EHSAAS

Chapter 1

by @fatoumspassion

(Nuristan Clinic)

Awani irin gudu nasoma ganin nurses suna fitowa daga cikin ainahin asibitin zuwa farfajiyar inda wata ambulance take karasowa cikin wani irin mahaukacin gudu kararta ta karade ko ina nacikin asibitin da kewayensa. yayinda nurses din jikinsu har rawa yakeyi dama wasu daga cikin likitocin don ace sune sukai nasarar ceto rayuwarta,aiko ambulance din na tsayawa sukayo kanta cikin azama aka fito da ita ana turata akan gadon marasa lafiya zuwa cikin asibitin babu abinda kake gani daga jikin mara lafiyar amman duk wanda ke gefe da gefen gadon yana jiwo muryar marar lafiya wanda da alama macece tana ambaton sunan Allah,tana rokonsa yakare mata shi kawai,sosai nurses din ke mamakin halin datake ciki bama wai rokon Allah take yasauketa lafiya cikin matsanancin halin nakudar datake ba, amman sena yatsare mata wani can daban SIR EHSAAS sunan datake ta ambata kenan har aka shigar da ita dakin CS. inda duk masu mata rakiya da nurses dinsuka tsaya se manyan likitocin da ake jidasu ne suka karasa shiga ana kullo kofar wasu daga cikin nurses din mamakine yacika su ganin yariman nata da taketa ambata har akai kusan minti talatin da shigarta aiki babu shi babu dalilinsa dukda yajja jami'an tsaro suka karaso suka yiwa kofar section din da take kawanya bame shiga se wanda suka kawota haka nurses din keta gulmar abin cikin ransu. Itakanta uwar soro dake kai kawo tareda Mai babban daki sun shiga rudani domin sunkasa gane tashin hankalin da yarinyar taji kota gani dayasa ta cikin wannan halin taketa ambatar sunan EHSAAS,uwar soro kanta yakulle gaba daya domin koda EHSAAS baya garin tabbas tasan da ankira angaya mishi halin da Islam din ke ciki tabbas zebar duk abinda yakeyi ya taho ko ya kira yaji lafiyarta amman me harta wayar tasa bata shiga. mai babban daki ce tashiga kwantar mata da hankali tana gaya mata cewar "maybe ko network ne shiyasa har yanzun basu sameshin ba" nan yay daidai dashigowar wani dattijon mutum kana kallonsa kasan babban mutum ne dawani saurayi abayansa yana tafe yana dada kai waya kunnansa,adaidai yana karasowa gun matayen ya katse kiran yana kallon uwar soro data zuba mishi ido tana jiran kosun samu wani bayani gameda EHSAAS din,ganin ya girgiza mata kai tunkan tai magana tadafe kanta kawai. saurayinne yakaraso yana rungumeta cikin sigar kwantar mata da hankali yake fadin "uncle will be fine in sha Allah Great G kidena damuwar nan kinji," jinjina kanta kawai tai, Mai babban daki takalli dattijon tana tambayar sa "ko yasamu su galadima awaya? sune wadanda aka tura nemo yariman,amman me suma babusu babu labarin su wannan abu yakara ta yarma da uwar soro hankali dan saurayinne yacigaba da kwantar mata da hankali yana me sanar mata "gimbiya mima nanan akan hanya in sha Allah komai ze zo cikin sauki Allah ze sauki auntynsa Islam lafiya yakuma dawomai da kawunsa gida cikin aminci," daidai nan wutar da ke kunne lokacin da akemata CS ja yamutu ba jimawa likitocin suka soma fitowa daga ɗakin cikeda nutsuwa babban likitan yakalli uwar soro yana mai gayyatar ta zuwa office dinshi domin yimata karin bayani akan jikin Islam din. amman me tambayoyin da wannan dattijon da me babban daki suke masa kan me akasamu? shinko islam din ta haihu? abin yaso batama uwar soro rai bama ta lafiyar yarinyar sukeba ta lafiyar jikansu dake cikinta sukeyi, doctor yasan cewar Islam is highly confidential patient yasan cewa fadar abinda ta haifa sakaka batareda iznin mai martaba ba hakan ze iya sakata acikin hatsari mai girma da ita da jaririn musamman kasancewarsu a asibitin bayason yajawa kanshi wata matsalar. kallon da uwar soro kuma ta auna masa yasa yakara tabbatar da zarginshi akan mutanen kawai yamike yawuce office dinsa takalli dan saurayin tana fadin "yaymata jagora zuwa office din doctor din" sakamakon yajja taji kafafuwanta sundan mata nauyi dasauri mai babban daki tadawo gefenta tana fadin "ranki yadade bari na temaka maki" wani kallo data watsa mata yasa tashiga taitayinta don dole saurayin wanda take kira da Prince Aman ya dafota suka nufi office din likitan shikansa yana kaita sanin baida hurumin tsayawa din yasa yafito dukda kuwa yana matukar son yaji yaya jikin aunt din nashi yake, amman me yasan dokar aikin likita baze taba fada agabanshi ba.

