Chapter 7
(Prettiest eyes) Cikin lokaci kankani EHSAAS yay adapting da rayuwa a Oxford,he is not very social amman yana da kyakkyawar mu'amala da duk friends dinshi da roommate dinsa,wanda shima a balliol din yake amman different major yakeyi ba irin na EHSAAS ba. EHSAAS English lit major ne shikuma philosophy major ne,dan kasar spain ne sunanshi Noah,zamansu kowa sabgarshi yakeyi rayuwar mind your business suke baruwan wani da wani ba abinda yashafi sabgar wani data wani, duk wani book club na African students ya kanyi joining don asassan juna though wasu ko yace he is african basa taba yarda saboda kalar fatarshi. seda yay wata daya cif sannan yakunna wayarshi,fulani yafara kira ba wani fada datai masa kawai tambayarsa tai "if he is okay," ya amsa mata da "yes," beyi mamaki ba jin tana tambayar shi ko yanajin dadin zaman Oxford din yasan daman dole mai martaba zeyi tracing duk inda yake afadin duniya indai harta jirgi yaje yace mata "eh," yanaji tace masa "ai yakyauta," "kuma yatabbatar duk rnr daya dawo garinnan da matar aure don duk yaran da aka tsayar masa iyayensu sungaji da jira sun aurar dasu karsu wuce shekarun aure," dariya sosai yashiga yi sanin cewa da wasa takeyi haushi taji don yagudu beyi aure ba,yana dariyar yake fadin "Aisun kyauta sosai kuma karta damu ze dawo mata da suruka kyakkyawan gaske," tace "aukama maidani sa'ar ka koh,zaka sanine zakazo kasameni har inda nake kai burinka kaita jawomin abin fada amasarautar nan koh EHSAAS, yanzun gashi Erfan yace daman da biyu na hanaka dawowa don kar ka auri yarsa maisoon," "maama" yafada ashagwabe irin bayason maganarnan tace "shikenan nayi shiru kai duk abin NURISTAN bakason ji ko tohm dadai bamusan asalin balbela ba setace mana daga madina take asalinka nanne kagama guje gujenka karatun da shekara ukune aizaka dawo kasameni" yace "maama is four including MA din dazanyi a journalism," dukda batta gabanshi yasan bude baki tai tarufe tace "MA,BA din be isheka ba kenan," "maama pls," "EHSAAS shekaru hudu zanyi kenan banganka ba, maimartaba yayi fushi inata lallashinsa kan yabarni inje inganka yahana yanzun kai zaka iya shekara hudu baka ganni ba" yace "I'm sorry maama I'll come zanzo inganki in sha Allah," tace "tohm kuma inada tambayar yimaka is being months since katafi yace baze sake turama kudiba kudin gurin ka nasan sunkare wayake baka kudin kula dakanka" dan murmushi yay yasosa keya yana fadin "maama we are in thehe 21st century I do some trading online and its profitable," tace "trading din danake jin anacewa cacane ana guduwa da kudin mutane" dariya yashiga mata yace "maa is legit don't worry I'll explain another time, especially bayan innakaiki makkah da kudin" Yakarasa yana dariya tayashi tashiga yi "Tana fadin tohm inajira ammin alkawari kardaga baya azo acemin ba hakaba" "Karki damu habibty,ai kujeranki daban," Yana jiyo murmushin ta,yadorada "yanzun inada programme din dazanyi attending a London I'll call you later kinji send my regards to your highness," yakarasa yana kashe wayar, sosai yake kewar mahaifiyarsa anan take yay deciding in sha Allah zeje hutun New year.
