Episode Forty Eight: The Past and the Future
by @mamanmaama
Na jima a haka ina kuka mai tsuma zuciya, jikina har rawa yake yi. Why is my life always so complicated, me yasa komai ni baya zuwa min da sauki. I hate hurting Ibrahim. Ya sha wahala sosai akan soyayyata, he deserves happiness from me now, but I can't give it to him because it is not mine, it belongs to somebody else. Lallai kaddarar rayuwa kowa da irin ta sa. Ina jin wayata tana ta ringing, kira na wajan goma kenan, amma ba zan iya dauka ba saboda ba zan iya magana ba. Da zuciya ta da kaina gabaki daya sun toshe kaina sam babu wani abinda yake fahimta, abinda nake tunawa shine naga Ibrahim, kuma soyayyata da na gani a idonsa ta ninka wacce na san yana yi mini a da kafin mu rabu. A hankali na fara abinda na saba yi indai ina so in saisaita tunani na, na fara kiran sunayen Allah daya bayan daya idona a runtse, a hankali nutsuwa ta fara shigomin kuka na ya fara tsayawa. Na bude ido na ina kallon titi, gari ya fara duhu dan tuni anyi sallar magrib. Na fara tunani straight. So Ibrahim did came back like he promised he would. Yanzu kuma saura kwana goma bikina, bikina da Sultan. Ibrahim har yanzu yana so na, yana sona fiye da yadda ya soni a baya. But ya dawo rayuwata a little bit too late. My heart already belongs to another. I loved him before. Nayi masa son da a lokacin nake tunanin ba zan taba yiwa wani irin sa ba. But it is all gone now, abinda ya rage a zuciyata a game da shi shine respect and good wishes. Sultan ya cike dukkanin guraben da suke a zuciyata. Ibrahim yace Allah ya hada mu ne a yau saboda we have a future together, in haka ne kuwa to ba zabi na bane kenan. Even if da akwai sauran son Ibrahim a raina to yana can kasan zuciya ta wanda tono shi sai an dauki lokaci, and time is what we don't have. Even if an tono soyayyar Ibrahim a raina ta yaya zan iya facing iyayena ince musu na fasa auren Sultan wani kuma daban nake so? Wanin kuma da a baya na gaya wa Daddy cewa he is not serious akan magana ta. Komai sanyin Daddy na tabbatar sai naga bacin ransa ballantana Mommy da inajin sai ta kaini psychiatric hospital. I couldn't even imaging tunkarar Sultan da maganar wai na fasa aurensa saboda wani tsohon saurayina da muka rabu kusan seven years back. Duk wanda yaje ya gaya wa Sultan wannan maganar will be like committing suicide. I couldn't even imaging my life without Sultan. Kamar yadda Ibrahim ya fada hakane, God have reasons for everything He did. Tunda Allah ya hada mu yau to da akwai wani abu daya boye a cikin haduwar tamu, ko da kuwa ba aure bane. I just hope that whatever God has planned for us zai kawo happiness a rayuwar Ibrahim sannan kuma ba zai wargaza rayuwa ta da Sultan ba. Waya ta ta cigaba da ringing, na dauka ina kallon sunan Sultan har ta katse, a cikin dictionary din Sultan babu wata kalma wai ita giving up, he never gave up, yanzu kiran nan da ya ke yi min zai yi ta yi ne har sai na dauka ko kuma sai charging wayar ya kare. Na duba missed calls naga 23, amma 5 daga Mommy ne, sauran kuma nashi. Na fara tunanin abinda zance musu tunda duk cikin su babu wanda zan iya gayawa gaskiyar abinda ya faru yau. Mommy na fara kira, bugu daya ta dauka tace "ina kika shiga? Sai da nace muku fa kar ku kai magrib gashi har after seven baki dawo gida ba?" A nutse nace "Mommy mun dan samu matsala ne shagon, Amira ce suka dan samu sabani da wata cashier shine abin yayi delaying din mu, kuma nabar wayata a mota shi yasa ban san kuna ta kira na haka ba" ta dan rage fadan da take yi tace "to amma ai da ko wayar ita Amiran sai ki karba ki kira ki fada mana halin da kuke ciki, ni ba sai inzo da kaina ko in turo