Chapter 6
(Diary)
Wuni yawuce kwanaki sun shude sati yatafi yanzun ana wata daya kenan da rasuwar EHSAAS ga Islam taki lpy ko ina amasarautar NURISTAN mourning mutuwar adalin prince dinsu suke kusan atare lpyr Islam data mai Martaba take kara tabarbarewa ba tareda kowa yasani sai fulani da uwar soro dake kaikawo suna faman dawainiyya dasu. sosai EHSAAS junior yayi kubulbul abinshi domin uwar soro raino take masa ingantacce tana kula dashi in kaganshi ahannun mahaifiyarsa tohm yunwa yakeji kullum yana tareda uwar soron se kuma Fulani dake tayata rikonshi wani lokacin, Islam ji takeyi gaba daya rayuwarta ta rasa ma'ana tana bukatar makusanta nakusa ma'ana dan uwa wanda zata zauna ta karanta masa damuwarta, amman tasan yanzun duk inda ta tinkari wani nata dole mahaifinta ze samu labari kuma in yasamu labari tabbas wannan dan uwan daya saurareta zeshiga cikin matsala babba. Duk yajja gimbiya mimah ke shige mata don su dawo kamar yajja suke abaya Islam din taki bata fuska sedai ma intazo suyita gwabawa juna magana atakaice tadaura hope din rayuwarta akan rayuwar yaron tane kawai domin duk sanda taji ta sare kmr ta kashe kanta tabi EHSAAS duk inda yake se taji bazata iyaba tana gudun halin da danta zeshiga a masarautar NURISTAN idan babu idanta sannan tana kwadayin samun rahamar ubangiji batason ace gashi tamutu tazama yar wuta, sbd EHSAAS yagaya mata duk wanda yakashe kansa tohm inya mutu tabbas wuta zeshiga. yau samu tai dataji jikinta yadanyi karfi tafito tana zaune kamar kullum tana aikin tinani don garden din gidan daya kasance gurin zamansu tareda EHSAAS nanne yazame mata gun zuwa duk sanda take kewarsa tana tina irin good memories din dasukai sharing together,tayi zurfi cikin tinani taji andafata tana dagowa suka hada ido da Aman,bayabo babu fallasa take kallonshi don tunda akace mijinta yamutu tamanta da yajja ake murmushi, "Aunty inata magana tundaga can baki jini ba" yanuna mata nesa da inda suke yanzun, "are you okay?" tajinjina kai kawai tana kallonshi,yace "Aunty kidaure kidena saka damuwa acikin ranki irin haka kinsan wanda yamutu baya dawowa idan da uncle zedawo kinsan bazeji dadin ganinki cikin wannan halin ba koh," jinjina mishi kai kawai tai ya ajje brief case dinshi saman table din chair din da take kai ahankali yake fadin "uncle needs our prayer not tears Aunty, shiyasa kikaga natsaya tsayin daka domin protecting lineage dinsa" yaciro wani babban littafi tana kallonsa tasheda shi, "His diary" tafada aranta EHSAAS diary littafin da sunsha yin fada akanshi tamanta sau dubu nawa tai attempting sace littafin donta karanta amman seya kamota yakwace abinshi yace mata sirrine babba aciki bazata ganiba se rnr dazeyi publishing dinsa. kasancewarsa journalist,yana rubuce rubuce masu ma'ana irin iri na littattafai da labarai da articles harda journals ma,yace mata wannan littafin shine bakandamiyar sa kuma duk lokacin daya bugashi ita zefara mallakawa original copy din duk bin kwakwaf dinta yaki bata ko plot din labarin wanda yake kiransa da diary bacin duk wani draft nashi kan ya sakeshi seta karanta sau ba adadi amman akan diary ya hanata shiyasa takwallafa ranta akanshi yau gata ga diary babu EHSAAS din dayake rubutawa shin anya zata samu courage din karantawa idan takaranta tohm waxata bawa feedback din yaza'ai tasoma cin gyaranshi inda bema kamata aigyaran ba tashiga tsokanarshi yana kumbura mata fuska. Tinawa da babu yasa ta jin wani daci aranta yasanya hawaye masu dumi suka shiga fitowa daga idonta Aman daketa mgn batama sauraronshi yace "Aunty pls stop crying shikenan in bakiso zan mayar dashi office dinshi kawai" zemaida book din jaka dasauri tamika hannu takarbe tana rungume littafin akirjinta tamkar EHSAAS dinne haka takejinsa, Aman yace "Aunty prince publishing needs that book,sells dinmu yana kasa,tun bayan rasuwar uncle babu enough talent din dazamu buga our genius is gone amman yabarmana wannan idan