Maimoon

Episode Sixty Seven: Lost But Found

by @mamanmaama

Ibrahim's POV Last thing da ya gani kafin motar sa ta fadi shine fuskar Moon, and she looked so scared. Sanda motar sa ta fadi babban tsoron sa na shine mutuwa ba, tsoronsa shine kar wani abu ya samu Moon because of him. A lokacin daya dawo hankalinsa abinda ya fara tunawa shine Moon, fatan sa Allah dai yasa babu abinda ya same ta, dan haka kalmar daya fara furtawa itace "Maimunatu" muryar mamansa yaji a kusa dashi tana yi masa magana, sannan kuma yaji shigowar wani namiji yana tattaba shi, mutumin ya bude idonsa ya haska masa wata karamar fitila, daga nan kuma ya koma bacci. Sai daya farka for the second time sannan ya fahimci kwanansa uku a asibiti unconscious, ga maman sa da little Moon sun zo daga Ibadan, amma ita maman sa abinda aka gaya mata shine accident yayi, ba ta san dalilin accident din ba, dan haka ya san bata da labarin ko Moon taji ciwo ko bata ji ba. Doctor ya saka ya kira Amina, wacce tun da ta kai shi asibiti kullum sai ta je ta duba shi, haka ma Daddy, Doctor ya gaya wa Amina cewa ya farfado kuma yana nemanta, ba'afi awa daya da wayar ba sai gata tazo. Sosai ta nuna murnar ta daganin ya dawo hayyacinsa, ta ringa yiwa doctor din tambayoyi akan lafiyar Ibrahim din har sai da ta fahimci babu wani muhimmin concern dangane da lafiyar tasa, shi kam Ibrahim kallonta kawai yake yi yana murmushi, sai da doctor ya fita sannan yace "har haka aka damu dani dama ni ban sani ba?" Tace "no, ba damuwa nayi da kai ba. Naso ace ka balla spinal cord yadda ba zaka sake bin mata da miji ba" yace "yes you are right. Nasan banyi dai dai ba, komai yayi min ni na jawo wa kaina, I was just scared he would hurt Moon" Tace "matarsa ce fa? In ma menene zaiyi mata ina ruwanka? Kuma ma Sultan will never hurt Moon. Yanzu gashi sanadiyyar abinda ya faru sunyi rigima, har ya kwanta a asibiti ma. She is pregnant fa. You ought to get over her by now" Yace "I am over her. Abinda ya faru nima ban san ya akayi ya faru ba and I feel sorry na jawo problem a tsakanin su. Is she OK?" Tayi ajjiyar zuciya ta zauna a kujera tace "yes she is fine" yace "please can you go to her ki bata hakuri on my behalf? Ki basu hakuri ita da mijinta" ta bata fuska alamar bata son zuwa, ya marairaice murya, "please kinga bani da lafiya fa. Take little Moom with you in suka ganta sai sufi hakura". Har ran Amina bata so zuwa ba, ita a ganinta menene kuma na zuwa wani bada hakuri? Ai kamar kokarin tayar da magana ne kuma, aikin gama ya riga ya gama, daga Ibrahim har Sultan kowa jikinsa ya gaya masa shikenan magana ta wuce sai dai fatan a kiyayi gaba kuma. Amma sai ta yarda zata je din to put his mind at ease. Ta dauki little Moon suka tafi tare. Moon ta tare su sosai kuma taji dadin ganin takwararta amma kamar yadda Amina tayi tsammani sam ba ta ga alamar soyayyar Ibrahim a tare da Moon ba, sai care da mutunta juna, tace mata zata zo ta duba Ibrahim amma ita kan ta Aminan ta san fada kawai Moon tayi ba zuwan za tayi ba. Da zasu taho Moon ta hada kaya da yawa ta bawa takwararta suka dawo asibiti gurin Ibrahim. Suna shiga dakin suka tarar Ibrahim ya tashi zaune suna magana da Mama, Amina ta durkusa ta gaishe da Mama wacce ta amsa mata da fara'arta, daga nan Mama ta fita ta basu guri suyi magana. Ba tare daya kalli Amina ba yace da little Moon "sweetheart menene wannan a leda kika samo haka?" Ta karaso gurinsa tana washe baki tace "namesake dina ce ta bani" ya karba yana dubawa "wow duk wannan naki ne ke kadai, bata baki komai ki kawo min ba?" Tace "ba abinda ta bani in kawo maka" yace "kuma bata ce tana gaishe ni ba?" Tace "eh bata fada ba" ya dauki yarinyar ya dora a cinyarsa, yana shafa kanta "sweetheart yau kinga namesake dinki ko? How do you find