Office dinne yadauki wani shiru uwar soro takalli likitan irin kallon ina sauraronka dinnan murmushi yay yana fadin "kyakkyawan labari ranki ya dade Allah yasauki Princess Islam lfy munciro mata baby boy me kama da mahaifinshi sak sak," nan take uwar soro tadurkushe kasa tana sujjada tanawa Allah godiya da ni'imar dayay musu, takalli doctor tana fadin "uwarfa? yaya jikin nata? dan jim yay before yace "ranki yadade Islam jininta yayi mugun haurawa cikin kankanin lokaci don ko last time da sukazo itada prince komai nata normal yake amman da alama tatsinci kanta cikin wani tashin hankali daya jefata cikin mummunan shock din da jininta ya haura haka kuma, shiyasa tafara nakuda tunkan edd dinta yacika,kuma barinta tahaihu da wannan High BP din abune da baze yiwu ba" uwar soro tausayin yarinyar taji ya kamata tanata wondering wani kalar abune taji haka daya birgitata lokaci guda haryake neman mata illa babba cikin rayuwarta. tace "likita zadai tasamu lafiya koh? yace "eh toh tabbas in sha Allah zata samu sauki domin mun daurata akan magunguna masu kyau kuma nasan da taimakon prince in sha Allah komai zaizo cikin sauki don nasan yajja yake ji da ita baze barta cikin damuwa ba,yana ma inawai? Shida mukai dashi tare za'a shiga dakin haihuwar dashi Allah beyi dakanta zata haifaba muna mata aikinma sunansa taketa ambata," uwar soro tace " likita ai sha'ani kawai jikina yana bani yarinyar nan taji ajikinta wani abu mummuna ya sameshi shiyasa tadaga hankalin ta hakan kasan subiyun hanta da jinine ba'a rabasu tohm haryanzun dai bamu sameshi ko awayaba sukuma mutanen can garin sun tabbatarwa da mai martaba yataho antura dai mutane nemansa muna jiran dawowarsu" likitan cikeda jimami da nuna kulawarshi yake fadin " Allah yatsareshi Allah yadawo mana dashi cikin aminci" tace "ameen ya hayyu ya qayyum" anan take taimishi umarni shirya Islam din sumaida ta can cikin gida tunkan tafarfado anan din don zamanta a asibitin be mata ba tace mishi babu tsaro wadatacce domin kowa ze iya cewa zezo yaganta itada jaririn amman in agidane tana sashena babu wanda ya isa yay wannan gigin. da alamun likitan yagamsu da bayanin uwar soron yace "badamuwa zuwa yamma sukaga karfin jikinnata shidakansa zekawota tareda ma aikata amintattu kuma zeke zagowa duk safiya kan yakarasa aiki yadubata" tai na'am da kyakkyawar shawarar tasa dakanshi yafita yakira mata Aman suka fito tare.

