Maimoon

week

by @mamanmaama

Hakan kuwa akayi, kusan duk garin Abuja lungu da sako, unguwannin masu kudi da kuma unguwannin talakawa babu wanda bai samu sako na ba. Nan take 'yan jarida suka samu abinyi, Sultan kin zuwa yayi office a satin, Takawa kuma yace a rufe gate din palace kar abar wani dan jarida ya shigo. Kamar yadda nayi tsammani, talakawan duk da Sultan yake taimakawa, wadanda nasan labarinsu da wadanda ban sani ba, haka suka ringa fitowa suna gaskata maganganuna na cikin takarda ta, wadansu ma shi kansa Sultan ya manta dasu, haka aka ringa dauko dukkan files dinsa na gurin police ana resolving cases din. A haka har zancen orphanages dinsa ya fito shima, 'yan jarida kam sun samu abin yi, nan suka dukufa bincike har suka tonawa dan majalissar da yace shine yayi orphanage din farko asiri. A satin, kusan duk jaridar daka dauka hoton Sultan ne a front page dinta, anyi masa title 'Our Prince' wadansu kuma su rubuta 'Our Lion'. Sultan kam har yanzu bai ce komai ba, in ma na kunna TV ana maganar sai ya chanza channel. Ni kam babu abinda nake yi sai godiya ga ubangiji da yasa plan dina ya zama successful. Sultan's name is now clear a cikin mutane. Babu wanda in Sultan ya wuce zai zage shi, ko an samu mai zagin ma, to kuwa tabbas za'a samu masu kare mishi. 'Ya'yana ba zasu tashi ana musu gorin babansu was a criminal ba. Wannan kenan. Satin biki ya kama. Gidan mu ya chika kamar yadda aka saba in za'ayi biki. Ballantana wannan da yake bukukuwa ne ba biki ba. Hatta Zainab din ya Walid an dauko ta an dawo da ita Abuja, anan za'ayi bikin baki daya. Hafsat ta dawo gidana, tace can yayi hayaniya da yawa, dan haka daga nan za muke shiryawa mu fita tare. Sultan ma tunda bikin yazo kullum suna tare da su Ya walid, amma kuma hankalinsa gaba daya yana kaina, dan badan Ummee ta saka baki ma ba da ba lallai ne ya barni zuwa bikin bama gaba daya. Yanzu ma kuma babu kwana, sai dai inje in wuni da daddare in dawo gida. A tare muka hada amaren mu da angwayen mu muka kama su rana daya duk a gida. Akayi mothers eve ranar thursday, ranar friday kuma za'ayi wuni, Saturday a yi daurin aure, da yamma akai amare sannan da daddare ayi dinner. An kai dinner din Saturday ne saboda ana son Fadila amaryar ya Habeeb ta samu damar halarta itama. Tun a ranar Thursday da daddare na lura kafafuwana sun fara kumbura, nasan wannan normal ne ga mai tsohon ciki musamman kuma ga hidimar biki da muke yi, dan haka da daddare na kwanta da wuri na dora kafata akan pillows, sam ban nunawa Sultan ba saboda ba karamin aikinsa bane yace bazanje ranar wuni ba, ranar wuni muka shirya da sassafe muka fita, aka wuni ana shan shagali, sai dare sannan muka dawo gida. Muna zuwa gida Hafsat ce tayi min maganar yadda kafa ta ta kumbura suntum, tace "Moon you should stay home tomorrow, ki huta, daurin aure ne sai kai amare, dinner da daddare za'ayi kafin nan kin huta" nasan gaskiya take gaya min, I already have high bp, wannan kumburin nawa is not normal edema, it may be pre-eclampsia, amma sai nayi tunanin ai in naje goben ba wani abun zanyi ba, zama kawai zamuyi, in za'aje kai amare da dauko amarya zan iya zama na inki zuwa, sai da daddare in je dinner. Na riga Sultan kwanciya dan