Wata kamar rana shekara kmr wata haka cikin kankanin lokaci EHSAAS yagama freshman year dinsa,yaso yaje gida awannan lokacin amman se wasu extra programs daya dauka yanayi suka rikeshi beje ko inaba yana cikin dakinsa yana ganin yajja su Noah keta shirye shiryen zuwa London gidansu budurwarsa anan zasuyi celebrating tareda iyayenta,shida Noah na respecting eachother basa shiga sha'anin addinin juna but deep inside EHSAAS tausayinsa yakeji inyaga yajja yakeda tsanani dabin ka idojin addininsa yana memai kwadayi inama shi musulmi ne yakeyi wa addininsa hidima haka,sallama yay masa bayan yayi mai tayi ko ze bishi yace mai a'ah seya dawo kawai yafice abinshi yabarshi,dagashi se system dinsa yanata aikinsa.
Ashekararsa tabiyu sosai yafara zama famous cikin students sbd kokarinsa da kuma kyanshi musamman yan mata daga lady Margaret hall suke zuwa ganinshi da gaisheshi. gifts kuwa iri iri yana receiving during valentine's da easter and thanks giving insuka taru tattarawa yake gaba daya yay donating wa mabukata, Noah har tsokanar shi yake kodai mata basa burgeshi ne se maza amman taya za'a ce mata iri iri from different countries tribe daban daban skin daban daban suna bibiyarka amman baka kula kowa acikinsu, dariya kawai yay mishi yana gaya masa baze ganeba don yasan ko kusa kaf cikin matan dasuke bibiyarshi babu wacca za'ai accepting a NURISTAN,kuma shi kansa babu wacca tamai balle akai ga yakaita gida yatada dan karamin yaki amasarautar su yasan yajja yazabi karatunshi yabar batun auren wuri mai martaba na kule dashi duk sanda yatashi auren shi ze zaba mai ko yaki koh yaso saidai daga baya yay tashi shikuma koh kadan beda ra'ayin auren mata biyu arayuwarsa sbd yana ganin dukda shiba me yawan sa ido bane amman yasan zaman doya da manjan da akeyi tsakanin mahaifiyarsa da kishiyoyinta donma dai ita fulanin bame fitina bace da Allah yasa mahaifinsu nada yara dayawa da wata mgnr akeyi ba wannan ba,don babu yajja za'ai suyarda ma aringa fifita danta sama da nasu.
Karshen shekara na zuwa yagama tattara komai daze bukata yay heading to London don yahau jirgin daze kaishi NURISTAN surprise yakeso yaywa Fulani don be sanar da ita cewa yau din yataho ba.
Heathrow Airport din Acike take da hayaniyar Mutane suna ta karɓar boarding passes, wasu na jira a layi, wasu suna shan coffee, wasu kuma suna ta maida wayoyi kafin su tashi. An saita komai cikin kulawa saboda lokacin hutu ne - Christmas Eve kenan. Ehsaas zama yay cikin Business Class Lounge, sanye da jacket mai kauri da backpack ɗinsa a gefe, don he arrived alittle bit early sbd zumudin yau ze tafi gida, bayan shekaru biyu a Oxford,burinshi kawai yaganshi a NURISTAN kusada mahaifiyarsa don ba karamin kewarta yay ba. Adede lokacin yaji ana kiransu wanda zasu hau jirgin British Airways flight 798 to NURISTAN, yamike ahankali yana gyara agogon hannunsa yanufi gate din daze sadashi da ainahin gurin da jirginsu yake,hayaniyar dayaji tana tun karoshi ce tasa yadan dakata yajuyo, surutu kawai sukeyi ba kakkautawa sunata hira abinsu,kungiyar wasu teenagers yagani mata,suna sanye da Oxford High School (GDST) blazers, suna tafe cikin farinciki da daga murya. Ganin kamar sauri suke yasa ya matsa musu hanya don su wuce,yan matan sukamai murmushi dayar harda daga mai hannu kana gani kasan akwai gigin kuruciya ataredasu don yanajin dayar tana cewa itafa burinta wannan Christmas din tai trending social media. idanuwansane suka sauka akanta tana binsu abaya anitse take tafiya cikin sanyi kamar wata babbar budurwa yar shekara ashirin