Episode Seventy Four: Maldives
by @mamanmaama
Riyadh; Three weeks after the gender reveal party. Sosai Takawa yake putting pressure a kan Sultan, Sultan ya kara saka ni nayi wa Ummee magana amma wannan karon ko kallon kirki ban samu daga gareta ba. Sai ma ce min tayi in gaya wa wanda ya turo ni yazo ya same ta da kansa. Sam yanzu Sultan bashi da cikakkiyar nutsuwa, yana son komawa gurin babansa kuma baya son ya bata wa ummeen sa rai. Ina yin iyakacin kokarina gurin kwantar masa da hankali amma nasan Sultan is a busy person, zaman banza da rashin aikin yi shi yake irritating dinsa, duk da ya samu Ahmad sun kulla abokantaka, kullum zai zo ya dauke shi su fita amma hakan is not enough for Sultan. Yanzu har ya kai matakin in Takawa ya kira Sultan sai yaki dauka, he is out of excuses. Rannan ina shiryawa zan shiga gurin Ummee Sultan kuma yana kwance akan kujera ya rufe idonsa, nasan ba bacci yake yi ba, sai da na gama shiryawa sannan na durkusa a kusa dashi na hura masa iska a fuskarsa, ya dan bude ido yana kallona, nace "zan shiga gurin Ummee" ya mayar da idonsa ya rufe yace "zan shigo an jima" na tashi na tafi jikina babu dadi, bana son ganin Sultan cikin damuwa sam, sai inji duk nima na shiga damuwar. I must do something about this. Ban sha wahalar hada Sultan da ummeensa dan in cigaba da ganinsa cikin damuwa ba, amma kuma menene abinyi? A harkar da ta shafi iyaye dole mutum yayi taka tsan tsan. A bedroom na sami Ummee tana zaune a kan gado da system a gabanta, na shiga da sallama, ta amsa min idonta akan screen din system din, sannan tayi min alama da hannunta na inzo in zauna kusa da ita, ina zama ta juyo min da screen din system din, fuskarta dauke da murmushi tace "what do you think of this?" Na kalli abin da take nuna min, model ne na dakin baby, with complete furniture, crib, drawers, night stand, changing table da komai, dakin yayi kyau sosai, amma kuma Sultan ya gama tsara mana baby room din mu tun sanda yake zana plan din gidan mu a Abuja. Na kasa bawa Ummee answer, ta cigaba da magana "ina tunanin bedroom din tsakiya na part dinku za'a mayar nursery, Sultan sai yayi mana dan renovating dinsa kadan, yayi closet a ciki, sai mu fara order kaya kuma, furnitures first, sai electronics sannan sai mu dawo kan clothings" tayi ajjiyar zuciya, "we have alot to do, list ya kamata mu rubuta..." Sallamar Sultan ce ta katse mata maganar ta, muka amsa masa a tare, yana kallon mu yace "yau hirar ta daki ce kenan" ta dan bubbuga kan gadon kusa da ita tace "come Abubakar, sit with us" ya karaso ya zauna yana satar kallona, tace "we were just talking about the baby, nursery muke so mu fara shiryawa, muna bukatar taimakon ka gurin renovating dakin" ya dan dafe kansa kamar mai ciwon kai yace "Ummee babyn nan fa yana da atleast wata uku kafin yazo, besides already yana da room dinsa a Nigeria" take naga murmushin fuskarta ya kau, tace "Nigeria? I tot I made myself clear cewa babu zancan komawa Nigeria ko?" Sultan ya bata rai, he has reached his limit. Ya saka hannu ya dauko wayar sa yana dialing, kawai sai gani nayi ya ajiye ta akan table din gaban gadon, tana kara sai kuma mugaji an dauka, muryar Takawa, yace cikin fada "Sultan wato ina ta kiranka shine kaƙi dauka ko? Wannan wanne irin aikin banza kake aikatawa haka? Kawai ka dauki iyalinka ka tafi dasu can wata uwa duniya ku zauna a can? Zaman me kuke yi har yanzu? Aikin da ka bari wa zai yi maka? Wa kake tunanin zai ke kular