her?" Tace "she is beautiful and nice" yace "yes sweetheart she is the nicest person I have ever known". Amina ta ajiye ledar hannunta ta juya zata fita, sai a lokacin ya tuna tana gurin, yace "wait" bata juyo ba yace "Maimunatu Please wait" Chak ta tsaya kafin ta karasa kofar, ta juyo a hankali tana kallonsa, a nutse ta fara magana "I am not Maimunatu, I am Amina" ya tsaya kawai yana kallonta dan shi bai ma san ya kirata da Maimunatu ba sai data fada. Ta kalli little moon akan cinyarsa tace "Moon je ki nuna wa Mama kayan da kika samo" Da sauri yarinyar ta dauki ledar ta fita da gudu. Bayan ta rufe kofa sukayi shiru suna kallon juna, yace "am sorry, I didn't mean to hurt you, ban san ya akayi bakina ya kauce ba" tace "cut it. Dalilin da yasa ka tura mu gidan Moon kenan wato, because you still love her, duk abinda kake fada min cewa you are over her duk ba haka bane ba, kace baka san dalilin da yasa kabi su a baya ba amma ni nasan ka bi su ne saboda har yau baka hakura da ita ba. To bara in gaya maka wani abu, she is more than over you. Tun kafin tayi aure ta daina son ka ballantana yanzu. She is happily married. She is not coming back to you. The sooner you get this into your thick head the better for you. Am not Maimunatu I am Amina, duk da mun hada jini da ita hakan ba yana nufin feelings din mu da halayen mu daya ne ba. Duk da munyi kama da ita ba hakan yana nufin zan iya rikidewa in zama ita ba. I am my own person. I can't be a substitute for someone, I refuse to be a substitute for Maimoon. You loose something a rayuwar ka Ibrahim, ka koma baya kayi tracing may be You will find it. Idan kuma baka samu abinda kayi loosing ba then I pity your soul" ta juya ta fita. Ibrahim ya dafe kansa tare da cewa "ya salam" ya koma da baya ya kwanta akan gadon. "What is wrong with me dear God" Duk abinda Amina ta fada gaskiya ne, sai da ta fada kuma sannan ya kara tabbatar da cewa gaskiya ne. He enjoys being with her only because in yana tare da ita sometimes yana jin kamar yana tare da Maimunatu ne, amma kuma yasan ba maimunatun bace ba. Sannan kuma da gaske ne har yanzu yana son Moon, no matter how much he tells himself and others cewa he is over her but shi ya san he isn't. Amma kuma mai take nufi da he lost something, tana nufin yayi loosing Maimunatu? But ai that's obvious, to menene yayi loosing?. Gaba daya ji yayi ya kasa sukuni, duniyar duka tayi masa kunci, me yasa shi rayuwarsa take a haka ne? Sam ya kasa samun farinciki tun ranar da ya juya bayansa ya tafi yabar Maimunatu a gidansu tana kuka, ba zai iya tuna ranar da yayi farin ciki ba, genuine farin ciki, ba kuma zai iya tuna ranar da wani yayi farin ciki domin sa ba. Hatta mahaifiyarsa kawai yasan hakuri take yi dashi amma bajin dadinsa take yi ba. What did he miss? Moon is over him ya sani, dan har a cikin idonta yana gani, his love is gone, amma shi why can't he get over har? Satin sa daya aka sallame shi daga asibitin, cikin satin nan ya kara zama miserable, dan har 'yar karamar Moon ma tsoron sa take ji dan daga tayi wani abu kadan zai daka mata tsawa, daga asibitin Mama cewa tayi ba zasu je gidan sa ba, yaje yaci kansa shi kadai, ta dauki jikarta su kayi tafiyarsu tasha suka hau mota suka koma ibadan. Shi kadai ya koma gidan sa inda yake zaune shi kadai, ya kira number din Amina yafi cikin charbi amma bata dauka ba, yasan in yaje gurinta ma ba fitowa zatayi ba kuma shi din ma yana tunanin mai zai ce mata in yaje din? Ranar daya koma gurin aikinsa sai da ya kori mutum uku daga aiki, ya bawa wadansu query, gaba daya kowa ma haushi yake bashi, shi kanshi haushi yake bawa kansa. Rannan ya dawo daga office kawai yaki komawa gida, to in ya koma gidan ma me zaiyi a can? Wa zai gani a can? Ya kama driving yana zagaya