Abuja Nigeria

Awani irin mugun speed take taka motar suna tafiya sunware kida budurwar kana kallon yajja take jan motar kasan takware a iya tukin ganganci arayuwanta yarinyar dake gefen sit name zaman banza wacca bazata wuce shakara shadaya sha biyuba tura farin eye glasses dinta tai kan fuskarta yar kararta tana sake binwakar dake ci amotar cikin daga murya tana fadin Weather na winter or summer I dey bravados Savannah living life seeing my fire burning bright.......... Tana dukan gaban motar don sosai take enjoying drive din nasu, "muje mana ya mehtav more speed gurl" yarinyar tashiga fadi tana ziga budurwar dake tuka motar,dukda tana sane dacewa sosai suke nufar hanyar fita daga garin,juyawa tai tana fadin "Abeey the speed is okay indai baso kikeyi mukashe kanmu ba kinsan daddy besan mundakko motar nan ba," tsaki yarinyar taja tana fadin "matsalata dake shegen masifaffan tsoro da ace nice nake tukinnan dakinga yajja ake driving yah mehtav you'll feel it har cikin blood dinki," cikeda kulewa yajja ba'a taba pleasing Abeey duk abinda za'ai take fadin "ko ke zanbawa kituka ne yar rainin hankali," tajuyo tana bada attention dinta ga Abeey duka. Abeey tsaki tai tana kallin gabansu ganin babbar mota nayo kansu yasa dasauri tafasa kara tana fadin "Yah mehtav look, kikauceeeeeeee" cikeda birkicewa mehtav tajuya kan wheel din motar tai gefe da niyyar kaucewa motar daidai nan taga wani mutum jikinsa duk jini yayo kan motar tasu bata iya controlling motar tasuba haka sukai sama dashi dau kake ji yafada yagangara gefen titin motar tasu ma haka tatsayar da ita chak tsabar tsoro daga ita har abeey numfashinsu kokarin daukewa yakeyi. sunkai minti goma ahaka bawanda yamotsa acikinsu kafin karamar tadago cikeda tsoro take leka gaban motar tasu dasauri tadawo baya atsorace ganin mutum kwance cikin jini tafashe da kuka tana fadin "Yah mehtav we killed him wayyo Allah nashiga uku banason inyi prison I'm just a minor" tasoma jijjiga mehtav da har lokacin bata dawo hayyacinta ba "sister mehtav do something,kice wani abu dan Allah" se asannan tajuyo jin kukan Abeey din yacika mata zuciya da kwakwalwa, "Abeey we kill him" itama tafada suka rungume juna suka soma rera kuka cewa prison kawai za'a kaisu, mehtav tace "Abeey lets run mugudu kawai tahaka bawanda zesan mune mukai," girgiza kai Abeey tasoma yi tace "inmuka gudu zezama ba accident ba murder zezama inagani a animation sentence dinmu zekaru sister mehtav lets check muje mu kaishi gurin family dinsa mu rokesu suyafe mana muce mu marayu ne bamuda mama," dasauri mehtav tabude motar taikan mutumin dako fuskarshi ba'a iya ganewa don jini ya rigada yawanke masa ita abeey tabiyo bayanta tana lekasa cikeda tsoro ganin bakowa atitin suka soma tattabashi wai suji ko yana numfashi abhi ce harda daura kanta saman kirjinsa wai taji bugun zuciyarsa babu abinda takeji din kuwa hakanne yasa tadago tana fasa wani kukan take fadin "yaya yamutu wllh munshiga uku" zata mike caraf taji anrike hannayenta azabure tafasa kara mehtav dasauri tai kanta ganin mutuminne ya riketa yasanya tai saurin kallonshi,tana fadin "kana raye? kana jinmu? babu abinda takeji dukda taga yana motsa bakinsa, Abeey tasoma girgizashi tana fadin "sister mehtav mukaishi asibiti karya karasa mutuwa lets help him" dasauri mehtav tajinjina kai suka soma kokawar daukarsa,duk yajja sukaso daukar nashi kasawa sukai don yamugun fin karfinsu domin irin karfafan mazannan ne doka doka masu tsayi dakauri dukda bazakace mai me kibaba amman jikinshi amurde yake, daga karshe dakyar suka jashi suka saka shi abayan motar su dukda yajja jininsa yabata jikinsu baki daya basu damu ba Abeey ce tazauna abayan motar tare dashi dukda kankantar shekarunta haka tadaura kansa saman cinyarta tacigaba damai mgn na tana rokonshi karya mutu yarufa musu asiri batason taje prison karya mutu,bama tasan ya rigada yasume ba harsuka karasa asibitin Dr kafaya.