muka buga wannan aunty ina metabbatar miki bama iya NURISTAN ba kaf fadin duniya se yakarbu sbd EHSAAS yabani tabbacin hakan lokacin dayake rubutashi," jinjina kai kawai tai tarintse ido before tace "tohm meyasa baka bugaba you will gain alot tunda yafada," yace "because I need your permission, am sorry I open it amman wllh iya first chapter nagama because I don't think uncle zeso ace nine nafara karantawa bakeba is for you Islam, this book is about you guys baze yiwu inbuga batareda izninki ba," jinjina kai kawai tai yace mata "zebata lokaci takaranta inyaso intagama seta kirashi tagaya masa ra'ayinta" da tohm ta ansa mishi kawai for the last time ya kalleta yasake bata hakuri tareda bata tabbacin uncle be mutu abanza ba he is digging on it yamata alkawari kowaye behind it se yayi paying for what he did sosai taji dadin maganganun nashi sukai sallama yatafi ganin lokacin sallah yayi yasanya tanufi wani tap da ake amfani dashi agarden din alwala tadaura dasauri maid dinta takaraso tana shimfida mata sallaya agurin tatayar da sallah bayan ta idar hannu tadaga sama tama rasa me zata roki Allah kawai seta fashe da kuka tadau tsahon lokaci tana kuka kafin tadena azkhar din takarasa kawai tazauna anan gurin tana lumshe ido kafin idonta yakai kan littafin data ajje agefenta. Hannunta tasa asanyaye tadakko littafin tana budewa hoton sune subiyu,yayi hugging dinta tabaya tana kallon camera taturo baki shikuma yana kallonta yana murmushi "this is one of their craziest pictures da Sir EHSAAS ke matukar so Aman ne yay musu shekara daya data wuce," rnr birthday dinta akamusu shi,takai minti goma tana shafa fuskarsa acikin hoton kafin tabude next page din harda date da time din lokacin daya fara rubutu tsintar kanta tai da murmushi in beyi hakaba baza'a ace shine EHSAAS ba sarkin rubutu,the best writer im the world agurinta all his works are the best. rubutun yafara da fadin
"They say I'm the prince-heir to the throne, master of kingdoms… but the moment you smiled, I willingly handed over the crown. Now I fetch your snacks, guard your sleep, and recite sweet nothings like royal decrees. Sometimes I wonder-am I the ruler, or just your glorified palace pet in a crown?"
Tsintar kanta tai da rufe baki tana dariya its so like her Sire,daman yace ai itace Queen shi he is her slave acikin queendom dinta haka yake cewa dariya take harda hawaye sbd jitake kmr yana gabanta yake rubutun tana kallon fuskarsa a idanuwanta, yana mata wannan murmushin nashi na miskilai with his angelic eyes and dimples.
Cigaba da karantawa tai inda nima zanshiga indauko muku rahotan abinda take karantawa don shiya kunshi gundarin labarin,mafarin komai.
Tushen labari
Masarautar NURISTAN babbar masarautace ta musulunci wacca ake jida ita ayankin Africa da kewayenta,(kirkirarriyar kasace karkuje kuna neman NURISTAN a google kuce fatima ce tafada muku😎😉) NURISTAN takasance daula me dunbun tarihi,wacca take fafatawa da manyan masarautun duniya dasuke mulkin musulunci ire iren persian, Indonesia,da Iran daulace mai dumbun tarihi da ake jida ita Kuma itace babbar daular musulunci dake Africa,ana mata take da masarautar datafi kowacce masarauta dake nahiyar zaman lafiya ga hadin kai da kaunar talakawanta, lokacin da sarki EHSAAS nafarko yarasu lokacin ne hadin kan royal family yasoma rarrabuwa don asarakan baya da akai basu cika aure aureba amman shi sarki EHSAAS ya auri mata har hudu bayan kuyangu dayake dasu sunfi ashirin,yakuma yi hakanne duk don samun magajin daze gaji sarautarsa don yajima besamu haihuwa ba, zuriarsu basu da yawa sosai hakanne yasa Allah yadaura musu soyayyar yayansu natashin hankali, musamman shida yake sarki kuma lokacin girma yazo masa yaga be haihuba hankalinsa yatashi. kuyangarshi tafarko ce tafara haihuwa acikin daular Inda sarki EHSAAS yay matukar farincikin samun wannan karuwa yakuma kwallafa ranshi akan wannan da data haifa kasancewarta