maka da companyn ka?" Sultan yayi gyaran murya yace "barka da yamma" Takawa yace "bazan amsa ba, me ya hanaka dawowa har yanzu?" Sultan yana kallon Ummee yace "bani na hana kaina tahowa ba, Ummee ce tace bazan dawo Nigeria ba a Riyadh zan cigaba da zama, na saka ka a speaker phone yanzu tana jin abinda kake cewa, sai kuyi magana a tsakanin ku" na kalli fuskar Ummee naga wani mixed emotions, sama sama take numfashi, ta kasa magana, Sultan ma ita yake kallo ita kuma wayar take kallo. An jima a haka sannan Takawa yace "Khairat, kin san dai bai kamata kice zaki hana yaron nan dawowa gidan su ba ko?" Ta hadiye yawu ta kara bata fuska tace "why not? Nan ma ai gidan su ne, kamar yadda yake da iko da gidanka haka yake da iko da nawa. Kamar yadda kake da iko dashi haka nima nake da iko dashi, in fact na ma fika iko dashi, nace ba zai dawo ba and that is final" Yace "you can't do that. Aikin sa kuma fa?" Tace "wani zan samar masa anan" yace "'yan uwansa kuma fa da suke ta nemansa anan me kike so in ce musu? Mutanen gari fa da suka dogara dashi me kike so in ce musu? He is a Prince for God's sake Khairat, he has a role here, ko anan ma zaki samar masa matsayin Prince din ne?" Tace "bazan mayar dashi Prince anan ba amma zan bashi rayuwa fiye da wacce zaka bashi a matsayin Prince din, zancan me zaka gayawa mutane kuma oho, that's your problem not mine, abinda na sani shine dana yazo gurina kuma babu abinda zai kuma rabani dashi sai mutuwa" Ya kwantar da murya Yace "Khairat wannan maganar tsakani na da ke ce, ki bar Sultan ya taho tare da iyalinsa, kin san dai halin da Moon take ciki, she needs her family besides her, in yazo sai mu taho tare dani dashi mu zauna muyi maganar sosai" ta danyi dariya tace "am not a kid ballantana kayi min wayo, Maimunatu will remain here ita da abinda yake cikinta, idan family dinta suna son ganinta da kansu zasu taho nan su ganta and she is free to go and see them anytime she wishes, ai dama aure babu inda baya kai mutum, aure ne ya kawo ta Riyadh, kuma babu wata care da zaku bata a can wadda bazan bata a nan ba" Yace "amma dai kinsan nima ina da right akan su ko? Yanzu abinda za'ayi tunda sunyi wata biyu a gurinki, ki turo su suyi wata biyu anan sannan sai su take dawowa, kinga shikenan kowa will spend sometimes with him babu wanda zaice an cuce shi" Tace "wata biyu? Cuta? You must be joking, sai da yayi shekara talatin ban ganshi a idona ba, how can you tell me wata biyu? In so kake a raba sai ka bari in yayi shekara talatin anan sannan ya koma gurinka" da sauri yace "shekara talatin? Do you think zan kara shekara talatin a duniya? Me yasa kike nema ki zamo mai son kanki ne?" Tace "son kai? Ai sai dai inyi maka wannan tambayar, tunda har ka iya bugo waya kace masa ya koma gurinka, saying you will let him come back again, bayan you don't keep your words, you never keep your words, you will keep me waiting and waiting till eternity" ta fada muryarta tana kakkatsewa kamar zata yi kuka. Ya danyi shiru da alama maganar ta shige shi sannan yace a hankali "am sure Sultan ya gaya miki duk abinda ya faru bayan rabuwar mu, so am sure kinsan ba wai a sona na barki zaman jira tsahon shekaru ba" tace da karfi "that's your problem not mine" yace "yes, it is my problem amma let me ask you something, ke menene ya hanaki zuwa kiga dan naki har tsahon shekaru talatin, ko kina son kice daure miki kafa akayi duk tsahon shekarun nan, baki damu dashi ba tunda har