Dr kafaya takasance likitar gidansu ce ta musamman kawar karatun mahaifinsu ce tare suka tashi Abeey ce tafice dagudu takarasa office din Dr kafaya din tana sanar mata da abinda yafaru cikin tashin hankali tabiyo bayanta yayinda mehtav ke kokarin fitowa dashi daga cikin motarsu,sosai Dr kafaya tashiga tashin hankali domin kuwa ba karamin jikkatuwa mutumin yayba domin aka ida irin wannan raunin basa karna seda yan sanda,wasu nurses ne maza tasaka suka shigar dashi takalli mehtav da Abeey tana fadin "in my office now! tashige ciki aikuwa tana karasawa suna karasawa suma sukai tsuru tsuru agabanta kamar shege arabon gado, "we have to call your father now yataho da police domin ba xanyi taking risk din taba wannan patient dinba yamutum min a asibiti ba tareda sa hannun hukuma kowani daga cikin ahalinsa ba," dawani irin sauri Abeey da mehtav suka kalli juna domin sunsan idan har mahaifinsu yasan abinda suka aikata kashinsu yabushe don tasu takare,cikeda tsoro mehtav tasoma fadin "don Allah doctor kiyi hakuri kirufa mana asiri karki kira paa yanzun mu zamu gaya mishi dakanmu don Allah save this man first karya mutu ransa yarataya awiyanmu dangirman Allah" Kallon Mehtav take irin bama kida hankalinnan Abeey se rarraba ido take kafin tai saurin kallon doctor kafayat tana fadin "pls pls aunty kitemaka mana we promise you zamu gayawa daddy dakanmu," "hmmmmm" kawai doctor kafayat tace before tafice daga office dinta tanufi ER da aka wuce da EHSAAS tanata wondering rashin ji irin na yaran Engineer Habib. A office din suka zauna sukai tsuru can Abeey tataso tamatso kusa da mehtav tana rike mata hannaye take fadin "yaya mehtav idan yamutu fa," dasauri mehtav tace "Abeey shut up idan bazaki fadi alheri ba kiyi shiru kawai," hawayen dake bin kuncinta tagoge tana fadin "banason aunty doctor tafadawa paa munsake daukar motar mom munfito kinsan dai last time yamana gargadi duk sanda kika kara dauka seya mayar damu kauye gurin inna,ni banason zama akauye mehtav I hate it there," tsaki Mehtav taja tana fadin "will you shut up Abeey kibar mutane da abinda sukeji kinzo kina sake dagan hankali da negative thoughts dinki bawani kauyen daza amayar damu kuma zetashi yakoma gun family dinsa lafiya kuma nasan doctor kafaya firgita mu kawai take bazata fadawa paa ba, indai harmuka lallabata muka bata kudi you know how much she loves money" Dan jim Abeey tai before tace "but mehtav bamuda kudi kinsan shekaranjiya duk kudin da paa yaturo mun kashe asiyayyar New year," dan cizon yatsa mehtav tai tana fadin "kumafa hakane mezamu bata yanzun tohm? Abeey can tai saurin mikewa tana fadin "your gold earrings da mom tabarmaki kikai inheriting," "are you highAbeey" cewar mehtav "abin mom din zanbayar," Abeey ce takatse mata tinani tana fadin "tohm kinada wani abinne nakudi wanda zaki bata taishiru da bakinta bayanshi," jinjina kai mehtav tai tana Fadin "zansiyar da iPhone 16 dita sabone karkar babu abinda ya sameshi sena bata kudin nasan she won't say no," sanin Abeey tafita kaunar iPhone 16 dintata yasa tai shiru tana kallon Abeey din tana jiran me zatace domin wayar tatace amman wuni takeyi hannun Abeey tana dauke dauken hotuna aciki,amman ga mamakinta se taga Abeey ta amince da idea din suka tsayar akan susaida kawai subawa doctor kafaya kudin tayajja bazata gayawa babansu abinda suka aikata ba.

Suna nan zaune kusan awanni uku sega doctor kafaya tashigo kayan aikinne ajikinta ko cirewa bataiba tazube saman kujerarta don ba karamin wiya aikin yabata ba tadade bataga case irin wannan ba na rashin imani karara da akaiwa bawan Allah nan dasuka kawo Allah ne kawai yay da sauran ranshi domin yajja aka lulluma mai makamai aciki batai tinanin ze rayuba ga concussion, doctor is he alive? Tambayar da Mehtav tai mata ce tadawo da ita daga cikin tinanin data tafi takalleta tana dan jinjina kai kafin tace "he's in short coma dai yanzun muna jiran farkawarsa aikin is successful, Allah yayi da sauran kwananshi," Abeey da mehtav rungume juna sukai suna murna don jin cewar mutumin be mutu ba, "Amman Abeey tacemin kun bugeshi amotane bugewar mota me yakawo sara acikinsa," dan jim sukai suna kallonta mehtav tarintse ido tana tina yajja abin yafaru dasauri Abeey takatse mata tinani tana fadin "aunty doctor wllh tangadi