Maimoon

Episode Forty: The New Family Members

by @mamanmaama

Sultan ji yayi maganar wani iri, sam ba abinda yayi tsammani ba. Ya jima kansa a kasa kafin yace "Daddy bansan me zance ba" Daddy ya gyada kai yace "I understand. Kafin ince zan baka Moon ko ba zan baka ita ba, dole ina so inga how far you can change, dan haka nake son chanza maka environment zuwa gurina. Amma da akwai sharadi, indai har ka amince zaka dawo gidan nan dole zaka bi sharuddan zaman gidan nan, na farko babu yawo, zaka iya fita iyakacin cikin gari amma in dai zaka bar gari sai na sani kuma sai na amince, a cikin garin ma duk inda kake in lokacin cin abinci yayi zaka dawo gida saboda tare muke cin abinci a gidan nan, lunch dinner duk tare muke ci, kuma duk inda kake 9pm tayi maka a gida inda har ba wani kwakwkwaran uzuri ne da kai ba, babu wayon dare. Sannan sallar subh tare zamu fita jam'i muyi, haka magrib da isha. Sannan the most important thing, ba zanyi tolerating koda single drop of alcohol a gidan nan ba, kuma koda a waje kasha ba'a gidan nan ba zan sani kuma ni kadai nasan hukuncin da zan yanke maka amma na tabbatar a zai yi maka daɗi ba. I also want a total change of friends daga gareka, Amir will still be your friend for the mean time amma shima in naga bashi da niyyar chanza hali dole zan raba ka dashi, ga Walid nan shine sabon friend ɗinka zan kuma gaya masa kar inji kuma kar in gani a tsakanin ku. Abu na gaba kuma gida na ba gidan 'yan dambe bane, ko da wasa kar inji ance ka daki wani a cikin ma'aikatan gidan nan, tsakanin ka dasu ya zama girmamawa da mutunta juna. Next thing is you will need a change of wardrobe, saboda kamar yadda nake yawo da Walid haka zan ke yawo da kai kuma ba zan ke shiga da kai cikin mutane da wannan shigar a jikin ka ba. Wadannan sune sharuɗai na, in kaga zaka iya yarda dasu then you are one step to getting Moon, in kuma kaga ba za ka iya ba shikenan sai ka chire ta a ranka Allah ya hada kowa da rabonsa" Da sauri Sultan ya dago yana kallon Daddy wanda shi kuma ya dora kafa daya kan daya ya dauki jarida yana kokarin budewa, alamar ya gama magana kenan. Sultan wani iri yake jinsa, wani irin feeling mixed with kunya, tunda yake ba'a taba ce masa yi kaza ko kar kayi kaza ba amma yau gashi Daddy ya wanke shi tas kuma a matsayinsa na surukinsa to be. Da sauri Sultan yace "Daddy na yarda, ni kam na yarda da duk sharudan" Daddy ya ajiye jaridar yace "madallah da wannan hukunci, gobe da safe zanje fada da kaina zan nemi alfarmar dawowar ka gidan nan a gurin mai martaba sarki" Sultan ya girgiza kai yace "ba zai ce komai ba, ba zai noticing ma bana gidan ba" Daddy yace "whatever, hakkin sa ne a gaya masa, kuma ni da kaina zan gaya masa. Yadda muka yi dashi Walid zai kira ka ya gaya maka. You can go now" Sultan ya kasa tashi, shi maganar bata ishe shi ba, shi da za'ayi ta masa fada so yake yi, can ya dan taba Amir yayi masa rada "ask him ina Moon take" Amir ya dan yi gyaran murya yace "Daddy ko zamu samu ganin Moon kuwa" ba tare da ya kallesu ba yace "you will see her when the time is right" still Sultan bai tashi ba, he have one more question, ya matsa gaban Daddy sosai yace a hankali "Daddy, dan Allah a cikin informations din da kake dasu, I want to know, did my parents.... " sai kuma ya kasa karasa maganar, Daddy ya ajiye takardar hannunsa sa yace "ina jinka" sultan ya hadiye yawu yace "did my parents marry before...... Did they marry kafin su haife ni?" Daddy ya jima yana kallonsa ya kasa magana, tausayin yake ji har cikin ransa, jin Daddy bai yi magana ba yasa Sultan ya mike tare da cewa "thank you Daddy, dama ina so ne kawai in sani, I always thought wannan shine dalilin da yasa babana baya sona" daga haka yayi hanyar fita, har ya kai bakin kofa Daddy ya kira sunan sa, ya tsaya ba tare