EHSAAS

Chapter 5

by @fatoumspassion

(Exposed)

"But how comes EHSAAS kejin fulfulde" tambayar da Mehtav tashiga yiwa kanta kenan bayan sungama waya da paa dinsu don dakyar suka lallaba EHSAAS suka mai wayo yazauna acikin gurin kayan nasu har suka kammala,amman yace musu shima next time ze gaisa da paa din donshi yadauka babansa ne shima. ganin EHSAAS din zeyi wanka taja hannun Mehtav suka dawo parlour inda Inna ke kallon arewa24 badon sunajin dadin kallonba suke tayata na tsawan awa guda se dariya take tana basu labarin abinda akai abayan wanda bama ganewa sukeba donba bin series din datake kalla din sukeba. Abeey ce tafara mikewa tana hamma tace musu "ita tatafi seda safe" kafin Mehtav tarufa mata baya inna dai tatabe baki kafin itama ganin dare yayi takashe takulle ko ina tai addua tashige nata dakin,sanin inna natashi cikin dare ta dubasu kota zagaye gidan haka kawai tana addua yasa Mehtav saka key adakinsu. takalli inda Abeey ta bararraje akan gadonta harta fara barci EHSAAS dake taje dogon gashin sa Kamar namace take kallo ta cikin mirror shirin barci yake amman yajja kasan wanda zeje gasar kyau se wani iyayi yake,aranta ta raya qiladai wannan koda can anyi masifaffan dan iyayin jaraba,don kasa hakuri tai yajja taga yanata shafe mata oily perfume dinta ajikinsa alhali barci zeyi yasa tadauke abinta tana fadin "ya isa haka" kallonta yay before yace "no be isa hakaba," tace "tohm ninace ya isa aiba naka bane kabari innasiyo ma naka sekaita shafeshi inma arana daya zaka karar baruwana" takarasa tana bude drower jikin mirror din ta zubasu tarufe. tabe baki taga yayi yamike complete pajamas dinshine ajikinsa taga yayi tsalle kamar wani karamin yaro yafada kan gadonta yana mata dariya,irin don yabata haushinnan tamayi mamaki dataga gadon be karyeba don yajja yadira akansa gashi kato seya baka tsoro da dariya,littafin Abeey datake karanta masa yamiko mata yana fadin "come and read this for me," harararsa tai tana fadin "nizan maka karatun aiko sede karka karanta" takarasa tana nufar closet kayan dazata saka tadibo takalleshi tana fadin "sleep" tashige bathroom gaba daya atakure take jinta se faman yawo takeyi da hijab ajiki sbd battason kallon dayake mata ahaka, kulle bandakin tai,wanka tafarayi tai brush tadauro alwala acikin bandakin tasa towel tagoge jikinta taxira kayan barcinta tamaida dogon hijab dinta tafito dauke da kayan data cire ahannu closet tanufa tazuba kayan a basket din laundry tafito. duk atinaninta yayi barci tanufi gadon Abeey tana kashe wutar dakin takwanta agefenta tana karanto adduar barci, "yah Mehtav" taji yafurta cikin sassanyar murya hakanne yasa tace "na'am Islam," "yah Mehtav you don't like me koh? ya tambaya yana tashi zaune,mikewa tai itama tana kallonshi dukda wutar dakin akashe take bedside lamp din gadon da yake yasa take iya ganin yajja yake making sad face yana tura baki,tace "waya gaya maka haka Islam? ni.....ni ni kawai" tama rasa mezatace tai shiru,yace "bawanda yagaya min but your facial expressions does tell something duk abinda nai se kinyi fushi kinyi fada,your not ugly but you do look very ugly like zombie when your shouting," danware baki tai jin abinda yake cewa yabonta yay ko kuma dai zaginta afakaice, "ni banason muyita fada nidake yah Mehtav kina bani alot of meat and I like you for that, pls stop being angry with me, and like me pls, kinji ya mehtav" wani irin soft spot taji yana samu acikin zuciyarta cikin sanyayyar murya da ita kanta batasan tana dashi ba tace mishi "Islam I like you very much kawai dai inkai laifine kaga dole inmaka fada as a responsible sister to you and Abeey koba hakaba, I want to take care of you," murmushin sannan yay dayasa dimples din both cheeks dinshi lobawa yake fadin "really? you like me,nima I want to take care of you ai Abeey tace nine babba nagirmeki koh yafada yana kirgawa da hannayensa," tace "of cause you can my babban yaya" dadi ne ya kamashi jin tace mai he can kuma babban yaya. yace " we are friends now ko? we will no longer fight" jinjina masa kanta