yakeyi dajini ma ajikinsa lokacin da motanmu yay kansa muka kasa tsayar da ita tabbas," doctor tadan buga table dinta tana fadin "no wonder," mehtav takalli doctor tana fadin "but doctor me hakan yake nufi," tace "nafi tinanin kila ko matafiyi ne yan ta adda suka ritsa dasu yagudu tunda abun abayan gari yafaru ko kuma dai wasune suka biyoshi zasu kashe purposely infact the man doesn't look like us," Abeey tace what? Jinjina kai tai tana fadin "kuzo kuga" mikewa tai suka bita abaya har suka isa kofar dakin da aka maidoshi,tasaman glass din mehtav tahango farar fuskarsa tartar dukda Oxygen din dake temaka mai gun numfashi behanata ganin tsantsar kyawunshi da hasken jikinsa ba,sosai zuciyarta tashiga dukan tara tara kodai aljani suka dakko bata saniba, Abeey taji tana jan doguwar rigarta dalilin tsahonta baze kaiba dukda dagen da taketa kokarin yi. Mehtav ganin Abeey din tazaku da son ganinshi yasa tadan ciccibota dukda tayi mata nauyi tana nishi amma seda tadagata tagano fuskarsa wow! taji Abeey tashiga furtawa, "he's so handsome sister" jin Abeey ko tsoro ma batajiba se santin kyanshi takeyi yasanya tadireta tana fadin "handsome my foot! sarcastically. tajuyo tana tambayar doctor "kosun tsinci wani abu atare dashi daze nuna shiwaye ko kuma daga ina yake," girgiza kai doctor tashiga yi tace "kayan dake jikinsane kadai abinda ke tare dashi bayanshi babu abinda ze iya ma indicating daga ina yake," jinjina kai kawai mehtav tai suka wuce office din doctor suka zauna ganin doctor nashirin kiran babansu suka shiga rokonta karta kirashi tarufa musu asiri,cikeda son kudi irinna doctor kafaya tashiga basu hakuri tana nuna musu taso tarufa musu asiri amman bayajja zatai dole zata nemi engineer don yazo yabiya kudin treatment din mutumin don ita asibitin ta ba gun charity baneba, ba akyauta zata duba musu shiba,bayan sune sukai aika aikarsu ba itaba. dakyar suka lallabata harseda mehtav tai mata alkawarin biyanta kudin aikin da komai da komai sannan ta amince akan tana jiranta gobe kawai tabata inbata kawo nata kudinta ba zata kira shi tasanar mai. godiya kmr sukai mata suka fito don ganin yamma tayi zasu koma gida, Abeey ce taketa jaddada ma doctor kafaya takula musu da mutuminnan dan amana ne tunda tsintarshi sukai,tun doctor na reassuring dinta harta gaji taimata banza. Koda suka shiga mota Abeey ba abinda take yi se zuzutawa mehtav irin kyan wannan mutumin tanata guessing shidin kodan wana garinne allahu a'alam,kuma data rigada ta gane Mehtav battason yajja take zuzutashin se takara kaimi tacigaba domin ita Abeey duk sanda mutum yace tai hagu tohm dama takeyi inkace tai dama hagu takeyi batajin magana nagaske. mehtav ce babba amman zakai mamakin yajja Abeey tafita wayo take iya juyata yajja takeso kuma data hayayyako zatai mata tsawa seta shiga matse ido tana amfani dacewar don anga mamanta batanan tamutu ita marainiya ce shine za'a ringa mata tsawa da fada,tana tinawa da mehtav cewan ai babarsu tabarmata amanarta ne yajja kasan agabanta aka bada amanar, yarinyar da ana haifarta Allah yaywa mahaifiyar rasuwa gun haifarta,shiyasa suka daura son duniya akanta mahaifinsu babban engineer ne,yana amsan manyan contract na kasa da kasa shiyasa kwata kwata baya zaman wata daya cikakke atare dasu,gashi kaf danginshi ya hanasu daukar masa yara sbd yanaga kmr za'a takura musu ko aimusu rikon mugunta tunda mahaifiyarsu bata da rai. mahaifiyarsa kakarsu kenan wacca suke kira da inna itace take zama dasu amman itakanta bata son zaman Abuja da weekend yayi take tafiyarta kauye harse rnr Monday da sassafe take dawowa bayajja engineer Habib bayayi da ita akan tadawo nandin dindin din amman ta ki acewarta inyanaso tazauna tare dasu dindindin sedai yabatasu sukoma kauye duka shikuma yarantse yayansa ba zasuyi rayuwar kauye ba bama zasu iyaba don yasan kalar renon dasukai musu shida mahaifiyarsu. Wannan kenan. Koda suka karasa gida har anfara kiraye kirayen sallar magrib dakinsu suka wuce,don basu taba kwana ba'a daki daya ba tunda suke dakin mai girma sosai yana dauke da gado matsakaita guda biyu kana kallon dakin kasan na yara matane domin yasha decoration iri iri sashen Abeey fosters ne na Disney Princesses iri iri,komai nagurin baby pink ne da tarkacen teddy bears dinta wasuma sunyi girmanta