baki neme shi ba" Nan da nan hawaye ya taru a idon Ummee, ni dai ina zaune sai in kalli Ummee in kalli wayar, Sultan ya mike tsaye yace "wait, all of you, ya ishe ku haka. All of you are forgetting something, am not your little love anymore. Am not a toy da zaku ke playing around with har kuna lissafin zaku ke passing dina around for one one month or one one week. Wannan duk maganar da kuke is between the two of you, dani da iyalina ba zamu kasance in the middle of it ba, ba zamu zama ball ba balle wannan ya buga ya bawa wannan ya buga. We will go away. Duk ranar da kuka yi settling kanku just give us a call sai mu dawo, amma ku tabbatar a cikin settlement din babu zancan muje gurin wannan sannan mu sake komawa gurin wannan, we are not toys, we are our own people" Ya mika min hannu na kama ya daga ni tsaye, babu wanda yayi magana a cikin su sai Ummee data fara ruwan hawaye, ya cigaba da cewa "Daddy wannan waya tace kuke fada a cikin ta, kana iya kiran wayarta sai ku cigaba a fadan acan" Takawa yace "Sultan listen to me, kar ka dauki yarinyar mutane da ciki kana yawo da ita gari gari, zanzo Riyadh din, we will talk things out" Sultan yace "in kun gama talking things out din just give us a call" ya kashe wayar yana kallon Ummee, ita din ma shi take kallo, ba tare daya ce mata komai ba ya ja hannuna da sauri muka fita. Muna shiga part din mu ya zarce bedroom ya fara fito da kayan mu yana zubawa a kan gado, sannan ya jawo akwatina yana jerawa a ciki, hada wa kawai yake yi da nawa da nasa baya ware wa. Ni dai kawai ina tsaye ina kallon sa, nace "are we really going?" Yace "yes, and don't try to talk me out of it" nace "I won't. Amma ina za muje?" Bai kalle ni ba yace "am not stupid, so kike in gaya miki ki gaya mata ko? But know one thing, ba America zamu je ba saboda can ne inda Takawa zai fara neman mu. In sun gama fadan zamu dawo. Zamu bar wayoyin mu a bude yadda zamuke magana dasu" Nace "idan haihuwa ta kama ni a can kuma fa, mu kadai ya zamuyi?" Yace "a haka suka haife ni su kadai. And believe me, ba zasu kai har lokacin haihuwarki basu shirya ba, duk kansu kowa yana so ya zauna a waiting room ranar da zaki haihu" nayi murmushi dan nasan irin lissafin da Ummee take yi kullum, wani lokaci har tunani nake yi anya kuwa zata ke bani babyn ina dauka?. Tare muka zauna muka shirya kayan mu. Basics kawai muka dauka yace ma sayi kayan sawa sosai a can, dan haka kananan jakankuna kawai muka dauka guda biyu, lokacin an kusa sallar magrib, muna fitowa daga part din mu na nuna masa part din Ummee ya makale kafada "I don't want to see her crying" na tafi ni kadai, na tura kofar na shiga, tana zaune akan kujerar data zauna ranar da na fara zuwa gidan, idonta akan kofa, ta saka hannayenta a tsakanin cinyoyinta. Na tsaya a bakin kofa ina jin tausayinta har raina, Takawa zai iya tafiya neman Sultan amma ita she is tied to saudiyya, dan haka dole sai dai azo gurinta ita ba zata iya zuwa wani gurin ba. Ta mike tsaye tana jujjuya hannunta tace "bai gaya miki ina zaku je ba ko?" Nace "yes" tace "yana ina?" Na nuna mata waje, na karasa kusa da ita na rike hannunta nace "I will call you daga duk inda muka je" tace "magrib tayi yanzu, kice masa ya bari sai da safe sai ku tafi" nayi shiru dan nasan ba zai yarda ba, Sultan is soo headstrong in ya saka kansa abu babu mai hana shi, ta dora hannun ta akan cikina taji yadda dan cikin yake motsi sai ta danyi murmushi tace "be safe, ki kula