haka na rufe jikina bai ga kumburin ba, kuma da sassafe ya fita, zasu fara zuwa bauchi daurin auren yaya Habeeb sannan a dawo Abuja a daura na ya Walid da Zainab da kuma na Amina da Ibrahim. Ban bi shawarar Hafsat ba saboda ina ganin babu yadda za'ayi in zauna a gida bayan ana can ana shagali a gidan mu. Sultan yana tafiya nabi Hafsat muka tafi gida. Komai lafiya lau yake tafiya har aka yi daurin aururruka aka gama, aka zo hidimar kai amare. Dama already wadanda zasu dauko Fadila sun riga sun tafi, sai aka tafi kai Zainab tunda ita ta gida ce ba sai an jira anzo an daukar ta ba. Basu dade da tafiya ba sai ga masu daukan Amina sun zo, nan fa kallo ya koma sama, duk aka fito compound ana kallonsu dan wani sabon bikin suka bude, sun yi shigar su irin ta yarabawa sunyi kyau sosai, sun taho da kaya sukace a bawa Amina ta saka, ina daga kwance naga kallo zai barni dan haka na mike nima na fita, wata 'yar matashiyar budurwa ce tazo ta tsaya gaban Amina ta karanta wata doguwar takarda mai dauke da dogon jawabi akan irin soyayyar da Ibrahim yake yi mata da alkawarin da yayi na zai rike ta amana, inta amince to ta bisu su tafi, in kuma bata amince ba to ta zauna a gida. Daga haka ta mika wa Amina hannu, Amina ta saka hannunta a cikin na yarinyar, nan take guri ya kaure da murna. Hayaniyar gurin ce tasa naji kaina yayi wani mugun sarawa, na rike kan da sauri, ganin babu wanda ya lura dani ya saka na lallaba na koma daki, ina duba hannayena naga sun kumbura suma, na kwanta akan gado na lumshe ido na ina jin ciwon kaina yana karuwa ga kide kiden da akeyi tamkar a cikin kaina suke kadawa. Na lalubi wayata na kira Hafsat amma wayar tana ta ringing bata dauka ba. Na koma na kwanta. Cikin hikimar ubangiji aka daina kidan, ina jin karar motoci alamar an tafi kai Amina itama. Take naji gidan tsit dan kusan babu kowa a manya, babu kuma wanda yasan ina dakin, kowa zai dauka na tafi kai daya daga cikin amaren. Na danji kan ya rage ciwon, na tashi na nemi jakata na sha magungunana sannan na koma na kwanta. Take bacci mai nauyi ya dauke ni. Muryar Mommy ce ta tasheni, tana tabani tace "Moon dama kina gida? Ya akayi kika zauna ke kadai? Da wani abun ya faru fa?" Ni dai bance mata komai ba, tunda wani abun bai faru ba ai shikenan. Har yanzu akwai ciwon kan, na tashi zaune ina rike kaina Mommy tana ta jera min sannu, na kalli agogo naga har anyi magrib, dan haka na shiga toilet nayo alwala, ina dawowa dakin na kalli fuskata a madubi naji gaba na ya fadi, gabaki daya fuskar ta kumbura, na kalli hannayena naga har kyalli suke. I really needed to go to the hospital right then amma bana son in tayar wa da mutane hankali ana cikin biki. Na tayar da sallah, nayi magrib da isha gabaki daya, ina kallon mutane sai shirin tafiya dinner sukeyi amma ni kam nasan wannan dinner din babu ni a cikin ta. Na koma nayi kwanciyata. Mommy ta shigo ta samu guri ta zauna tana kallona. Nace "Mommy baki fara shirin tafiya ba?" Tace "Moon ina zanje baki da lafiya? In naje ma ba zanji dadin dinner din ba, dan hankali na biyu zai rabu" sai naji babu dadi a raina, dan nasan kawayen Mommy da yawa zasu je gurin kuma za'ayi ta nemanta, nace "Mommy kiyi tafiyar ki kawai, ai ba wani abin ne