bangaren mehtav kuwa kpop idols ne iri iri,da wani madaidaicin mirror na yan mata inda kayan shafarta kenan anjere su iri iri, dakin dai gashinan da tarkacensu iri iri hakama cikin closet dinnasu ba'a magana dukda kowa da section dinshi amman hakan baya nufin wani yashiga sabgar nawani suyita fada kamar sa annin juna, ita mehtav rashin hakuri itakuma Abeey tsaurin ido se suyita yi kmr wasu maguna. Mehtav ce tafito daga wanka idonta yasauka akan Abeey dake kan gadonta dare dare sanye da t-shirt dinta data kawo mata cinya ta,da babban ball tahado Quaker oats aciki tana sha,kwafa kawai tai tana kallon sashen gadon Abeey din dakenan agyare wato bazata hau kannata tabata ba senata itace marainiyar wayonta amman sanin cewar inta biye mata masifa zasuyita yi yasanya tanufi closet PJ's dinta kawai tasako tashimfida sallaya tashiga yin sallah,seda ta idar tadago tana kallon yajja Abeey tashanye oats dinta tature ball din saman gado tana kwanciya daidai. "bazaki tashi ki sallah ba" Mehtav tafada bawasa acikin muryarta hakanne yasa Abeey tamike batareda tadauke kwanon ba tashige toilet don dauro alwala girgiza kai kawai mehtav tai tamike tazare hijab din jikinta tadauke kwanon tai waje dashi kitchen takarasa nanma taga kalar wulakanci da Abeey taimata gurin hada Quaker oats din tafito da komai tayi filla filla dashi kuma babu abinda tagyara balle tamayar inda yake. agaggauce tashiga gyara kitchen din jin ana kiran sallar isha'ee yasanya tai saurin dawowa dakin ganin Abeey na sallar isha'ee alamar gama magrib dinta kenan tadaura da ishar yasa itama ta tayar da tata,bayan sun idar sunjima azaune suna addua,kafin Abeey tamike tana saurin dauko wayar mehtav don lokacin kiran paa dinsu yayi,mehtav ce ta shiga ninke mata sallayar data idar da sallar da hijab din tana jinta tana magana da baban nasu cikeda shagwaba tana bashi labarin abubuwan dasuka faru ayau din kafin accident din duka tayi mamaki yajja Abeey duk surutunta ta iya rike bakinta ko alamu bata nunawa babansu cewar wani abun yafaru dasu ba,seda mehtav tagama tadawo gefenta tana zama suka cigaba da hiran gwanin birgewa dukda yaso yagano akwai damuwa amuryar Mehtav din amman seta bagarar dashi tahanyar sanar mishi kawai dai project supervisor dinta take tsoro kada Monday in taje yasake maidota nan yashiga kwantar mata da hankali yana gaya mata tai focusing tayi iya yinta he trust her yasan she will make it in sha Allah. taji dadi sosai dukda hakan bashine ainahin damuwar tanba amman shima dai yana daga ciki kafin faruwar accident din,nan yace mata ta tabbatar sunci abinci sun kulle ko ina suyi addua sannan banda kiriniya,suka cemai in sha Allah zasuyi kafin su katse wayar duka,kitchen suka tafi susu biyun gaba daya Mehtav bataji dadin yajja suke boyewa babansu wannan mgnr ba indomie tadaura musu don ba abinda zata iya dafawa mai nauyi awannan daren,shiru tai tana kallon Abeey dake danna mata waya tamaidata kamar tata. "Kodai mufada ma paa gaskiyane, Abeey banason muringa mai karya" zaro ido Abeey tai tana fadin "yah mehtav kinmanta waye engineer Habib Bai ko tohm bari kiji ban tabajin paa yafadi abu yafasa yi don wani dalili ba iname tabbatar miki kina fada masa wannan mgnr gobe akauye zataimana duk mu biyun," Abeey tafada tana dirowa daga saman kitchen island data hau tai dare dare, "but Abeey kinsan fa karya bakyau" Abeey cikeda wayo take fadin "aibamuyi masa karyaba kawai dai munboye masa gaskiya ne for our own good,ko kina tinanin paa inyaji mgnr nan ze hakura ga inna agefe daman burinta kenan inaaaa banafa nashiga jss 1 koso kikeyi inkoma bakauyiyane amaidani makarantar da ake karatu a tabarma kodan ke kinga your future is already intact degree ma zaki kammala don't be selfish kinsa....." ganin Abeey zata soma mata emotional drama data sabayi takarya mata zuciya yasanya tace "fine I won't tell him amman gobe yana farfadowa zebamu lambar yan uwansa mu kirasu suzo sutafi dashi that's final" tafada tana bude tukunyar ruwan indomie daya tafasa, murmushi kawai Abeey tai tana gyada kai don itakam mutuminnan yagama kwanta mata yashiga cikin ranta daram gani take Mehtav nafadar hakane kawai saboda tsoro amman inso samun Abeey ne kawai ma sudakko shi sutaho dashi gidansu taita kallon kyakkyawar fuskarshi harse yawarke gaba daya.