dashi kamar yadda kika saba" nace "insha Allah" na juya na fita ina goge hawayen fuskata. Ina fita na tarar Sultan har ya dauko daya daga cikin motocin gidan ya shiga yana jirana, na shiga ina cigaba da kuka na, yace "cry cry baby, dake da ita bansan wanda yafi wani ruwan hawaye ba" sai kuma naga ya juya yana kallon kofar shiga gidan, nima na kalli gurin, Ummee ce a tsaye, tayi folding hannayenta a kirjinta, mayafinta ya sauko kan kafadarta, iskar da ake yi a gurin tana ta yawo da gashinta, she looked so lonely and depressed. Sultan yayi sauri ya dauke kansa ya ja motar da gudu muka bar gurin, ni kuma har muka fita gate idona yana kanta. Muna fita naga ya dauko wayarsa yana kiran Ahmad, tambayarsa yake hotel me kyau inda zamu iya kwana, Ahmad yana tambayarsa lafiya amma bai gaya masa komai ba, daga karshe dai gidan Ahmad din muka fara tafiya muka dauko shi sannan ya rakamu hotel din, yana ta mitar me yasa to ba zamu kwana a gidan saba amma Sultan yaki yarda, kuma sai da ya saka shi yayi masa alkawarin ba zai ce da kowa komai ba, ya gaya masa zamu dawo wata rana amma ba yanzu ba. Wani lafiyayyen hotel ya kaimu, Sultan ya biya kudin kwana daya, ya tambayesu in da akwai motar da take zuwa airport da safe suka ce masa eh, kawai sai ya bawa Ahmad key din motar da muka taho da ita yace ya ajiye motar a gurinsa, Ahmad ya tambaye ni ina zamu je na ce masa nima ban sani ba. Dan karamin daki ne single room mai hade da toilet, amma kuma ya hadu sosai. Sultan yayi mana order abinci sannan ya dawo ya zauna a kusa dani fuskar sa da alamar da yace "Moon, do you think what am doing is right?" Bance masa komai ba saboda bansan abinda zance masa ba, yace "I don't know what to do shi yasa nayi haka, ina son komawa Nigeria dan acan rayuwata take ba nan ba, amma kuma bana son inyi hurting Ummee, ba zata iya bina ba saboda shi is tied to saudiyya, I don't know what to do, we will just let them figure out me zasuyi sannan sai mu dawo" Na ce "ina za muje?" Ya danyi murmushi yace "do you promise not to tell any one?" Nace "can I at least tell Mommy?" Yace "yes, only Mommy" nace "OK. I promise" yace "am taking you to the Maldives. Dama nayi miki alkawari tun tuni amma ban samu na cika miki ba" yana murmushi yace "we are going to have our honeymoon" nayi dariya na nuna masa cikina, yayi kissing cikin yace "he is welcome to join us". Ranar Sultan bai kwanta da wuri ba, yana ta making phone calls, ya saya mana ticket, ya kama mana hotel a can Maldives din, sai daya tabbatar komai is settled sannan ya kwanta. Washegari daga nan Riyadh muka shiga wani dan karamin jirgi zuwa Maldives. Tun a jirgi nasan lallai da gaske Sultan honeymoon din yake so, nima na biye masa. Kusan duk wadanda suke cikin jirgin couples ne, tunda shi Maldives guri ne da ake zuwa mostly for vacations and honeymoons. Maldives kasa ce amma ba kamar sauran kasashe ba, tana consisting thousands of islands a indian ocean, saboda yawan islands din wadansu islands din ma babu mutane a ciki. Capital dinsu shine Malee, wanda shine babban island din da yafi kowanne girma, kuma anan ne mutanen kasar suke zaune, sauran islands din duk an barwa tourist, wadansu islands din ma saboda kankantarsu hotel daya ne kawai a gurin, wadansu ma babu hotel din sai dai ayi 'yar bukka ayi decorating gurin mutane suna zuwa su wuni ko su kwana. A Velana international airport muka sauka, which is an island on it's own, daga nan kuma kowa sai ya fadi inda