kawai tai tana fadin "yes Islam," "tohm come and read the story for me," mikewa tai tana fadin " Okay" takarasa tana zama gefen gadonta wanda yake kai,kwanciya yay yana kallon fuskarta yana murmushi har tsakiyar zuciyarta takejin murmushin nashi yana burgeta,tabude littafin tana duba inda Abeey tai alamar nan tatsaya,dan jim tai jin wani iri iri yajja yake kallonta closely, "start " yafada yana lumshe ido,ahankali tasoma "The lion king was very Kind to rest of the party,after dawn tortoise start spreading rumours about how the tiger was........" haka tashiga karanto mishi daki daki tana murmushi itama sbd labarin dabbobin itama ya kayatar da ita jinshi shiru baya mata tambayoyin da yakema abeey insuna karatun yasa tajuyo ga mamakinta barci taga yayi tarufe littafin tana murmushi, tagyara mishi gashin kanshi da yazubo yarufe fuskarsa aranta taraya he needs haircut domin lokacin da suka tsinceshi gashinsa ba ahaka yakeba fitowa ya ringayi har yakai haka that means yanada suma sosai irinsu se sunayin aski akai akai inba hakaba kansu irin namata ze koma. Addua tai mishi tana komawa saman gadon Abeey tasoma tinanin idan dai Islam bafullatanine that means dan Nigeria ne kuma garinsu zezama within arewa kodai takoma inda sukai accident ne tadanyi bincike ko zata samu wani abun dangane da family dinsa don sosai take tausaya masa tanason shima yakoma ga iyayensa kila sunacan sunata nemansa ahaka tanata sake sake bayan ta gama addua barci yay awon gaba da ita,as usual karfe biyar paa yay kiransu donsu tashi suyi sallah,mikewa tai bayan tatashi Abeey tanufi toilet,fitsari ta farayi amman ganin period dinta yazo yasa tai wanka agurguje tagyara jikinta tana fitowa, Abeey ce tashiga tai alwala tafito se alokacin suka tashi Islam yana kunkunin da tashinsa dasukai yashiga yayo alwala yafito sunsaba sallah duka su ukun tare, Abeey tashimfida musu sallaya tana fadin "yah Mehtav kitaho mana najiki shiru," cikeda dan jin nauyi tace "just pray Abeey am off" dake Abeey tasan metake nufi suna rayuwa tare tace "alright," Islam yakalli Mehtav dake danna wayarta yace "sallar ne bazaki ba your off kefa kikace mana duk wanda bayayi Allah ze konashi awuta kema kinason Allah ya konaki awutar Kenan" dafe kai tai tana ji aranta dole tanemo iyayen Islam ta aikashi gidansu tunkan yasa mata hawan jini naba gaira ba dalili wllh,tace "ai akwai exception just pray lokaci na tafiya" tafada tana kashingida saman gado se taga ya nannade sallayarsa shima yace "nima I'm off tunda akwai exception' Abeey dariya tashiga yiwa Mehtav tana fadin "mutumin fa kinrikita shi," yakalli Abeey yana fadin "muma baza muyi ba tunda baxa taiba" dariya Abeey tasoma kafin tace "pls Islam lets just pray she's off tunda kaji tagaya maka bako yaushe mata sukeyin sallah acikin month akwai days din dasuke bleeding Allah yadauke musu," dan zaro ido yay yana fadin "bleeding irin najini naciwo na, yaushe kikaji ciwo yah Mehtav" Ya tambaya yana kokarin karasowa yadubata Mehtav tace "Islam just pray ba ciwon danaji I'm okay," Abeey ce tajanyo shi tana fadin "lokaci yana tafiya,zanmaka bayani inmuka idar," se asannan ya yarda sukai sallar aiko suna idarwa yakalli Abeey alamar tai masa bayani karasawa tai tana dakko wayar mehtav data ajje agefe tanason komawa barci. browsing tashiga yimasa,tana gamawa tasoma karanta masa ma'anar MP da yajja yake zuwa da duk abinda mata keyi da wanda basayi lokacin sosai kunya tarufe Mehtav ganin yajja Abeey ke karanta masa shikuma ya kafeta da ido irin fahimtar nan yake,seda tagama tsaf sannan yace mata "tohm itama aimace ce meyasa battayi kuma tai sallah," dariya tashiga yi kafin tace "I'm a kid shekaruna ne basukai ba,idan nakai shekarun nima aizanyi ko yaya Mehtav" tatambaya tana kallonta,banza Mehtav tai musu tanajin haushinsu duka, "yah Mehtav we are talking to you,' "eh" tace afusace tana mikewa tafice daga ɗakin suna cin karo da inna zata turo kofar,dafe kirji tai tana fadin "Inna" da da karfi don Abeey dake cikin daki taji,aiko karaf akunnen Abeey din dasauri takama hannun