NURISTAN Ahankali Islam tabude idanuwanta datake ganin wani irin dishi dishi sakamakon allurar barcin dabata gama sakinta ba, ahankali kuma cikeda nitsuwa tadan tashi zaune kunyace takamata lokacin da sukai ido biyu da fulani wacca ke gefen ta tana sakar mata murmushi kamar gonar auduga se alokacin ne ma tasake karema dakin da take ciki kallo,dakin barcin uwar soro ne tatabbatar da hakan sbd tashigo sau ba adadi tareda SIR EHSAAS, "sannu my daughter" fulani tafada tana dafa hannunta cikeda kauna take fadin "sannu kinji Allah yay miki albarka, Allah ya albarkaci rayuwarki keda abinda kika haifa" se alokacin tai saurin shafa cikinta tana kallon fulani tanason tambayar wai harta haihune amman tanajin nauyinta,kanta harwani sarawa yakeyi abinda yafaru karshe kafin tasuma yasoma dawo mata kwakwalwarta dallah dalla,zaburar datai yasa fulani mikewa tana hawa gadon gefenta, "meye faru diyata me yasameki? hawaye tagani yanabin kuncinta, "kimin mgn yata," "Maamaa MY SIRE" tafada tana kankameta, "yana ina? ta watso mata tambayar da ita kanta shi takewa jama'ar gidan tunjiya amman anrasa mebata ansa tohm ita tayaya zatasan me zatace wa yarinyarnan bayan itama batasan inda yakeba, "maamaa ina yake? takara tambaya tana dagowa daga jikin fulani girgiza kai tashiga yi tana fadin "Islam nima bansani ba bama wanda yasani," "maamaa I heard him yace sukashe shi yace karsubarmin shi darai kuma....waziri......." dasauri fulani tarufe mata baki tana fadin "don't say anything bakya cikin hayyacinki Islam fadar magana a irin gidannan batareda kwakkwaran hujjar dazata tabbatar da maganar kiba makiya zasu iya juye maganar tadawo kanki kinji yata be wise kada kisake kifadi abinda bakida hujja akansa" dasauri islam tadago tana fadin "maama wace irin hujja ake nema bayan ninajishi da kunnena daman yarantse seyaga bayansa,wllh shine maama wai bakison Sir EHSAAS ne kece fa kika haifeshi yakamata......." shigowar jakadiyyar fulani ahaukace ne yakatse islam daga maganar datakeyi don tasan bata saba fado musu hakaba cikin rawar jiki tazube tana goge hawayen dake idanuwanta,cikin tashin hankali fulani take fadin "ke kuma lafiya zaki fadowa mutane bako sallama banace duk ku tsaya awajeba waya baki damar shigowa nan kaitsaya," cikeda ladabi jakadiyyar take fadin " Allah shitemake ki kiyi min afuwa sakone yazo afujajan daga gurin mai martaba yanason ganinki keke kadai a turakarsa yanzunnan kuma .....kuma.... inajin rade rade radi......" kasa karasawa tai,cikin daka tsawa fulani take fadin "rade radin me kikeji bazaki bude baki kiyi mgn ba kina rainama mutane wayo," tace "daga bangaren mai babban daki naji kishin kishin wai su galadima sundawo antsinto gawar yarima yayi hatsari ahanyarsa ta dawowa," tau kakeji bata ankaraba marin yasauka akan fuskarta hakanne yasa har hantsilawa seda tai cikeda firgici idanuwanta kamar garwashi tashiga nuna jakadiyya da hannu tana fadin "the next time kika kara hada kalmar yarimana da mutuwa kezan fara kashewa indaidaita rayuwarki,munafukai kawai duk abinda ke faruwa kunsani babu abinda baku saniba," tajuyo tana zuwa gaban fulani jikinta rawa yashiga yi tana fadin "maamaa karyafa takeyi karki yarda da ita daman bangaren Mai babban daki duk munafukaine basasonmu basason Sir EHSAAS dina,amman nayarda dashi baya karya yacemin duk sharrin su baze kamashi ba he won't die and leave me,yamin alkawari tare zamu rayu kuma