EHSAAS

Chapter 2

by @fatoumspassion

(The lost prince)

Washegari da sassafe kasancewar yau Monday sallamar innarsu ce ta tashesu dawowar ta gidan kenan,agurguje tashiga tashin Abeey datake dada jan bargo tana kunkuni alamar batason zuwa makarantar duk Monday haka ake fama da ita kan tashi zuwa makaranta amman ahaka iya ta fizge bargon tana mita taturata bandaki dake sunrigada sunyi sallar asubah don duk asubah ko ina babansu yake seya kirasu yatashesu sallah domin bayason wasa da sallah ko yayane,atsaye yake akansu kan hakanne yasa duk baccin dasuke lokacin sallar nayi zasu tashi kobasu tashiba shi zekira yatashesu. Inna ganin Mehtav batada lecture sassafe dake timetable dinta ta hardace kaf yasanya bata tasheta ba, Abeey tafito daga wanka dakanta ta shiryata dukda zumbura mata bakin datake itafa alallai tagirma abarta tashirya dakanta amman yajja inna ke treating dinta kmr jaririya dada kular da ita yake,fitowa tai cikin hadaddun uniform dinta black skirt ne karami iya gwiwa da doguwar farar sama da bakin takalminta dase kyalli yake yasha polish ash din shirt ce medogon hannu se tasamanta wacca ake daurawa kamar suit se Barret din kanta data daura tana kunkuni bayan inna tamata donut da gashin nata tariko mata jakarta tsabar tsokana suna karasawa bakin kofa zasu fita ganin Mehtav mabarci dafa'an yasanya tai wani reverse tadira saman gadon mehtav tana kwalla kara. afirgice Mehtav tamike tana salati tana ware idanuwanta shekewa da dariya Abeey tai tana mikewa tasoma kakkabe uniform dinta danma karsuyi squeezing take fadin "good morning Princess" tsabar takaici kasa magana tai inna ta dafe kai tana fadin "kedai abeeda har abada bakison zaman Lpy arayuwarki yanzun fisabillahi abinda kikai kin kyauta" afusace Mehtav tamike zata cafkota amman harta arce tafice adakin tanai mata gwalo da dariya haka ta hakura tabarta don yanzun tasan inta biye mata haka takeso seta makara bus tatafi tace tafasa zuwa makarantar burinta kenan. breakfast din da inna tashirya musu ta tuttura sama sama tana karbar launch box dinta wacca tagama mita kanta karba wai ita kudi za'a bata tayi girma da zuwa makaranta da abinci shikuma babansu beyarda dabawa yaro karami kudiba saidai duk abinda take bukata zesiya mata,suna fita school bus na karasowa nanfa tafara kwalla tana cewa ita fa battason zuwa makarantar nan kowa ana bashi kudi ita kadai aka tsana ba'a bata yanzun haka zata ke fadowa agaban kawayenta in ana kashe kudi badon iyah tasoba tazaro naira dari biyar tabata tana fadin "kidau dari biyu kidawomin da canjin" badan Abeey din zata dawo dashiba domin kashe kudin Abeey din har tsoro yake bata kuma bawai abu me amfani take siyaba uhm uhm ci banza ci wofi kuma ita ke bata kokuma Mehtav,indai Abeey takyalla taga sunada kudi tohm sefa sunkarar akanta zata ji dadi semin wannan zanci wancan ahaka insunyi magana se tace ai money is for spending insuka kashe sunnuna godiyarsu ma Allah daya basu kuma ze kara musu,haka dai Abeey tashige bus tana cunkushe fuska, seda inna tadena ganin motar tadawo,idonta ne yakai kan motar dake fake a parking space din gidan cikeda zulumi tashiga tatarar da Mehtav tana share falon domin tagama barcin kuma tunda Abeey tarigada tatasheta. Gaisheda inna tai tana mata sannu da dawowa badon tayi farinciki da dawowar tata ba,don tasan zata samata ido ne kawai itace kmr CCTV din babansu,amsawa tai takarasa tana zama saman dining table abincin da Abeey tarage takara wani akai tashiga ci tana tambayar Mehtav ya weekend din nasu, Abeey taje tahfeez dinnan kuwa,jinjina mata kai kawai tai don bata cikason suyita takurawa Abeey kan karatuba yarinyar nan fa makarantar wuni takeyi islamiyya da boko ahade duka weekend dinma bazasu barta tahuta ba sesun sata awata tahfeez shiyasa duk randa inna battanan mehtav kece mata tai zamanta ba inda zataje itama tahuta, "Mehtav naga motar can ta Aisha a waje kmr agareji akasata fa wancan lokacin koba hakaba" sak Mehtav tai tana wiki wiki da ido kafin tai saurin fadin " inaji service za'a mata shine jabiru driver yafito da ita" "service kuma? inna tatambya cikeda zargi dasauri Mehtav ta jinjina kai tana murmushin yake, "tohm inma dai hawa zaki kika fito da ita kiyi gaggawar mayarwa babanki yagargadeki da tukinnanaki na ganganci shiyasama yakwace lasisin tukin ki kada kisake yaji mgnr fito da motar nan," tabe baki tai cikin shagwaba take fadin "shikenan... shikenan ni inna kullum nice acikin Laifi wancan tsohuwar motarma mezanyi da ita" takarasa fada tana nufar waje tana waiwayan bayanta ganin inna bata biyota ba yasa tai saurin karasawa bakin gate inda driver su jabeeru da dan liti megadi ke zaune suna karyawa,sallama tai musu kafin ta mika masa makullin motar takaranta masa abinda takarantawa inna kancewar koda paa dinsu yadawo inna tamai gulmar suce masa haka kada wanda yasake cikinsu yace tahau motarnan inba hakaba zata dena basu allowance din datake musu. washe baki sukai suka shiga mata kirari irin wama ya isa yaja dake dinnan suna fasa mata kai suka ce angama hjy tana hura hanci tadawo cikin gidan tatarar da inna ta mimmike kafa takunna TV tana kallon film a MBC Bollywood yajja kasan tasan me akecewa Mehtav taraya aranta tana dariya tana ayyana da Abeey nanan datini sunfara rigima akan remote,daki takoma takira doctor kafaya tatambayeta jikin mutumin don dashi takwana aranta anan kafaya take gaya mata he is recovering sedai ciwon kannashi bayan sunmai hoto sunga kmr yasamu wani damage amman karta damu zasuyi tackling abin cikin sauri, godiya taimata tareda jaddada mata karta fadawa paa zata taho da kudin yau yau dinnan. tana kashe wayar takalli agogo karfe tara sanin batada wani lecture se ganin supervisor dazatai yau yasanya ta shige wanka bayan tafito tashirya cikin riga da skirt na atamfa dasuka nata masifar kyau tafito tai das abinta tadaura dankwali ta yafo gele dayay matching da kayan tadakko jakar makarantar ta,kiran wayar me mata gyaran waya nura tai tagaya masa zata seda iPhone 16 dinta sabuwa ayau yau takeda bukatar kudin inda mesiya,dan jim yay before yace "mata gaskiya dai sedai tazo yarakata kasuwar waya donshi yanzun baida customer daze siyi iPhone 16 sbd sabon fitowace kuma meyanzun yanzun se Allah" fitowa tai kawai, breakfast dinma sama sama tayi tacewa inna ita tawuce makaranta cikin mamaki take fadin "base karfe daya supervisor din ze ganki ba kame kame tafarayi kafin tai saurin cewa yacanza shawarane kuma bama iya mgnr project zata kaini ba,zamu danyi wani research a library dawasu friends dina" jinjina kai kawai tai tana fadin "Allah yakiyaye hanya" dasauri tafice don tasan inna dukda tsufanta ba karamin fahimtane da itaba komai a ankare take dasu, mota dayace agidan bayan wacca suka hau jiya kuma itace wacca babansu yabada iznin aringa amfani da ita ana kaisu makaranta da zuwa siyayya haka, Jabiru already yamaida wancan motar yadawo mata da makullin ta takarba tai masa godiya,sanin intace yakaita wani gun ba makaranta ba bazeyi ba sbd yajja babanta yay warning dinsa yakuma mai alkawari kan hakan yasa tace makarantar zekaita kawai har kofar faculty dinsu ya ajjeta tafito tana mai bye bye harseda tashige sannan yaja mota yafice amakarantar. tana labe tana kallonshi, bayan tatabbatar daya tafi tafito already takira Uber yadauketa zuwa babban shagon nura megyaran waya,shima kanshi dan abokin babansu ne hakanne yasa suka dan saba don indai wayarta tasamu matsala shi paa yake aikowa har gida yakarbi wayar yaje yagyaro mata yadawo mata da ita,acikin taxi din ta tsaya takirashi yafito suka gaisa sallamar taxi din yay suka shiga tashi motar anan yake tambayar ta "meyasa bazata tambayi babanta kudiba inkudi take bukata baseta seda wayarta ba tasan in babanta yasani ransa zebaci" " hmmm" kawai tace mishi don battason tasaki jiki tagaya mai abinda kefaruwa kuma azo asamu matsala,harda cewa "intanaso shize iya ranta mata adadin datake bukata inyaso daga baya tunda anrigada anzama daya seta biyashi kawai," Tagode kawai tace mishi amman yakaita tasiyar kawai,yace mata "ai shikenan" shago shago haka yaringa rakata sunai mata tayin wulakanci ganin amatse take karshe dakyar suka siya a 1.5m haka suka mata transfer taiwa nura godiya sosai tareda cewa yabata account details dinsa tasamai wani abun, fir yaki yace mata aiyiwa kaine kawai tabarshi tunda taki karbar nashi temakon agareta,cewa tai yamaidata makaranta, agurguje takarasa office din project supervisor dinnata,ganin time yarigada yawuce wanda yabata bata lura lokaci yajaba tana murda kofar office din tajishi akulle alamar yafita tsaki taja kawai tana fitowa gashi ba wayar dazata kira jabiru tacemai tagama dukda karfe hudu tace masa zata dawo,fitowa kawai tai daga cikin harabar nile din tana kallan inda jabiru yake tsayawa in yazo babushi babu alamar shi,haka tafito da kafarta seda tatsaya a mosque tai sallah sannan tai titi tasamu abin hawa yakaita har asibitin doctor kafayat aikuwa tasameta cikin sa'a don rashin tsoron Allah da mugun son kudi irinna kafaya bill din 1m tabata tace " aishi mara lafiyar yaci kuma idan bazata iya biyaba zata jira enginneer kawai tafada masa shi yabiyata" bayajja Mehtav ta iya tasan daman za'a rina haka tabata katinta tacire mata kudin tanaji tana gani,sannan tarakata har dakinsa yau ancire mishi Oxygen din hakan yakara bayyana mata tsantsar kyawun da Allah yabashi ada tana ganin kanta afara kuma mekyau but ganin mutuminnan yasa taraina kanta don duk inda ake bukatar namiji ingarman namiji hadadde zurere wannan bawan Allah yakai tagama concluding he is not from here kawai maybe ma dan wani kasarne daban ta ayyana aranta tana kallon zara zaran eyelashes dinshi dake kwance kmr me barci. kafaya takalli irin kallon da Mehtav take masa murmushi kawai tai tana fadin "nurses har rige rigen zuwa yimasa dressing sukeyi kawai don suganshi he's handsome right" dan jinjina kai kawai mehtav tai tanawa Dr kafaya murmushi, Dr kafaya tace "Mehtav ki kejin labarai haka koda wani zezo yay claiming nasa tunda kinga haryanzun be farkaba" da tohm ta ansa mata kawai ganin murmushin Dr kafaya nayau na dabanne ma kawai donta bata kudi,wayar Dr kafaya ta ara takira jabiru tasanar mai ga inda take yazo yadauketa bajimawa se gashi tahade rai tashige owners corner tai zamanta donma karya tambayeta waya kawota nan din. wayarsa tace ya ara mata bamusu yabata takira nura tace mishi "don Allah karya gaji koze iya kawo mata waya mekyau amman mara tsada sosai,yajja paa baze kirata yaji shiru ba" yace mata "ba matsala gashinan ta howa wace iri takeso tace masa ko Samsung karama akasamu" dukda deep down tafison iPhone kodan Abeey tasan yajja Abeey is so obsessed with apple stuffs,bata jima dashiga gidan ba tai wanka tai sallah tafito ganin abinda inna tadafa yasa tadafe kai ita wllh bazataci Dan wake ba ana zaune kalau, cornflakes tahada ma kanta kawai tafito parlour tazauna tana wondering yajja zasu kare da supervisor dinta inta kirashi anjima mutumin beda wani sakin fuska kuma baida wulakanci amman yatsani katake mai dokar dayasa musamman bata lokaci he hate it with passion tafi kowa sanin haka kuma tamasa hakan kusan sau uku Kenan, tanaji kila tarigada tashiga blacklist din Dr kamal kamaluddeen already. kwankwasa front door taji anayi hakanne yasa tamike tana komawa daki tadakko gelenta data dawo dashi tayafa kan yan figigiyar rigar shan iskar jikinta tafito tana tambayar waye,dan liti ne yasanar mata da zuwan nura komawa tai ciki taziro hijabi tafito suka sake gaisawa tana mai godiya yabata wayar sabuwa karkar yar madaidaiciya Samsung dince kuma,yace mata 300k ce amman yamata ragi tunda itace tabada 250 kawai godiya tai masa takarba tana jujjuyawa batama yi expecting za'a samu waya mekyan gaske a irin kudinnan ba. tace "masa yatura mata account details zata samai" da tohm ya ansa mata sukai sallama tashige gida daki ma takoma don kar inna tafito tasaka mata ido tamaida sim dinta tasaka wayar a charge tana jiran dawowar abeey don sosai kewarta ta addabeta tinawa da dan wake inna tai yasanya tafara dariya don kila shi ta aikama da Abeey as lunch amakaranta tasan yau za'a sha mita kenan Abeey zatace anyarfata agaban kawayenta bata gama dariyar ba taji kwala sallamar Abeey tana kiran inna! inna! inna! nadawo! fitowa tai daidai inna nafitowa tsabar rudewa ma ko zaninta bata gama daurawa ba,tana gyare gyare don bawanda beji ihun kiran da Abeey kemata ba, "inna meye wannan? tafada tana dangwarar mata da kyakkyawar pink food warmer din da aka aikamata school,inna taja tsaki tana fadin "banason tijara da yammarnan banason iya shege dan wakenne bakisani ba komai," kwalla Abeey tasomayi tana fadin "yanzun kmr ni the great Abeey Habib Bai ni za'a kawoma dan wake as lunch inna daman kinyi ne donki wulakantani cikin kawayena wanda basukai matsayin daddy bama ba'a kawo musu irin wannan abincin makaranta seni don anga banida mama shine za'a ringa cusgunamin wllh sena fadawa daddy" tafada tana zubewa akasa tasoma birgimar rigima inna tasoma masifa tana fadin "uban naki waye sarki ko gwamna kajimu da yara kibi duniya a sannu fa nida na haifi Habib naci kashinsa naci fitsarinsa babu abinda banaci agidannan amman yarannan kundau duniya kundau rawa kanku,ke yar mitsitsiya harkin wani iya zabar abinci azamaninmu tarbiyya ake mana kikasan wazaki aura ko ubanka nada kudi ba'a baku abinci medadi kullum nima shinake kokarin gwada muku kuma meya aibin dan wake abin marmari abinda se...." bata karasaba Abeey tadago tana fadin "wayace maki mu zamu auri mazaje broke men ni wllh se me jirgima xan aura wanda ze ringa kaini hutu duk sati Paris,my standards are high kuma ya Mehtav ma bazata kula wanda baida kosisi ba kidena mana fatan masifa rike baki inna tai kmr sa'anni haka inna da Abeey suka shiga cacar baki," daga karshe dai innace tasakko don Abeey use emotional intelligence gurin blackmailing inna cewa don ba idon iyayanta take cusguna mata inna tarungumota tana lallashi hardai aka samu aka shirya taimata alkawari bazata sake tura mata da dan wake makaranta ba kuma hakan bashine yake nufin injibi tayi tuwan dawa tasake zubawa takaima Abeey dinba kuma Abeey badon bataci ba a'ah in agida akai akabata zataci harda side kwano don inna ba daganan ba gurin iya girki masha Allah kawai battason aringa binta dashi school ne wai kawayenta suna mata dariya suna zunbenta irin fasinnan dai na teenagers ita ala dole yar gayece battacin su tuwo su dan wake karshe adakin inna ma tai wanka tashiryata hardai mata manya manya kalba. se bayan sallar magrib tadawo dakinsu Mehtav tadauka Abeey tama manta da maganar mutumin dasuka kade kawai taji tajefo mata tambayar " yayake kotaje tadubashi," nan tashiga laburta mata duk yajja akai tundaga siyar da wayar da zuwa asibiti da yajja sukai da kafaya da kuma sabuwar wayar da nura yakawo mata Abeey tace "Allah dai yasa handsome yafarka dawurwuri donna kagu inga idanuwansa," sakin baki Mehtav tai tana kallon Abeey tace what? tace "yes is he not handsome? Mehtav kalarfa mazan damuke gani a TV ne ashe they exist dani duk duniya gani nake Dr ki Kamal yafi kowa haduwa ashe ko taka kafar wannan beba koyama sunanshi, mehtav gobe bazanje makaranta ba dan Allah kije dani inganshi," girgiza kai mehtav tayi tana fadin "you have to go to school kinji Abeey nima bawai kullum zanringa zuwaba tunda haryanzun befarka ba kinsan idan nafiya fita ina zuwa asibiti daga school akwai yan sa ido za'a iya gayawa paa anganni" tace " kumafa hakane amman don Allah next time idan zakije kije dani pls" da tohm kawai ta ansa mata kafin tashiga kuma tofa albarkacin bakinta kan san kudin kafaya tana tsige kafaya wai se tasa daddy yasallameta daga zama likitar su kila wataran garin san kudinta se abiyata tama cire musu kayan cikinsu basu saniba takarbe wayar dako dubata Mehtav bataiba tashiga operating dinta yajja kikasan tata se kukkusheta takeyi amman ahakan tahana me waya wayarta,da mehtav tagaji d surutunta tattara tabarmata dakin tawuce study room dinsu tashiga rubuce rubucen wasu thesis.

