Chapter 4
Dream
Bayan tagama bashi abincin dakanshi yadau ruwa yashiga sha ta lura lemo becika damunshi ba domin jiyama yajja ta ajje haka tazo tatarar dashi tana kitchen tana wanke Abeey tana assignment dinta taji motsin mutum abayanta jin kmr ana kallonta yasa tajuyo suka hada ido wannan murmushin nasa ya sakar mata,tace Islam what are you doing here? Dan lumshe ido yay kafin yajuya yadan kalli kofa yana hango Abeey a living room tana ta rubutu,yace "I'm bored and she's writing" dan waro ido tai tana fadin "inyeeeeeee waya koya maka fadar your bored with this your thick British accent uhm," Takarasa cikeda tsokana don turancinshi kwata kwata ba irinnasu bane hakama hausarsa,accent dinshi is very thick gurin turanci kanaji kasan ya goge da zama cikin asalin turawan England,kokuma dayan biyu ya ilimantu sosai tafannin turanci and she admire that alot, dan murmushi yay yakarasa kusa da ita daf daf kamar zeshige jikinta yake fadin "aunty doctor" jin yace haka tasan maybe kafaya yaji tafada one way or the other don ita Abeey ke cewa aunty doctor kuma shi duk abinda Abeey tafada shiyake maimaitawa. "tohm yanzun kazone in tayaka hira kome Islam? tatambaya tana cigaba da wanke wankenta,be bata ansaba sejin hannunsa tai cikin kunfar data hada yana laluben abinda take wanke kwanukan dashi ma'ana ze tayata hannunta yakamo aciki yadago yakalleta yakalli hannayen nata yan kananu marasa tsayi sosai,dage mata gira daya yay wannan kuma batasan a ina yakoyo ba kuma battason yacigaba dayi don inyay haka ba karamin kyau yakeyi mata a ido ba, "uhm nakama hannunki" taji sassanyar muryarsa tana fada, murmushi tai tana nunamai daya barin sink din tace mai "zanringa wankewa se inna miko ma kana daurayewa kana gogewa kagane? jinjina kai yay alamar yafahimta seda ta gwadamai sannan suka fara tunda tasan yanzun tace zata koreshi waje yafita fushi zefara da ita,sosai yake enjoying abinda sukeyi din tare alamu sunnuna atattare dashi dukda bawani abin kirki suke cewa ba tawanke ne kawai ta mikomai ya dauraye fess yagoge ya ajje gefe,ahaka suka gama tsaf tashiga wanke sink din seda tagama tsaftacewa sannan tace yazo tawanke masa hannayensa dakyau,handwash tazuba mishi tashiga wanke mai hannayensa yana kallon fuskarta kmr meson gano wani abu aciki amman yakasa harta gama tukunna itama tazuba zata fara wanke nata jitai yakama hannayenta yashiga wanke mata amman gently bakamar yajja tamai ba abinna mata kmr da gangan yake hakan don yasan yana affecting dinta sosai taji kafafuwanta na kokarin kasa daukarta kuma hannun yafita amman still be sake mata hannun ba bekuma kashe famfon ba seda taji wani karfin hali yazo mata dasauri tajanye hannunsa cikin nata tana kashewa tace "thank you muje wajje ko tunda mungama" murmushi yamata yana jinjina mata kai agurguje tajere kayan suka dawo falon already Abeey tagama aikinta ta harde kafa daya kan daya tasaka tashar Nickelodeon tana kallon Ariel dinta,daman indai idon Abeey biyu da rana TV tatace da inna suke fafatawa kuma tunda battanan babu yajja Mehtav zatai da ita sedai tajira bayan tayi barci da daddare takunna koh kuma tai kallo a system ko waya wanda bata cika son hakanba,daki takoma tabarsu sunata kallon cartoon dinsun shima Islam din da alama yanajin dadin cartoon din don Abeey ke bashi labarin tundaga farkon abubuwan duk da akai be kallaba yana gyada mata kai,maganinsa tadakko takawo mishi haka yana yamutsa fuska yasha badon yana soba sedon yajja tatsaya agaban TV tahanasu proper view harseda yasha yanasha kuwa se barci anan ya kwanta saman kujerar Abeey ganin yayi barci yasa tarage mgnr tacigaba da kallonta abinta kusan rnr wuni yay yana barci don maganin daman yana saka barci sbd susamu nutsuwa sosai sallah kawai suke tashinsa yi ko abincin rana beciba,basu cika cin abincin dareba daman indai bawai inna Kenan ba,su saidai suyi ciye ciye su kwanta,ajjemasa tai saida yatashi kusan daf da magrib tukunna tamai reheating ganin Naman kaza bajaja aciki abincin yasa yaketa fara'a yanajin dadi kuma yaci couscous din sosai ya kumasha leman coconut data hada musun,intaji kiran sallah so tari tana mai sha'awar zuwa mosque amman tinawa da halin dasuke ciki yasanya kawai batama taba mentioning musu ba,sosai Abeey kedada shakuwa dashi itakanta Mehtav batasan shakuwa dashi take sakeyi ba har setayi tinanin rnr da inna zata dawo gidannan koya zasuyi dashi ta tambayi kanta allahu ta'ala a'alam.