da ya juyo ba saboda wani irin zafi da yake ji a ransa, Daddy yace "Sultan iyayenka sunyi aure kafin su haife ka, you are a legitimate child, abinda ke tsakanin ka da babanka is totally different from haihuwar ka" Hmmm Kamar yadda Daddy ya fada haka ya aikata, washegari yaje fada akayi masa iso gaban mai martaba sarki, bai yi tsammanin zai gane shi ba amma sai yaga ya tare shi sosai da fara'a da wasa da dariya yace "Muhammad baka da kirki, ace kana garin nan da iyalinka amma ba ka zuwa mu gaisa? Kasan ni nauyi yayi min yawa bazan iya ziyarar abokanai ba" Daddy yayi murmushi yace "Allah ya taimake ka ai ni ma ba zaman garin nake sosai ba, kuma in dai nazo to abubuwa sukan yi min yawa har sai na koma. Amma ayi min afuwa, in sha Allah zan ke lekowa lokaci zuwa lokaci" Har fadar da yake saukar manyan bakin sa ya saka aka shiga da Daddy, nan suka zauna gaba dayan su akan carpet suka fara hirar yaushe gamo da labarin karatun su da friends dinsu wadanda yanzu kowa ya kama gabansa. Daddy yayi mamaki sosai yadda yaga Takawa ya zage sosai yana hira da dariya, saboda shi ya dauka maganar da zasuyi formally zasu yi ta maybe a gaban mutane ma, ashe dai Sadiq din is still the same person da ya sani kawai dai nauyi ne ya hau kansa yanzu. Anan suka zauna har aka kawo musu lunch sam daddy bai lura da yadda lokaci ya tura haka ba, he totally couldn't believe cewa wannan elegant well mannered mutumin shi yayi raising Sultan. Da kansa mai martaba yayi serving dinsu suka ci, suna cikin ci Abbas ya shigo a nutse yazo ya gaishe su sosai sannan ya fada wa babansa sako cikin girmamawa ya fita. Daddy yayi noticing wani abu, Abbas totally baya kama da Sultan, ba zaka taba cewa 'yan uwa ne ba. Sai da suka gama sannan Daddy ya gyara zama yace "Allah ya taimaki sarki magana ce ta kawo ni. Akan ɗan mu Sultan" Daddy ya fada yana kallon fuskar Takawa, abinda yayi tsammani kuwa shi ya tarar, just mentioning sunan Sultan ya goge dukkan fara'ar dake fuskar Takawa, komawa yayi kamar bai taba dariya ba. Yace "Wani abun yayi?" Daddy yace "babu abinda yayi ran sarki ya dade, ina neman alfarma ne in da hali ina so ya koma gida na da zama" Takawa yace "saboda me?" Daddy yace "ba wani abu kawai mun hadu da shine sai naga kusan sa'an yaron waje na ne Walid shine sai naga ina sha'awar in hada su a gurina for sometimes, in ka amince of cause" Takawa yayi shiru yana shan lemon hannunsa, har Daddy ya fitar da ran cewa zai yi magana sai kuma yace "you can do with him as you wish. Kawai dai ka tabbatar duk abinda ya aikata maka kai ka jawo mu babu hannun mu a ciki, kuma ka tabbatar duk abinda yayi kar ka danganta shi da mu" daga haka ya ajiye cup din hannunsa ya mike tsaye yace "in ka kammala da akwai servants a waje zasu raka ka motar ka. Na gode da ziyara Allah ya bar zumunci" Da yamma Sultan yaji wayar Walid da sakon sarki ya amsa maganar Daddy, Sultan sam ya kasa tantance me yakeji a ransa, few things dinsa ya dauka ban da kayan sawa tunda daddy yace baya son irin su. To shi yanzu ina zai iya saka wata shadda ko yadi ne kam. Bashi ma da tailor. Yana zuwa gidan ya tarar da Walid da Habeeb suna jiransa a compound, direct part dinsu suka wuce dashi fuskokinsu babu yabo babu fallasa dan sukam sam basa murna da wannan hukuncin na Daddy. Four bedrooms ne dama a part din, sai palo mai hade da dining area duk da dai ba mafani suke da dining din ba sai dai in bakon da ba za'a shiga dashi babban palour ba. Walid ya bawa Sultan key din daki daya da kuma spare key din part din. Sultan ya bude dakin ya shiga, ba laifi yana da girma, da gado da dan karamin closet sannan sai toilet. Yana gama duba dakin ya fita yana tambayar ina masu share share aka nuna masa su yace "dan Allah aron kayan cleaning nake so" da mamaki suke kallonsa, suka ce "ai mu zamu gyara