Nuristan

Kukan jaririnne yafarkar da Islam daga dogon barcin daya dauketa ba tareda tasan ma tayiba medauke da mafarkai masu dadi kala kala gameda ita da mijinta tayi mafarki wai Sir EHSAAS yadawo yaga yaronshi yanata murna har yana gaya Mata yajja yay kewarta ita da dansu,mugun shirun dataji garin yadauka yay matukar bata mamaki bayan kukan jinjirin dake gefe hannu se uwar soro da shigowarsu kenan batajin komai ita kanta uwar soron bata iya ganin fuskarta tamika matashi kawai tana fadin "yunwa yakeji,tunjiya beci komai ba Islam kiduba ko ruwan maman yazo kibashi kar mudau alhakin yaronnan" karbarshi tai tana kokarin leken fuskar uwar soro dataketa boyewa kukan yaron yadawo da hankalin ta kansa,ahankali tasoma kokarin feeding dinsa gashi yaki karba da alama besan meye abinba se kyanyara kuka yake yana sake bankarewa sosai kukan nasa yaso yafirgitata. tashiga kuka tana fadin "bazaka shaba pls ka karba yunwa fa kakeji" kanajin mgnr tata kasan akwai tsantsar yarinta aciki,dakyar datamu yaron yakama wani irin zafi taji yana ratsa jikinta tarintse ido tana tina yajja itada babansa suka ringa practicing zuwan wannan rnr domin sauda dama yasha kwanciya akan cinyarta acting like a baby yace tagwada bashi yasha,haka zasuyi tayi harse yamata yawo ya tattabeta, tuna irin good memories din dasukai sharing yakawo ruwa cikin idanuwanta. shigowar jakadiyyar fulani tana me kiran uwar soro fada yakara gigita tinaninta ta tina yajja ta yayyarfa mata mari dazu da safe, uwar soro cikin dakewa tacewa, jakadiyya takula da islam din kuma karta barta tafita sbd jikinta be riga yagama kwari yahade ba don haka dole seta ringa kaffa kaffa da kanta,jakadiyya tace "zata kula in sha Allah" kafin uwar soro tafice tunkafin islam tashiga mata tambayoyi,seda tagama bawa yaron mama yakoshi talura yama yi barci ta cireshi tana rungumeshi akafadarta takalli jakadiyya tana tambayarta "prince yadawo ne,taji fadar tsit koh taron zuwa tarbarsa akeyi afada, itaba agaya mataba aka boye mata? tatambaya tanason tai convincing kanta hakanne abinda ke faruwa deep down tasan ba haka baneba batason tai losing hope ne ma rayuwa baki daya domin idan har yatabbata EHSAAS yabarta battada sauran rayuwa aduniya itama. Diif jakadiyya tai yajja kasan da gunki take magana, "ohhh aibansan kinzama kurma ba seyau bazaki bude baki kiban answer ba" tadan daka mata tsawa jakadiyya kanta akasa tace "Allah yahuci zuciyarki gimbiya islam kuma sarauniyar gobe uwar magaji matar magaji, Allah yaja zamaninki banida ansar tambayarki nima shiyasa kikaji nayi shiru" ahankali tamike tana fadin "zoki kamani muje fadar nima inji me ake cewa," se asannan jakadiyya tadago tana fadin "ranki yadade bazan iya shallake umarnin ta soro ba kuma kaf gidannan ma bame iyawa don haka ki temaka kiyi min rai kibi umarnin ta kizauna anan dakin karkice zakije ko ina" kallon banzan da Islam tawatsa mata ya isa yasanar mata bazataji maganar tata ba,tasoma zira takalmanta da danta akafadarta, jakadiyya rikicewa tai tana rokonta tai mata rai bata saurareta ba daidai zata fita sukaci karo da gimbiya mimah,kallon kallo aka aikama juna kafin tariko hannun islam tana fadin "ana bukatarki afada yanzunnan," "daman can zanje" tabata answer tana gyara mayafinta,gimbiya mimah tamika hannu tana fadin "tohm kawoshi kinsan dai yarone bazaki iya fita dashi batareda izni bako," tace "inke kika haifarmin shi aiseki gayan haka" takarasa tana jan tsaki tai gaba kwafa gimbiya mimah tai kawai aranta tana ayyana yaro besan wutaba seya taka tana ganin yarinyarnan sumi sumi ashe kwanci kwanci taimusu tai luff tagama sanin halin kowa shine yanzun zata ce zata jadasu koh ta isa har ita din wacece. bin bayanta kawai tai cikin son ta kuntata mata take fadin "zadai ki iya gane mijinki cikin kowana Hali ko," murmushin takaici tai tana fadin "ai ballagazun mata masu yawo atiti kullum sune za'a mawa wadannan tambayoyin ba irin islam ba ita islam kullum tana cikin turaka tareda mijinta,don haka babu wanda ya isa yagaya mata wayeshi kuma yaya yake aduk wani yanayin daze shiga," gimbiya mimah tace "peace kenan gantalinma aise wanda ya isa yakeda yancin yinsane keyi,zama cikin turakar miji koda yaushe bahaka yana nufin kinfi kowace mace daraja bane kokuma kinsameshi ahannu baze sake kallon wata macen bane bayanke wani darasin zaman turaka da I love you baxata taba baki shiba harse kinshiga babbar makaranta duniya tayi miki karatun tanutsu kuwa,ko acikin rayuwar dakika baro sun karanta miki zama baiwar miji kullum kina nanike dashi shikesa namijin ya zamana nakine ke kadai....." Islam murmushi tai mai ma'anoni kala kala tana fadin "daman nasan za'a zo gurin nan watan watarana dama kema kinbar boye boye abayan fuskar mutanen kirki kin kirani da kalar sunan da munafukan addini irinki suke kirana ako yaushe," daidai suna karasowa gaban fadar mai martaba NASHWAN EHSAAS NURISTAN, "Inaga ayau dani dake za'a tantance waye munafikin addini yayin da zamuga yajja zaki karbi kalar kaddarar data sameki,banajin xaki iya cinye jarabawar nan hajjaju peace, don anan addinin dakike claiming kinshiga zeyi aiki zamuga karfin imaninki yayinda kikai tozali da wancan gawar datake gabanki" tai mata nuni da cikin fadar tana dauke kwallar datazo fuskarta tsabar shock da islam tashiga kasa motsawa tai harseda uwar soro tafito akai mata iso aka sanar ga gimbiya Islam matar yarima EHSAAS uwar magajin yarima EHSAAS takaraso nan aka mike gaba daya don mika girma zuwa gareta. fadar iya shakikai kuma jiga jigan masarautar ne aciki,fulani tahanga can karshe saman Inda kujerar mai martaba yake zaune yayi turus daman shi baka gans emotions din fuskarsa koda yaushe haka fuskarsa take don zatace tunda take bata taba ganin murmushin bawan Allah nan ba se rnr da EHSAAS yay mishi albishir dacewa yakusa zama grandfather. kuka fulani takeyi wanda bakara se ruwan hawaye inda mafiya akasari daga cikin fadar kuka sukeyi wiwi wasu nafadin shikenan sun rasa gatansu a duniya domin kowa kam yasan EHSAAS bayane goya marayu duk wanda ya rabeshi seya fadi irin tarin alkhairansa gareshi dukda abaya bayannan yasha samun matsala da mafiya akasari daga cikinsu dalili aurensa da Islam din bayaga haka babu wanda zefito yacema ga wani mugun halinshi garesa,kallon fuskokin mutanen fadar dake kuka daya bayan daya takeyi se takega kamar ma dariya sukeyi suna nunota,se takega kmr ma cemata suke sun kasheshi din tayi abinda zatai din,amman dukda haka tana rungume da jinjirinta kam kam,takarasa gaban fulani takalleta itama kallon nata tai tana fashewa da kuka tausayin kanta itada yarinyar seya kamata don tasan babu wanda zekaisu maraicinsa sekuma wannan yaro da beji ba begani ba ammaidashi maraya takarfi da yaji se asannan jikinta yasaki ganin zata saki yaron yasanya uwar soro saurin amshesa tana tare islam din ajikinta nuna gawar takeyi numfashinta nakokarin barin jikinta take fadin wannan... wannan waye? Uwar soro cikeda tausayin yarinyar da kauna da kuncin halin dasuka samu kansu aciki take fadin "yarima ne, Islam...... yarimane kije gareshi kece matarsa keke kadaice xaki iya sheda mana ko gawar tashice koba tashi bace antsinceshi cikin mummunan hali motarsa tayi hatsari shida driver sunkone kurmus bama a iya gane komai dake jikinsu," dasauri Islam takarasa cikin zafin nama zata yaye linkafanin fulani tarike hannayenta tana fadin "ba ananba yata ba ananba," Islam din girgiza kai tashigayi tana fadin "bafa shibane inda shine tundaga can waje zanji zuciyana tana bugawa maamaa he is EHSAAS I do feel him when he is around,wannan bashi baneba," mai martabane yay umarnin "akai yarima ciki sukebe da matarsa da mahaifiyarsa don su duba koshi dinne," Islam rike kanta kawai tai tashiga kaiwa da komowa har aka dauke gawar a idonta sedai takalli fulani tace mata "ki kwantar da hankalinki bafa shi baneba," har fulani takamata suna shiga ciki waziri yaje yana radawa mai martaba "matar yarima fa rashinsa yasa taxauce bayajin ko shidinne zata yarda dacewa shine din domin idan yaduba yarinyar batada wani karfin imani dubada...." be karasaba mai martaba ya dakatar dashi yana fadin "babu wanda yasan waye yafi wani karfin imani se ubangiji wannan ba hurumin sa baneba" ganin ran mai martaba yabaci yasa yace "mishi mezai hana kawai adau gawar tunda yamma ta rigada tayi bazai yiwu akaishi yauba ayi DNA don kawar da shakku daga zuciyoyin mutane dasu kansu," mai martaba yay na'am da wannan shawarar ya bukaci ganin manya manyan masu gwaje gwaje na NURISTAN baki daya.