wani yaji matsalar da aka samu ba? Na kira wancan yaron ma yace shima yana ta kiranki baki dauka ba, duk kin tayar mana da hankali wallahi" na danyi murmushi a raina nace 'I love you too Mommy' nace "gani nan zuwa yanzu, zan kai Amira gida ne kawai in taho" da sauri tace "NO, duhu yayi kuma unguwar su Amira akwai nisa. Ku tsaya a inda kuke ki kira shi yazo ya same ku sai ya kai ku ya dawo dake gida" nace "yes mother" na kashe. Ina katsewa kiran Sultan yana shigowa, sai da nayi bismillah sannan na dauka, ina dauka yace "damn it! where have you been?" Cikin sanyin murya nace "am sorry Sultan, na manta waya ta ne a cikin mota, muna cikin wani supermarket ne kuma muka samu wata 'yar matsala, but everything is Ok yanzu na kai Amira gida zan taho gida nima" kamar sun hada baki da Mommy yace "no, ki zauna a gidan bara inzo in dauko ki, dare yayi kuma hannunki bai yi kwari ba" nace "yes sir" ya sauke ajjiyar zuciyar da har sai da naji ta ta cikin wayar yace "you almost gave me a heart attack. Gaba na yana ta faduwa, kuma ina ta kiran wayarki tana ta ringing baki dauka ba. Please don't ever do this again in ba so kike zuciya ta ta buga in mutu ba" kalmar mutuwar da ya fada ce ta saka ni nayi murmushi nace "kar ka zama ragon maza mana, ko three hours fa ba muyi da waya ba" yace "anything can happen ai a cikin three hours din, kin san babu abinda ban aiyana a raina ba? Har sai da na hango ki a kasan tirela" nayi dariya, yace "yanzu shikenan date din na mu ya wargaje? Har nayi musu waya nayi mana reserving table" nace "am sorry, in sha Allahu I will make it up to you. Yanzu Mommy tana can tana jirana in muka tafi fada zata yi. Insha Allahu zan lallabata ta sake bari na fita sai muje" ya shagwabe murya yace "baki ga kwalliyar da nayi miki ba fa" nayi murmushi nace "really?, show me, I want to see" yace "how?" Nace "kayi snapping picture ka turo min yanzu" yayi dariya yace "no, it is kind of special, in kina so ki gani sai dai kisan yadda zaki samar mana fita da wuri. Yanzu cirewa zanyi ma in boye" mukayi sallama yace gashi nan tahowa. Na tayar da mota, I have one stop to make, gidan su Amira. A hankali nake tuki saboda hasken fitulu da yake kashe min ido, addu'ah ta Allah ya kaini lafiya kuma Allah yasa kada Sultan ya riga ni zuwa. Cikin sa'a naje na tarar bai zo ba. Na debi kayan ta data siya ta bari a motar na shiga. Mama ce kadai a palour tana cin abinci, na gaishe ta ta amsa cikin kulawa tace "ya akayi kika zo da daddaren nan bayan dazu ta dawo daga gurinki itama?" Nace "wani sako na manta bance ta taho min dashi ba, kuma gobe zan yi amfani dashi" tace "da fatan dai ba ke kadai kika taho ba" nace "a'a kawo ni akayi" tace "kin ga yanzu tsayawarki ta shiga daki amma tunda ta dawo tana kwance a palourn nan, tace bata jin dadine, ki shiga tana ciki" na mike na shiga dakin. Ina bude kofa ita kuma tana shigewa toilet. Na rufe kofar na karasa bakin toilet din na zauna a kasa. A hankali na fara magana "why? Me yasa kika yi min haka? Me tasa kika kasance me son kanki da yawa? Me nayi miki da nayi deserving wannan cin amanar daga gareki?" Shiru babu amsa. Na cigaba "ban taba koda jin labarin mutum marar imani marar tausayi irin ki ba. Nayi miki soyayya ta hakika amma ke ashe duk duniya babu wanda kika tsana irina. Amira babu abinda baki sani ba na wahalar da nasha akan soyayyar Ibrahim amma ashe ko sau daya baki taba tausaya min ba, maybe ma dariya kike min a bayan idona, Amira kina kallona a kan gadon asibiti amma ashe kina da maganin ciwo na kika boye kika hanani. To ki sani, ni babu abinda zan yi miki, na barki da Allah, kuma na tabbata Allah sai ya sakamin cin amana ta da kika yi. Kuma ki