Islam tana fadin "the zombie is here lets hide" bamusu yabita taboyeshi cikin bandaki dede Mehtav suna shigowa da inna,tace "inna ina kwana tana dan rarraba ido na rashin gaskiya" tace " lfy Abeeda yau kece har yanzun baki koma barciba," dan jinjina kai tai tana fadin "inna barcin naji bannaji kawai," tace "kintabbatar koda yake aibabu makiyar taki makaranta shiyasa kya tashi" dariyar yake Abeey tai, Mehtav tace "inna zomuje kitchen in tayaki girki aikinga lafiyar Abeey din" tace "kaji yar jakar uba se kace da din tayani kike kowa yay nasa banason shishshigi da kwal kai afaranti," Mehtav zumbura mata baki tai tana fadin "daga temako Allah baki hakuri" dakin tashiga karewa kallo don har kasan ranta taji hankalinta yakasa kwanciya jiya da daddare tazo tajishi akulle tanason taga mesuka lallata dasuka kulle daki basason tagani amman ganin bakomai yasa tafice. tana fita Mehtav takarasa tana saka key akofar tana tambayar Abeey "yana ina? tanuna mata toilet karasawa tai tabude,atsaye taganshi yana kallon kofar datake tsaye agurin yanxun, "are you okay Islam? tatambaya tana karasawa gunshi, lumshe ido yay don sosai suka darsamai tsoron inna har cikin ranshi yajinjina kai "let's go" tajuya zata fita kawai tajishi yajawota tabaya yarungumeta yana daura kanshi saman kafadarta yake furta " I'm scared," memakon tamai masifa seta tsinci kanta da tausayinsa tace "it's okay" ahankali "I'm here for you" sunjima ahaka kafin Abeey ta leko ganinsun ahaka yasanya Abeey kunshe dariyarta tana dan gyaran murya "ehem ehem ehem" se asannan yadago yana turowa Abeey baki,tace "tatafi fa kufito" tanawa Mehtav kallon irin kikace bakkyason shinnan fitowa sukai. shinema yakoma barci Abeey takalla tana daukar jakar makarantar ta da wayarta tace mata "takula da Islam zata leka school ko Allah zebata sa'a tahadu da Dr kamal kamaluddeen, sannan tatabbatar yaci abinci yasha maganinsa inya tashi kartabar dakin abude balle inna tashigo," da toh kawai ta answer mata taimata bye bye takalli Islam dake barci tashafa kanshi tana fadin "zan hadaka da iyayenka very soon in sha Allah," wayarta taciro takyasa masa hoto guda daya tamayar jaka tanufi hanyar fita ko breakfast bataiba tai sallama da inna,driver ne yakaita har makaranta gurin offices din malamai straight tanufa cikin sa'a tasamu Dr kamal tasan sarai dan shan kamshine shiyasa itama batta wani sakar mai fuska,inda kikasan ammata dole haka tashiga office din ko bata iznin zama baiba tasamu guri tazauna tana ciro project dinta saman table ta ajje tana fadin "gashinan Sir nagama kaduba in akwai sauran gyara you can call me I have somewhere to be" tamike daniyyar ficewa daga office ganin rainashin da Mehtav ta farayi tunkafin ma yafurta abinda ke ransa yasa ranshi yay kololuwar baci yace "inkika fita daga office dinnan I'll make sure ancire sunanki cikin graduating students wtf do you think your doing? nixaki shigowa office ki ajjema aiki without even asking for permission miss Bai are you high," juyowa tai don abinda Dr kamal kemata yasoma kaita bango tace "pardon me sir if I asked will you have allowed me to? uhm? tatambaya tana tsareshi da idanuwanta dukda ba wani girma garesu amman seda sukai masa kaifi yadauke nashi yana fadin 'bazan dubaba," tace "then I won't have any option zanyi reporting wa school management acanzamin supervisor since you don't like me,and that is affecting my work progress, kowa yagama nashi I'm the only one left behind just because of your hatred towards me" sosai maganganun yarinyar yasa jikinshi yay sanyi shifa be tsaneta ba hasali ma abinda yakeji gameda itane yasanya yake treating dinta indifferent sbd karta gane sirrin dake ranshi amman me be dauka zatai tinanin tsanarta yayba ganin zata faramai kuka yasanya yace "I'm sorry! you can go I'll check it," dasauri tafice tana zaginshi azuciyarta don batason rainin hankali kwata kwata shikuma Dr kamal taga da alama dan latsi ne nagaske. wayarta taciro takira Uber cikin kakannin lokaci tazo tadauketa tai masa kwatancen harzuwa inda sukai accident din.