Acikin dakin daga galadima wanda yake matsayin kanin mahaifi ga EHSAAS se islam da Fulani yabude musu gawar kallo daya Fulani tai masa tafashe da kuka don babu abinda baiyi fata fata ba ajikinsa harta da gashin kansa,bata sake iya saka ido takalleshi ba,galadima yace "fulani kidena kuka dole muna bukatar kuduba don kawar da shakku daga zukatan jama'a," girgiza kai tashigayi tana fadin "bansani ba EHSAAS nada kunya tunda ya shekara takwas aduniya bayama iya cire kaya agabana bansan ya yanayinsa yakeba tayaya kake tinanin zan shaida abinda bansani ba" takarasa tana kuka kmr ranta zefita, Islam data kure gawar da kallo dagowa tai tana kallon fulani kafin takarasa ta rungumeta tace mata " wancan " tana nuna gawar "ba mijina bane ki kwantar da hankalinki", rungumeta itama fulanin tai tana fadin "Islam menene hujjarki tafadar haka babu fa abinda ake ganewa ajikinsan" tace "maama is a trick sunsamo mutum metsayinsa me yanayin jikinsa sunkona fatar jikinsa kurmus,sunkawo sunce shine ba mijina bane," galadima cikeda fusata yakalli islam yana fadin "fulani yarinyar nan tazauce taya zata ringa fadar irin wannan maganganun,ku damafa arna bakusan meye daukar kaddara mekyau da mara kyauba yarima dai Allah yakarbi abinsa inzaki bude kwakwalwarki maganar nan tashiga kibude inkuma ba hakaba..._ juyowa tai tana kallonshi ido cikin ido " inkuma ba hakaba mene nima zaku konanin ne eh" dasauri fulani tarufe mata baki tana bawa galadima hakuri kan rashin da'ar Islam din tace "yarufe gawar suje suyi mata wanka bekamata suke tsayawa kace nace haka agaban gawar yarima ba," ficewa yay daga dakin yabarsu suka dawo fadar aka tambaya kosun iya shedashi straight Islam tace " itafa ba mijinta bane ba inma za'a daina cewa yamutu sudaina yamata alkawari tare zasu rayu kuma baze mutu yanzun ba," waziri yace " gimbiya ai rayuwa da mutuwa na Allah ne ba dan Adam ba ko lokacin dakike karatun tauhidi ba'a miki wannan bayanin ba," kallonshi tai da tafasassun idanunta zatai magana kawai fulani tasa hannu ta toshe bakinta tana fadin "enough Islam accept it sunyi nasara dana yamutu Islam mijinki is gone idan kika cigaba da fito da fito dasu yajja suka rabani da EHSAAS kema zasu rabani dake inason kirayu I want you to live for me and the baby" maganganun ne suka shiga harcikin kahon zuciyarta jin tayi dif fulani ta bude bakinta tana dagota daga jikinta jin yarinyar bata numfashi yasa tashiga girgizata tana ambaton sunanta " Islam Islam wake up," galadima ne ya karaso cikeda tashin hankali yake fadin " meya samu peace din,ke peace" fulani rasa amsar dazata bashi tai ze durkusawa yay yana kokarin daukarta uwar soro ta dakatar dashi tana fadin "aiko giwa tafadi tamutu tafi karfin kiyashi yadauke ta karta sake taga hannunsa koda wasa jikin matar yarima" abinnan yamai ciwo nagaske ganin jama'ar fada su turaki su bai su wambai duk ansoma yimusu kus kus, "amman me bewani damuba don yasan lokacin daze mallaki Islam din yakusa yi nan bada dadewa ba kishin sa na lokaci metsayi yakusa samun ruwan daze kurba yaji sanyi azuciyarsa," wasu daga cikin bayin uwar sorone suka dauki Islam din suka maidata sashenta aka kira likitan ta yashiga dubata panic attack tashiga due to shock din abinda yafaru hakanne yasa numfashinta yadauke ga kuam hawan jini datake fama dashi,allurai yamata yasaka mata ruwa yace "yarinyar nabukatar bed rest fa haihuwa tai kuma bawai normal haihuwaba akwai complications aciki don haka indai baso suke su rasata ba sukula da lfyrta sosai" bayan yagama yiwa uwar soro bayani sosai tace "in sha Allah zasu kiyaye ta sallameshi yatafi"

Zama tai gefen gadon Islam din tasoma tinanin anya itama wannan yarinyar ba barin kasarnan zatai da itaba kmr wancan lokacin da akasaka Fulani agaba ta batar da ita bata tashi dawowa da ita fadar ba harseda EHSAAS yay wayo sosai koshi mai martabar bata bari yasan inda take ba,amman wannan lokacin ba kmr wancan ba tasan intace zatakai Islam kasarta ta haihuwa Nigeria,ba lallai masarautar su tai maraba da itaba domin sosai dan uwanta yanuna rashin amincewarsa da auren Islam cikin zuriarsu duk kaunarsa da shakuwarsa da EHSAAS baze taba iya accepting convert cikin zuriarsu me dumbin mutunci da tarihi irin borno kanem empire ba,inaaa dole dai tasan yajja zatai takula da islam da danta don ganin babu wanda ya cutar dasu surayu cikin aminci.