kuyanga mafi soyuwa agareshi amman babbar matsalar shine matansa hudu yaso ya maidata mata amman babu wannan damar amman dukda haka yadauki son duniya yadaurawa danta wanda aka samai suna Erfan shine wazirin NURISTAN nayanzun. bayan ERFAN ganin shekaru sunja babu haihuwa daga gurin matan sarki yasa sarki EHSAAS yafara shirye shiryen nada yaron matsayin crown prince kwatsam se aka tsinci matar sarki ta karshe amaryarsa hjy Aisha(uwar soro) tanada juna biyu farinciki gurin sarki EHSAAS nafarko kamar ya hadiyeta gata yar uwarshice daman tajini wannan abin ya bakantawa kuyanga nadra rai sosai domin tana ganin kamar Aisha zata zama obstacle wa danta gurin samun mulki ba kalar attempting din zubda cikin da bataiba amman Allah bebata nasara ba har Aisha ta haifi santalelen danta namiji wanda aka samasa suna NASHWAN bin EHSAAS,haihuwar NASHWAN ba karamin tsayewa kuyanga nadra taiba domin kowa yasanda cewa shidin cikakken dane ba kamar danta ba dayake dan baiwa kuma har yau ba'a yantata ba kwatsam aka tashi da rasuwar daya daga cikin matan sarki mutuwa ce wacca tayita fuji'atan babu ciwo ko kadan,hakan yadasa zargi dayawa a zukatan mutane bayan anshafa arba'in sarki NASHWAN ya auri kuyanga nadra hakan yasa jinkanta yakaru kuma take tura danta Erfan gaba gaba aduk wani harka data shafi masarautar. ERFAN yataso ada mai biyayya babarsa duk wani mugun halinsa boyewa take agaban mai martaba duk abinda tasan ze burgeshi shitake sawa yayi don duk yaga cancantarsa amatsayin wanda ze gajeshi don tariga tagama sawa aranta cewa itace zata zama Queen mother. Hjy Aisha dake hankalin ta bama yakan sarautar bata wani damu da itaba hakama danta NASHWAN donshi yakan kwan biyu ma ba'a ganshi azaman fadaba,lokacin manyan ce yazoma sarki EHSAAS kuma se alokacin matarshi tafarko me babban daki ta wancan lokacin ta haifi danta namiji shima aka saka masa suna JALALUDDEEN BIN EHSAAS suna mai lakabi da JAY lokacin duksu Erfan da NASHWAN sun zama manyan samari,itama seta fara daura buri akan sarautar kasancewarta yar sarki itama se iyayenta suka ringa nunama sarki EHSAAS cewar jikansu ne yadace yacancanta yazama sarki,duk yana sauraronsu bece musu kowaba yana ganin yajja kowannensu yake baza mulki yana nuna shi shine. Rana daya kwatsam yatara taron manya manyan masu sarautar garin NURISTAN da kewayenta da al ummar gari yay declaring NASHWAN dansa nabiyu matsayin crown prince wanda ze gajeshi hakane yasa matan sarkin suka fara fito nafito dashi kan lamarin musamman uwargidansa da ita bata iya munafunci ba afili tafito ta kalubalance shi akan rashin adalcin sa agareta ita da danta bayan danta ne yacancanta kasan cewarsa dan matarsa tafarko kuma dan sarki jikan sarki gaba da baya be saurari kowacce daga cikinsu ba yasoma grooming NASHWAN dan yazama sarki me adalci. itakanta Hjy Aisha tayi mamaki da sarki yazabi NASHWAN ba JAY ba,kuyanga nadra taji bakincikin hakan matuka amman seta kwantar dakai tanuna tabbas tana tareda mijinta akan duk abinda ya yanke kwatsam rana guda akatsinci NASHWAN ansa masa guba acikin abinci,kuma agurin uwargidan sarki yaci abinci na karshe hakanne yasa duk wata hujja tanuna cewar mahaifiyar JAY ce tasa masa guba,abin ya harzuka sarki EHSAAS inda yakulleta akurkuku natsawan shekaru biyu tareda sakinta bayan tagama zamanta yamaidata garinsu da wannan bakincikin tarasa ranta domin tasan ita bata aikata ba itakanta uwar soro tanajin har cikin ranta cewar ba laila ce ta aikata ba amman hujjojin da aka samu akanta masu karfine hakanne yasa batada yajja zatai tanemar mata sassauci,sedaga baya tasoma zargin anya ba nadra bace ta aikata tai framing dinta,rikon JAY hannun nadra yakoma lokacin akaima Erfan da NASHWAN zabin matan aure,da yar sarkin daura da yar gidan wazirin garin na wancan lokacin,sune candidates din, straight nadra tacema Erfan yar sarkin Gabas takeso yazaba sbd sune sukeda suna da babban ahali da mulki wanda zasu temaka