sani, kanki kika yiwa. Shi wanda kike claiming kina so shi yafi kowa wahala a cikin duk abinda ya faru, shine kuma still har yanzu a cikin wahalar bani ba. Kuma ki sani, duk da Allah ya kaddaro babu aure a tsakanina da Ibrahim to kema ba zaki same shi ba, saboda Ibrahim baya sonki kuma bai taba sonki ba, kuma ba zai taba sonki ba, especially yanzu daya gano gaskiyar makircin ki, he hates you and I hate you too. Kuma ina gargadinki da kiyi hankali da dosar inda yake saboda yace in dai ya ganki sai na lahira ya fiki jin dadi. Ina fatan zaki halarci bikina nan da kwana goma, ina so kizo saboda ki gani da idonki irin farin cikin da zan kasance a ciki, ina so ki gani da idonki irin sakayyar da Allah yayi min tun a duniya kafin muje can. Ga kayanki nan da kika bari a motar mijina" na mike tsaye, ina jiyo sheshshekar kukanta a cikin toilet na fice, nayi sallama da maman su na fita. Ina fita ana sauke Sultan a taxi. Da sauri ya fito yana bani hakurin ya dade, ya karbi key muka tafi. Muna daukan hanya, ga mamaki na sai naji yace "what's wrong?" Nace masa "me ka gani?" Yace "you look and sound different, kamar akwai wani abu a ranki" na tattaro dukkan charms dina nace "Hey, I am suppose to be the psychologist ba kai ba" yayi murmushi yace "kin san ance zama da madaukin kanwa" nace "to babu abinda yake damuna, kawai dai na gaji ne, kwana biyu bana fita kuma yau mun dan yi yawo, gashi ni nake driving" yace "sorry, kuma gaki dama da son jiki ko? Wannan duk sanda aka fara bikin nan bansan ya zaki ke yi ba" nayi dariya nace "ai wadansu events din skipping zan ringa yi, na gaya muku bana son big wedding kun dage sai anyi" yace "karki damu after the wedding zaki huta sosai and I will be there to help you rest" na harareshi duk da babu haske, dariyar mugunta yake min ban ce masa komai ba, yace "ya kika yi shiru?" Nace "oho maka, kai ka sani" Muna zuwa gida yace wai shi lallai sai dai mu zauna a mota muyi ta hira ba zan shiga gida ba, ni kuwa nasan dan dai gidan da akwai baki ne yasa har yanzu Mommy bata kuma kirana ba amma tana sane da cewa ban dawo ba. Da kyar na samu da lallabashi na gudu. Ina shiga bayan na gaishe da Mommy na tafi dakin Hafsat, kawai so nake in samu in gaya wa wani abin da yake raina ko na dan ji sanyi. Ina shiga na tarar tana lallaba little Khairat, tayi min alama da inyi shiru, na rufe kofar na jingina da jikin kofar ina kallon su, sai da ta kwantar da ita sannan ta juyo tana kallona da murmushi tace "rigimammiya, wai ita lallai a jikina zata yi bacci ba zata kwanta ba" sai kuma ta kura min ido tace "lafiya na ganki kamar wacce aka koro?" Direct nace mata "I saw Ibrahim today" ta dan tsorata da maganar sai kuma tayi sauri tayi getting composure dinta tace "what? A ina? I really hope baki kula shi ba ko baki tsaya kin saurare shi ba" na karaso dakin na zauna a bakin gado ina kallon fuskar Khairat da take ta baccin ta peacefully, nace "na tsaya na saurare shi, ba dan komai ba sai don ina son inji dalilin da yasa yayi abinda yayi" Hafsat ta watso min kallon tuhuma tace "and? I really don't like inda maganar ki take dosa Moon" nayi murmushi nace "inda kike tunani ba nan na dosa ba, I am not going back to Ibrahim, but he will always have a special place in my heart" Daga nan na bata labarin duk abinda ya faru tsakanina da Ibrahim da Amira, bata ce komai ba har na kammala, ina gamawa naga ta mike ta na kokarin saka hijab, nace "ina zaki je?" Tace "I am going to kill that conniving bitch" nayi murmushi nace "shi yace zai kasheta ke kince zaki kasheta, a cikin ku bansan waye zai yi nasara ba amma nasan cewa koma me zakuyi mata ta riga ta aikata abinda ta aikata, kuma duk hukuncin