Masarautar gaba daya tadau mutuwar yarima EHSAAS dukda babu official announcement daga fadar mai martaba NASHWAN amman me ba'a iya boye abu natsawan lokaci acikin masarauta duk girmanta kuwa,harta da mgnr DNA seda tafita ko ina katsaya sekaga bayi na kuskus damasu cewa ba hatsari bane kasheshi akai damasu ayyana cewar hatsarine adena zargi,da daddare bayan ganawar sirri da mai martaba yay damasu gwaje gwajen suka dau sample dinsa dana EHSAAS suka tafi dashi donsu gwada washegari da sassafe suka dawo cikin wata ganawar sirrin aka kawo sakamakon seda suka fita mai martaba yakira aturamai maga takarda anan ne yabashi umarnin sanar da mutuwar EHSAAS ga kafafen yada labarai dake NURISTAN baki daya,waziri cikin kunci da tsananin tausayin dan uwannashi daya rasa magajinsa kwaya daya rak duniya yashiga kuka gaban me martaba yana cemai "ko kar asanar kawai suyi komai asirrince don mutane zasuzo ne su karo musu damuwa akan wacca suke ciki" mai martaba yaki yay na'am da shawarar yace "lallai lallai asanar da duk alumma don suna da hakkin sanin EHSAAS dasuke mutuwar so suke kauna yazama sarkinsu yatafi don haka yazamana dole su cire rai daga shi su fawwalawa Allah komai kmr yajja suma iyayensa suka fawwalawa Allah dukkan lamarinsu," kafin yasallamesu baki daya bayan yasanar dasu karfe tara za'a kaishi. Daga cikin gidanma koke koken matan ne ketashi tako ina anata jaddada alheran EHSAAS din dawanda sukamai ganin karshe da kus kus din dalilin kisan nasa dake tashi tsakan kanin bayin mai babban daki dana bangaren Fulani kuwa fito nafito suke da juna takarkashin kasa inda bayin Fulani ke ganin kamar mai babban dakice keda hannu amutuwar yarimansu na mai babban daki kuma suka fito suna kare uwar dakinsu,sam sam fulani batasan mema akeciki ba itadai tashige turakarta takulle kanta ba abinda takewa danta se addua da rokon masa rahmar ubangiji itakuma mai babban daki gani takeyi fulanice take sawa ai bayinta suyita batata acikin gidan da idon Al umma baki daya,tacika tai fam. gimbiya mimah nata lallashinta tana megaya mata cewar "fulani jimamin mutuwar EHSAAS matakeyi bata da lokacin yada habaici da gutsiri tsoma tafasan halinta tun tale tale," sarauniya hassana ce tashiga taya me babban daki suka yiwa mima tas tas kan yajja taketa kokarin kare fulani taki bin bayan mahaifiyarta harda kiranta da mara zuciya taje can sun sallamata wa Fulani. bayan fitar mimah me babban daki takalli sarauniya hassana tana fadin " yanzun wannan yarinyar banda asarar haihuwa da namiji ce da EHSAAS ma ya isa ya kalli kujerar can ta mulki," hassana tace "ina kojin kamshi ma bazeba ballantana yama hau," jinjina kai kawai mai babban daki tai tana fadin " yanzun fa se a iya cewan dan kafirar can da aka haifa shine ze gaji mai martaba kuma wllh baze yiwuba bayan ga Aman nan yagirma yazama saurayi can masarautar ubannasu ma anfi karfinsu nanma haka da ace mai martaba zewa mimah adalci aida yabashi" hassana wata shewa tai tana kallon mai babban daki tace "kinsan wannan lamari baze taba yiwuwa ba badai amasarautar NURISTAN ba ko,domin bantabajin inda dan mace yay mulkinta ba atarihi," " hmmmmm" kawai mai babban daki tace before tace "nasani hassana amman da ace ai nace,but ba damuwa yanzun ni garama abawa daya daga cikin wadancan tsinannun Erfan ko jay domin da inga mulkinnan yakoma dakin Fulani ko yawone gara nayi tsirara din inga nahana hakan,," "hmmm" kawai hassana tace tana gasgata mgnr biye biyen malaman da ake cewa mai babban dakin nayi dukda bata fito fili tagaya mata ba duk yajja suke itama kuma battada zarrar tambayar tata,tunbayan da labarin rasuwar yabaza kasar NURISTAN mutane kezuwa daga guri guri cikin kankanin lokaci fada tacika da masoyan EHSAAS domin halartar ta aziyyar sa,lokacin da kakanshi yakaraso lokacinne mai martaba yatsugunna gaban gawar dan nashi yashiga yimai addua iri iri babu hawaye ko kadan idanuwansa sbd me martaba irin murdaddun mutanen ne dabazaka taba gane emotions dinshi ba duk bin kwakkwafin ka har suka fito dashi dumban al umma suka sallaci gawar EHSAAS Bin NASHWAN Bin EHSAAS NURISTAN,bisa jagorancin kakansa nagurin uwa mai martaba Fuhad Khalilullah sarkin Askira daya daga cikin masarautun borno kanem empire,aka nufi hanyar kai EHSAAS gidansa na gaskiya,sosai jikin fulani yarikice daga bangaren ta harseda aka danganeta da asibitin cikin masarautar itama jinin natane yahau sakamakon rashin tilon dan nata da takejin bazata iya rayuwa babu shiba har abada tana iya tina kalar azababbiyar rayuwar datai acikin gidan kafin haihuwarsa dayajja yazo yazame mata garkuwa yanxun Allah daya batashi yafita sonshi yakarbi abinsa hakanne yasa zaman makokin mata kacokam yakoma bangaren mai babban daki kasancewar itace uwar gidan sarki kuma me masaukin baki na fadar. taji dadi sosai ganin yajja manya mutane keta kai kawo asashen nata nan tashiga treasure kasa tana order dafe dafe kala kalla iri iri cima se wacca kazaba itakanta gaisuwar bangare bangarene harda gun VIP inda ake saukar masu kudi jiga jigai damasu mulki dake zuwa daga bangarori da dama na kasar da ketaran ta da bangaren talakawa wanda sune ainahin masoyan EHSAAS din sune ake bari daga farfajiyar sashen nata anata kawo musu kayan tabawa wasu kam nan suka samu gurin zuwa cin safe,rana harda dare anan sukeyi haka akayi sati cif cif ana karbar gaisuwar mutuwar EHSAAS mai martaba be zauna ba amman behana kowa zamaba bangaren maza hakan ne yabawa su waziri kofar zaman su suka rika amsar gaisuwa suma bangaren nasu jari hujjar suke bazawa tako ina ana wadaka da dukiyar sarki NASHWAN batareda saninsa bama.

Daga bangaren Islam farkawarta tafarko da rigima tatashi alallai lallai mijinta be mutu ba DNA din da akai uwar soro da kanta taje gurin mai Martaba ta karbo mata,tunda idanuwanta yay tozali da DNA dinnan tadena uhm bare uhm uhm bama wanda ake bari yashigo gurinta ko gaisuwa uwar soro keta dawainiya da ita ga jariri ga tsufa amman dukda haka bata gajiya da bawa Islam din kulawa wacca haryau ko kukan rashin EHSAAS din ta kasayi domin zuciyarta takasa yarda ta amince cewan yatafi yabarta ranar da akai sadakar bakwanshi mai martaba yaywa yaron huduba da sunan mahaifinaa EHSAAS bin EHSAAS bin NASHWAN bin EHSAAS NURISTAN.

kuma bayan yagama hudubar ne yay official sanarwa dacewar ya nada yaron matsayin crown prince na masarautar shine zegaje shi wanda shine matsayin mahaifinsa Ada lamarin yamatukar girgiza al umma da masu ma harinsa cikin masarautar don andauka mai martaba zeji tsoro ko yaja da baya ko yay kokarin protecting yaron amman me sema nunawa masu harin nasu dacewa har abada jinin fulani shine ze mulkesu hakan yasa suka jada baya suka soma sabon shiri kan yajja zasu farmakin jinjirin dabesan komai aduniya ba,domin sun sha alwashi babu dan bakin dazezo yamulkesu har abada.

Abuja Nigeria Daga bangaren su mehtav kuwa asace kusan kullum take zuwa gurin mara lafiyar nasu daga school abin kamar wasa haryau yaki yafarka dukda wani lokacin yakan motsa wasu gabban najikinsa batareda yabude idanuwansa ba zuwa yanzun ita kanta Dr kafaya tafara losing hope. rnr asabar Bayan sundawo daga training din safe da sukeyi itada Abeey a estate dinnasu tashiga lallabata kan "dan Allah itama yau taje da ita gurin handsome din tanason taganshi,don Allah" tace mata " tabari se inna tatafi tukunna" aikuwa suna komawa sukaga inna ringidi ringidi da kaya anloda mata a taxi din tasha drop aka daukar mata zekaita har kauyen,wani irin farinciki ne ya lullubesu kuma inna naganin farinciki karara afuskarsu tasoma wondering meyasa don dukda zaman doya da manjan dasukeyi agidan wani lokacin zakaga indai zata koma Abeey tata rokonta kena karta tafi ta barsu zatai kewarta amman yau setaga kamar ma Abeey tafi mehtav murnan tafiyarta zuciyarta setaki kwanciya da tafiyar. tace wa Abeey "ko dai in fasane Abeeda naje wani satin" dasauri Abeey tabude mata taxi din tana fadin " haba inna bafa kitaba fashin tafiya kauye sati satinnan ba nasan su dada sunacan suna jiran zuwanki karkuma muzama masu sonkai koh innata takaina kitafi kawai Allah yakiyaye hanya karki damu bazanyi kiriniya ba kuma zan ringa jin mgnr mehtav koh sister mehtav," mehtav dasauri tajinjina wa inna kai don sosai itama takeson innar tabarmusu gidan su sarar inna badon tasoba tashige motar tana jaddadawa mehtav takula da gidan takula da Abeey karsuje koh ina daga makaranta se gida. tajinjina mata kai kawai harseda suka dena ganin motarta sannan suka koma ciki Abeey tadau remote taware disco tashiga waka tana fadin "enjoyment is free, finally tatafi," itakuma mehtav tashige kitchen fridge tabude tadakko gashin kazar da inna taimusu na musamman tace sukwana biyu sunaci karsu taba mata nama suyi almabazzaranci kafin tadawo tadakko musu rnr ko girki basuyiba kajin suka cinye tass suka hada da yoghurt irin duniyarnan tasamu. da yamma suka fesa wanka,duk yajja mehtav taso karsudau motar mamansu seda Abeey tazigeta "wai inbasu mori motar ba waye ze mora" tasan dai jabiru baya aiki weekend indai ba daddy ne yay requesting ba aikuwa suka fito amman tace "ba zasuyi gudu ba," zuge garage din gidan sukai suka fitoda classic car din susu biyu sukai dusting dinta suka shige Abeey zata kunna kida mehtav tai mata gargadi murmushi tai tana janye hannunta tace "bari nabari karmu sake kashe wani," suna fitowa da motar kuwa dan liti yabisu da kallo,kmr mehtav tasan mgn ze musu ta kirawoshi tana fadin "kmr fa wata yay nisa ko baba dan liti" ya jinjin kai yana sosa keya "ya za'ai hjy mehtav" purse dinta Abeey tazuge tana fadin " tohm ga wannan sekasa kati" dubu biyarce tabashi aiko yaringa godiya kmr ya durkusa musu suka fice agidan bece musu uffan ba, dariya suka shiga yi Abeey harda gwada yajja baba dan litin keyi,mehtav tace " kan uba Abeey kudi fa duniyane wato money can buy everything," Abeey tajinjina kai tana fadin "shiyasa nace miki duk rintsi duk wiya karki sake ki kiyarda ki aura mara kudi bakiji duk saurayin dayace yanason ki ina kare masa kallo naga wagairahun ne sena koreshi ba," mehtav tace "Abeey bakida kirki amman aiba kudi ake dubawa azabi mijin aureba in mara kudinne nagarin fa," wani irin kallon karfa kifaramin wa'azi Abeey tamata before tace "shiyasa aimuke addua shi Allah zebamu kome muka roka kiroki nagari kuma mekudi kinji ya mehtav I'll never allow you to go out with a broke guy unless....." sekuma tai shiru,mehtav tace "unless what? tace "sede if he is handsome as handsome as our handsome patient sister," girgiza kai mehtav tai tana fadin "shut up your not serious let me drive in peace" haka Abeey taita mata surutu harsuka karasa cikin asibitin straight dakin dayake ciki Abeey tawuce itakuma mehtav tatafi gun Dr kafaya don jin yaya yanayin jikinnasa yake.

Abeey cikin sanda don kadama wata nurse din taganta tahanata shiga tai saurin shigewa tana tura kofar dakin ahankali cikin sadaf sadaf tajuyo tana dafe kirjinta ganin tashigo ba wanda yaganta bude idon da zatai idonta yasauka cikin nasa dara daran kwayar idonsa masu kalar mage yafirgitata,ihu takeson tayi amman tinawa dacewa wani ze iya jiyota azo akoreta yasanya tai saurin toshe bakinta tana kallon sa shima kallon yajja take kallonsa yakeyi, glasses din fuskarta tacire ta murza idonta before tamayar tasake ganin ita yake kalla, "so he is awake? so tari tasha imagining yajja idanuwansa zasu kasance inyana farke amman aduk hasashenta bata taba hasaso kyawawan grey eyes irin wadannan ba,his eyes look angelic, murmushi tai masa tana karasawa gaban gadon nashi tana ganin yajja aka nade mishi goshinsa da bandage, bewani ji rauni afuskaba se jikinsa dayake sanye cikin rigar asibitin green colour,sosai take sake ganin kyawunshi kamar wani balarabe, hannunta tadan mai waving ganin ya kureta da ido yana kallonta ko kiftawa bayayi,tace mishi "hey" ganin bece mata komai ba yasa tamika hannu tana kamo hannayensa wanda babu drip ajiki tace "I'm Abeey kaifa ya sunan ka? kallonta yay tace " yes Abeey kaifa? tana nuna shi, ahankali ya kyafta ido yana nuna kansa tinanin ko bayajin Hausa tace mishi "yes! what about you? What is your name? "Me" tanuna kanta " I'm Abeey"