As she expected gurin shiru babu kowa don highway ne se manyan motocin tafiya da DAF dake yawo agurin gaba tasa me uber din yay da ita aiko suna shan kwana taga wata yar kanti kwaya daya tal da ake seda ruwan sanyi da lemo fitowa tai taciro da katinta takarbi ruwa mai sanyi tasa abaki tanasha don tasoma gajiya,mai kantin yace "hjy da alama kinsha tafiya muna seda cincinma inzaki siya seki hada da lemo don kamar akwai yunwa atare dake" murmushi tai tana fadin "wllh kamar kasani bawan Allah ban cincin din" benci yaja mata yace tazauna me uber din na tsaye yana jiranta mutumin yadibo mata cincin din a leda yabata ta mikamai kati tace yabata harda lemo ma zama tai tana ci,mutumin yana jera kayanshi yake fadin "da alama daga cikin Abuja kika fito ko? baki kalar wacca ke shigowa ba" dan murmushi tai kafin tace "me kagani" yace "kinyi kala da yayan masu kudin canne" dariya kawai tai wata idea tafado mata jin yanada surutu tace "kaganni nan kafa ya kafa nazo garinnan naketa yawon gararin neman dan uwana har yanzun ban sameshi ba kuma antabbatar min kwanaki anyi hatsari anan dan baya ana tinanin koshine," "laaaaaaa" cewar me kantin kodai shine wanda wadancan mutanen ke yawan zuwa nema,zumbur tamike tana fadin "wasu mutane kuma? yace "kwanakin baya kadan wllh wasu maza biyu suna yawan zuwanan sunamin siyayyama,suna tambayata ko anzo tambayar wani abu gameda shi ko kuma anga asibitin da aka kaishi nace musu nidai bansani ba don ina nan hatsarinma se daga baya nake samun labarin anyishi," tace "sunnuna maka hotonsa ne? yajinjina kai yana fadin "sosaima kuwa irin fuskarsa ba wacca za'a manta da ita bace farine sosai namiji iya namiji amman yabace bat ba'a san inda yakeba," tace "kosun gaya maka sunanshi yace anya gaskiya basu fadamin ba amman sunbani lambarsu sunce indai naji labari akan shi inkira su" tace "ko zaka iya bani lambarsu kila su iya bani wani bayani akanshi din," yace "meze hana kedama kikace dan uwankine," hoton EHSAAS tabude awayarta tace "shine wannan" dasauri yace "shine wllh shine kuwa hjy" yana farinciki irin yayi temakonnan murmushi tai tana godewa Allah dayasa tasamu yan uwan Islam cikin sauki haka. wayarta tazuba lambar tana kira taji ba kati dan cije baki tai tana fadin "kozaka aramin taka wayar don Allah kaga tawa katin yakare ashe" yace "hjy ba damuwa" yamika mata wayarshi seda takusa tsinkewa aka daga nan suka gaisa aka tambayeta wacece bayani tashiga yimusu akan sune suke neman dan uwansu me kama kaza kaza ta zayyano musu kamannin Islam cikin abinda tafi kira da jindadi da zumudi suka rude suna cemata "sune sune" tace "tohm itama tana da maganar dazatai akanshi suzo Hilton restaurant in an hour bawaya ahannunta don haka susaka bakaken kaya tayajja zata ganesu in tagansu," suka amince cikin sauri suka kashe wayar ta mikawa me kanti tamai godiya tawuce tashige taxi din datazo,harta kunna data don tasa Credit a kirasu seta tina bayanin Dr kafaya "what if mugayen dasuka sassareshi ne suke nemanshi donsu karasashi don baze yiwu ace yan uwanshi dake can garinsu sunsan adede nan yay hatsari ba,amman dai bari taje tagwada koza suyi leading dinta zuwa inda yan uwanshi suke," akofar Hilton me taxi din ya ajjeta drop ta daukeshi for the whole day hakanne yasama bewani damuba yajirata,tashige tana kalle kalle,kallo daya taiwa mutanen dake can karshen wata corner da babu mutane sanye da kananan kaya bakake harda p cap taji gabanta yafadi dukkansu bakake ne aranta tasa Islam nada haske don