maka" ya girgiza kai yace "thank you, zanyi, ba wani abu" Sultan sam bai yarda wani ya gyara masa dakin sa ba saboda gani yake ba za'a taba yi masa dai dai ba, tunda ya fara aiki bai gama ba har magrib, sannan ya shiga toilet yayi wanka ya chanza kaya ya fito da sauri, yana fitowa yaji dad yana cewa a kirashi su tafi masallaci, tare suka yi sallah suka dawo gida, suna zuwa suka zarce cikin gida, shi dai Sultan duk wani iri yake jin sa, yana zuwa masallaci ya bi jam'i wani lokacin amma bai taba zuwa tare da mahaifinsa ba ballantana ace wai harda siblings. A palon suka tarar an jera abinci a dining amma sam babu Mommy, basu yi magana ba saboda kwana biyun nan haka take yi, kuma Daddy ma baya son su hadu da Sultan har sai yayi mata magana a kansa. Suka zazzauna a dining din suna kallon kallo, can Daddy yace "Sultan ai sai kayi representing Moon, kayi serving din mu" nan da nan Sultan ya washe baki har kunne, ance yayi representing Moon, ya mike har da nade hannayen riga ya fara lafta musu abinci, Walid yayi dariya yace "wannan uban abincin duk kana tunanin zamu cinye?" Sultan yace "why not?" Sai da kowa ya rage nasa abincin amma Sultan ya chinye nasa tas. Daddy ne ya fara tashi ya koma kan kujera, Sultan ne na karshen gamawa, nan ya fara kokarin kwashe kaya, Habeeb yace masa "ka bar shi fa, za'a kwashe ai" Shi Sultan ya saba da yiwa kansa komai, tunda aka kaishi america shi yake yiwa kansa komai, daya dawo Nigeria ma haka. Ya karaso palon, har zai zauna sai kuma yaji ajikinsa kamar zai shiga hurumin da ba nasa ba, sai ya mike zai fita yana jin ba dadi a ransa, Daddy ya kira shi ya dawo ya zauna yace "ina maganar kayan sawa da muka yi da kai?" Sultan ya dan bata rai yace "daddy ni ban taba dinki ba, ban masan inda ake siyar da yadikan ba ballantana wani tailor, amma in na samu zanyi" Daddy ya kalli Walid yace "gobe ka kai shi gurin tailor din mu ya auna shi, sai kuma ku shiga kasuwa kuyi siyayya" sai kuma ya juya gurin sultan yace "zaka iya ci gaba da saka kananan kayan ka a gida, amma duk sanda zamu fita ina so in ganka da manyan kaya da hula" Sultan ya shafa kansa, lallai akwai rigima kenan, shi kam rabon da ya saka traditional hula tun kakansa yana da rai. Daddy ya juya kan su Walid yace "ga Sultan nan, ina so ku rike shi tamkar shima dana ne da baya gurin mu amma yanzu yazo, kar inji kar in gani a tsakanin ku" duk suka amsa. Daddy ya sake cewa da Sultan "yi min bayani akan yadda kake gudanar da aikin ka" nan Sultan yayi masa bayanin yadda yake yi, Daddy yace "abinda za ayi yanzu shine, head office zaka bude, ka dauki ma'aikata sosai, ka saka wa gurin suna yadda zaka yi registering dinsa a matsayin legal firm, da haka zaka ke samun contracts sosai. Na duba ayyukan ka naga suna da kyau sosai dan haka nima zan kara yi maka advertising dan kake samun contract a projects din government. Ina ganin hakan shi zai kara rage kama yawo, in ka samu abinyi zaka fi zama a guri daya" Sosai Sultan yaji dadi, babu wanda ya taba bashi shawara akan me zaiyi da rayuwarsa ko aikinsa. Ji yake yi wata soyayyar Daddy tana shigarsa. Daga nan suka fara hirar su abin sha'awa, a tsokani wannan2, har mamaki Sultan yake dama haka family yake? Dama haka uba yake a cikin 'ya'yansa? Bayan sun tashi daga hirar sunyi sallah isha Daddy ya hau saman su, dakin Mommy ya shiga ya tura kofa, tana zaune tana aiki a computer, taji shigowarsa sarai amma bata dago ta kalleshi ba, a ransa yace 'wai ita menene problem dinta ne?' A bakin kofar ya tsaya yace "Fatima, ina so in sanar miki cewa Sultan ya dawo gidan nan da zama" zumbur ta mike har tana ball da system din gabanta ta karaso kusa dashi da sauri tace "Sultan fa kace?" Sai kuma hawaye "haba dear, ya zaka dauko yaro kamarsa ka hada shi da yaran mu, so kake suma ya bata mana su kamar