da biyar yajja yay estimating shekarunta bazata wuce 17 ba,amman yajja nutsuwa ta ratsata zaka dauka tafi shekarunta sosai yarinyar taja hankalinshi ba iya nutsuwarta kalar fatarta tafita daban da sauran,kalar fatarta is-deep, smooth, warm-toned-wanda yake tina masa da rich West African earth bayan ruwa,kmr cocoa and cream, idanuwanta sanye suke cikin white glasses daya shiga wondering ko medicated ne kokuma dai na gayune kawai saboda yayi mugun dacewa da fuskarta,kasa dena kallonta yay musamman ma idanuwanta da sukenan gwara gwara acikin glass din dukda girmansu basu yiwa fuskarta yawa ba sema kara mata wani irin charm dayay tunda yake aduniya betaba ganin me ido kalar nataba, "she wasn't just beautiful" yafada aransa "she's haunting." duka kallonnan in seconds yay mata lokacin da sukazo wucewa hankalinta itakam bama ya kanshi gaba ki daya harsuka shige be dena kallonta ba kuma tanada tsayi sosai dukda dai begama tabbatar da cewar boot din kafartane ne yakara mata ko kuma dai tsayin natane. dan sosa keyarshi yay for the first time arayuwarsa yatsaya ya karema mace kallo macen ma yarinya karama yar highschool scolding kanshi yashiga yi. Mamakine ya kamashi lokacin daya shiga ganinsu yay sun tsaya abakin jirgin sauran yaran nata daukar group pictures da alama ba guri daya zasuje ba don yaga jiragen da zasu tashi daban daban,tana gefe sunata iyayi suna daukar hoto amman hankalinta baya gurin aranshi ya raya kome take kalla allahu ta ala a'alam.
For the first time yaji inama economy ya hau ba business class ba da kila ze zauna aguri daya da ita kobasu zauna guri dayaba ze iya canje da wani yabashi gefenta,haka kawai yaji ranshi yasosu da hawa business class din dayay yau yaciro wayarshi yasa earpods akunnenshi yashiga sauraron karatun alkur'ani don yasamu nutsuwa don ji yake yarinyar tatafi da nutsuwarshi baki daya. be kure volume ba don yana iya jin shigowar few people dasuke cikin business class din,hayaniya yaji tadan karu yabude ido yana kallon yanmatan dasuke shigowa susu biyune kacal wannan karon, biyunne ke surutu suna bada labarin yajja suke daukin zuwa gida don celebrating Christmas tareda ahalinsu,kallo daya yay musu yadauke ido don bega wacca yake nema acikinsu ba kuma betaba yiwa wata mace kallo sama da daya ba arayuwarsa bayan wanda yaymata dazun. aranshi yaji yanason yasan ita inane garinsu wana jirgi tahau ko kuma kila tana economy ne,be gama tinanin da yakeba yaga shigowarta dake yana farko farko,hada ido sukai wannan karon gwara gwaran idanuwanta dasuka tsareshi da ido sukasa yakasa dauke gaze dinshi daga nata, seeing her this close yakara ganin charisma dinta kmr magnet haka yakasa janye idonshi ya dena kallonta. ganin yaki dauke ido daga kanta yasa tazare mishi gwara gwaran idanuwanta masu bakaken kwaya dayay bala' in haska farin da ya zagaye kwayar idon,shima tsintar kanshi yay da zare mata nasa idon, Rolling eyes dinta tai in a way da yakusa saka wa ya kware dukds babu abinda yake bakinsa don tsabar yajja idanuwanta suka kada sukai tasiri a zuciyarsa,taciro yan kananun hannayenta dake cikin aljihun rigarta dasafa ahannayenta hakan be hanata nunashi da yatsanta na tsakiya cikin sigar gargadi alamar kar yasake kallonta tashiga jujjuyawa,shi dariyama tabashi waishi takema warning dubeta wata yar karamma da ita dukda tsayin kafar dayaga tana dashi dakuma tsayin takalman dasuka kara mata tsayi yatabbatar yarinyace daga fuskarta yafahimci hakan da kuma abinda tai yanzun,wato bawai shiru shiru bace akwai tsiwa da alama yaraya aranshi.