yake min ciwo ba, kawai dai ina bukatar in huta ne shi yasa ba zanje ba" ta jawo pillow tana murmushi tace "nima ina bukatar hutun ai" nayi murmushi, dan nasan babu abinda zan gaya wa Mommy wanda zai saka ta tafi gurin dinner din nan ta barni a gida, God bless our mothers. Hafsat ma ta shigo tayi tayi Mommy ta tafi ita ta zauna amma Mommy taki yarda. Ni dai daga nan na koma bacci. Karar waya ta ne ya tashe ni, na duba naga 'my Sultan' na dauka ina jin ciwon kaina yana karuwa, yace "Moon baki da lafiya me yasa baki kirani ba?" Ji nake kamar a cikin kaina yake maganar, nace "ai muna tare da Mommy, babu wani abu, kayi zamanka in an tashi sai kazo mu tafi gida" yace "you dey craze? Ya zanyi in zauna anan babu ke? Am coming right away" daga nan ya kashe wayar. Mommy tana zaune tace "zuwa zaiyi?" Nace mata "eh, dama ki shirya, in yazo kawai sai mu tafi gida ke kuma sai ki tafi gurin taron" ta gyada kai tace "bara yazo din tukunna sai in shirya. Ina baba gajin ki? Anan gurinki take kwana ko?" Nace "eh, anan take kwana. Ummee ma ta karo min wata baba Sa'a". Muna tare da Mommy Sultan ya aiko a gayamin yazo, Mommy tace ace masa ya shigo dakin, ita kuma ta fita ta tafi nata dakin. Ina kwance ya shigo, ya tsaya a bakin kofa, na tabbatar ya lura da yadda jikina ya kumbura, yace "menene yake miki ciwo yanzu?" Nace "ciwon kai ne, sai jiri da nake ji inna tashi" ya karaso ya zauna a bakin gadon ya taba wuyana yace "your temperature is also high. BP din ne ko?" Na gyada masa kai. Yace "dama abinda nayi ta lissafi kenan. Wannan hayaniyar da zirga zirga is not good for you" na kirkiro murmushi nace "an gama ai. Babu dadi idan aka ce banzo ba, Amina babu abinda bata yi min a bikina ba. Ga su ya Walid suma ba zasu ji dadi ba" ya bata rai yace "da baki zo ba duk zasu fahimta, ai sunsan condition dinki" bance komai ba na rufe idona, dan maganar ma karamin ciwon kan take yi. Mommy tayi knocking ya tashi ya bude mata, ta shigo tana kallonsa tace "zaku tafi ne ko anan zaku zauna?" Yace "gwara mu tafi can din dai tunda yafi shiru zata fi hutawa sosai" tace "hakane, dan ana dawowa daga gurin dinner wanda bashi da high bp ma sai nashi ya tashi" ta juyo tana kallona na dan yi mata murmushi nace "bye Mommy" tace "bye-bye, sai munyi waya" sai da muka ji tashin motar ta sannan Sultan ya kama ni na mike tsaye muka fita, a hankali muke tafiya saboda jiri da nake ji, daga karshe ma dai dauka na yayi ya sakani a mota, ya zagaya ya shiga ya kunna motar yana kallona, na kirkiri murmushi nayi masa shima ya mayar min, amma nasan nashi murmushin bai kai zuci ba. Ya kama hannuna daya ya rike a hannunsa daya, yayi intertwining fingers din mu ya dora akan gear sannan ya tura hannayen mu a tare muka saka gear muka fara tafiya a hankali, hankalinsa rabi akan titi rabi akaina, hannunsa daya akan stirring wheel daya a cikin nawa. Na kwantar da kaina a jikin kujera ina jin dadin kamshi da sanyin motar, amma maimakon inji bp dina yana sauka sai naji yana kara hawa, na kalli Sultan na tuna da ranar dana fara ganinsa, a hankali naga ya fara zama dishi dishi, this is my worst fear tun sanda na samu ciki, preeclampsia, a raina nace 'ko yanzu na tafi, at least nayi wani abu a rayuwata".