masa gurin claiming NURISTAN idan sarki EHSAAS ya rasu,dagashi har EHSAAS babu wanda yataba ganin matan koda sau daya, har lokacin da akai presenting dinsu gabansu. sarki EHSAAS kasancewar NASHWAN ne crown prince se yace masa ya zabi wacca yakeso acikinsu straight yace masa yabarmasa zabi duk wacca ya zabar masa itace zabinsa,yatambayi Erfan yace masa "shi yar sarkin Gabas yakeso," bamusu aka bashi aurenta shikuma NASHWAN aka daura mishi aure da yar waziri itace mai babban daki Asiya, lokacin jikin sarki EHSAAS yakara tsananta. Erfan ne yafara samun haihuwa kafin NASHWAN, yahaifi yara mata tagwaye abin bemusu dadiba shida mahaifiyarsa amman dukda haka sunji dadin cewar shi yafara haihuwa kafin NASHWAN din, Erfan yakwallafa rai akan sarautar sbd yajja mahaifiyarsa ke kwadaita masa mulkin garin,daidai wannan lokacin sarki yaywa NASHWAN tayin karin aure da yar babbar amininsa sarkin borno kanem empire baki daya abin yamusu ciwo matuka domin kowa yasan daularsu tafi ta Gabas komai da komai,kuma alakace wacca za'a kulla ta qasa da qasa idan abin yatabbata zasuyi supporting NASHWAN sosai gurin karfafa claim dinsa akan sarautar NURISTAN. kuma yartashi ance ita dayace tilo acikin yan uwanta maza,rabi shuwa ce rabi bafullatana mahaifiyartace giwar masarautar bornon, inda ake kiranta da Fulani Hajar, kyakkyawa ce tagasken gaske sbd kace nace da akeyi da yayan sarakuna gun neman aurenta dasu kansu sarakunan yasa mahaifinta ya kawowa amininsa kukan cewar shi besan waze bawa waze hanaba,kamar wasa yace masa ai NASHWAN dinsama yana bukatar karin aure saboda har cikin ransa yanason yaywa NASHWAN auren gata da gata aure na gani nafada nabugawa ajarida da yar sarki se Erfan yay saurin cewa yazabi yar sarkin Gabas kyaleshi kawai yay shiyasa yanajin batun Fulani Hajar din takai munzali aure yacewa mahaifinsa yabarmusu kawai tunda su ba kasar su daya ba kuma NURISTAN kasace me zaman kanta don haka shi abarmusu kawai kmr wasa yace yabashi.
cikin kankanin lokaci akasoma hidimar auren NASHWAN din da Fulani Hajar abinda yaywa gimbiya nadra ciwo danmeyasa ba Erfan aka bawa ba se NASHWAN duk yajja taso ta lalata auren kasawa tai har aka daura,ita kanta hidimar bikin da akai ba kalar wacca suka saba gani a NURISTAN bace don ko ina seds yasan cewa crown prince zeyi aure da yar mashahurin sarki Abdullah. kuma dake Hajar yarinyace mai hankali da sanin yakamata bawanda bata darajawa agidan dukda kasancewarta princess hakan besa tanuna musu jinkai koh tanuna tafi matar NASHWAN tafarko daraja ko kimaba tini sukaja matar NASHWAN tafarko jikinsu suna nuna mata daman can basonta yakeba kara yake mata waya mutu wayay rai shiyasa ya zagaya ya auro wata kodon batasamu ciki dashi ba,Asiya tahau tazauna tazama yar dakin sarauniya nadra tana ganin duk duniya babu mesanta a NURISTAN se ita.
Ana haka Allah yaywa sarki EHSAAS rasuwa mutuwar data girgiza NURISTAN da kewayenta sosai babu bata lokaci dattawa suka hada meeting aka maye gurbinsa da NASHWAN kmr yajja sarki EHSAAS din ke buri,rnr gimbiya nadra da Erfan kamar su kashe kansu suka fara yadawa amasarautar cewan NASHWAN juya ne yaza'ai shekara da shekaru yanada aure da mata har biyu ba wacca tataba koda batan wata, duk tana hakane kuma saboda batada wasu manya agari kasancewar ta baiwa tun asali kingmakers kwata kwata basa wani ganin girmanta kamar yajja duke daraja sauran matan sarkin,shiyasa duk wata hanya dazata batawa NASHWAN ko uwar soro suna setabi don suma tarage musu darajarsu gurin kingmakers din. cikin kankanin lokaci mutane suka fara yadda da zancen inda ba'a samu maganar ta game ba Allah yabawa uwar gidansa Asiya ciki,cikin da take jidashi kmr ranta tadaura burin duniya akansa sanadin cikin sanin su Queen nadra basason NASHWAN din yahaihu taraba kanta dasu tanajin itama takai tasoma zuba mulki yajja takeso acikin masarautar,tana yada habaici ga Fulani iri iri wacca ko cire kai takalleta battayi.