haka dole daya daga cikin yan uwanshi asamu fari kobe kaishi ba amman dai yadan haska, amman wadannan bakake ne wulik hakan yasa taxauna a bench din bayansu tayajja zata saurari duk abinda suke cewa ba tareda sungane ita baceba. waiter ne yazo gunta don tambayar metake so cappuccino kawai tai order,tanajin dayan yana fadin "kodai raina mana hankali kawai akai, kusan two hours haryanzu fa batazo ba muware kawai," dayan yace "calm down mana kasan inmuka ware yajja zamu kwasheta hannun ogah dolene mukarasa aikin da muka fara don musamu payment dinmu kan lokaci," wayar dayan ce tashiga ringing yakalli dayan yana fadin "ogah ne! kafin yadaga yana fadin "hello ogah" daga dayan bangaren batajin me ake cewa amman se taga kawai sunmike,dayan yana tambayar "lafiya," yace "ogah yace mubar gunnan ze iya yiwuwa yaroncanne yatashi yamana set up kasan basirarsa amman dai tunda muntabbatar yana cikin garin Abuja kuma darai duk inda yake semun nemoshi munkarasa shi domin shidin yazama matacce a idon duniya da kowama,ogah baze lamunci dawowarsa duniya ba kaikasan da wannan" suka fice cikin hanzari dukda bata gama fahimtar inda maganarsu tadosa ba amman me? zarginta yatabbata tabbas suna neman rayuwar Islam ne,she won't allow it kuma,zatai protecting Islam da iya iyawarta zata tabbatar babu wanda yay harming dinshi,kowaye ma ogannasu baze taba ganin Islam ba balle ya kasheshi takarasa tana shiga taxi duk jikinta yay la'asar,agajiye tashiga gida suka gaisa da inna dake yankan farce tanufi dakin su kwankwasa wa tai ahankali yajja inna bazata jiba Abeey takaraso seda tai dage taleka taga waye tajikin dan karamin abin gani na kofar tabude tana fadin "oyoyo ga yah Mehtav" tarungumeta tana kissing cheeks dinta itama cheeks dinta tai kissing tana fadin "I miss you Abeey," don duk rigimar dasuke tsakaninsu suna matukar kaunar junansu wiyarta daya yawuni bega daya ba, Islam tagani yamike yana mata murmushi yakaraso in seconds abin yafaru kawai taga islam ya rungumeta yayi kissing cheeks dinta kamar yajja Abeey taimata yana fadin "I miss you yah Mehtav " Abeey ganin Mehtav kamar wacca aka sankamar tashiga yimata dariya tana tsokanarta "wai sekace dodone yatabata tawani sandare" sanin Abeey bazata gane abinda takeji in Islam din yamata hakaba yasa tai saurin fadawa bandaki tasa key tasakarma kanta shower sam tamanta bata shigo da kayan sawarta ba. wani irin yar yar takeji har lokacin ajikinta cheeks dinta tasoma shafawa tana dan murmushi ahankali tana hango dimples dinshi dasuka lotsa lokacin dayace he miss her,dakyar tasamu tai wankan seda tagama tatina bata shigo da kayan sawarta ba takaici ya tsaya mata awiya,towel tadaura tana fadin "Abeey dan mikomin kayana acikin closet pls," jin shiru yasa takara fadin "Abeey wannan wana irin wulakanci ne," Islam dake sauraronta mikewa yay yanufi closet yatsaya gaban kayanta hannunshi kan wata doguwar rigar rubber takai yaciro ta kawai yafito yana nufar kofar bandakin, "here" yafada yana mika mata jin muryarsa yasanya tai saurin fadin "ina Abeey," yace "outside" Hannunta taziro tA karbi rigar tatura kofar dasauri tana kallon rigar taja tsaki gashi tarigada ta wanke innerwears dinta,inda takesa pants da pad tabude taciro tasaka ta zira doguwar rigar data kamata tafidda duk wani shape najikinta awaje ita kanta kunyar kanta tashiga yi tohm tayaya zata fita gun Islam ahaka dawannan shegen dan iskan kallo dayake binta dashi ako yaushe tana shanye innerwears din tadaure tafito tasaka towel