suna zama kuwa aka fara announcing tashin jirgin sosai yakeson yajuya bayansa can inda gurinsu yake yaga me takeyi amman jin kannan na yayan sarauta yasa yay banza yama nuna kamar besan da zamansu ba kuma tun zaman sun biyun basuyi shiru ba basu dena magana ba se labarin yajja zasuyi sukeyi,daga mgnr su yafahimci sudin Christians ne hakanne ma yasa yadauke hankalinsa yatattara ya mayar kan film din da yake kalla na dead poetry jikinshi yay sanyi sosai sanin bawata hulda dazata hadashi da kafiri har abada seta kasuwanci da zaman tare amman banda abota ko makamancin abinda yaji yadarsu aranshi gameda yarinyar yanzun, dukda kunnenshi nakan conversation dinsu,ji yay dayar tana tambayar wacca tamai warning dabatai magana tun dazun ba, peace kefa meye zakije gida kiyi mekike shiryama Christmas, Hmmmmm yaji tace before tace "I'm not interested," dan juyawa yay ta tsakankanin kujerar yake kallonta,muryarta yar karama both she sound very matured kmr wata boss lady. tana kokarin maida kanta zuwa ga littafin datake karantawa,dayar ce ta fizge littafin ahannayenta tana fadin "I won't give you this book unless kingaya mana plan dinki for Christmas, if you are planning to stay indoors all day this year again....." kallonta tai tana fadin "what's wrong with staying indoors all day during holidays sasha? I have jane Austen and Brontë with me they'll keep me company" takarasa tana kallon littafin ta da yakwace, dayar tsaki tai tana cewa "you'll never change, when will you be excited about Christmas newai peace," tace "why would I be excited with someone else's birthday at the first place,when I'm not allowed to celebrate my own birthday," takarasa da fada fada,wacca takira sasha tace "peace talk with manners your talking about Jesus's birthdays not any commoners birthday" tace "is he not a human being like us,d" ayar mike wa tak tashiga karanto addua tana rokon kada peace tasa atabar dasu yanzun ajirginnan, EHSAAS idonshi alumshe yatsayar da film dinma yana sauraron conversation dinsun yafara wondering tohm why is she not excited bayan itama yalura arniyar ce. Sasha tace "but at least peace zama awannan katon gidan naku ke kadai every year won't do you good pls celebrate with us," tace "yanzun misali idan nace zanyi celebrating Christmas tohm suwa zanbi ku yan Catholic Church, Anglican Church, Lutheran Church, Methodist, Baptist, Evangelical churches dakuke bin Gregorian calendar zanbi ko kuma su Favour dasuke bin julian calender yan Eastern orthodox zanbi,and what about mommy datake following Armanian apostolic church,kinsan on 6 january suke celebrating both birth and baptism of jesus," favour cikin son dakatar da peace din take fadin "peace stop this bullshit pls...." tace "kuxancema you should stop thi bullshit,sbd it doesn't make sense at all come to think of it my daddy is also a Christian amman kuntaba ganinshi yana celebrating Christmas,no right? takarasa taba bawa kanta ansa, "sbd he is a Jehovah witness, he do not celebrate it,he believed the true god name is Jehovah and not Jesus because jesus is his son" takarasa tana dariya,sasha tace "peace your insane, kinzauna kinata zagin addininmu anan koh kunya bakyaji kenan kema bayan daddy dinnaki zakibi kenan you are talking like a Jehovah witness too," tsaki tai tana fadin "no way I'm just me I'm peace I don't believe in all this sbd shikansa bible din duk kowa ya maidashi nashi yarubuta abinda yakeso aciki,the one true god akwaishi but known of you will understand that yimuku bayani ma baida amfani yanzun I'd rather be a pagan than being one