lokacin haihuwa nayi tahaifi diyarta mace wacca aka samata suna gimbiya mimah,abin yawa hjy Asiya ciwo domin taso ace ita tahaifi magajin sarki NASHWAN inda shikam yadaura soyayyar duniya akan mimah itace yarsa mafi soyuwa har wayau shakuwarta da mahaifinta ta dabance kusan fulanice taraini mimah dukda yajja hjy Asiya (mai babban daki)take zaginta tana hanata zuwa amman bata iya rabuwa da Fulani sbd kaunar da fulanin take nuna mata tana kaunar kananan yara sosai. cikin da Fulani tasamu nafarko Allah be barshi ba taayi barinsa,dukda uwar soro ta fahimci kamar dasa hannun magauta aciki ba irin kuntatama Fulani da ba'a yi acikin gidan domin Queen nadra ta sakama yarinyar kahon zuka kullum cikin yada mata da habaici take ana kiranta da juya bakin cikin ba danta ke aurenta ba kuma hakurin da juriyar Fulani hajar yasamar mata da gurbi me fadi cikin zuciyar mai martaba NASHWAN,kuma lura dahakan yakara kiyayyarta azuciyar su sosai musamman hjy Asiya datake ganin kmr Fulani tamata shige bayan itace matarsa ta farko,se kunga yajja Queen nadra kenuna ma NASHWAN iko kmr itace uwar soro shikuma yanada kauda kai darajar mahaifinsa yasa yake bata respect sosai bawai don yana tsoronta ko wani abin ba. Fulani sau hudu tana samun ciki yana zubewa a NURISTAN palace, hakan yadamu uwar soro da mai martaba sosai ga wani irin laulayi datake me dan banzan wiya duk sanda akace tasamu ciki tagama lfy kenan,hakan yasa uwar soro na ankarewa tasamu ciki na biyar tafitar da ita daga masarautar asirrince tamaida ta gidansu batareda sanin shikansa mahaifin Fulani hajar ba awancan lokacin daga ita se mahaifiyar hajar din suka tayata renon cikin duk irin duba da tambayar da mai martaba NASHWAN yaywa uwar soro kin sanar mishi inda take tayi harseda tahaifi danta santalele fari tass mekama da mahaifinsa da mahaifiyarsa,yaci sunan kakanshi EHSAAS Bin NASHWAN Bin EHSAAS NURISTAN. ansanar da haihuwar inda tai mugun tayarwa da queen nadra hankali domin tagama sakankancewa sarki NASHWAN baze taba samun magaji ba bayan kulle kullen da sukaiwa Fulani ciki yadena zama ajikinta,takasa tsaye takasa zaune se tashiga yada maganar cewa aikilama Fulani ba dan NASHWAN tahaifa ba shiyasa ake boyeshi aka ki bari kowa yasan dashi in gaskiyane afito da yaro mana kowa yaganshi asanshi yasansu suma. wannan batu yamatukar batawa NASHWAN rai duk hakurinshi haka yatara bayin dasuke yada mgnr aka matsasu kan lallai lallai kosu fadi wanda yake fada koh akashesu,sun firgita sosai, jakadiyyar Queen nadra tace ai uwar dakinta ce tafada beyi mamakin jin cewar daga bangarenta abin yafito ba hakan yasa batareda ya saurareta ba duk hakurin data ringa bashi tana cewa ai sharri aka mata yasa aka koreta daga NURISTAN baki daya aka bada tsatstsauran dokar cewa duk inda aka ganta ko kusa da NURISTAN akasheta hakanne yasa Erfan yasake kullatar NASHWAN din yanaganin kmr daman kiris yake jira ya tozarta mahaifiyarsa saboda yasan batada mai tsaya mata,amman babu dama yay fito na fito dashi karshima akoreshin be dau fansa ba tukunna. Jay dayake agun nadra yatashi se shima yadau abin da zafi sosai dukda karancin shekarunsa amman gani yake kmr NASHWAN beyi adalci wa su dasuke ma nadra kallon uwaba yasallameta daga masarautar sbd asalinta baiwa ce batada wani galihu, kuma sosai dangin mahaifiyarsa ke sake cusamai tsanar NASHWAN sbd suna ganin adalilinsa mahaifiyarsa ta hadiyi zuciya tamutu.