Yau suna gama wayarsu da paa dinsu Abeey ta bingile da barci don ko wankan dare batasamu yiba kuma duk yajja Mehtav din taso tashinta kitai haka ta hakura bayan tagama karance karancenta tafito,tea tahada ma kanta takashe wutar falon tajona Netflix a TV tadau remote tai playing Bridgerton, blanket dinta tasaka tarufe cinyoyinta dasuke cikin dogon wandan pajamas dinta,tana sipping tea dinta tana kallo,ita kadai ko tsoro bataji don tasaba indai tanason kallo cikin lumana se Abeey tayi barci yawanci take iya tsayawa tai sbd Abeey bata cika kallon film inba cartoon ba,kuma itama bata son kallon American movies da Abeey dokar paa dinsuce indai movie is rated tohm kar abar yarsa takalla sbd tarbiyya ahakama Abeey idonta a tsaitsaye yake balle abarta babu kula. Kamar motsi taji abayanta dasauri tajuya tinaninta Abeey ce inuwarsa tagani yajingina da kofar dakinshi yana facing dinta,kallo daya tai masa tagane shi batai yunkurin mikewa ba harseda yakaraso inda take ya zagayo yana zama kusada ita,koda bata kalleshi ba tasan turo baki yay taga yasa hannu yazare mug din tea dinta yana kaiwa bakinsa "shshsshsshs yah Mehtav zafiiii" yafada yana kada harshensa yana kokarin fiffitawa da hannayensa ita naturally batama shan tea inba tafasassheba ba lallai ne shayi dazata sha wani ya iyasha dariya yabata ganin kwadayinshi yaja masa yazo dawani karfin iko yakarbe mata tea don tace bazata bayarba kuma yasoma mata rigima, "tohm sorry" tafada tana tayashi fiffitawar da hannayenta tabiye mashi,tana kallon yajja bakin nasa yakara jaa,shikuma ta lura hankalin sa yakoma kan movie din,adede wani explicit kissing scene da ita kanta kunyar kalla zataji ita kadai bare dawani atareda itaba wanin ma namiji kmr Islam jitake kmr ta nitse agurin tashiga laluben remote dan ta canza Islam dayake ganin abinda ake yi a TV very strange yasa yazuba ido yana kallan yajja suke,ganin kamar remote din yayi tsuntsuwa yasa tamike tsaye tana sake duddubawa chan taganshi dasauri tasaita zatai switching TV din taga yasa hannu yakarbe remote din karfinsu ba dayaba hakanne yasa daya fizge batai musu dashi ba, "whats that? yafada yana nuna mata TV "Let's watch" yakarasa yana kashingida a inda tatashi yana murmushin gefen baki da batasan namagani da menene ba inyana wannan murmushin haka kawai setaji duk ta tsargu sbd mugun kyan dayake mata, Islam kaga dare yayi mema yafito dakai nima barci zanyi ka koma dakinka ka kwanta abinka girgiza mata kai yashiga nuna mata gefensa tazo tazauna yajja suke shida Abeey insuna kallo, "Islam" tafada tana tsayawa gabanshi tarike kugu "is time to sleep," maqe mata kafada yay yana kokarin tureta daga gabanshi don tayi blocking view dinshi, "move" yafada yana daura hannayensa saman nata da niyyar janyeta bata ankaraba sbd ta sakankance taji tana kokarin loosing balance zata afka kanshi,in seconds cikin zafin nama taga yamike agurin tafada saman kujera dariyarsa ce tadawo da ita hayyacinta don nuna ta yakeyi yana dariyar keta ganin yajja tabi tarude baki daya,aranta tace "inbe iya dariyar mugunta ba aiba ace masa aminin Abeey ba," yakalleta ganin tayi kicin kicin da