Ahankali cikin wata irin deep musculine voice irin wanda yatashi abarcinnan so slow yet so deep and melodic taji yace "Abeey" yana nunata ta jinjina kai tana ta jin dadi yakira sunanta,setaji yace " I'm Abeey" kyalkyalewa tai da dariya tana fadin "no I'm Abeey not you," setaga shima ya kyalkyale da dariya sosai dariyar yaymai mugun kyau har dimple gareshi yana fadin "Abeey," dafe kanta Abeey tai irin kash dinnan yayake duk abinda tai,tace masa "name,suna, suna,isim," su Abeey harda larabci tace "ma ismuka? Setaga yadan tamke ido yana jujjuya kai suna daya ne yake yawo acikin kwakwalwarsa tunda yafarka babu abinda kunnuwansa keji se sunan,yakalleta yana fadin Islam? Da alamar tambaya,tace "Islam? sunanka islam? shiru yay don be fahimci me take nufiba cikin daburtaccen larabcin nata take fadin "ismak Islam? nanma yay mata shiru, Abeey rasa yajja zatai tai setace masa, "if laaaaaaa laaaa, inna tambayeka kai, girgiza min kai" tafara jujjuya kanta "if na'am na'am idan natambaya seka jinjina min kanka haka" tafada tana jinjina kai,don ita kawai atinaninta larabci yakeji,tace ismak Islam? Jinjina kai yashigayi ganin shine last abinda tai kuma shiya rike cikin kwakwalwarsa da take empty bakomai aciki se wanda tazuba din ayanzun sekuma sunan Islam dake echoing a brain dinshi batareda yasan daga ina yake fitowa ba,kujera Abeey taja tana fadin Islam yajikin naka? Kallonta kawai yake,dan jim tai tana tinanin tohm taya zasu keyin hira tunda bayajin hausa bayajin turanci gashi kuma ita bajin larabci takeba se wanda take tsinta a bakin malamansu sama sama,itafa bata iya zama batai mgn ba hakanne yasa takalleshi tana fadin " amman fa Islam sunan matane ashe akwai maza masu irin sunan,bakada suna se wannan," tatambayi kanta da kanta,sekuma tai murmushi tana fadin "bamafa jina yakeba" seta karasa tazauna saman gadon shi wannan karon tana fadin "anta....uhm.... anta handsome" tana murmushi,shima murmushin yaymata ganin abinda tai masa kenan dadi taji sosai atleast tasan yaji dadin ganinta tunda yana mata murmushi, " handsome" tasake fada masa, lumshe ido yay kawai yatsinci kansa dacewa "beautiful," zabura Abeey tai tana fadin "laaaaaaa ashe kannajin turanci" kamar tanitse tsabar jin dadi kafin tace "bari naje nakira maka likita da ya Mehtav," zata fice taji yariko hannayenta, tajuyo tana kallonsa gani tai ya kwakkwabe fuska yace "don't go," mamaki yakara kasheta ganin yajja tagama wage baki tanamai larabci dazun sarai yana jinta,tadawo gefensa tana fadin "ashe dagaske kanajin turanci tohm kai dan wani garinne? ta tambayeshi da harshen turanci, gari? Yamayar mata da tambayarta don yanajinta amman kalmomin besan ma'anarsu kokuma amsoshinsu ba shiyasa yakasa answer mata ta jinjina kai tana fadin "eh garinku? yace "Islam" tace " eh nasan sunanka Islam garinku fa," yasake cewa "Islam" tagumi tai tana fadin "wai kai baka iya cewa komai ba nima sunaan Abeey amma sunan garin mu Abuja kaifa yasunan garinku," shima yace mata "Abuja" dariya tasashi agaba tafarayi yana tayata dukda amsawar dakansa keyi dede nan Dr kafaya tashigo tareda mehtav abayanta wacca ta gamawa bayanin halin da patient din keciki tunsafe sunata kokarin mai mgn yaki cemusu komai kmr ma bayajin mesuke cewa ita atinaninta Allah yasa bawai yasamu total blackout na memory dinsa bane donshi suke zargi tuntuni don ba karamin bugu yaji a brain dinsa ba,harsunyi concluding daurashi kan magungunan total amnesia that means yamanta komai na rayuwarsa harta da sunanshi baze iya tinawa ba amma me se taganshi yana kyakyata dariya tareda Abeey mamaki yakamata sosai haka zalika mehtav takaraso tana fadin Abeey what are you doing here? Tace "sister Mehtav zokiji abinda handsome patient dinnan yake cewa fa duk abinda nafada shine yake maimaitawa kuma yanajin turanci," ganinsu Mehtav yasanya ya kafesu da ido duka subiyun fuskarsa tadena dariyar, Abeey tace "Islam kaga wannan sunanta yah Mehtav, wannan Aunty doctor" tana nuna masa su,bin bakinta yashigayi tasake maimaita masa yace " yah mehtav " tai sauri tatafa hannu tana fadin " karike wannan" yalumshe mata ido tace wannan Aunty doctor,yace "Aunty doctor" tace " wow Islam your a fast learner," "wow Islam your a fast learner" taji ya maimaita aiko tasake kyalkyalewa da dariya domin kwaikwayarta yay harta da muryarta, Mehtav takalli Dr itama takalleta donsu sunsan akwai matsala amman Abeey duk tinaninta wasa ake mata ne kawai shiyasa yake maimaita duk abinda take fada Dr kafaya takalli Abeey tana fadin wayace miki sunanshi Islam shine yagaya miki hakan? Tace " ehmn koba hakaba islam? aisunanka Islam ko? yalumshewa Dr kafaya ido don girgiza kan namai wiya, Mehtav dai tatsaya kallonshi da alamar itada Dr kafaya basu masaba don tunda sukazo yadena dariyar da yakeyi me matukar kyau, Dr kafaya tatsaya akansa tana dan observing dinshi before tace mishi Islam how old are you? Bude ido yay yawatsa mata su batareda yace uffan ba,takalli Abeey ganin kmr yafi sakewa da ita tace mata "ask him" Abeey tace "islam handsome wai Dr tace shekarar ka nawa,ni shekarata 11 kaifa," dan jim yay before yace "I don't know" mehtav takalli doctor, doctor tace masa islam from which state kazo? Kallon Abeey yay yace "Abuja" don dazun tayi feeding dinsa dawannan knowledge din, girgiza kai Abeey tai tana dariya tacema Dr " karki yardafa dazun niyaji nace Abuja shine shima yafada," "islam kagaya mata daga wani gari kake" yasake maimaita Abuja,dariya Abeey tashiga yi amman ganin Dr da mehtav basa dariya yasanya tai shiru tana kallonsu, Dr tace " Islam garuruwa nawa kasani aduniya? yasake cemata "Abuja" rike kai Dr kafaya tai tana kallon Mehtav ta dafata tai waje alamun tabiyo ta suka barshi da Abeey. tunkan su karasa office Dr kafaya take fadin "yazama dole ku gayawa engineer abinda ke faruwa domin shishi kadaine ze iya nemo ahalin gayennan,mehtav he is lost marabarshi dayaro dan shekara daya daya bata babu banbanci babu abinda yake iya tinawa se Islam wanda banma tabbatar ko sunan nashi ne na ainahi kenan ba aje sunanshi ne tayaya kike tinanin Islam kadai ze yi leading dinmu to his family uhm Mehtav, dolene kiyi hakuri kidaure kigayawa mahaifinku lamarinnan inba hakaba zansanar da kafafen yada labarai kilama iyayensa nacan suna nemansa basu sameshi ba" dasauri mehtav tadago tana fadin "Dr karkiyi haka dakanki fa kikace kingafa raunika ajikinsa idan wasune sukeson halakashi kinbasu information din inda zasu sameshi cikin sauki kenan doctor look at him katon saurayi acting like that is heart breaking" tafada tana zubda kwalla, "I'll help him dan Allah kibarshi anan zuwa lokacin da daddy zedawo zan gayamai da kaina kinsan idan nagaya mai yana abroad zedaga hankalinsa yabar duk abinda yakeyi yace zedawo sannan he won't take it lightly let me tell him in person don Allah doctor" dan jim tai domin tafi kowa sanin halin engineer duk abinda Mehtav tafada gaskiya ne amman tabbas guy dinnan need his family close,sune zasu temaka gurin recreating memories din da zasusa yatina wani abu cikin past dinshi,zamansa tare dasu anan sake goge masa rayuwarsa tabaya ze ringayi ahankali ahankali harse yakai yakawo ko ya gansun baze iya tina komai fa game dasuba,bayanin da Dr kafaya tashiga yimata Kenan. It's fatoumspassion EHSAAS Don't forget to like Share & comments

Follow *** page @fatoumspassion And arewabook @fatoumspassion

[13/04, 08:11] Fatima Rufa'i Nasidi: *** EHSAAS It's fatoumspassion EHSAAS

Another exclusive piece from the passionate writer of AYSAM And INTENSE LOVE.

The widower

Hey Hey Hey Taji ana whispering acikin kunnuwanta, Dawata irin sleepy and deep voice yake mgnr a kunnuwanta wannan karon jitai yana shafa mata kunnuwan da tattausar fatar lebenshi ahankali yake fadin "wake up! is noon already,your baby is missing you" "Let me sleep pls Sire, I didn't sleep properly last night," "Uhm.... uhm nidai sekin tashi" yashiga juyo da ita cikeda shagwaba tasoma ko kawar komawa barcin nata tana tura mishi baki wanda tasan murmushi yake mata "alright I'll go get some maid, tunda bakison kula da mijin naki ita zatamin wankan aita ban abinci inci kuma tai duk yajja nakeso without complaining" aida sauri tamike tana kallon grey eyes dinshi da dara daran bakaken kwayar idonta tana galla mai harara kafi tadau pillow tasoma buga mishi cikin wasa take fadin "tohm kaje mana narike kafarka ne aidaman nasan idonka nakan duk yanmatannan da ake kawowa dasunan bayi suna kaikawo a palace dinnan donsu ja hankalin mazan mutane tohm kaje din kagani nima aina dena sonnaka zanje nasamo wani mijin baruwana dakai ma" takarasa fada tana bugunshi tajefar da pillow tana kwantawa tajuya mai baya rungumeta yay yana dariya tabaya yake fadin "who told you akwai macen da aka haifa da EHSAAS zekalla bayan peace dinshi your my peace forever,your mine nini kadai and I'm yours! juyo gareni Princess peace uwargida kuma amaryar agurin EHSAAS," yana jiyo dariyarta kafin tajuyo tana fadin "promise I'll be the only woman in your life,bazaka sake cewa zakaje gurinsu ba,kuma you'll live with me forever and ever Sire" " I promise" yafada yana kissing saman dogon hancinta, " I can't do without you Islam, I'll always be with you".