EHSAAS a borno yafara tashi yashiga daukar ilimi agurin kakansa Abdullah bayan yagane cewar ai Hajar din nacikin masarautar shi aboye, EHSAAS yasamu good foundation na karatun addini sosai,inda ya haddace al Qur'ani cikin kananun shekaru,yashiga karanta fassarar sa tareda littattafan addini iri iri gurin kakanshi,sarki NASHWAN kasa hakuri yay da rashin matarshi da danshi akusa ganin Queen nadra batanan yasanya yaje dakansa yataho da matarsa da danshi don sosai yayi kewarsu ba kadanba. cikin ikon Allah tundaga kan EHSAAS fulani bata sake samun ciki ba, EHSAAS yatashi cikin gatan iyayensa da kakanninsa yanada matukar tausayi ga hakuri wanda yagada daga gurin both iyayensa bayason damuwa ko kadan,yanason carefree life domin rayuwar gidan sarautar NURISTAN ta banbanta dawacca yataso acikinta sosai domin dukda amatsayin sa nadan sarki daya tashi kakanshi baya kafkaffa dashi koya hanashi shiga cikin yara yan uwansa wasa kmr yajja akemai a NURISTAN,a NURISTAN harta da motsinsa ana watching abinna matukar damunsa, jinsa yakeyi kamar wani prisoner yajja suke tattalinsa da kulawa dashi,bewani jima tare dasuba akaiwa mimah aure a kasar Turkey,sunmugun sabawa da ita hakanne yasa yashiga zazzabin kewarta gaba daya rayuwar NURISTAN tabi ta isheshi da farko mai Martaba yadauka ze saba amman ganin tilon dan nashi na kokarin shiga wani irin kunci shida Fulani suka yanke shawarar turashi madina can gurin babban yayanta dake zama yana karantarwa acan.
Zuwanshi Saudi Arabia yadan ragemai kadaicin da yake ciki dukda yana matukar kewar mahaifiyarsa amman yayi saurin adapting da rayuwar can musamman yajja uncle dinnashi yatsaya tsayin daka akanshi though kusan rayuwar da yakeyi tanan data NURISTAN din ba banbancin don duk inda yake zakaga security na binshi aboye,harta da makaranta baya zuwa shi kadai seda jami'an tsaro lokaci lokaci mai martaba da uwar soro suna zuwa ganinshi kuma hakan yana mai dadi sosai ita Fulani kam tamaida visiting dinshi duk bayan two months wani al ada shiyasa shakuwarsu dashi tafi yawa sosai,kuma duk wani abu mai mahimmanci inya taso tunkan yakai munzali mai martaba yakan daukeshi yatafi dashi zuwa tarurruka na kasashe da dama sbd yanason yasamu experience akan rayuwar al umma ma banbanta. matar Uncle dinsa ma dake yar kasuwa ce tanayin tafiye tafiye don saro kaya iri iri yasanya takan daukeshi lokaci lokaci suna zuwa tare idan yasamu hutu,abin yana mai dadi sosai kuma yana enjoying din freedom din da yake samu idan baya site din yan uwanshi da iyayenshi shi girmannan da ake bashi kowa yaganshi yazube yana gaisarwa sam baso yake ba amman yayi learning haka rayuwarshi take don haka dole yay accepting wayeshi.