fuska tahade rai yaturo mata baki gaba yana fadin "sowieeeeeee" irin cikeda tsokanar nan before yazauna agefenta,kamar yartsana yasa hannu yajawota jikinsa yana fadin "natashine don karki fado kaina katuwa dake ki karyani, Abeey tace idan aka fada kan mutum karyewa yakeyi,kuma inya karye zeji zafi kuma inyaji zafi za'a kaishi asibiti nikuma banason komawa gurin aunty doctor," "sakeni" tafada bayan ta gamajin dogon bayanan nasa dayake gaya mata daki daki anitse kmr wani dan jarida, kallonta yay yana jawota gabanshi sosai bata iya ganin fuskarsa sosai sbd scene din dare da ake nunawa,yazage cikinta da hannayenta yana kwantar da kanshi saman kafadarta jitai kmr andauke mata jini agaba dayan jikinta sbd rawar daya somayi ita tunda take aduniya tunda babarta ta haifeta bata taba hada jiki da namiji irin hakaba bayan mahaifinta,akunnenta taji yana rada mata "stop talking lets watch in silent" With serious tone kaikace yanada wani cikakken hankali nawucin gadi tamanta cewar shifa besan meye daidai daba daidai ba amman me ai ita tasani tasan Islam ba muharraminta bane kuma tabatan dayake dukda akwai lalura amman be dace ba gaba daya,kokarin mikewa takeyi ajikinsa amman yaki bata dama,kasakeni nace stop touching me I don't like it," "Why? taji yarada mata akunne dayasa tsigar jikinta gama tashi "innalillahi" kawai tafurta tana rintse ido before tai gathering strength din fizge kanta tamike tana fadin "sbd bedace ba haramunne bakyau and today should be the last day dazaka sake tabani kaji koh," what's that? Taji yatambayeta What's what? Tafada a hassale don yagama kular da ita Gani tai yace "stop shouting,haramunne, bakyau what are they? Takaicine yaso tsaya mata akirji tasan cewar bakomai yake ganewa ba se ana ganar dashi amman is very hard for her ace duk abinda tafada se tamai fashin baki akai,tsaki kawai tai tana fadin "seda safe your so annoying" takarasa tana kashe socket din TV gaba daya tadau blanket dinta tana kallonshi "goodnight" tafada ranta abace,tajuyo tanufi dakin seda takai daidai bakin kofa taji muryarsa can kasa yana fadin "yah Mehtav are you sad? Nine nabata miki rai," Juyowa tai taga yajja yay kalar tausayi yana mata puppy eyes kamar wani Abeey,wani irin soft spot takeji tana bashi azuciyarta wanda tasan be dace ba amman takasa hana zuciyarta falling for him, "I'm not sad get some sleep Islam we will talk tomorrow kaji" takarasa tana shigewa daki tatura kofar tana dafe kirjinta dake dukan tara tara kodai she like Islam ne inba hakaba me zesa taji duk abinda yake mata bayan tasan baida lfy tana bashi wani ma'ana da gurbi acikin zuciyarta tatambayi kanta tana karasawa saman gadonta tajima ahaka batai barci ba tanata juyi lokaci lokaci tana juyawa taga Abeey na barcinta hankali kwance. Islam ganin ran Mehtav yabaci yasa yakwanta saman kujerar parlour yashiga tinanin tohm waishi mema yay dazatai fushi dashi sosai yakejin ba dadi don bayason yaringa ganin mutum da sad face tun lokacin da Abeey tamai identifying kalolin facial expressions yaji cewar bayason sad face haka kawai yanason yaringa ganin kowa yana murmushi ahaka barci yadauke shi.
