Episode Fifty Two: The Cook
by @mamanmaama
Ranar baƙin gidan mu suka zo yi mun sallama, daga 'yan 'yalleman har 'yan Niger duk washegari kowa zai tafi gida. Zuwan su ne ya saka na manta da hirar mu da Baba Gaji. Nan take 'yammata na suka fara hidima dasu, sun iya aiki sosai dan ba sai nace ayi abu ba zanga kawai anyi, da kyar na samu kebewa da Amina nace mata "Amina kin kira Ibrahim din kuwa?" Ta dauke kanta ta bata rai tace "na kira shi ones, bai dauka ba ni kuma na rabu dashi" sai naji ba dadi a raina, it has been three days, ya kamata ace an san halin da yake ciki. Nace "please Amina ya zaki yi haka, gashi gobe zaki tafi and I don't know who else zan saka" ta daga min hannu tace "relax, ba tare zamu tafi dasu ba, Mommy tace in zauna anan for the time been" nayi ajjiyar zuciya nace "please Amina, kema kinsan ai ranar in kika kira shi ba zai dauka ba amma yanzu at least na san ya dan huce zai saurare ki" Ta kara tabe baki tace "I will try amma ban miki alkawari ba, in naga yana daga min kai I won't go around chasing him" na yarda a haka. Sai bayan zuhr Sultan ya dawo, tun daga waje yaga motocin gidan mu dan haka sai ya zagaya ta baya ya shiga ta great room dinsa sannan ya kira ni a waya ya ce min ya dawo. Ina shiga palourn sa na ganshi a zaune ya kunna TV da remote a hannunsa, na tsaya daga bakin kofa nace "sannu da zuwa" ya juyo yana kallona sai ya nuna min cinyarsa yace "come here" na makale kafada, yace "to ni ma bana cin mike, bana amsa gaisuwa daga nesa" na karasa shigowa na rufe kofar nace "Sultan baƙi ne a gidan, in na zo nasan ba bari na zakayi in fita da wuri ba" ya bata rai yace "da ni da bakin waye yafi muhimmanci?" Ban bashi amsa ba nace "amma ai su tafiya zasu yi ko? Sallama suka zo yi mana fa" yana kallona kasa kasa yace "OK, just a kiss, shikenan" na karasa gurin sa na tsaya, ya nuna min lips dinsa yace "here" na matso da fuska ta dai dai tasa, ina kallonsa har da lumshe ido wai shi nan za'a yi masa kiss, na cije shi kadan akan hanci na juya da gudu, ina jinsa yace "ouch, zan kama ki ne" na juyo nayi masa gwalo na fice. Sai bayan la'asar baki na suka tafi, na koma gurin Sultan na tarar yana lunch din da na kai masa tun dazu, nace "au baka ci abincin ba sai yanzu?" Yace "bayan yau wulakanta ni kike yi dan kinga 'yan gidan ku ko? Tun dazu nake jiranki kizo muci abincin shine kika ki zuwa ko?" Na karbi cokalin a hannunsa nace "am sorry, ban dauka zaka jira ni ba, nasan halinka da abinci" na diba na fara bashi a baki, yaji dadin hakan sosai, na tambaye shi "how are the kids?" Take naga fuskarsa ta haska da murmushi yace "they are fine, suna ta tambayarki, wai suna so su shirya mana surprise party" nayi dariya nace "then it is no longer a surprise tunda sun gaya maka" yace "kuma bayan gaya min din da akayi har list aka bani na abubuwan da suke bukata for the party" ya dauko wata takarda muka fara karantawa, tarkace ne nasu balloon da ribbons, har da cake, wai suna so a jikin cake din a rubuta 'happy married life mom and dad, we love you' muka yi ta dariya nan na kara abubuwan da basu saka ba. Bayan Sallar magrib sai ga Hafsat da Zayed da little Khairat suma sunzo mana sallama zasu koma England. A palourn Sultan zauna dasu muna ta hira. Hafsat da tsegumi har bedroom din Sultan ta shiga, yace "Hey lady, me zaki yi min a daki ne? Baki san cewa bedroom dina sirrin mu bane ba?" ba tare data kalleshi ba tace "koma menene ba sirri ba sai na gani, nasan babu abinda zan tarar sai kazanta" ta shige ciki, ta dade kafin ta fito, knowing halin Hafsat nasan har toilet ta shiga, tana fitowa Sultan yace "kin dau bashi, duk sanda naje gidan ku sai na shiga dakinki" mu dai dariya muke musu ni da Zayed. A nan Hafsat take gaya min in sun koma England Zayed zai dauki leave zasu je saudiyya, dan 'yan'uwansa da yawa basu santa ba ga kuma Khairat itama babu wanda ya santa. Tare muka yi dinner ina ta mamakin yadda Sultan yake sakewa da Zayed duk sanda suka hadu, dan yadda yake yi masa ko yaya Walid da suka saba sosai baya yi masa haka. Sai very late sannan suka tafi, ji nayi kamar zanyi kukan rabuwa da Hafsat tunda ban san kuma ranar da zamu sake haduwa ba in dai ba wani abun ne ya tashi ba. Sai bayan mun kwanta bacci sannan na fara bitar hirar mu da Baba Gaji, na kalli Sultan naga idonsa a rufe amma nasan ba bacci yake ba, nace "Sultan" yace "uhmm" nace "will you one day like to see your mother?" Yayi shiru kamar bai ji abinda nace ba, na daga kai na kalleshi sai naga ya bude idonsa yana kallon ceiling, ya jima a haka sannan yace "No" da mamaki nace masa "why?" Da murya mai kaushi yace "I don't need her now. Sanda nake bukatar ta a lokacin ta ajiye ni ta tafi. I wish her happiness a ko ina take a duniya but I don't wish to meet her. Me yasa kika tambaye ni akanta yanzu?" Nayi tunanin in gaya masa labarin ta da na samu sai kuma nayi tunanin bani da wata concrete magana for now, zan gaya masa amma sai na sami more answers, nace "babu komai, kawai dai naji ta fado min a rai ne" ya kara jawo ni jikinsa yana saka fuskarsa a wuyana yace "forget about her kinji, itama yanzu ta manta dani, am sure ta haifi wasu 'ya'yan yanzu. I have you, I don't need anybody else". Washegari muna palour da Baba Gaji naji sallamar Amir, Baba Gaji tace ya shigo, ya shigo muka gaisa nace masa "wato kwana biyu ko leƙe ko?" yace "ni da aka kora ina zan kuma dawowa" muka yi dariya yace "tare da bakuwa muke" na kara fadin murmushi na nace "really? Tana ina?" yace "Amira ce" take murmushin fuskata ya bace, yace "ta gayamin duk abinda ya faru tsakanin ku, tace ta turo miki message cewa tana so ta zo amma baki ce mata komai ba, shine nace bara in kawo ta in taya ta bada hakuri, she made a mistake na sani and you have every right to cut her off, but tayi nadama, kuma duk ɗan Adam yana kuskure......" Na dakatar dashi nace "it was not a mistake. Mistake shine abinda zakayi daga baya kayi realising cewa kayi ba dai dai ba sai ka bada hakuri kace kayi mistake, amma ita bata yi realising ba har sai da Allah ya tona asirinta, dan haka ba wai nadama tayi ba kawai dai an riga an kama tane babu yadda zata yi" Ya gyada kai yace "na fahimce ki, amma ina so ki saurareta, ta baki labarin in her own version, na tabbatar zaki yafe mata" na daga kafada nace "ni ai already na yafe wa Amira, abinda bazan yi ba shine ba zan kuma bata space a rayuwata ba ballantana har ta kuma cin amana ta" Yace "OK let me call her in now" ya tashi ya fita sai gasu sun dawo tare, fuskarta tamkar ba Amiran dana sani ba, idanuwanta sunyi circle din baki alamar kuka da rashin bacci, bakinta duk a bushe, bana jin ko mai ta shafa ballantana kwalliya. Tana shigowa nace da Baba Gaji ta bamu guri, sai da ta fita ta rufo kofar sannan Amira ta karaso inda nake zaune, nace "sannu da zuwa" bata amsa ba sai ta durkusa a gaba na, hawaye ya fara bin fuskarta tace "Moon dan Allah ki yafe min abinda nayi miki. Dan girman Allah. Wallahi nayi nadama ba tun yanzu ba. Son zuciya ne ya saka ni nayi abinda nayi da kuma sharrin shaidan. Tun da dadewa nake so in gaya miki amma na kasa gaya miki saboda bana son ki yanke friendship din mu" nace "Amira, ni na yafe miki already, saboda ni ma ina da laifuffuka na a gurin ubangiji kuma ina son idan na nemi yafiyarsa ya gafarta min. Amma hakan ba yana nufin cewa we are back to friends zone bane ba. I can never be at ease with you again" Ta goge hawayen fuskarta tace "ni hakan ma yayi min. Dama can I never deserve to be your friend. Tun sanda aka kawo ku muna jss 1 naga kin burge ni, 'yar karama dake gaki kyakykyawa, sai daga baya na fahimci how smart you are, duk mun fiki girma da shekaru amma kin fimu kokari. I wanted nothing more than to be your friend. Ban dauka zaki kula ni ba, na dauka zaki zamo mai girman kai amma sai naga ba haka bane ba, naga kina da saukin kai fiye da duk sauran mates din mu. Moon you will never know how much I admire you. Sanda aka yi hutu kika bani address din ku nazo sai naga how rich your parents are, how awesome your family are, you have everything, you are everything I wanted to be. You were my role model, I always wanted to be like you but I couldn't" "Lokacin da su Ibrahim suka zo, you guys were laughing at them. I liked him kallon farko da na yi masa. In kuna yi masa dariya har haushin ku nake ji a raina amma ba zan iya fada ba saboda bana so in bata miki rai. I didn't know love then, kuma ko da na sani ma I doubt in zan iya fada masa ina son sa. Ban san ya akayi ba kawai sai na ganku tare a matsayin saurayi da budurwa. I was angry as to how can you have everything I wanted and then still have him? Amma babu abinda zan iya yi akai dole na hakura nake kallon ku, lokacin da ya fara yi min