Cikin aminci yakammala karatunsa na secondary a manarat Al madeenah international inda yasamu ilimi na addini mai zurfi dana zamani sakamakon zamanshi da uncle dinnashi domin daurawa yay daga inda kakanshi yatsaya,ga makarantar dayay kuma combining modern knowledge take da strong islamic studies Allah yamasa wata irin kwanya mai girma domin kusan a scholarship yakammala karatunshi sosai ilimin addinin dana zamani ya ratsashi domin nutsuwar EHSAAS kadai ta isa tasheda maka cewa lallai lallai wannan yakarantu kuma ga jinin sarauta dake tare dashi. Alokacin ne mai martaba yabukaci yadawo gida, shima yana matukar sha'awar komawa gida kodan mahaifiyarsa da kakarshi amman me yasan cewa yakai shekara goma sha takwas kuma al'adar NURISTAN ce suna shekara goma sha takwas ake musu aure,yasan plan din mai martaban Kenan, yakira mimah yar uwarshi itace ta tabbatar mai ai anma gama komai na auren nasa itama tagama hada trolley dinta jira ake kawai yasauka afara shagalin biki acewarshi he is just eighteen ko jami'a befara ba tayaya Ze iya karatu da rike iyali alokaci daya "he is not ready" dariya tashiga yimasa tana fadin "garashi za'a iya bashi option kan wanda ze aura ita se rnr aurenta taga mijinta don haka inze dawoma yazabi mata cikin jerin matan da suke candidates yadawo batawa kanshi lokaci yake" straight yace mata "shi baze aure yanzun ba kuma koh aure zeyi shi wacca yakeso ze aura baza aimasa irin auren zamanin daba," mimah dariya tashiga yimasa jin yajja yake mata korafi kan al adun garin nasu anitse kmr me tattaunawa,jin tama ki daukar zancen nashi serious yasa yakashe wayarsa kawai yana tinanin yajja zeyi,tabbas baze koma NURISTAN ba don in yakoma yasan cikin mafarkansa da abubuwan da yakeso yay arayuwa ba wanda zeyi. adaidai lokacin kiran Fulani yashigo masa sanar dashi tai kan cewar harma anriga ansamar mai gurbi ababban jami'ar NURISTAN din yana dawowa farawa kawai zeyi,cikeda nutsuwa yake tambayarta "sunsan course din dayakeso ne dahar sun samar mishi admission," murmushi tai tana fada mishi "ai mai Martaba ne yace acike masa economics sbd yanason ya iya kulada personal family business dinsa da kuma tattalin arzikin NURISTAN in yazama sarki," "hmmmmm" kawai yacewa Fulani cikeda yar damuwa take tambayar sa ko akwai matsala,gudun karyasa ta adamuwa yace mata "babu komai kawai Allah ya amfana" taji dadi sosai jin yay na'am da abinda suka zabarmai din though tana tantama inhar cikin zuciyarsa ya yarda din,yana kammala waya da Fulani yafice zuwa makarantar su daya gama options din scholarships dinshi daya samu yace su nuna mashi ba musu shugaban makaranta yabashi file din yana sake kwadaita mishi jami'ar kasarsu don bayason su rasa wannan hazikin dalibi, murmushi kawai yay yabi list din da kallo kafin yay mishi godiya ya bar office din ta online yay komai cikin kankanin lokaci aka turo mishi da admission letter dinsa yatsaya kawai yana kallon screen din computer yana tinanin is this the right decision daya yankema rayuwarsa,deep down he is feeling guilty nakin gayawa iyayensa amman yasan suna kaunarshi kuma zasu fahimceshi domin betaba nuna yanason wani abu sun hanashi ba kawai dai yasan in yagaya musu zasuce yafara komawa NURISTAN ayi bikin yatafi da matarsa shikuma gaba daya beshirya rayuwa da maceba ne ma akananun shekarunsa.
kawunnashi shima bai haihu dawuri ba yarsa guda dayace jal wacca takasance first cousin din EHSAAS jalila dukda zamanshi natsawon shekaru agidan bewani saba da jalila ba tsakaninsu gaisuwa ce ta mutunci da girmamawa dukda yajja jalila keson tashiga sha'anin sa amman baya bata fuska hakanne yasa lokacin daya gama secondary dinsa zetafi hankalinta yakasa kwanciya dukda kananun shekarunta tafahimci tana matukar son EHSAAS din shiyasa tanacewa mahaifiyarta kan lallai lallai tanason taje NURISTAN hutu gurin Fulani,aranta tasa in taje NURISTAN bazata dawo ba harseta kwadaitawa Fulani ra ayin hada aurenta da EHSAAS, atinaninta EHSAAS NURISTAN ze koma,kiransa kawunnashi yay yasanar dashi cewan "ga jalila nan tace zataje gurin Fulani don haka yayi musu komai tare ze hadasu da bodyguards biyar don tsaron lafiyarsu shi ze biyosu daga baya" kasancewar har yanzun suna cikin semester su basu yi hutu ba, EHSAAS sosai yaji haushin jalila da tace zata bishi amman sanin be iya musu da manyaba yace wa kawun nashi "tohm amman iyashi da jalila zasuje basa bukatar bodyguards har biyar he is grown up now," murmshi both kawun da matarshi sukai don sunsan EHSAAS bayason aita aikin tsaron lafiyarsa badon kawun yasoba yace "tohm" kawai ranar da za'ai tafiya har Riyadh uncle dinnasa ya rakasu inda suka wuce king Khalid international airport straight seda yatabbatar sungama komai sannan yajuya yatafi yana tafiya EHSAAS yahade rai ya mikawa jalila passport dinta da ticket dinta batareda yabata fuskar mai wasu tambayoyi ba ya rakata har cikin jirgin dake shima kawun yasiya mai ticket din zuwa NURISTAN,a business class din yabarta bayan yabata wani envelope yace tabawa fulani,layi yabata yace intaje airport tasanja tasaka takira lambar data gani aciki za'a zo adauketa jinjina masa kai kawai tai idonta yakawo ruwa don ta fahimci ba tafiyar zeba kuma batada guts din tambayarsa ina zeje sbd sosai take shakkarshi,tafiyarsa yay yabarta tana ta zare ido don yaune karonta nafarko da zatai tafiya ita kadai arayuwarta.