Acikin barcinsa yaji wata murya kamar tasa tana fadin "Islam just go inside," bayaganin komai sai wani irin haske a idanuwashi sejin murya yay tamace wacce yakasa tantance Mehtav ce ko Abeey tana fadin "I'll go with you,don Allah karka tafi kabarni I'm gonna die without you," " I said go inside" yafada da dan daga murya wannan karon dishi dishi yaga bayan mace tajuya yana jiyo shashshekar kukanta, ashe shima kukan yake azahiri besani ba Abeey da fitowarta kenan daga daki tatashi daga barci taci karo dashi yana rintse ido yana hawaye "Islam, Islam" kawai taji yana fada,dasauri Abeey tai kanshi tana kiran sunanshi "Islam wake up meke damunka kukan mekakeyi? tashiga tattabamai fuska daidai Mehtav tafito daga ɗakin jin muryar Abeey cikin tashin hankali,bude idonshi yay yana kallon Abeey for a moment yakasa gane wacece kwakwalwarsa tatafi wani gu daban, "Islam are you okay? tatambaya tana curving face dinshi, "Abeey" yafada yana rungumeta itama rungumeshin tai cikeda tsoro take fadin "is just a dream kabar kuka kaji," Mehtav tausayinsa ya kamata yadago yana kallon su duka biyun yace "she's crying someone is crying, and I shouted at her,Islam is crying" yafada yana sake zubda kwalla haka kawai yakeji akwai wani gibi nacikin rayuwarsa daya manta dashi yake kuma son yatina amman me yakasa tinawa duk yajja kwakwalwarsa taso hakan,wani hole yakeji akirjinsa yakasa cikewa kmr yarasa wani bangare najikinsa. su Mehtav carko carko sukai agabanshi hardai yasamu hankalinshi yakwanta yadena maimaita kalmar someone is crying, Mehtav ganin lokaci naja yasa tace " yatashi yaje yay sallah " har daki suka rakashi yay alwala yafito already tashimfida masa sallaya yatayar da sallar asubah dabeba wanda seda Abeey tasake jaddada mai raka'a biyu akeyi don kar yamanta,dasuka idar shida Abeey zaman bitar karatun ta suka shigayi tanayi yana tayata kuma haryanzun yakasa tina ya akai ya iya karatun ko kuma a ina ya iya din Mehtav tana fita takasa zaune takasa tsaye domin sosai tashiga damuwa kodai yafara tina rayuwar shi tabayane kokuma abinda tamai jiyane yatsaya mishi arai tasan gradually ze koyi komai yagane komai amman gashi impatient dinta yasa tana mai tsawa tana gaggaya mai abinda yafi karfin kwakwalwarsa ko breakfast kasa shiryawa tai tatsaya harseda karfe takwas tai tadanna ma Dr kafayat kira. bayan tadaga suka gaisa tana tambayarta "ko lpy? tace mata "alhmdlh everything is fine daman tambaya zata mata regarding Islam" tace "Islam kuma bakun kaishi gidan ajjiyaba" tace " eh sunkaishi" cikin dan in ina narashin gaskiya da yin karya take fadin "matarce takirani dazun ina tashi, tace min wai yana having weird dreams haka yatashi yana fadar maganganu kmr someone is crying, Islam is crying sannan yatashi hankalinsa atashe yana kuka sosai," dan jim Dr kafaya tai before tace "kuma babu wanda yabata masa rai kafin yakwanta," Mehtav kamar tana gabanta taji tarude dasauri tace "nima dai bansani ba Dr bamuyi mgnr da itaba," tace "kinsan special case ne ko a amnesia din na Islam is kind of different,maybe ko anmai wani abunne yatsaya mai arai yashiga tinaninnikan dayay nasarar binciko wani memory daya shafe acikin kwakwalwarsa kuma wannan alamar magungunan damuke bashi suna aiki kenan,amman still ki gaya mata abishi ahankali,idan ba.hakaba inyana cigaba da tinani continuesly tohm ze iya shiga damuwar dazata haddasa masa wani shock ko