zaije sai yayi hiring speedboat a kaishi. Malee Sultan ya fara cewa za muje, nan mukayi ta zagaya garin muna kallon haduwarsa, muka shiga mall dinsu mukayi siyayyar kayan da zamu bukata a hotel din da zamu sauka. Ni kam maternity gowns nayi ta siya, sexy maternity gowns, Sultan kam kananan kaya yayi ta diba, ya siya min wadansu nima amma ni nasan cikina ba zai barni in saka ba, na dai samu wadanda nasan zasu saku na dauka, bama bukatar abinci ko toiletries duk hotel din mu zasuyi providing. Daga nan muka tafi port din su muka hau motor speedboat dinsu zuwa Island din Soneva Jani, wanda shine hotel din da Sultan ya zabar mana. Tun a cikin boat din Sultan ya fara karbar amarcinsa, dan sanda muka zo hotel din ma bamu sani ba sai da me boat din yazo yayi mana knocking yace munzo. Muna sauko wa na saki baki ina kallon gurin, ni in ana cewa hotel abinda yake zuwa kaina shine dogon gini da manyan glass Windows da balconies, sam ba haka gurin yake ba, cabins ne separate from each other, gaba dayansu a cikin ocean suke, sai hanyar da tayi linking from one cabin to another. Daga gefe kuma beach ne, the sand is as white and as soft as snow sai tall trees a zagaye da beach din. Ruwan ocean din is so clear yadda har kana ganin kifaye suna swimming a ciki, ga hasken rana yana reflecting on the ocean, iska mai dadi tana kadawa. This is totally a paradise on earth. Allah kasa muna da rabo a cikin aljannar ka. In za'a samu guri mai kyau irin haka a duniya ya kake tunanin aljanna take? Sultan ya kama hannuna yace "welcome to my dream. Tun ranar dana ganki na fara sonki, kuma tun sanda na fara sonki nake mafarkin kawo ki gurin nan" nace "ka taba zuwa ne dama?" Ya girgiza kai yace "just pictures nake gani ina saving" nace "it is really good, kamar mafarki, kamar ba gaske ba" A bakin beach din muka tsaya hand in hand muna kallon sunset, it looked so good, gani zakayi kamar sun din lumewa take yi cikin ocean, sai kuma ta bada rainbow colors a cikin ocean din. Sai da rana ta gama faduwa sannan muka shiga reception cabin din, muka ciccike wadansu takardu, aka tambaye mu how long zamu zauna Sultan yace "indefinitely" gaba daya sai da mukayi dariya a gurin. Desk officer din ya kalli cikina yace "so, are you guys on honeymoon?" Sultan yace "yes, the baby decided he wants to enjoy the honeymoon as well" muka sake yin dariya. Mutanen gurin were very friendly. Cabin din mu single room ne amma katon gaske, in kana so zaka iya raba dakin biyu da labule, da round bed karamin na dakin Sultan a abuja, sai kujeru manya masu kama da gado, da kuma kananan kujeru guda biyu, da duk kan electronics din da aka san mutum zai nema da akwai a dakin. Kowanne cabin da akwai dan karamin swimming pool din da aka jawo masa ruwa direct daga ocean, yadda har kifaye suna iya biyo ruwan su shigo cikin swimming pool din. Setting din dakin looks so romantic yadda bai kamata ma mutum yaje shi kadai ba. Room service yana gama ajiye mana kayan mu, yayi setting komai na dakin sannan ya bamu keys ya juya ya fita, yana fita na juya ina kallon Sultan nace "let's stay here, forever" yace "am glad you like it" ya daga ni ni da cikina ya ajiye akan gado, na dan ture shi nace "ba muyi sallar magrib ba fa" yace "dama ai sai munyi wanka za muyi sallar, gwara mu jefi tsuntsu biyu da dutse daya". Ya saka dan yatsansa yana zagaye lips dina da suke dauke da murmushi, sannan a hankali ya dora red lips dinsa akan pink lips dina.........