Kukan yaronne dayake canyarawa yadawo da ita reality din da take ciki EHSAAS yamutu kuma wannan din junior dinsane ke kuka acikin kunnuwanta,juyawa tai gefe kawai tana kallon yaron da aka kwantar dashi agefenta da alama shima daga barcin yatashi ya rare makogaro se uban kuka yake irin na jarirai farar fuskarsa irinta babansa tayi jajir kasa daukarsa tai kawai tamike zaune tana kallonsa itama tana zubda hawayen shigowar uwar soro ne yadawo da ita cikin hankalinta tana tambayar "me yasameshi? kallonta Islam tai takoma takalli fuskar jaririn kmr wata mutum mutumi take fadin "kuka wai yake" "dayake kuka bazaki daukeshi ki rarrashe shi ba yaronnan tunsafe yake barci tashin sa kenan kilama yunwa tatayar dashi bazaki daukeshi ki kula dashi ba" tashiga mata fadan da yakara tunzura zuciyarta tacigaba da kukanta yaron kam kmr karo mishi volume ake uwar soro daukar sa tai tana daurashi saman cinyarta "maza gashinan bashi yasha yakamata koke kokennan yatsaya haka muma duk munsan munyi rashi kuma bamuda madadinsa har abada amman kisani Allah daya karbi EHSAAS yafimu sonshi kuma yayi hakanne don yagwada imaninmu ko zamu karbi kaddarar rashinsa, Islam dakika fadi kalmar shahada ba'a gaya miki cewar imani da kaddara mekyau ko mara kyau yanada ga cikiba, Islam wake up EHSAAS is gone baze taba dawowa ba azabtar dakanki da kikeyi da kuma wannan yaron bakya kula dashi kinason ubangiji yay fushi dake kina nunawa baki gode masa da ni'imar dayay miki ba kalli yaronnan kinsan da ubansa nada rai ehem yaji yace se ranki yayi mummunan baci bama xaki somaba" takarasa tana goge kwallar data kawo idonta,se asannan taga Islam tarungume jaririn tashiga dan jijjigashi yana kuka tana kuka harseda yadanyi tsit sannan tadaurashi saman cinyarta har lokacin bata wani iya tsayawa tabashi mamar dakyau ba kasancewar haihuwar farice seda uwar soro tatemaka mata kuma maganganun uwar soro bakaramin taba mata zuciya sukai,tayaya zata kasa karbar kaddarar data sameta takula da yaronta wanda shine komai nata aduniya yanxun,kuma tasan Allah ne merayawa da kashewa kuma tasan mutuwa wajibi ce gadukkan abin halitta amman me bata dauka zetafi yabarta dawuri hakaba bata dauka journey dinsu baida tsayi ba da tayi amfani da duk wata damar da Allah yabata wajen gwadawa EHSAAS soyayyar dabata tabai masaba lokacin yanada rai tabbas da ko second daya bazata barshi yayi ba yana atare da itaba. uwar soro ganin tarintse ido tana kuka yasa tadanji sanyi aranta atleast intai kuka wani kuncin zefita don bakaramin firgicewa da fita hayyacinta taiba and takasa kukan tuntuni takeson taga Islam tayi kuka kozata fara moving on daga cikin kuncin datake ciki,dede nan jakadiyya tai wa fulani wacca batajima da fitowa daga asibitiba iso zuwa cikin dakin.

tunda akai rasuwar bayan sheda gawar Islam se yanzun take ganin Fulani,sosai taji zuciyarta takarye ganin Fulani tawani irin ramewa takara wani mugun haske akan wanda take dashi domin EHSAAS dukda cewa da me martaba yake kama hasken mahaifiyarsa yadakko dawannan grey eyes din Fulani yar kwalliya, Fulani da zakaga jikinta kullum cikin wankan gwalagwalai da ornaments na asalin gaske,yau fulani babu komai ajikinta face dogon rigar abaya baka data saka tanade kanta da gyalen abayar se shekarunta suka fito sabanin da da bazaka taba ganinta kace tama haifi saurayin da kmr EHSAAS ba, idanuwanta sun kumbura suma kmr nama sunyi jajir tsabar kukan dataci tagode Allah yaune ma tasamu karfin gwiwar fitowa don duba jikin Islam din da abinda ta haifa, gudan jininta jikanta dan danta kwaya daya abin alfaharinta. Itama dataga Islam seda ta tausayawa yarinyar don gani take acikin abinda yasamu EHSAAS kmr da sakacinta da har tabar mai martaba yake zartar da duk hukuncin dayaga dama akan dansu da ace lokacin daya turashi wancan garin bayan yakawo kukansa bayason zuwa ta bashi goyon baya sun saba umarnin mai martaba kila da har yanzun yana tare dasu tinawa tai da yajja yadaura goshinsa saman nata yana fadin "maama banason intafi inbarku, Islam batada lfy zata iya sauka ako yaushe,maama ki kulamin da ita" "Maama" muryar Islam tadawo da ita daga tinanin wucin gadin data tafi kawai se sukaga tajuya ahanxarce tafice adakin tana rufe bakinta da hannayenta battason tai kuka gaban Islam takarya mata zuciyarta amman batajin xata yafewa kanta barin EHSAAS yatafi datai. uwar soro takalli Islam tana fadin "ki kula dashi ina zuwa," bin bayan fulanin tai kmr yajja tai tsammani bata fita asashen ba domin baxata iya fita tana kuka agaban bayin su ba shiyasa tatsaya ababban falon taci kukanta tagode Allah uwar soro na bayan ta bama talura da zuwanta ba harseda tamike xata fita, taji uwar soro tace "Hajar koma kizauna" kasa dakanta tai domin akwai alkunya da tsananin ganin mutuncin juna dake tsakaninta da surukar tata, komawa tai tazauna amman wannan karon akasan carpet don bata taba zama kan kujera uwar soro nasama tana sama ba,Uwar soro tazauna ba abinda taimata se nasiha kan yarda da kaddara da yajja takeso tadaure takarfafa jikinta da imaninta suhadu sukula da yarannan Islam da danta don yanzun sunfi bukatarta akan kowana lokaci tagaya mata adduar ta danta yake bukata ba koke kokennan ba,ta tinatar da ita dangane da ni imomi da dama wanda Allah yaymata tana mebata hakuri da lallashi da nasiha da banbaki kuma sosai Fulani taji sanyi azuciyarta don zuwanta so tai tadauki Islam din takoma sashenta da zama ko ganinta kullun da dan zesa ta manta danata dan,nan tasanar wa da uwar soro shawarar datake azuciyarta uwar soro tai jim kafin tace subar Islam asashen ta kawai domin tanason subarta tasaba da kadaicin zama ita kadai,domin ayanzun itace giwar masarautar su uwar magajin sarki,don haka dole tazauna takoyi rayuwa cikin mutanen da basa kaunar ta batareda kariyar daya daga cikinsu azahirance ba amman zasuyi ta bayan fage tasanar da fulanin haka,badon fulani tasoba tabi mgnr uwar soro don bata taba fada ta fada ba duk tsawon shekaru 35 da aurenta.

Daga bangaren su Mehtav kuwa patient dinsu haryau jiya iyau babu abinda yake tinawa dangane da rayuwarshi tabaya,se sunansa Islam, Islam baya taba yarda dakowa a asibitin harta da Dr kafaya, sedai Abeey ko abinci aka bashi indai Abeey bata zoba anan yake wuni baze ciba don ita tafara koyamai ma yajja akecin abincin ga dan banzan iyayi haka Mehtav take cewa "yana magana daidai kmr wani basarake" don seka bada attention dinka sosai zakaji meyake cewa shida Mehtav basa wani shiri amman kuma basa rashin shiri,shidai Abeey ce tasa itakuma babu abinda yake burgeta dangane da handsome patient din se yajja babu abinda yasani komai yagani seya tambaya Abeey tazama kamar wata malamarsa don taciro sabon biro da book acikin kayan karatunta tataho masa dashi asibiti wai xata fara koya mai yajja ake karatu da rubutu wani bin insuna shirmensu da Abeey seka rantse shima yarone me kamar shekarunta kuma tariga tasoma feeding din kwakwalwarsa da nonsense din abubuwan yara yanxun babu abinda yake burgeshi irinsu. kuma haryau asace suke zuwa asibitin batareda sanin kakarsu ba duk wata hanya da zatasa kakartasu ko mahaifinsu yazargi wani abu Mehtav ta tosheshi don bakaramin tausayin guy din takeji ba dukda sometimes gani takeyi kmr ma kallon tara saura kwata yake mata,cikin sa'a wata nashiga babansu yaturo musu kudin kashewa aiko itada Abeey suka shiga boutique suka kwaso masa kayan sawa iri iri suka taho dasu asibitin rnr da za'a sallameshi kenan, itakanta Dr kafaya dukda basa shiri da patient dinnata sosai tashiga jimamin inda zasu kaishi bayan ansallameshi tunda babu wanda yasani nashi har yanzun amman jin Mehtav ta sanar mata ai akwai wani gidan marayu dataiwa mgn akanshi tabasu kudi zasu ajje mata shi kafin paa dinnasu yadawo taji dadin mgnr ko tsayawa nazari akan mgnr bataiba tarubuta musu takardar sallama tabasu. suna fitowa takalli Abeey cikeda tsoro take fadin "wllh nidai tsoro nakeji kinsanfa bawani gidan marayun dazamu kaishi kinsa namata karya" Abeey tsaki taja kamar wata babbar budurwa take fadin "kinsan cewa ko akwai bazan bari handsome yaje ko inaba ko, gida zamu tafi dashi and I promise you no one will know cewar yanacan wannan satin fa kinsan na midterm ne ko inna nazuwa kauye tai sati paa baze dawo ba kinsani se yagama abubuwan dayake bama shida rnr dawowa meyasa zamu barshi a street, yah Mehtav kisani kema zaki iya fadawa halinda handsome keciki zakiso awulakanta ki abarki haka aki kula dake? dan jim tai before tace "but Abeey kinsan is wrong, paa zeyi fushi damu sosai inyagane," Abeey tace "aikan yagane memory din Handsome zedawo badai yanashan magani ba zamu kaishi har gidansu shima," jinjina kai Mehtav tai tana na'am da shawarar Abeey domin batada wani abokin shawarar sama da ita kuma sau da dama ko batai agreeing da abu ba deep inside tasan is wrong don farincikin Abeey seta biye mata,atare suka tura kofar dakin,yana zaune da kayan asibitin ajikinshi yanata bitar karatun da Abeey takoyamai na one 1,don yau tace zata ji kuma inbe iyaba tadena wasa dashi. "handsome" tafada tana karasawa dagudu tafada jikinsa ta rungume shi shima rungumeta yay back yana sakar mata murmushin daya sanya deep beauty points dinshi bayyana kansu agefe da gefen fuskarshi, Abeey tadago tana kaimasa peck gefen kumatu take fadin "I miss you," yace "I miss you too" don tini Abeey takoya mishi yazauna dam akwakwalwarsa,zamewa tai tazauna agefenshi tana fadin "karatu kaketa yi haka" yajinjina mata kai yana kallon Mehtav data shiga hada masa kayayyakin dasuke kawo masa irin su tea plask,milk,bournvita kulolin abincin jiya da su toothbrush da toothpaste da daisauransu, "tohm biya muji" muryar Abeey tasa attention dinshi yakoma kanta, murmushi yay yashiga biya mata One 1 Two 2 Three 3 Four 4 Har yakai twenty,tafa masa Abeey tashiga yi ita kanta Mehtav was impressed dayajja yay saurin kwashe komai da komai don tana jinsu jiya da daddare suna tayi kala bata cemusu ba. Abeey tace masa "Handsome kaga an sallameka yau" tawarware takardar tashiga nuna masa yanzun zamu tafi gida can gidanmu anan zaka zauna tare dani dakai d yaya Mehtav. sosai yashiga murmushi yana jin dadi daman kusan kullum se anyi drama rabasa da Abeey inzasu tafi yaringa kunci kenan harse Mehtav tadaka musu tsawa daga shi har Abeey din sannan suke rabuwa da juna,. Mehtav tagama shirya kayan tsaf suna hira yawanci Abeey ke cikasa da surutu da alama kodacan shiba me wayan magana bane amman he is a good listener don duka labaran da Abeey take bashi jiyake yana nata murmushi wasuma babu abinda yake ganewa har tagama. All set guys kutashi mutafi, Abeey tariko hannunshi tana fadin " aise yafara cire kayan asibitin tukunna bari naje nakira nurse dinnan yazo me tayaka wanka yazo ya koyama yajja ake cire riga asa kaga gida zamu koma don ka koya ko handsome" jinjina mata kai kawai yay tana ficewa adakin kayan da Mehtav ta ajje mishi asaman gadon yakalla kawai yajawosu don yarigada ya iya yajja akeyi tuntuni yana bari amai ne don yadada kwarewa,zare rigar asibitin yay faffadan kirjinsa fari sol yabayyana cikakke gawani irin abs ajere ashafaffan cikinsa idanuwanta kan murdaddan muscles dinsa yakai,he is very fair and huge Yan tabbukan ciwukan dayaji tuni suka soma dishashewa wani irin abu taji yatsaya mata amakoshinta ganin shiko ajikinsa kokawar sa shirt din yake bayan bema balle bottuns dinba yasanya takarasa gabanshi tana mika mai hannu yabata rigar amman wannan karon idonta wani guri yake kalla bamusu yabata tashiga zare buttons din ta mika mishi zirawa yay,yana kallon side view dinta,wani abu data lura dashi shine baida yawan kallon mutane amman dazarar tazo guri in yakafeta da ido kmr meson gano wani abu atattare da ita sam baya gajiya da kallonta kuma tashamai gargadin yadena amman kwata kwata bayajin mgnr ta. dan mikewa yay agabanta taga kanta wata yar tsigil dukda yajja itama ba gajera bace kuma ba doguwa bace amman dukkanta batai kafadarsa ba, "the buttons" yafada yana kallon ta daga kanta tai suka hada ido da mayun idanun nan nashi da takeji inyana kallon nata kamar ta fizgesu don haushi take fadin "kabari nurse dinka yazo, nibazan saka maka ba," tajuya zata fita adakin,taku biyu tai taji hannunsa cikin nata unexpectedly wani irin mugun taushi taji da dumi hannayen nasa ko ita datake mace albarka,wasu irin goosebumps ke yawo mata ajiki " yah Mehtav plsssss" yagaya mata ashagwabe irin yajja Abeey kemata intanason abu gurinta kuma aguntan yakoya sede taji nashi yafita daban yana neman tsaida bugun zuciyarta dede nan Abeey da nurse din suka shigo Abeey cikeda farinciki take fadin "handsome ashe harka fara sawa yah Mehtav ke kika nuna mishi" dasauri taji mehtav tace kusameni amota inkun gama tazuri kwandon da tagama zuba kayayyakinsu tai waje Abeey tabita da kallo kawai batareda tafahimci komaiba kafin hankalin ta yakoma kan Islam.