mummunan ciwon dabama fata,takula dakyau shi Islam yanxun kmr jaririne bama kmr Abeey ba sbd Abeey yanzun tasan fari da baki tasan daidai da ba daidai ba don haka don Allah they should treat him nicely karsuga kobashi da gata ko wani abin yaronnan Allah ne kadai yasan daga ina yafito kuma menene matsayinsa aduniya domin kwata kwata beyi kalar wanda yafito daga cikin matsi ko kuncin rayuwa ba,akula dashi dakyau dakyau ki jaddada mata duk abinda yatambaya abashi answer dede da kwakwalwarsa wacca take ta yara ayanzun inyayi badede ba banda tsawa cikin kulawa da lallabi za'a nusarse shi," jinjina kai kawai Mehtav tai kmr tana gabanta tanajin tausayin Islam din nasake shiga cikin zuciyarta, godiya sosai tashiga yima kafaya kafin takashe wayar Abeey tagani atsaya da alama tagama sauraron me suke cewa, ganin Abeey din batace komaiba yasa takalleta tana fadin "he will be fine don't worry," jinjina kai kawai taga Abeey tayi is so unlike her, Abeey "mekike tinani dangane da case din Islam kodai zamu daukeshi a hoto mudaurashi a social media koza asamu wanda yasanshi,mudan tutturawa bloggers," dasauri taga Abeey tadiro agabanta tana fadin "akanme? ko kingaji dashine har haka,bayan nasan ke kijama yashiga halinda yashiga I'll not forgive you inkika min talla da dan uwana a duniya, mahaukaci zasu cemai nikuma my handsome brother is not mad,his story is not cheap daza asaidama bloggers sunemi follower's dashi,inkin tsaneshi kidena kulashi nizan kulada brother na," sakin baki Mehtav tai tana fadin " kambalai the last time I checked shine, I'm your only sister yaushe kikai dan uwan bansani ba Abeey" juyowa tai tana galla mata harara tace "Islam is like my blood brother kicigaba damai wulakanci don kinga yana sonki ma shine kike wani shareshi kina mai wulakanci," Sona kuma Mehtav tafada tana wara ido waje Abeey tamatso daf da Mehtav tana fadin " eh sonki yake kuma kema kina sonshi, I'm not blind I saw the way you guys are looking at eachother, kuma muna gama bita yaban labarin abinda kikamai jiya,kuma yace min he like you amman ke inya kulaki seki ringa bashi sad face kina wani shamai kamshi," sosai mgnr tabawa Mehtav dariya kawai tamaze tace "shi Islam dinne yagaya maki haka ko kekike fadar hakan on his behalf" tace "shine yagayamin yana ganinki amafarkinsa and he wants to recreate the dreams memory,kuma he like you," Mehtav tace "Abeeda" tana riko mata hannu tasan indai tace mata abeeda that means magana zatai mai mahimmanci,tanutsu kuwa tana kumburo fuska tana kallonta, "nafarko kinsan duk lalurar dake tareda Islam base natina miki hakan ba,besan kansaba besan waye shiba bamusan waye shiba bamusan daga inda yakeba dalilin dayasa muka kawoshi cikin gidannan don musauke hakkin dake kanmu abisa abinda mukai masa,he don't know what love is he don't even know me yakeji right now besan kowaba semu, how can he not like us uhm?" Takarasa da sigar tambaya, Abeey amaimakon ta amsa mata se tace " amman aike kinada hankali kuma kinsan mekike, rantse you don't have feelings for him," rike kanta tai ganin Abeey bama taji abinda tagama mata bayani ba, "my feelings doesn't matter" tamaimaita mata tana mikewa tsaye,bin bayanta Abeey tashiga yi "why is that for the first time naga sonwani a idonki your just trying to deny it kinsan you can't lie to me" "Abeey let me be ke wai bakisan ke yarinya bace ina shekarunki bansan duk wadannan