din tana tsane gashinta data jika,tana fitowa suka hada ido yana kan gado yana kallon kofar bandakin da alama jiran fitowar ta yake, "come" yafada yana mika mata hannunshi alamar tazo sekace wata yarshi,harara tagalla mai irin ta wasannan tanufi closet in seconds taga yatsaya agabanta,dagowa tai suka hada ido,tace mai what? Cikin sassanyar murya yace "I had a dream," tai jim tace when? earlier when you left" tace "and what did you see?" Tana kafeshi da ido kmr yajja yaymata, "a girl yafada yana dan dauke idonshi kan fuskarta yagangara zuwa lips dinta,dasukenan very cute yan kananu, "And?" tatambaya tana jiran jin ko irin najiya yayne takira Dr kafaya tatambaya me hakan yake nufi taji yay curving fuskarta, "she looks like you and I touched her like this," jin lips dinshi saman nata wuta yadauke akanta gaba daya,besan yajja akeyi ba kawai dai yasan he did touch her like this cikin dream dinshi Mehtav talumshe ido tanajin tausassan lips dinshi kannata though bawai kissing yakeba amman the feelings are heavenly,kasa hanashi tai ko motsawa yadago dakanshi yaga yajja talumshe ido cikin shirme irinnasa yake fadin "when I woke up, I was in pain, my heart hurts" yasa hannayensa yana kamo hannunta yadaura saitin zuciyarsa "is like I'm longing for something that isn't here,and something strange happened here too," hannun yadauka yana kokarin daurawa agaban wandonshi dawani irin hanzari tafizge hannunta tana fadin "what are you doing Islam? yace "I dunno the thing hurts earlier," nan duka yasoma nuna mata kasa mararshi its hard I nearly died," innalillahi tashiga maimaitawa aranta tai saurin fadawa closet jin ze biyota yasa tai saurin fadin " I'm coming don't follow me da bango tajingina itafa ba likita bace tayaya zatai tackling problem dinshi that means he has feelings like a normal adult too," amman besan meye ba tabbas dole tanemo solutions zamansu guri daya is not good for him and her kwata kwata dakyar tasamu tacire rigar tazira bra dinta tasamu atamfa tasaka tafito taganshi kwance saman gadon takarasa gefensa tazauna takalleshi tace "Islam ka gayawa Abeey wannan maganar" girgiza kai yay yana fadin "no I didn't," tace "why?" yace "because I saw someone like you not her," dan jinjina kai tai before tace "karka gaya mata kaki kaji, she's a kid she won't understand, zatai getting confuse" mikewa yay zaune yana rike hannunta "I'm also confused yah Mehtav help me what is happening with me? cikin son basar da zancen tace "mishi kasha maganinka," dan girgiza kai yay yana fadin "nah" tace "kamar ya? meyasa baka shaba" yace "two days banasha, Abeey tace indena sha ba dadi daci," tace "what?" tana mikewa afusace tai parlour tama manta da inna harseda taganta tukunna tace "Abeey meet me inside" tawuce fuu afusace inna tace "itakuma lpy" Abeey banza tai taki mikewa harseda mehtav takwala mata kira daga daki sannan tamike tana kunkuni ta nufi dakin takulle cikin fada Mehtav take fadin "danmeyasa zaki hanashi shan maganinsa his brain is damaged kinsan illar da hakan ze haifar masa kuwa wannan wana irin shirmene da shirirta," Abeey kasa dakanta tai tasan tayi laifi amman ko kadan batai regretting hanashi dataiba, "talk ina miki magana kinmin banza kin maidani mahaukaciya ma kenan," "pls stop" cewar Abeey "I did it for you," "for me?" Mehtav tatambaya sarcastically, "yes for you! I know you love him banason yacigaba da shan magani yatina shi waye ko yakoma gidansu I want him to be here,with us, with you! I want you