tare zamu mutu, yace indai ina numfashi shima numfashinsa baze tsayaba saboda zuciyoyinmu abu gudane maama baze mutu yabarni ba ko? rungumeta Fulani tashiga yi tana fadin "ki kwantar da hankalinki Islam haihuwa kikai jinin ki yahau kitemaka ki nutsu kodan abinda kika haifa da EHSAAS bazasu so suganki cikin wannan halinba dan Allah kidena kukannan" ganin Fulani kamar bazata kwato wa mijinta yancinsa ba yasanya tai saurin raba jikinta danata,tana dan ja da baya da baya dukda jirin dake dibarta, "ina zakije islam? fulani tatambaya cikeda kulawa "xanbiki turakar mai martaba inji mezakuce akan mijina inji wana mataki zaku iya dauka akan wadancan mutanen idan ku bazaku iyaba nizan iya zandaukar mai fansa da hannayena sena ga bayan duk wanda yatabashi aduniya damai babban dakin da galadima da.......," jin muryar uwar soro tadaka mata tsawa tana fadin "ISLAM" damanyan baki yasanya tajuya tana kallon ta da abinda tarungume wanda koba'a gaya mataba tasan babyn data haifane, "kishiga hankalinki kisan dawa kike mgn" uwar soro ta gargadeta, ganin wacce take abayan uwar soron yasan Islam saurin karasa gurin uwar soro bakunya takalleta tana fadin is this my baby? Jinjina mata kai uwar soron tai tana mika mata shi dasauri takarbeshi tana rungumeshi akirjinta,hawaye daya bayan daya nabin kuncinta kwakwalwarta ta cunkushe ba abinda take bukata se mijinta atareda ita awannan lokacin batasan tsawan lokacin data dauka tareda babyn ba amman dai tanajin fitar fulani daga dakin kuma koh kadan batai da nasanin gaggaya mata maganganun datai akan EHSAAS ba don bata taba ganin mace me hakuri kauda kai da kuma tsantsar dattaku irin fulani ba, amman me enough is enough itaba fulani bace kuma itakanta Fulani lokacin karbar yancinta yayi acikin gidan aurenta amatsayinta na sarauniya mafi daraja wacca tahaifi yarima wa sarki Nashwan. Ahankali takoma kan gadon tana zama tareda dan ajikinta uwar soro da gimbiya mimah suna kallon yajja ta kwakube yaron kamar wani ko wata zata kwace mata shi,mimace ta dafata ganin tasoma gyangyadi take fadin "Princess ko zakije ta soro ta hada maki ruwan wanka kifara wanka tukunna seki dawo ki kwanta tareda new prince dinmu," wani irin kallo taga islam din namata da gwara gwaran idonta masu firgitar da mutane sunyi jajir kamar danyar nama sun kumbura amman dukda haka behana girmansu fitowa, "excuse me, dauke hannunki ajikina" cewar Islam tana kallon ta,sosai gimbiya mimah tashiga shock ganin yajja islam din tai treating dinta kmr wata trash,uwar soro kanta tayi mamaki domin kaf gidan babu wanda islam din kedasawa dashi kamar mimah,mikewa tai tana bawa uwar soro babyn nata tace "amanatun amana nayarda dake shiyasa nabaki amanar sa shidi rayuwarmu ne nida SIR EHSAAS karki bari wani ko wata yarike koda dan yatsansane" takarasa tana kallon mimah kafin tanufi hanyar ficewa adakin tabarsu da sakakken baki amman sam uwar soro bataga laifinta ba sema jidatai ta dasama mimah ayar tambaya don kaf fadar tasheda kalar hakuri da kauda kan islam kusan iri dayane dana Fulani shiyasama ba'a taba jin kansu da wani ko wata acikin fadarba amman yau itake habaici agabanta tabbas dawalakin goro amiya.

#Amnesia #bestlovestories #PrinceEhsaas #Islampeace #Mehtavbai #Abeey #Nuristankingdom [11/04, 10:18] Fatima Rufa'i Nasidi: ***

EHSAAS Another exclusive piece from the passionate writer of AYSAM And INTENSE LOVE. It's fatoumspassion