da zaku dauka akanta ba zai dawo mana da hannun agogo baya ba, the past doesn't matter, what matters is the future. Ibrahim is my past, I have a great future to look forward to, I have Sultan" Hafsat ta yar da hijab din hannunta tazo ta rungume ni, I needed the hug, nima na rungume ta inajin zuciya ta tana sanyi a hankali. Mun jima a haka sannan ta sake ni tace "now, what are you going to do?" Nace mata "I don't know. Abinda na sani shine Ibrahim yana son in dakatar da bikina in bashi chance, which I told him I can't. Ya sha wahala akaina sosai kuma har yanzu yana sona, bana son inyi abinda zai kara masa bacin rai fiye da wanda yake ciki yanzu, kuma ni ba zan iya abinda yake so in yi ba. I don't know what to do. Na tabbatar kuma tunda har yanzu yasan bani da aure to zai zo gidan nan, it is a wonder ma da bai zo ba already, ina tsoron haduwar su da Sultan, Sultan is as unstable as a person can be, kuma bai san da labarin Ibrahim ba" Hafsat ta saki baki da mamaki tace "kina nufin baki gaya wa Sultan labarin Ibrahim ba?" Na daga kafada nace "ban taba tsammanin zan kuma haduwa da Ibrahim ba, so I thought there is no need in gaya masa, there is no point in tone tonen abinda yake a binne" ta kalleni da mamaki tace "Moon when will you stop keeping secrets? Duk abinda ya faru bakiyi learning lessons dinki ba. Kin boye wa iyayen mu Ibrahim, kin boye wa Ibrahim gaskiyar su waye iyayen mu, wannan shine asalin dalilin rabuwar ku da Ibrahim. Ki kazo kika boyewa iyayen mu Sultan sannan kika boyewa Sultan zancen project dinki, akazo ba'a kare ta dadi ba. Yanzu kuma you are keeping Ibrahim a secret from Sultan? Again?" Nayi shiru ina jinjina maganarta a raina, she is right, nace "I guess it has all being my fault, it is because I have always been afraid of loosing those I love" tace "gaya wa Sultan labarin Ibrahim ba zai saka Sultan ya rabu dake ba. Ƙin gaya masa sai yafi bata masa rai akan gaya masa" nace "amma ba kya ganin yanzu it is late? In na gaya masa zai ga kamar dan mun hadu da Ibrahim dinne, ya dauka kamar dan ina son komawa gurin Ibrahim ne ko wani abu. Baki san halin Sultan ba, he is unpredictable, kullum gani yake kamar zan iya cewa na fasa aurensa, har yanzu bai yarda cewa zai iya samun farin ciki a rayuwar sa ba, ko ya ya samu wani hint na wani abu ban san me zai aikata ba" Hafsat ta sake shiru sannan tace "what do you want to do?" Nace "so nake inyi iya kacin kokarina inga Sultan basu hadu da Ibrahim ba har bayan daurin aure, sannan sai in gaya masa, at least by then ya san dai na zama tasa already. Shi kuma Ibrahim ina so ya fahimceni ba tare da bacin rai ba". Nine Days to the D-Day Ban tashi da wuri ba saboda ban samu isheshshen bacci ba, kuma na tashi da ciwon kai. Amina da sauran cousins din mu na 'yalleman ne suka takura min da surutu a dakina dan haka na fito kan balcony na rufe kofar daga waje na zauna akan kujera ina jin dadin fresh air din gurin. Na jawo waya na kira Sultan, yana dagawa nace "hey busy body, ya kamata ka dauki leave ka samu ka huta, kar azo ana taro ka fadi ka hada mu da aikin dauko ka" yayi dariya yace "sai kace ke? An gaya miki kowa ma rago ne irin ki?" Nace "am serious, ya kamata ka huta" yace "alright amarya, yadda duk kika ce haka za'ayi. Besides, I need my energy for what is about to come" nayi kaman ban gane inda maganar sa ta dosa ba, nace "ina Amir?" Yace "baki bani amsa ta ba ai" nace "baka da amsa. Ina Amir?" Yace "OK, one day zaki buda baki sosai ki bani amsa. Amir ya dan fita, kina neman sa ne?" Nace "No, ka gaya masa kawai Amira bata jin dadi, so ya nemi Amina su cigaba da shirye shiryen da ita" ya dan yi shiru sannan yace "me ya sameta? I