to marry him shiyasa nace yadena shan maganin for your own good kinzo kinamin masifa se kace wata yarki I'm not your daughter miss Mehtav Habib Bai" " Abeey" tafada afusace tadaga hannu zata wanka mata mari Abeey tarintse ido tagama saddakarwa Mehtav tatsaya tana kallon innocent face din mamansu dake kan fuskar Abeey taya zata iya dukan amanar mamanta sosai take tausayin Abeey shiyasa batta iya tankwarata se abinda takeso takuma ga dama takeyi acikin gidan takamarta ita amanar mommynsu ce marainiya bame tabata bugun kofar inna yadawo da Mehtav hayyacinta "fadan uban me kukeyi bazaku bude kofarba, ke Mehtav karki sake kita bamin jika kika tabata kema se kinji ajikinki yau" inna tasoma babatu tana masifa kuma fir cikinsu akaki samun wacca zata tanka mata bare bude mata kofa, Abeey juyawar dazatai taga Islam kwance akasa kamar me barci,in seconds tagane suma yay dawani irin gudu takarasa tana kwala mai kira "Islam.. Islam wake up" tashiga jijjigashi hankalin Mehtav ma yatashi tashiga fadin "Abeey you cause this gashinan kinja ze mutu seda nagaya miki miki daman" Abeey cikin masifa take fadin "I cause this keh! kedai you cause it aikinaji doctor tace bayason hayaniya da fada kike masifa agabanshi ihunki ne ya kwantar dashi" Abeey tafada tana kokarin dagashi tadaura saman kujera inna jin ana ambaton sunan wata daban yasanya tashiga bala'i tana fadin "zaku bude kofaranan inga waye aciki kokuma sena kira muku ubanku, ko kashe kanku zakuyi da fada se kuyi agabansa alhaki ba akaina ba,bazaku budeba lallai ma" tajuya tanufi dakin ta dasauri Mehtav takarasa without thinking twice tabude kofar tana hawaye take fadin "inna ki temaka mana karya mutu," inna cikeda tsoro take fadin "waye zemutu ubanwa kuka ajje acikin dakinnan?" tai saurin dawowa tashige dakin, tozali da Islam datai kwance akasa kamar gawa Abeey nakuka kansa saman kafarta tana kiransa tana fadin "yatashi" inna tai taga taga tai baya zata fadi Mehtav ta riketa "wanene wannan?" inna tatambaya tana kallon Mehtav " a ina kuka samoshi mutum ko aljan," "inna mutum ne mana, mukaishi asibiti don Allah karwani abu yasameshi," inna taja dogon numfashi tana ficewa adakin Mehtav bin bayanta tai taga tayi bakin gate su dan liti da driver tasaka suka shigo har dakin sukansu mamaki suke suna kallon kallo don basusan da akwai mutum bayan matan uku acikin gidanba tace "su daukeshi su sashi amota cikin hanzari suka ciccibeshi sukai waje dashi aka sashi amota inna tazauna agaba Abeey tahaye cinyarta Mehtav da Islam agidan baya driver ya tukasu straight zuwa asibitin Dr kafaya cikin gaggawa Dr kafaya ganin inna da kanta yasa ta karbeshi tana tambayar "meya sameshi?" inna dai shiru tai kawai tana kallon yajja Abeey da Mehtav suka rungume juna suna adduar Allah yabawa Islam dinsu lfy tana mamakin shedancin yaran Habib ace wiyansu ya isa yankan da zasu ajje mutum sukutum da guda agida ba tareda sanin kowaba katon saurayi kuma ba wanda yasani ciki kuwa har ita datake ganin tafisu basira da wayo ashe kallonta kawai sukeyi. kasa jira likitoci sufito tai tanufi yaran tana fadin "kumuje waje zakuci ubanku yau,ai ubanku zezo zakuyi masa bayanin abinda kuka aikata" binta sukai abaya harsuka fita daga harabar asibitin tashiga jefa musu tambayoyi "a ina kuka hadu dashi? wayeshi? daga ina yake? kwanansa nawa agidan? dukkansu shiru suka mata ba wanda keda courage din bata ansa tai kwafa tana fadin "kunzama kurame kenan, aishikenan tunda nikun rainani shi habibun zankira