abubuwan dakika sani ba zan makeki kika cigaba da bina" takarasa lokacin da suka kai tsakiyar falon daga bakin kofa sukaji muryarta asama kamar yajja tasaba take fadin "dakuwa nima namake ki," gaba dayansu hankalinsu yay kan inna dake shigowa hannunta niki niki da wata bakko,gaba daya seda sukaji gabansu yafadi, musamman Mehtav datasan ba abinda yadamu Islam ze iya fitowarsa duk sanda yaga dama kamar yajja yasaba, amman me yadawo da inna yau Wednesday bayan aka ida se ranar Monday zata dawo don tasan Abeey nahutun mid term amakaranta. ganin sunyu carko carko atsaye yasanya inna fadin 'meye kuka tsareni da ido sekace kunga wata aljana agunnan baza kuzo ku temakamin kushigar da doyarnan ciki ba tsarabarta nayo gatanan kaya guda naganta nasan Abeeda naso," dariyar yake suka shiga yi kowacce tana addua Allah karyafito da Islam harse inna tashige ciki,bashiri Mehtav da Abeey suka tayata jan bakkon dukda nauyin datai musu haka suka wuce da ita cikin store dake kitchen suka ajje inna tazuge tashiga fito da manya manyan doyar tana fadin "kina kallonsu kinsan masu kyaune zasuyi laushi tana washe baki," "amman inna base ranar Monday kikece zaki dawo ba? Abeey taimata tambaya cikin rashin walwala,inna tace "aidaman nasan ba murnar dawowata zakuyi ba zan hanaku rawar gaban hantsi ko tohm yau nai niyyar dawowa kuma yau naga dama idan akwai wacca tacikawa habibu kudi yagina wannan gidan acikinku seta koreni a'ah nagadai danane nina haifeshi amman yara dakuka tashi kuka ganshi asama nema kuke kuringa nunamin kunfini iko dashi," jintafara masifa yasanya Mehtav fadin "Allah yabaki hakuri inna" takyarawa Abeey da ido alamun itama tabata hakuri,tana turo baki tace "tohm Allah yahuci zuciyarki innata takaina aikinsan muna murnar dawowarki fa kawai dai is unexpected," daidai nan inna tagama jere doyar cikin tsari takalla tana fadin "tohm kunga yajja ake don kar aje gidan miji aringa ajje abubuwa barkatai kmr gidan mahaukata" takarasa tana kallon Mehtav data nuna kamar batasan da ita takeba,nibari naje nadan watsa ruwa nafito, dukkansu suka fito suna biye da ita harsuka rakata bakin dakinta dukda taso gane manne matan dasuke basu da gaskiya amman seta share abin ganin bataga alamar sunyi wata barna akitchen ko falonba,tashige dakinta dake daf da wanda Islam keciki daga Abeey har Mehtav ajiyar zuciya sukai, Mehtav tacema Abeey takasa kunne taimusu gadin inna tana shiga wanka se ita kuma tafito da Islam tamaida shi dakinsu don dakin da Islam ke zama nan tamkar farfajiyar baje kolin shan iskar innar tasune,seta taji kulle kofar bandakin inna sannan taiwa Mehtav signal tashiga dakin Islam,fitowarsa daga wanka kenan bathrobe din paa dinsu daya suka dakkomai yake anfani da ita dasauri takarasa gabanshi zeyi magana tai saurin mai alamar yay shiru tahanyar daura yatsanta daya saman lebenta shshsshsshs! turo mata jajayen lips dinshi yay irin damme zata hanashi magana takamo hannunshi ganin zemata gaddama yasanya tac " pls pls " biyo bayanta yay suka fito tai wa Abeey alamar tatsaya tamusu gadin inna dasauri takarasa dashi dakinsu yatsaya kawai yana kallonta harta fita tashiga kwaso mishi kayansa dake can tana dawo dashi dakinsu saman gadon Abeey tajibge mishi kayan,daidai nan Abeey tashigo tana dafe kirji take fadin "I almost fainted yau,da ace inna taga Islam yau da tamu takare acikin gidannan" tafada tana karasawa gefensa inda yazauna