifin a gurin Mommy amma nasan wannan laifin nawa akan dai dai ne, can na hango shi ya taho inda nake da saurin sa duk da girman shekarun da yake da shi yace "ina kuka tsaya ne, kun bar mutane suna jiran ku" na karasa inda yake idona a kasa nace "Mommy ce....... Mommy ce tace ba zata tafi ba" ya dan yi shiru yana kallona sai kuma ya wuce ni da sauri kamar zai kifa ya shiga inda na fito, daga inda nake ina jiyo yadda ya rufe Mommy da fada, a karshe ya hada har da Daada ya wanke su tas yace ita ce take biyewa Mommy. Ina nan tsaye naga Mommy ta fito tazo ta wuce ni fuu kamar zata tashi sama, ni kuma na bita a baya ina jin dadi a raina, nasan zata huce ne a hankali. Ina fita na kalli motoci guda biyu da suke jiran mu, a lokacin idanuna suka sauka akansa. Yana tsaye ya jingina da jikin mota, light brown eyes dinsa a kaina. Shadda ce doguwar riga da wando dark brown a jikinsa, kalar shaddar ta kara fito da uniqueness din fatarsa, hularsa da takalmin sa light brown kalar idonsa. Yawan sumar kansa ta saka hular bata shiga kan sosai ba. Ya cire hular ya saka hannu ya hargitsa gashin sa sannan ya mayar da hular still idonsa a kaina. Kafafuwana naji kamar ba zasu dauke ni ba, what is he doing here? Muryar Daddy naji yana cewa "Sultan ina Walid din kuma ya tafi? Ku zo mu tafi mana, weather din sahara is unpredictable"