Mehtav kafafuwanta har hardewa suke sanda takarasa cikin mota tabude baya tazuba kayan tarufe tadawo gefen driver tana numfashi sama sama jin kmr bugun zuciyarta na kokarin tsayawa rintse ido tai tana gano grey eyes dinnan, "calm down Mehtav,calm down he is like a one year old kid haka doctor" tace "kwakwalwarsa babu abinda tasani, so stop confusing yourself" tafada kanta kafin kuma tai murmushi ita kadai wondering yajja zasu zauna agida daya tareda wannan rigimamman abokin Abeey din,bude kofa taji anyi karaf idanuwanta suka hadu cikin nasa shima kallon ta yake yana murmushi yana shafa motar don betaba fitowa ba balle yasan meye mota Abeey tashiga gayamai motace hawa akeyi aje gurare da dama kuma motoci akwai iri iri,gidan baya suka shiga shida Abeey tana gaya masa ai wannan motar babarsuce tadade motar bama ahawanta is one of the oldest car data taba sani,surutu dai iri iri, mehtav takalleta tana fadin "Abeey mekike nufi nazama driver kenan dazaki wani jashi ki kwafe a gidan baya," Abeey dariya tashigayi tana fadin "kai yah Mehtav bakiga shi bakon motarmu baneba bazaki barni inzauna dashi anan ba," kallonta Mehtav tai tana fadin " inkinfara biyana salary se inji, " nunawa Islam gaban motar tai tana fadin "in komacan handsome ko zaka zauna acan din, girgiza mata kai yay alamar a'ah" tace "tohm kinji yah Mehtav yafison inzauna akusa dashi don haka no drama kitayar da motar nan kawai mutafi," tace "Abeey kindaisan akwai yan sa ido agida da estate dinmu ko banason Susan munkawo wani kidawo nan idan yaso muna zuwa can semuce yakwanta abayan don karsuganshi," Abeey badon tasoba ta koma gaba tana gayawa Islam yayi hakuri next time shine ze zauna agidan gaban mehtav taiwa motar key komai datake tabawa acikin motar kalla yakeyi yana tambayar Abeey menene itakuma tana masa bayani kmr radio ahanya suka tsaya suka siya ice cream da tarkacen kayan ciye ciye suka nufi gida. suna fara hango masu gadin estate din dake motar ba tint bace,takalli Islam tana fadin " ka kwanta karsu ganka" dan yamutsa fuska yay yana kinyin yajja tace din,takalleshi kmr zatai kuka " zafa suganka don Allah ka kwanta," kmr da gunki take mgn seda Abeey tace masa "yay sleep" tukunna yature kayan data zuba agefe memakon yay kasa dasu salin ali suka zube kasan motar Mehtav kmr tafashe da kuka haka taji amman ganin yajja yay luf ya takure kansa bayan motar adole shi yayi barci yasan tai saurin mikewa tashige tawuce gate din,ko gaisuwar sannu da zuwa da suke mata bata tsaya ansawa ba harsuka je bakin gate din gidansu tahau yiwa dan liti horn aiko dasauri yashiga zugewa ta shigarda motar straight har garage don basu rufeba da suka fita inda ake ajjeta daman kenan ba kasan tent ba da ake ajje sauran motocin babannasu,kallon Abeey tai tana fadin "ungo dubu daya tamika mata kicewa danliti yasiyomin kati Airtel abakin titi kinsan bazanso yaga shigarmu da Islam ba karki matsa daga bakin gate harse kintabbatar yatafi tukunna seki min alama mufito," da tohm ta ansa gogan naka ganin Abeey zata fita tabarshi yashiga kiciniyar bude kofa zefito dasauri Mehtav tadatse lock din tana kallon yajja yake kokarin balla abin bude kofar yabi bayan Abeey sekace yaron da aka raba da uwarshi, " Islam kabari yanzun zata dawo" mehtav tagaya mishi amman yamata banza kmr badashi take magana ba ta mirror tahango abeey harta karasa bakin gate tabashi kudin ya amsa ba musu don bata cika aikensa ba inba doleba shiyasama baya mata kiwa,seda Abeey ta tabbatar dan liti yatafi sannan taimusu alamar sufito bude kofar tai dasauri tabudewa Islam ma yafito, "lets go" tafada tana yin gaba setaga yana kokarin nufar bakin gate inda Abeey ke tsaye dasauri tadawo tana kama hannunsa ciki zamuje ba waje ba tai masa alama shikuma hankalinsa yana kan Abeey datake musu leken asirin dawowar dan liti,haka suka shige ciki straight dakinsu tai dashi tana rufo kofar tajingina ajiki tana fadin "finally" tana dafe kirjinta kallonta taga yanayi daga yakalli fuskarta se yakoma yakalli kirjinta inda tadafe din, "kadena kallona" tafada tana hade fuska,shima setaga ya hade fuska ya maimaita mata abinda tace "nima kidena kallona' dariya taji tazo mata wato su Islam anwaye lallai haryanzun yafara tantance ki da ka don baya iyawa farko farkon farfadowar shi,seda Abeey takoya masa tace " shine ka tunda shi namijine itakuma itadasu yah mehtav da Dr sune ki tunda su matane," mazewa tai tana fadin "yaushe nakalle ka din," setaga yaturo mata da jajayen lips dinshi gaba cikin shagwaba yake fadin "now now" yana lumshe ido, harararshi tai tana fadin "ashe Abeey harda sharri dukta koyama," "meye sharri" yatambayeta yana binta ganin tashige closets dinsu da abeey tagama hargitswa gurin zabar kaya kansu fita,dukta watso da kayan waje tashiga tattarawa tana fadin "aibanice malamar kaba kajira wacca tazama dictionary dinka tazo zata gaya maka ko menene kadena bina," kya rantse bayajin metake cewa don duk inda tamotsa seya bita ganin tana tattara kayan shima yashiga tayata kwashewa kamar abin kirki, "nifa bansaka ba kakoma kazauna," daman tasan bazeji ba din don bajin mgnr ta yake ba yacigaba da tattara kayan hannayensa suka sauka akan bra dinta cikin kayan abeey tawatso ta bata sani ba dazun,yadaga yana kare mata kallo ba tareda yasan menene ba,hannu yasa yadan dafota tajuyo tana kallonshi menene? tatambaya bata ankare da abinda ke hannunshi ba, what's this? Yatambaya yana dagawa yana kokarin karawa ajikinsa aida sauri tafizge tana boyewa abayanta tashiga kifi kifi da ido tana fadin 'get out ni nasaka kane kafita kaban guri banson taya aikin inaruwanka da kayana" zeyi magana tadaka mishi tsawa tana fadin "I said out" sumsun yawuce yafice daga cikin closet din yakoma dakin saman gadonta ya haye yakwanta yana jin kuncin korarsa datai dakin ansa masa tambayar datai,ko takalmansa becire ba,dede nan Abeey tashigo,tanufi gurinshi tana fadin "handsome yakaga dakin namu kaida zantarbeka a side dina meyasa ka zauna agun yah Mehtav" banza yay mata yajuya mata keya don haushin kowama yakeji akan meyasa zata koreshi, Abeey bataji dadin ganinsa ahakaba ta zagaya ta inda yake take fadin "handsome meyafaru? kobakason zama tare damune,? jinjina mata kai yashigayi yana turo baki ashagwabe, meyasa handsome? tatambaya zuciyarta ba dadi lumshe mata ido kawai yay dede mehtav nafitowa daga closet da kayan data ware zata sasu a laundry,nuna mata Mehtav yashigayi,tace sbd yah Mehtav ne? jinjina mata kai yashigayi yana fadin "I don't like her" Abeey tamike tana fadin " yah Mehtav me kikaiwa Handsome,gashinan kinja yace baze zauna damuba fisabillahi me handsome ze tsare miki acikin gidannan uhm," Mehtav itama ta zaqalqalo mata cikin fada take fadin "sannu uwata tohm kar yazauna din kada Allah yasa yazauna din koni nace akawoshi nandin eh,idan bezauna anan ba kinada inda zaki kaishine dan meyasa yamin laifi namai mgn kuma ni ce za'a bawa lefin eh," tohm meyayi miki, kuma mekika masa? tatambaya ahasale, "I just shouted at him nacemai he should get out of my closet,yaban guri shine zece yaji haushi yadade beji haushinba," "ainaga closet din bataki bace kekadai dazaki koreshi handsome zomuje tashi inkaika kaga duk abinda kakeso" tafada tana juyowa ganin sukai yadaura pillow saman kunnuwansa yatoshe da alamar sundameshi ko yanason tinawa da wani abinne ya rintse ido gam gam dukkansu tsit sukai hankalinsu yasoma tashi don in tsakaninsu ne sunsaba dawannan hayaniyar ma juna, "handsome meyasa meka? meke faruwa? dasauri Abeey takarasa tana janye pillow tana riko kanshi,rintsewar yacigaba dayi yanajin hayaniyar tasu atsakiyar kwakwalwarsa, Mehtav ma karasowa tai tana fadin "I'm sorry Islam kankane yakema ciwo sannu," duk sunbi sunrikice Mehtav namai addua Abeey na kuka yadau tsahon mintina ahaka before yasoma bude idonsa dasuka danyi jaa suka sauya kala, ganin kanshi atsakiyar su suna aikin lallashi yasa yasakar ma Abeey murmushi kafin kuma suhada ido da Mehtav yaturmune fuska,alamar bemanta da tsawan datamai ba,ba tareda shakkar komaiba yakalleta yana fadin "get out," ganin lallai he is not okay yasa tamike tana fadin "let me get you something to eat kaji" tasauka akan gadon tashiga waiwayensa har tafice bata dena kallonsa ba shikuma hankalinsa yakoma kan Abeey yana rada mata abinda Mehtav tacemai kenan kuma shima yarama yaji dadi. Kitchen tashiga Allah yasa sunada miyar da inna taimusu dakkowa tai kawai ta dumama musu tadafa musu farar taliya cikin kankanin lokaci tagama tafito,tana shiga dakin ta tarar dasu shida Abeey saman sallaya sun wani daga hannu sama wai addua sukeyi kuma ahakan ashashence azkar din da akeyi bayan gama sallah take biya masa yana maimaitawa domin koda suka fara karatu,karatun sallah tafara koya masa, Mehtav ke kara koya mata yajja akeyi koda yaushe tana jaddada mata itakuma tana jaddada mishi,kuma yana sonyin sallah taga alamar har dadi yakeji in akacemai lokacin sallah yayi don yaje yay alwala yajika jikinsa sharkaf yafito yana rawar dari don kwata kwata talura bayason sanyi ko kadan. ganinsun ahaka ba karamin burgeta sukeba tanaji aranta dama ace Islam din babban yayansu ne ko wani dan uwansu na jini wanda ze zauna atare dasu na dindindin takalli Abeey tana fadin "abeey kidauki abokin ki kuje dining your lunch is ready zanyi wanka kinji," "tohm yah mehtav" ta ansa tana fadin "handsome let's go" mikewa yay Abeey tanade musu sallayar suka nufi falo mehtav tashige ciki tacire kayanta tana daura towel tanufi toilet din seda tafara wanke shi tsaf sannan tai wanka tafito agurguje tashirya cikin dogon rubber English gown free size tafito tadaura hula asaman gashinta dayaji kananun kitso masu kyau atsare,fitowa tai ta tatarar dasu har sungama cin