asaman gadonta yana jiran sumai bayanin kawoshi nan da akai yajja zegane, Mehtav takalleshi tana tinanin kalaman dazatai amfani dasu gurin sanards Islam din anan ze zauna kuma dagayau bashi basake lekawa waje,amman me takasa yajja yakafeta da ido kamar Abeey tasan metake tinani cikin hikima take fadin "handsome kasanme," daga " yau you'll stay here with us sbd wata zombie tadawo gidannan kuma cinye mutane takeyi," tafada harda zaro ido tana mai demonstration, looking confuse yashiga tambayarta " what is zombie? tinowa da cartoon din dasuke kalla tace mai ai irin zombie dinne waje ze cinyesa gani tai yakafeta da ido alamar be yarda da maganarta ba,tadanyi jim yace 'mata tohm amman ita aidaga wajen yaga tadawo kuma basu cinyeta ba," Mehtav wata dariya ce tazo mata tana kallon Abeey dake tinanin zataiwa Islam din wayo dukda kwakwalwarsa is not normal but he is kinda smart, dasauri Abeey tace "maza suke cinyewa kawai,maza kamarka farare masu kyau takebi gida gida tanaci" se asannan taga alamar tsoro a idonshi, Abeey takalli Mehtav irin kingani dinnan aizan iya, "yanzun inta cinyeni ina zata kaini," tace "you'll die kamutu shikenan bazaka sake ganina ko yah Mehtav ba do you want that?" girgiza kai yay tace "duk inda kaji motsin zombie dinnan kagudu kaji handsome banason nima tacinye min kai indena ganinka" tafada tana kama hannunshi looking dramatically sad shafa kanta yashiga yi yana assuring dinta baze fitaba baze bari zombie tacinyeshi tarabasu,. Mehtav dakasa rike dariyar ta excusing din kanta tai tashige bathroom tai abarta ta more seda tagama kuma tagani cakwakiyar dasukasa kansu aciki ya zasuyi suringa kwana da katon gardi kmr Islam adaki daya tasan besan komaiba but still is not okay musamman yajja takejinsa acikin rantannan haka,amman kuma inna fa. se ayanzun take danasanin rashin kawaye domin atleast datanada kawa ayau data kirata tabata shawarar yajja zasuyi sosai kanta yakulle. Ranar wuni zumbur adakin sukayi susu uku,inna jin shiru shiru dukda bashiri sukeyi ko yaushe ba suna xama suci abincin dare tare amman ga mamakinta, Mehtav nagama jera abinci a dining tashiga dibarmusu nasu a plate tana fadin inna we are eating inside zaki iya cinnaki museda safe,inna taji badadi tafara tinanin kowani laifin taimusu suke gudunta harbazasu ci abinci tare da itaba suna cikin cin abincin daren,sukaji kiran paa dinsu video call ne, Mehtav tarude sosai tana kallon gefen gadon Abeey inda Islam din ke zaune akasa sunata cin abincinsu a plate daya shida Abeey suna hirarsu tashirme takalli Abeey tana fadin Is paa! Abeey dasauri tamike tana fadin "pick up mana mekike jira" da hannu taimata alama da Islam kallonsa tai cikin harshen fulfulde dake inna tadage tana musu yasa suka iya ba laifi take fadin "kidaga in paa yatambayeni kice nashiga toilet zan rike islam acikin closet,find way kikatse wayar cikin mintina kadan nise indawo ke kikoma kizauna dashi cikin closet se nikuma mugaisa da paa din agreed? cikin harshen Mehtav tamayar mata dacewa tayarda,kamar daga sama sukaji sassanyar muryarsa yana fadin " I don't agree nima inason ingaisa da paa din," cikeda mamaki suke kallonsa that means yanajin fulatanci.
It's fatoumspassion EHSAAS Don't forget to share Like Vote & Comment. [17/04, 11:29] Fatima Rufa'i Nasidi: ***
EHSAAS Another exclusive piece from the passionate writer of AYSAM And INTENSE LOVE. It's fatoumspassion