thought you guys were together jiya" nace "tun jiyan dama bata jin dadi, yau ta kira ni tace ba zata samu zuwa ba" muka yi sallama na kashe wayar. I felt bad duk sanda nayi wa Sultan karya, saboda shi baya min, baya taba boye min wani abu daya shafe shi. amma ina jin tsoron gaya masa labarin Ibrahim. A ranar da yamma mai mun gyaran jiki ta zo mukayi, bayan mun gama tace min baza ta kuma dawowa ba sai ranar Saturday, wanda ita ce ranar daurin aure da kai amarya. Ta saka a ka fito mata da duk kayana da Mommy ta dinka min wanda zan tafi dasu gidan Sultan, dan babu abinda aka taba a lefe na duk already an kai su can ance in naje na dinka a can. Ta saka kabbasa ta hada turaren wuta ta turare kayan nawa dashi, tace duk wankin da zan yi musu kamshin ba zai fita ba, ita shine nata gudunmawar bikin. Nayi mata godiya sosai. Ranar Tuesday za'a fara bikin, za'a fara ne da kunshi sannan da daddare a yi bridal shower, Wednesday za'a yi kamu da walima, Tuesday mother's eve da dinner, friday za'a huta sai da daddare su Sultan suyi bachelor's night dinsu, Saturday 12 na rana za'a daura aure da la'asar akai amarya, da daddare kuma za'ayi welcome party wanda Amir ya shirya mana. Shikenan. Eight Days to.... Gidan kam a cike yake yanzu da mutane, daga maza har mata, Munir bai zo ba kuma naji dadi, dan bana son yazo ya kara min wani tension din. Mamansa dai da sisters dinsa sunzo, suna zuwa suka ishe ni da iyayin suna so suga angon, nasan abinda suke nufi, so suke suga waye ya kasa yayansu, babu bata lokaci kuwa na hada su dashi, tunda suka ganshi suka yi kus, babu wacce ta sake magana a cikin su. Da yamma na fita balcony, nan ne gurin zama na yanzu indai ina son in jini ni kadai ko in ina son muyi waya da Sultan. Na dafa railer na dauko wayata ina kokarin kiran Sultan kawai ina daga ido na na hango shi, duk da cewa da akwai distance a tsakanin mu kuma gari ya fara duhu amma na gane shi, yayi packing dan nesa da gidan mu kadan yana tsaye ya jingina da jikin mota ya rungume hannayensa a kirjinsa. Wata irin muguwar faduwa gaba na yayi, Allah kenan, babu yadda baya juya lamarin sa, da akwai lokacin da kullum nake tsayawa a balcony din nan ina kallon waje hoping zan ganshi amma yau gashi ina kallonsa amma maimakon inji dadi sai faduwar gaba na ji. Allah ne kadai yasan dadewarsa a gurin, Allah ne kuma kadai yasan dawa yayi magana. Nasan Sultan dai bai dawo gida ba, baya zuwa yanzu sai dare yayi sosai saboda mutane. Kamar ance ya dago ido sai ga idonsa a cikin nawa, da sauri yayi kamar me shirin tahowa ni kuma nayi sauri naja da baya yanda zai daina ganina. Saboda faduwar gaba har daci nake ji a bakina, na shiga uku, na leka a hankali naga har yanzu balcony din yake kallo. Na koma daki da sauri na shiga toilet, sai da nayi calming down sannan na kira Sultan. Yace "Hello Love" nace "hey kana ina ne?" Yace "naje karbo mana sauran dinkunan mune. What's up?" Nace "babu komai. Kawai dai ina so inji ya kake ne" yayi dariya yace "thanks Love, ko in taho ne?" Nace "I would appreciate that amma kasan gidan yanda yake yanzu, ballantana yanzu da yamma" yace "right, nima daga nan zanje wajan Daniel ne yazo gari, so sai dare zan shigo gidan, hope ba za kiyi bacci ba kafin inzo" nace "yeah, bazan yi ba sai kazo, bye" muna gama wayar na koma na leka balcony naga har yanzu Ibrahim yana tsaye. Da sauri na sauka kasa dakin Hafsat na same tana shirya kayan Khairat, tace "lafiya? Waye ya koro ki?" Nace "Hafsat Ibrahim ne yazo yana waje" tace "and? Kina nufin fita zakiyi gurin sa?" Nace "no, ke nake so kije" ta yatsina fuska tace "ni? Allah ya tsari gatari da saran shuka" nace "Dan Allah Hafsat kije kiyi masa magana, make