abincin daman tasan Abeey bata cika cin wani abincin kirki ba barta dai da ciye ciyenta amman abinci be dameta ba shiyasa gatanan kullum batta kiba jiya iyau sa anninta duk sunfita girma da cika ido, amman kuma shi ai tunda namiji she expects zeci abinci dayawa shiyasa tadafa taliyar guda amman setaga kawai tsakura yay,sedai sunkwashe naman cikin miyar kaf suncinye ko tsoka daya basu bari ba,tai kwafa kawai daman tasan Abeey mayyar namace ashe tasamu dan uwa kenan. "zan ramane" taraya aranta tazauna wanda suka rage takara akai don kar ai asararsa tazauna tashiga ci tana korawa da lemonta mai sanyi tana jiyosu suna buga video game tana kuma iya hangosu daga nan inda take Islam be iyaba Abeey took the advantage taketa cinsa kuma taki takoya mai yajja akeyi donkar yaringa cinyeta. bayan tagama ta tattara komai zuwa kitchen tai wanke wanke tagyara kitchen din tsaf takullo tafito tazauna atare dasu amman wayarta take dan duddubawa tashiga group chat dinsu tanajin yajja wasu da dama ke fadin su har sungama project dinsu sunyi submitting ma,fita tai tashiga mgnr datawa supervisor dinta takarshe kuma yana hawa online bawai baya hawan bane kawai bega damar bude tata mgnr ba kuma duk kiran da zatamai line busy take ji kilama blocking dinta yay taraya aranta tana tinanin yajja zata sameshi domin in tawuce next week bata kammalaba ze iya zamar mata matsala. kiran sallar magrib ne yatashesu daga game din tare suka koma dakin dukansu sukayo alwala suka fito sukai sallah atare seka rantse sun shekara da sanin sa yajja suke jansa ajiki musamman Abeey don ita jinsa take tamkar babban wa kawai ta samu. kur'ani Mehtav tasa tadakko tabiya mata haddarta da zatakai in ankoma ran Monday,dauka tai tiryan tiryan tashiga biya suratul Anfal daki daki,atsakiyar karatun tacake chak sakamakon batan datai mehtav dake kallon alkur'ani tace "tadawo tasake maimaita ayar" don batasan tatina mata dawuri,raurau tai da ido takara karantawa with thesame mistake Mehtav tace "badede bane tasake," kamar daga sama sukaji wata zazzakar Kira'a tana fitowa daga bakin Islam yana tinawa Abeey karatun shikansa besan daga ina karatun yafitoba kawai yaji yana zuwa kwakwalwarsa ne. daga Abeey har Mehtav kallonshi suka tsaya yi har yakai ayar, Abeey cikeda murna take fadin "handsome daman ka iya karatu waya koyama wannan qira'ar kmr wani shuraim," dan murmushi kawai yay yace "shima ji kawai yay ya iya," Mehtav tace masa "yacigaba da karatun taji" kallon gefen ido yay mata yana daukekai don be gama fushi da itaba,takalli Abeey da ido tai mata alamar ta sakashi, Abeey tamatsa kusa dashi tana fadin "tohm dan yimin wanda ka iya inji kaji islam kaga sekake koyamin," kallon Mehtav yay kafin yaturo baki yana makale kafada,alamar bazeba ganin tazaku dajin karatun nasa. Mehtav takarasa kusa dashi tana fadin "kai abu baya wucewa agurin ka Islam nace I'm sorry bazan sake maka tsawa ba kabiyamin karatun inji mana I have a reward for you" Abeey cikeda farinciki take fadin "eh zata baka wannan chocolate din medadi irin wacca nazoma da ita asibiti rannan" yace "really" tajinjina kai tana fadin koh ya Mehtav? Mehtav tai murmushi tana fadin "eh" yace "tohm she should stop shouting at me," Mehtav tace "bazan sakeba I promise" gyara zama yay kawai yalumshe ido yashiga karanto musu cigaban ayar da yatsaya kamar wani almara haka yaji suna dawowa kwakwalwarsa daki daki daki, Mehtav tatsaya tana kallon grey eyes dinshi da dan karamin lips dinshi dake karatun shima itan yake kallo tana murmushi me haske akan fuskarta har yakai karshen surar,kabbara suka farayi. Abeey tashiga jan gemunshi tana fadin "daman dai ashe beard dinnan na ustaxanci ne maybe shifa malamine babba awancan rayuwar tasa," tambayar ta yake "wace rayuwa" don haryau basu gaya mishi meyake cikiba kokuma waneneshi, Mehtav ce tazare mata ido don Dr kafaya ta gargadesu da kokarin forcing dinshi ya tina abu inya tina dakanshi is fine inbe tinabama suyi kaffa kaffa karsuce zasu tinamai hakan ze iya jawomai mummunan ciwon daze iya jefashi cikin shock dinda zeyi sanadin rayuwar sa. wayancewa Abeey tai tana nufar kitchen taje tadebo musu kayan ciye ciyensu nadazun, Mehtav kamar yajja tai alkawari tabashi chocolate din kuwa da alamar daman ma'abocin shan zakinne seda yasha biyar dukda irin girmansu ice cream dinne bewani shaba Abeey yabarmawa tahada da nata tashanye. Ana kiran sallar isha'ee suka tashi bawanda kejin yunwa acikinsu hakanne yasa bayan sun idar dede lokacin da babansu ke kiransu Mehtav taiwa Abeey dabarar takai Islam guest room ta jera masa kayansa acan zezauna. bayan tarakashi kuwa tabashi guri tadawo suka shige daki sukai video call da babansu ba karamin farinciki yajiba ganin girls din nashi yau kmr walwalarsu ta karu ya tambayesu meye sirrin Abeey tacemai "ai dadin hutunan takeji" yace "kidai fadi gaskiya uwatace dai bakiso don batta gidan kiketa murna" kumshe baki tai tashiga dariya ganin paa din yagano su,hira sukai cikeda kauna da kewar juna suna bashi labarai kala kala amman koda wasa daya daga cikinsu ko subutar bakin bashi labarin Islam bataiba se after 9 suka gama wayar. Jin Islam din shiru yasanya Mehtav da Abeey suka nufi dakinsa don duboshi daure da towel suka ganshi ya barbaza kaya yawatso su duka wai yana neman kayan daze saka,dasauri mehtav tarintse ido zata juya Abeey tarikota tana fadin "aikifa yasamemu yah Mehtav kinsanfa babu abinda ya iya se an koyamai," nan suka shiga kwashe mishi kayan Mehtav tamika mishi pajamas dinsa don yasaka ganin shi ko kunyar ma yawo ahaka agabansu bayayi,karba yay yana kokarin kwabe towel din agabansu Abeey tatsugunna mexatai inba dariyaba ganin yajja Mehtav tarude take cemasa "karya kuskura karma yasoma bari sufita" turo bakinsa yay gaba yanasa hannayensa cikin jikakken gashin kanshi dake sakawa yay looking very hot,koh kammala tattare kayan basuyiba Mehtav tajawo Abeey suka fito tana fadin "mutum ace baisan yakamata ba shifa wannan Islam din naga alama tsirara ma zeyi agabanmu ba abinda ya dameshi banson wannan tabarar fa besan mu mata baneba," Abeey dariya take mata tanafadin "yah Mehtav calm down now wai bakisan cewa kwakwalwarsa kmr ta jariri bane do you think waishi yana banbance mace dana namiji ne komai yaxo mai yi yake kinamai uxuri mana," kallon Abeey takeyi kawai sanin battajin irin abinda ita takeji intana ganinsa ahaka yasa tace "bazaki ganeba kawai" tawuce kitchen tadakko ruwa Mai sanyi tana korawa makogaranta bata sake bi takanshi ba har washegari dasafe a ka ida yau xata fita taje makaranta amman bazata iya fita tabarshi tareda Abeey kadai agidaba Allah ne kadai zesan irin fitinar da zasuyi acikin gidan kanta dawo agabannata ma dontana wiki wiki da idone,sosai Abeey take son fita dashi bayan gidansu inda sukeda garden me kyan gaske dake dauke da furanni iri iri,da wani dan karamin pond,amman Mehtav tahanata sbd tasan dan liti nashiga gurin koda yaushe shine mekula dashi don haka akwai high chance nacewa inya fita zasu iya haduwa abinda bata bukata kenan. Kuma ta lura Islam din is very choosy agun abinci don breakfast din datai yau kiri kiri yana dandanawa yaki ci yace mata "badadi straight to her face" kuma ita ta dandana taji the taste is great amman haka yaki ci duk yajja Abeey taso tagwadamai da akwai dadi yaci kiyay se indomie tadafa masa dataji veggies,tana ajje wa agabansa yakalli Abeey yace mata "meat" daga ita har Mehtav din dariya suka shiga yimai don yajja yaci serious abashi naman kmr wanda yabasu ajiya, Abeey tace "lallai Islam ashe kai dan gayune bakacin abinci ba nama,yah Mehtav aiki kam ya samemu besan cewa agidannan bako yaushe ake cinnama ba se uwar masu gidan taga dama," Mehtav tace "yadai sameki don mutumin kine ni innadafa mara namar yaki ci daukewa zanyi incinye abuna sedai yakwana da yunwar," Abeey tace "ayyah yah Mehtav your not nice," shidai yana zaune yana jiran namansa don ture plate din noodles dinma yay Mehtav takalleshi tana fadin "Islam kaga naman koh fito dashima banba a freezer bare kuma akaiga amfani dashi yanzun kaci da instant noodles, zatai sanyine kaci wannan yanzun later zan dafa maka me naman" turo jajayen lips dinshi yay gaba yana hade girarsa, looking very serious yashiga girgiza kai alamar baze ciba, Abeey tazuba tagumi tana jawo plate din gabanta take fadin "I promise you , you'll love it yah Mehtav fa ta iya girki sosai tanada certificate na koyan girki haa inbaka" kinbude bakin yay yatsuke shima,sosai rigimar Islam din take bawa Mehtav mamaki katon saurayi amman inta tina lalurar dake tare dashi se tausayinsa yakamata, Abeey ganin yakici yasa tasa cokali tashiga ci tana santi harda saka hannu tana zagayawa gefen kunnan wai dadin yana kada mata kunne ganin tayi rabin noodles din tana santin dadi kuma yana kallonta tagefen ido yasanya yay saurin janyo plate din gabanshi yasaka spoon yana mikawa Mehtav alamar tabashi yau yayi fada da mutuniyar mehtav tai murmushi tana debowa yabude mata dan karamin bakinsa harda rufe ido memakon tabashi se ta shagala da kallon kyawun fuskarshi,tana kallon zagayayyan bakin nasa dake abude tana hango harshensa da fararen hakoranshi, Abeey closely take watching yajja mehtav ke yawo da idanuwanta afuskarshi karaf yabude ido jin indomie batazo bakinsa ba har yanzun yasa yadan hade hadaddiyar girarshi guri guda datasa Mehtav takusa kwarewa dukda ba abinda takeci dakyar talalubo natsuwarta tashiga bashi indomie din abaki Abeey na kallonsu tana murmushi tana gyada kai kawai.

It's fatoumspassion EHSAAS Don't forget to share Like Comment And Vote. [14/04, 15:32] Fatima Rufa'i Nasidi: ***

EHSAAS Another exclusive piece from the passionate writer of AYSAM And INTENSE LOVE. It's fatoumspassion.