yanzun inmai bayanin duk abinda ke faruwa in yadawo seku fada masa dakanku," dasauri Abeey tadago tana fadin "inna pls don Allah kiyi hakuri karki gayawa paaa zamu gaya maki gaskiya,tsakani da Allah," tace "na gaura maki mari dazun danake tambayar ki meya hanaki ansamin aikuma damarku takare," suna kallo inna tashige mota tadau wayarta rakani kashi da lambar babansu ce kadai aciki seta mehtav take kira, se yan uwan dasune suke kiranta don gaisheta tasa kiran babansu sunaji suna gani basusan sharrin da inna takulla musu ba se gani sukai tafito amotar tana fadin "yana nan tafe gobe gobennan zakuci gidanku tunda ni kun rainani," dasauri Mehtav tabi bayanta suna komawa ciki take fadin "inna wllh bamu rainaki ba munsan you will act this way ne shiyasa bamu gaya miki ba inna you don't trust us," tace "daman taya zanyarda daku kunmin karya,kunraina min hankali muna zaune acikin gida daya inkasa gane me kuke ciki kun ajje katon gardi adaki kunboye ga inna muguwa zata cinyesa inta ganshi," Mehtav tace "inna gayawa paa zakiyi kuma gashi kinfada din kinsan yanzun halinda wannan bawan Allah ze shiga temakon sa mukai baida kowa besan kowa nashiba yanzun idan paa ya koreshi agidanmu ina zeje inna" juyowa tai alamun maganganun Mehtav sun soma shiga kanta Mehtav ganin haka tagyara tsayuwa kanta akasa tashiga bata labarin duk abinda yafaru tundaga kan fitarsu yawo amotar mommynsu da aka hana da yajja suka bige Islam dayajja suka sameshi duk seda ta zayyanawa inna,dayajja sukai zaryar asibitin farfadowarshi,lalurar data sameshi har yajja magauta keson ganin bayanshi dukda zafin inna macece mai matukar tausayi kan Mehtav tagama kwalla tataru a idonta tana fadin "Allah sarki bawan Allah kicedai mahaukaci yazama" Mehtav tadanji zafin danganta Islam da hauka da innar tai tace "inna total amnesia yasamu ba hauka bace bafa," tace "kusan duk abu daya ne ace mutum besan kanshi ba" tana shartar kwallar ta cigaba " mutum besan komai nashi ba yayannan dolene ku tausaya masa aini dakunmin wanga bayani tin farko da bandaga waya nakira habibu ba gashi yanzun yanufi filin jirgi damma amuruka da nisa shiyasa zekai gobe be isoba amman karku damu zamu temaka masa namuku alkawari bazamu korasa ba harse ansamu iyayensa, aini nakeda iko da habibu kawai dai bannason kukemin karya ku ringa kokarin fadamin duk abinda kuke ciki kunga bakuda wata kamarni dukda takurawar daneke muku yayannan ina mugun sonku kaf cikin jikoki ba wadanda nake kauna kamarku' tafada tana rungume susu duka harda Abeey dashigowar ta kenan sosai Abeey taji dadin saukowar inna din cikin kankanin lokaci, Dr kafaya tafito tana sanar musu he is stable now,amman next time aguji yin hayaniya agabansa ze iya zama barazana ga lafiyar kwakwalwarsa. takuma kira Mehtav office dinta inna se harararta take don taji kudaden da Mehtav tabata ita kanta kafaya borin kunya kawai takeyi dasuka shiga office tafara mata masifar tasan gida zata kaishi meyasa bata gaya mataba taimata karya aida bata barsu sun tafi yanxun gashi tunda inna tasani tasan dole engineer zesani kuma battason yaringa ganin kmr taci amanar abokan takar dake tsakaninsu akan kudin da basu taka kara sun karya ba harta gama kala Mehtav bata cemata ba sema ficewa datai tabarta don tasan duk kunyar inna ce tagama kasheta.

It's fatoumspassion EHSAAS Share Vote Like & Comment [18/04, 16:51] Fatima Rufa'i Nasidi: ***

EHSAAS Another exclusive piece from the passionate writer of AYSAM And INTENSE LOVE. It's fatoumspassion