him understand abinda yake so ba zai yiwu ba" tace "in baki shawara? Ki kira David ki hada shi da shi, nayi miki alkawarin ba zaki kara ganin sa ba" Na girgiza kai da sauri, Hafsat ba zata fahimci abinda nake nufi ba, babu wanda zai fahimci situation dina sai wanda ya taba shiga irinsa. Na zauna a bakin gadon ta nace "I don't want to hurt him I also don't want to hurt Sultan. Please help me" ta dan jima tana kallona sai kuma ta dauki hijab ta saka tace "amma kin san dama can ni ba shiri muke yi da shi ba, dan haka ba lallai ne yanzu ma mu fahimci juna ba" tana fita na koma sama da sauri na kuma shiga balcony na cigaba da lekensa. Ya baro jikin motar ya dawo dai dai opposite din gidan mu, ina kallon Hafsat ta bude gate ta fita. Yana ganin ta yayi saurin karaso wa wajanta, bana hango su sosai yanzu, sun jima suna magana sannan daga baya naga ya juya ya tafi wajan motarsa, kafin ya bude motar ya sake juyowa ya kallo balcony din sannan ya shiga ya tafi. Na dawo daki na zauna ina sauke ajjiyar zuciya, ina jin kuma babu dadi a cikin raina, but haka Allah ya tsara mana ni da shi, we are not destined to be together. Ina nan zaune har Hafsat ta shigo, ta jefo min wani complimentary card tace "gashi nan yace a baki, he is so hot headed sai da na kusa loosing temper dina, he believes hada ku aure akayi da Sultan, yace yaji labarin dan sarkin garin nan ne, shi a ganin sa kin yarda da auren ne saboda babu shi. Yayi yayi in bashi number dinki na hana shi shine ya bani card dinsa yace in baki ki kira shi, yace in baki kira shi ba zai sake dawowa gobe" Ta zauna a kusa dani tace "Moon, ki kira Sultan ki gaya masa halinda kike ciki, he will know what to do" na girgiza kaina nace "Sultan will definitely hurt Ibrahim in na gaya masa, he will act first and then think later" tace "to ki fada wa David ya hana shi zuwa gidan nan" nan ma na girgiza kai "securities will treat him badly and I don't want that" ta mike a fusace tace "to hada kayan ki ki kirashi yazo ya dauke ki ku gudu tare a fasa auren" ta fice a fusace ta bugo min kofa. Kwalla ce ta taru a idona ina jin zafi a raina. Na sunkuya na dauki card din nasa ina karanta sunansa kamar ranar na fara ganin sunan, kallo daya nayi wa number din na haddace ta na jefa card din a waste bin. Ina bukatar inyi addu'ar sosai in nemi Allah's guidance. Ranar kam da daddare haka na tashi nayi ta jero adduoi akan Allah ya fitar dani daga matsalar da nake ciki, Allah ya saka wa Ibrahim dangana ya fahimci cewa ni ba matar sa bace ba. Seven days.... Na tashi zucita ta fes kamar babu abinda yake damuna. Muna ta harkokin mu da 'yammata Amir ya aiko kiran Amina zasu je su gano venue din dinner. Muna zaune sai ga kungiya guda nan ta kawayen mu na sec sch, nan fa guri ya kuma hargitse wa, muna ta hira sai ga Hasiya nan ta shigo daga baya, tana zuwa tace "guess wa na gani a waje yanzu?" Tun kafin ta fada nasan waye, nan take cikina ya kada tace "uncle Ibrahim" nan da nan suka kuma rude wa "yana ina?" "Moon dama kuna da contact dashi?" "Ko sallama yazo?" Duk ban basu amsa ba, Hasiya tace "yana waje wallahi, ina ganin sa na gane shi, kunga yadda ya kara kyau kuwa? Ya goge sosai ya zama dan gayu fiye da yadda kuka san shi a baya" Walida tace "ke Hasiya, kina matar aure kike kallon wani ko? To wannan maganar kamar a kunnen abban Na'im" duk muka yi dariya tacigaba da cewa "da muka gaisa ma bai gane ni ba fa, wai yasan fuskar a cikin kawayen Moon amma ya kasa tuna sunan, sai da na gaya masa sannan ya tuna. Yace yaji labarin bikin Moon shine yazo yayi mata Allah ya sanya alkhairi amma ya rasa wanda zai aika ya kirawo ta, nace masa in na shigo sai inyi mata magana sai yace