EHSAAS ganin jirgin daze tafi NURISTAN ya tashi yay wani murmushi yanufi nasa destination din British airways yahau, for the first time arayuwarsa yazauna a economy harwani murmushi yake ganinshi atsakiyar mutane gaba da baya ya lumshe ido yana tinanin yajja zefara rayuwa as EHSAAS alone not prince EHSAAS.
Cikin awa bakwai suka sauka a birnin London Heathrow airport,acikin jerin passengers dake sauka yasakko yanata kalle kalle, jin wani iri sanyi na ratsashi yasanya yabude trolley dinshi yazaro cashmere coat dinshi yazira yana fitowa, yakalli agogonshi da already yasaitashi da lokacin London din ganin yanada sauran lokacin isa Oxford din yasa yakalli taxi driver din dake gabanshi dasuke daukar ma tafiya don kaisu masaukin su yace mishi "ko ze iya kaishi Oxford cikin darennaan dan kallonsa" yay kafin yace masa "eh ze iya amman payment din will be much" "bamatsala" yace masa yana shigewa bayan motar don sanyin yasoma damunshi. awa biyu cir sukai ahanya,yana kallon yajja motarsu tashiga M25 kafin tahau M40 motorway zuwa Oxford yanata kalle kalle kasar da alama ta burgeshi driver kemishi bayani duk inda sukabi yagaya mishi ai sunwuce garuruwa kamarsu high Wycombe,da Bicester EHSAAS nata kalle kalle kafin yabude bagpack dinshi daya sauke daga goyatan dayay yaciro katon littafinshi dayake amfani dashi matsayin diary yashiga rubutu, "I've had everything,yet today I feel empty and full at once.what will I become in a city that doesn't bow to princes?" Yakarasa yana murmushi yazira biron atsakiya yarufe yana cigaba dakalle kallenshi yana ganin lokacin dasuka shigo Oxford city. Seda motarsu tawuce Magdalen brigde,tazarce high street harta tsaya agaban balliol college dake broad Street,sannan ya ankare sunzo. Ginin kmr wani old book haka yake,yana cikeda abubuwan tarihi dana wayewa,yay murmushi yana tina cewa wannan ganuwar anginata kila tunkafin ahaifi kakan kakanshi. Fitowa yay yana kallon ko ina, daidai nan porter din school din yakaraso yana murmushi,yace masa "Welcome to balliol Mr EHSAAS" yayi mamakin ganeshin dayay koda yake sundan yiyyi mgn dashi ta online kila da profile picture dinshi yagane shi,shima murmushi yay masa yana mikamishi hannayensa suka gaisa jin wata nutsuwa na shigarsa don sosai yaji dadin kiransa da EHSAAS kadai dayay ba prince babu your Highness. wucewa dashi yay zuwa staircase XII,adaki mai lamba 38 suka tsaya yabude masa yashiga yana dan qamishi keys din EHSAAS yatsaya yana kallon dakin shibema taba ganin daki karami kmr wannan ba babu kayan alatu babu kwalliyar gold da yasaba gani aduk dakunan dayake rayuwa acikinsa nagida dana saudi,dakin babu komai acikinsa se wooden desk,single bed setaga wacca take kallon courtyard "it looks peaceful" yafada yana kallon porter din yaji dadi ganin EHSAAS kmr dakin yaburgeshi. It's fatoumspassion EHSAAS Don't forget to Like Share Vote & Comments.
Guys my comments section is dry bakwason more updates ne haba I need to be hearing your views regarding this book. [19/04, 17:40] Fatima Rufa'i Nasidi: ***
EHSAAS Another exclusive piece from the passionate writer of AYSAM And INTENSE LOVE. It's fatoumspassion EHSAAS