of this rubbishes," Favour kallonta kawai tatsaya yi da sakakken baki tana fadin "nagane wllh na tabajin ki kinajin wani muftin mutanancan yana fadan duk abubuwannan dakike gaya mana your allowing them to brainwash you peace,karki cemin burgeki sukeyi," peace kallonta tai cikin sigar wayancewa take fadin "no thats not the case girls, nifa inaji ne kawai because of my curiosity amman bawai don suna burgeni ba,ni....ni" muryarta tafara rawa sasha tace "wllh inma burgeki suka farayi gara sudena duk randa naji kinkara irin wadannan maganganun senaje nasanar da parent's dinki, peace Christianity is the only true religion, inkikace you'll revolt sekin shiga uku arayuwarki wuta xaki shiga ki wulakanta," peace tace "inkece god din aise kisani a wuta atleast su duk rabe raben kansu dakike gani they celebrate Eid on thesame day, Ramadan on thesame month ban tabajin wani yafito acikinsu yace ba ranar baneba,kuma ni karwacca takaramin magana acikinku, rubbish kawai" takarasa tana fizgar littafinta tacigaba da karatu se alokacin EHSAAS ya bude idanuwansa yadanyi murmushi yana fadin "peace you need guidance your on the right track,your very interesting," yakara dan lekata yajja tai focusing tana karanta the great Gatsby tsintar kanshi yay da kasa dena kallonta har lokacin da air hostess takaraso gurinshi tana tambayar meza abashi se asannan yadauke idonshi daga kallonta yana wondering a ina take a NURISTAN.
Throughout the flight har kawayenta suka gaji suka kwanta barci ita karatunta takeyi,lokaci lokaci yana dan kallonta ahaka har suka karaso babbar filin jirgin sama na Sir EHSAAS 1 NURISTAN international airport sunan filin jirgin is after his late grandfather EHSAAS na farko,tun da suka sauka yaga tamike ta rataya backpack dinta abaya sauran ma duk sun mike sunata murna finally sun karaso. dayar datake kira da sasha tace "peace zan biki gidanku zuwa gobe sena wuce garinmu nagaji dayawa baxan iya tafiya direct ba," straight tace mata "bazaki ba," favour tace "peace wai don munmiki mgn akan banzatar da addininmu da kikeyi shine kikejin haushinmu," banza tai mata tadau littafin ta tana fadin "I'll see you around inzamu koma" tai ficewarta yana kallon yajja take tafiya anitse har ya dena ganinta,kawayen yaji suna fadin "duk girman gidansu ita kadai fa take xama ko tsoro bataji kema sasha kamar mayya da kina da zuciya ko kallon inda gidansu peace yake bazaki sake yiba," sasha tace "bazaki gane ba gidansu peace is always peaceful, sannan bame takurama sannan akwai kudi yanzun inna koma gidanmu atareda kannena zankwana amman innaje gidansu peace daki guda za'a bani tana dakinta ina nawa kuma duk abinda nakeso shi mamansu zataimin gata wayayya yar gayu ba irin mom dina ba,tana bani kudi sosai," favour tace "dukda haka amman kinsan wulakanci da miskilancinta batason arabeta," tace "ni inaruwana taje taitayi indai ni zanji dadina ba abinda ya shafeni da miskilancinta tawuni bata kula niba ba abinda ze damen" dede nan yaga suna kokarin fita harsuka fice gaba daya sannan shima yadau backpack dinshi jiyake kmr ya tambayesu address din gidansu yarinyar amman kuma yasan "what he is doing is wrong, yaje yace mata me? meye hadinshi da macen da ba muharramarsa ba, Ya tambayi kanshi da kanshi.
It's fatoumspassion EHSAAS Don't forget to Share Comments Like & Vote
Join us in the comments section don sharhi akan chapter dinnan.
Menene ra'ayinku dangane da EHSAAS. [20/04, 21:24] Fatima Rufa'i Nasidi: ***
EHSAAS It's fatoumspassion EHSAAS Another exclusive piece from the passionate writer of AYSAM And INTENSE LOVE.