yadda ya so ya bata Moon? Dan Allah kayi hakuri idan punishing dina kake dan na dauke Moon, wallahi zan dawo da ita, please ka kore shi daga gidan nan" Daddy ya girgiza kansa yace "bazan taba korarsa ba sai dai in shine da kansa yace zai tafi, wanda bana jin zai ce haka, kuma badan kinyi min laifi bane yasa na kawo shi nan ba, a'a nayi haka ne dan naga wani chance ne na samun lada Allah ya dora akan cinyata, shi ɗa na kowa ne, baka san wane ne zai ji kanka ba wata rana, kuma ita rayuwa duk abinda ka shuka shine zaka girba, ina so in shuka alkhairi yadda ko bayan raina zuri'ata zasu girbi alkhairi na. Ban gaya miki ba har sai da ya dawo saboda ina son kiji zafin da naji nima sanda baki gayamin zaki boye Moon ba har sai da kika aikata din. Yanzu bazan matsa miki cewa ki dawo da ita ba har sai na tabbatar da changes din da nake so in gani a gurin Sultan tukunna" daga haka ya juya yayi tafiyarsa. Mommy ji tayi gaba daya duniya tayi mata zafi, lallai Daddy is even softer and weaker than she thought. Amma babu komai, ta tabbatar cewa Sultan will teach him a lesson. Ita kuma ba zata dawo da Moon ba har sai Daddy ya yi learning lesson a gurin Sultan tukunna. Cikin sati daya Sultan ya warware a gidan Ambassador MD. Ba laifi sun fara sabawa da su Walid, in da suke jinjina masa akan tsaftarsa dan gaba daya part dinsu ya chanza fasali kamar ba shi ba, har tsarin palourn sai da yayi rearranging ya chanja labilaye da carpet. Daddy ya samo masa building din da zai bude head office dinsa, wanda ya fara dauka aiki shine Amir wanda dama engineering ya karanta kuma dama tare suke aikin su, nan da nan ya zama busy wajen gyaran gurin da interviewing maaikata, sai yanzu ya kuma gane abinda Daddy yake nufi, dan in yana aiki sam mantawa yake yi da komai ballantana har yayi tunanin shan giya, ko a gida kuma har yanzu yana bin shawarar Moon ta karatun Alqurani duk sanda ya ji yana son alcohol. Shi kansa yana jin chanji akansa, dan nutsuwarsa ta karu sosai. In dai har baya wajen aiki to suna tare da Daddy, dan duk inda Daddy zaije tare suke zuwa dashi da Walid har gurin manyan mutane, nan ya fara koyon saka manyan kaya da yadda ake gaishe da manyan mutane. Rannan har gurin president suka je, kuma he found it very interesting dan babu wanda yayi masa kallon wulakanci babu wani security daya hana shi shiga ballantana suyi rigima. Kuma wani abu da daddy yake yi shine, duk inda suka je sai ya gabatar da Sultan a matsayin babban dan sarkin abuja, duk sai Sultan yaji banbarakwai in yaga mutane suna bashi respect A gida kuma malami Daddy ya dauko na karatun addini, bai ce saboda Sultan ya dauko ba saboda ba ya son Sultan din yayi feeling bad sai yace yaga duk kowa a gidan ya watsar da islamiyya dan haka ga malami nan duk weekend zai ke zuwa za'a ke karatu, har maaikatan gidan duk haduwa ake ana daukan karatu. Nan Sultan da kansa yaga chance dinsa ya dauko alquranin sa ya fito, surorin daya manta duk su suke bi suna tilawa tare da malam. A hankali karatunsa yake dawowa. In akayi dori ranar assabar ran lahadi kuma sai ayi tafsir, ko ayi karatun sauran littattafan addini, sai abin ya koma kamar discussion, kowa ya fadi abinda ya sani ayi masa gyara, in mutum yana da tambaya yayi. Sultan kam ya bude kunnuwansa sosai yana daukar karatu. Matsalar Sultan yanzu daya ce, he terribly missed Moon. Kullum yana so ya tambayi Daddy labarin ta amma baya so Daddyn ya bata rai ko yaga gazawarsa. Kullum da daddare sai ya dauko bathrobe dinta daya dauka a toilet a america, da ita yake bacci yana jin kamshinta. Idan yana zaune shi kadai kuwa sai dai yayi ta kallon pictures dinsu da videos dinsu yana ta murmushi. She really is a Moon, her arrival in his life have brought light to his darkness. Ina ma zamu zama iyaye kamar Daddy? Allahumma Ameen.