gari a hankali fresh air tana kada shi, ya fara tuno kalaman Amina, she said he lost something a rayuwarsa, she adviced him to trace back his life yayi finding menene yayi missing. To in zaiyi tracing back ta ina zai fara? Kafin ya koma gida ya yanke shawarar he is taking the next flight to Ibadan, tunda anan ne rayuwar sa ta fara, in ma yana da matsala anan ne zai samu solution. Da sassafe jirgin su ya sauka a Ibadan, ya dauki taxi ta kai shi unguwarsu. Ya sauka ya tsaya yana karewa gurin kallo, babu abinda ya chanja, ya kalli masallacin da a da babansa yake limanci, ya tuna da lokacin da suke zuwa masallacin tare da babansa, he was so innocent and happy then, what has happened? Ya shiga gidan su da sallama, jakarsa rike a hannunsa, mamansa da take wanke kwanuka ta tsaya tana kallonshi da mamaki. Shi kuma gidan yake karewa kallo, babu abinda ya chanza sai tsufa da gidan ya kara yi da lalacewa. Ya tuna da uwar dukiyar da yake tarawa yake ajiye wa a banza, for what? Ya ajiye jakar hannunsa anan tsakar gidan ya nufi dakin da Baba ya zauna kafin rasuwarsa, ya tura kofar ya shiga yana feeling kamar zai ganshi akan tsohuwar kujerar sa da alqurani a gabansa. Ya shiga dakin sosai yana kallon tarin littattafan addini a jejjere kamar yadda suke kullum. Cikin littattafan nan babu wanda bai haddace from page to page ba. Amma ina ilimin ya tafi? Ya juya ya kalli mahaifiyarsa da take tsaye still tana kallonsa, ya sani cewa jin dadin rayuwar mutum duniya da lahira yana jingina a jikin how much yake kyautatawa iyayensa, amma shi baya kyautatawa tasa uwar, duba gidan da take ciki duba gidan da shi yake ciki a Abuja. Amma ai da ba haka yake ba, da sanda bashi da komai amma dan albashinsa biyu yake rabawa ya kawo mata rabi, lokacin ma tana da miji ba yanzu ba da bata da kowa sai shi. Ya tuna da baban sa da yadda yayi making sacrifices dan yaga ya zama wani abu a duniya saboda yana da burin cewa shi ne zai rike mahaifiyarsa da kannensa duk sanda babu shi a duniya amma look at what he has become now, idan da Baba zai dawo ya ga yadda yake rayuwarsa mai zai ce masa? ta yaya zaiyi tsammanin rayuwarsa zata tafi masa a dai dai? how did this happened? When? When did he loose himself? Sai yanzu ya gane maganar Amina, ba wani abu yayi loosing ba sai kansa, he lost himself the moment da yayi deciding yana son yayi kudi dan ya auri Moon, tun daga ranar he became slave to the idea of becoming rich for Moon. Duk da karyar da Amira tayi masa cewa Moon tayi aure amma ya kasa cire hope din cewa zata dawo gurinsa, kuma yana son sanda zata dawo ta tarar cewa he is richer than yadda tayi tsammani. Duk tsahon shekarun nan komai yayi dan ita yake yi ba dan kansa ba. Hatta kaya in ya saka sai yayi tunanin in ta ganshi yanzu what will she think? In tunaninsa ya gaya masa ba zata so kayan ba sai ya cire ya saka wadansu. He became so obsessed in preparing for her to come back to him that he lost himself along the way. But insha Allah it is over now. He found himself now. Everything is going to be alright now. Mama ta karaso bakin kofar tana kallonsa tace da yarabanci "Seun lafiya kake kuwa? Yaushe kazo gari? Me kake yi a dakin nan?Ya juyo ya dawo gabanta ya tsaya yana kallon ta, noticing how old and tired she looked, sai kuma ya rungume ta da sauri yana jin hawaye yana taruwa a idonsa, yace "Mama dan Allah ki gafarta min. Nayi kurakurai a baya, rayuwata gaba daya bata tafiya dai dai. Dan Allah Mama ki yafe min kiyi min addu'ah ko Allah zai dube ni ya shiga rayuwata" Ta dago fuskar sa tana kallon sa tace "my son, ni ban rike ka da komai ba, kullum addu'ah nake maka Allah ya dawo da kai kan hanya. Kuma Alhamdulillah tunda har kazo ka nemi gafara ta to na tabbatar ka fahimci kuskurenka. Allah yayi maka jagora"