kawai ma sauri yake yanzu in bashi number dinta zai kira ta, shine na bashi" Hannu biyu na dora aka nace "kin bashi number ta fa kikace?" Ta kalle ni da mamakin yadda na rude tace "eh na bashi, Murna fa zaiyi miki shikenan, kuma ba'a daura ba ballantana kice kin zama matar wani ba zaki yi waya da wani ba" a raina nace "Hasiya had killed me" na tuna dramar da mukayi da Sultan akan musbahu ballantana Ibrahim. Duk abinda muke yi Hafsat tana jin mu bata tanka ba, sai kawai naji tace "'yan 'uwa ku matso in baku wani labari" duk suka juyo suna kallonta, ta cigaba "kun tuna rannan a makaranta da Ibrahim yace wata a ajin mu tana sonsa amma shi baya sonta?" Duk suka ce eh, tace "a lokacin nace muku zan fada muku wacece amma Moon ta hana, to yau zan fada muku kuma har da bonus na labarin duk abinda tayi" da sauri nace "Hafsat no, please don't do this" bata jira abinda nake cewa ba ta kwashe labarin Amira kaf ta gaya musu, ta cigaba da cewa "sai shekaran jiya sannan Allah ya toni asirinta suka hadu a supermarket, kun ga ikon Allah ko? Da Allah ya tashi kamata ita da kanta ta kai Moon har office din Ibrahim" Nan take gurin ya hargitse da hayaniya, daga masu dure2n ashar sai masu Allah wadaran halin Amira, Hafsat ta cigaba da cewa "na fada muku wannan ne saboda idan da akwai wacce take da saurayi to tayi musu katanga da Amira, mai miji ma haka, dan bamu san kan wanda zata koma ba kuma" Zulaihat ce dama masifaffiyar ciki ta mike tace "waye zai je gidan su Amira ya koya mata hankali?" Nan take duk suka mike har da Hafsat, dama ita tun shekaran jiya take son zuwa na hanata, na mike na sha gabansu, "dan Allah ku bar maganar nan, na riga na samu mijina ita kuma ta rasa Ibrahim din bashi kenan ba, shima Ibrahim Allah ya bashi matar data fini" ture ni sukayi gefe suna kumfar baki suka fice, Hafsat ce ta tsaya tana kallona tace "at least this will teach her a lesson tasan cewa tayi ba dai dai ba, amma in dai aka barta zata ga kamar taci riba ne ai, this will serve as a lesson to her da duk masu hali irin nata" Ni dai anan na durkushe a bakin kofa ina hawaye, Amira was a good friend to me, she was my best friend for about 13 years, ni in ta nine ma zan so Ibrahim ya aure ta amma nasan ba zai aure ta din ba. Maman ta kuma kawar Mommy ce, naso rigimar mu ta tsaya a tsakanin mu bana so iyaye suji. Waya ta naji tana kara na duba, number din Ibrahim na gani, na san za'a rina dama, na ajiye ban dauka ba, ya cigana da kira kusan missed calls biyar sannan ya hakura, message naji ya shigo, shima ban bude na karanta ba na goge shi. Sai can bayan la'asar sannan su Hafsat suka dawo suna ta dariya "dan Allah kuyi hakuri, ku bawa Moon hakuri dan Allah" wai haka Amira take cewa, kawai hawaye naji yana taho min, nace "da Amira ta raba mu da Ibrahim da kar ta raba mu, Allah ya riga ya kaddaro ba miji na bane ba" sukace "ke ai sanyin zuciya ne dake, da ace wani zai kashe ki ki sake dawo wa duniya ya baki hakuri cewa zaki yi kin hakura" Sai kuma suka koma gulmar Ibrahim, "kin san har yanzu yana waje?" Nace "oho muku ku kuka sani" Hasiya tace "ni wallahi tausayinsa nake ji, Moon yana sonki da yawa wallahi" na harare ta nace "to bara in hada su shida Sultan in aura kawai". Hafsat ta gama tsara musu yadda events din bikin zasu kasance sannan suka tafi suka barmu ni da Hafsat da Hamidda. Gab da magrib sai ga Amina ta shigo, fuskarta kamar gonar auduga, tana shigowa tayi tsalle ta fada kan gadon tana birgima. Muka bita da kallo da sakakken baki, sai da ta gama haukanta sannan tace "Albishirin ku" muka ce "goro" tace "at last yau wani yayi noticing cewa ni kyakykyawa ce" tsaki muka ja a tare ni da Hafsat, Hafsat tace "Allah ya shirye ki Amina" ta tashi zaune tace "am serious fa, anan waje muka hadu dashi bayan Amir ya sauke ni, ya taho da sauri yana yi min magana wai ya dauka ke ce" ta fada tana nuna ni, guiwata naji tayi sanyi na zauna akan stool, ta cigaba "ni ban san me yasa mutane suke hada kyakykyawar mace kamar ni da something like Moon ba, ni banga wani kama da muke yi ba" nayi dariya nace "shi yasa aka kasa noticing kyan naki ake noticing nawa" Hafsat tace "uhum, me yace miki kuma?" ta cigaba "cewa yayi he is a friend of Moon, yazo yana son ganin tane, daya ganni ya dauka itace shine ta taso. Yace muna kama sosai ko ni 'yar'uwarta ce, sai nace masa ni yayarta ce, shine yace shi Hafsat kadai ya sani yayarta, nace masa aini ba'a nan na taso ba a England na taso. Ya bani number sa yace in na shigo in kira shi sai in baki. Oh my God Moon ya hadu da yawa" na mike na shige toilet na rufe kaina sannan na jingina da jikin kofa na runtse ido na, a fanfon na tara fuskata na saki ruwa kawai sai da naji numfashina yana neman daukewa sannan na cire kaina na goge fuskata da towel na koma dakin, ina shiga naga ta danna wayar ta ta miko min tace gashi, na jima ina kallonta sannan na karba, tace bara taje tayi sallah ta fita. Na zauna a bakin gado na saka wayar a kunne na naji already ya dauka, nace "assalamu alaikum" sai da ya sauke ajjiyar zuciya sannan ya amsa. Nayi shiru. Yace " babu gaisuwa ma?" Nace "good afternoon" yace "yauwa ko ke fa, at least dai ai nayi deserving gaisuwa daga gare ki. Please Moon why are you doing this to us? Please don't punish me like this. Ba laifi na bane ba. I was led to believe kinyi aure. Kuma ko da hakan ma sonki bai ragu daga zuciyata ba sai ma karuwa da yayi. I know you love me too. I saw it in your eyes a office dina. You just have to tell Daddy cewa wanda kike so is here, a ajiye maganar wannan Sultan of a thing din....." A hankali nace "Sultan is not my parents choice, he is mine. In fact daga farko ma parent dina basa sonsa nina matsa cewa shi nake so sannan suka yarda" yayi sauri yace "saboda bana nan ne yasa kika zabe shi Maimunatu. I am back now. Mun sha wahala Maimunatu kar kiyi mana haka. Abinda Hafsat tayi ta cewa kenan wai ke kika zabe shi. Whatever you think you feel for this man, believe me it is not love." Nace "Ibrahim, please don't make this harder than it already is. I know you are hurting and believe me, bana jin dadin haka sam. Amma abinda kake nema daga gare ni is just not possible. Ko da ace Sultan ba zabi na bane ba bazan iya tunkarar iyayena at the dying minute in ce musu na fasa auren nan ba. Ballantana ni na zabe shi. Put your self in his position, ace kana da budurwa kunyi maganar aure da ita, you went through alot together, kun sha wahala kuka yi convincing iyayen ku, an gama komai hatta jere anyi sai kuma few days to daurin auren ku sai tace ta fasa auren ka, how will that feel?" Yayi shiru for some seconds sannan yace "very bad" nace "good, to believe me it will feel more than very bad to Sultan, it will destroy him completely" yace "me yasa nasa zaifi na kowa zafi?" Nace "because he is kind of special" da sauri yace "ouch, that hurts" na danyi dariya nace "sorry" ya dan jima baiyi magana ba, sannan yace "do you think you will be happy with him?" A hankali nace "yes" muryarsa very deep with emotions yace "then I will be happy for you" wasu hawaye masu zafi naji sun taru a idona. Muka sake shiru sannan yace "Can I at least see you one last time?" Na danyi jim ina tunani, nace "not now, Sultan zai iya zuwa anytime" yace "OK, I understand. Nagode for at least talking to me. Good night" ya katse wayar. Na ajiye ina jin zuciyata babu dadi.